Showing 48001 words to 51000 words out of 267381 words
Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta “Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.
. Umma..” saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik’on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk’ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik’on hannunta had’ida dakatar da ita “K’yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banid
a haufi an canzata dare d’aya.”
Fad’awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata.
Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K’ungiyar asiri ta fad’a.
Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake z
aune gefe. Ta d’an yi adjusting mayafin “Hajja Asshe Ya kikaga k’warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d’aya fah ta birkice..”
Asshe ta murmusa tace “Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa ak
a kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k’unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had’iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta.”
Umma ta zaro idanu “Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mut
u ba ai…”
Asshe ta d’an murmusa kad’an had’ida dafe kafad’ar Umma guda “Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d’inki sa
i Sun shaida auren gata da za’a mata..”
Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad’i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d’inta tayi aure kota halin k’ak’a ko ba da
n komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama’an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul.
**
A b’angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak’ar Jeep d’in nan mai lullub’e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama
da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga ‘ya’yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida.
Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin.
“Adda anya ba gaskiya Mama take fad’i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k’u
ngiyar asirin ta shiga ba..!” Tai maganar kaman mai tsoron furtawa.
Ummul tai saurin d’agowa tana dubanta “Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?”
“Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan… Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanaki
n nan..? Sann meyasa ta tafi ta k’yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k’afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d’in nan. Ga ado
da tayi irin wanda bata tab’a yi ba. Wata matace zatayi wad’ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad’i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki.”
Sau
k’e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace “Kinyi gaskiya… Akwai tarin tambayoyi k’unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abu
buwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad’ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa.”
Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba.
**
Abuja.
Laptop ne gabansa waya manne kunnen
sa yana duban wasu sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba’ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d’in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d’in
ya k’ura ma waje guda idanu.
Dareen da waya ke mak’ale kunnenta ta kuma lek’ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had’ida matse wayar jikin kunnenta sosai “How would I know.. He’s been acting strange lately..”
Daga d’aya b’angaren muryar mutumin y
a katseta “What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!”
Ta d’an rausayar da idanu had’ida furzar da huci “Look, I see him everyday but I can’t grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne
Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha’ani.”
Mutumin yace cikin tsawatarwa “Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarw
atsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba.”
Lumshe idanunta tai had’ida bud’esu “Fine, zanyi iya k’ok’arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi ga
ngancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.!”
Ya murmusa “Kar ki mance I’m the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran.
Furzar da huci ta kumayi kafin tai k’ok’ari
n kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune.
Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa “Love..” Ta fad’i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d’ago fuskarta tana dubansa “Is something bothering you..? You seem preoccupied… Is it about work..? Ko kaje
duba Mommy ne..?”
Tambayan da ta masa na k’arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b’angaren “I’m fine..” Ya fad’i a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba. A ‘yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak’
o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta
ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik’ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d’in dake jikin
sa.
Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d’in ta bud’e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d’in tana karantawa.
Aiki yake sosai kan project d’in da takeda masaniya yanata fad’i tashi akai. Toh
kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k’asa. Ba yanda za’ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk’i.. She needs to find out meke faruwa.
**
Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma wai
wayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d’aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d’aya ta ma mance da batun Tasi’u da halinda kud’ad’en shagon Abba ke ciki.
Yau d’in ko asibiti wajen
Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi’a da Azeema yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d’aya idan ta fice Suwaiba na iya zuwa gidan wajen ‘ya’yanta Shiyasa ko k’ofa ta gaza fita.
Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da
aibata Suwaiba ‘yar k’ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann.
Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik’eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik’es
a tana tambayarsa meke faruwa waje.
Yaron yace “Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k’atotuwar mota tanata rabon kud’i a waje..”
Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum
. Take suma suka take ma su Mama baya.
Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k’iris Mama bataci tuntub’e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d’aga kud’insa sama.
Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan
al’ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak’ar shirgegiyar mota tana rabon kud’i ma Al’umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak’o suna amsan kud’ad’en da Umma ke rabawa.
A haka Umma ta k’araso gaban Mama.
Ta murmusa tana dubanta “Tani ya muka sameku..”
Mama ta kuma bud’e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Wa
ima Yaushe Suwaiba ta sami ‘yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk’uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had’ida mugun k’auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yard
a da hausar nan da ake cewa Shege na k’auye.. Idan bak’auye ya samu faraga yafi d’an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d’an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita
kanta bata tasa k’afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad’i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar
Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k’aramar ‘yar iska take mata. Ita a daidai wann gab’ar ma ta baje Rumfar barikinta.
Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummu
l sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk’ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d’aki ma ya koma b’angaren kud’i. Kira Salima z
ata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud’ad’en cikin hamshak’in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa ‘yar aikinta sak’o.
Mama tai sakare tana duban Suwaiba.
“Ungo amshi mana..!” Umma tace tana
mai kamo hannun Mama had’ida damk’a mata kud’ad’en ciki.
Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d’add’aya sai juya ma Tani mazaunai take.
Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta.
Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gaban
ta rik’eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak’umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad’ida Azeema ta rik’eta sosai bata iya tsayuwa kan k’afafunta.
Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k’afafunta
Har hard’ewa suke.
Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik’eda hannun Ummulkhairi tana fad’in “Ba sai Kin d’auki komai ba.... Maza tashi muje direba yana jiranmu..”
Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki Kai ‘Yaruwata Umma..?”
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*17*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki kaita Umma..?” Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta “Umma shin abinda mutane ke fad’i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asal
in Ummanmu da muka sani..?”
“Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki ‘yaruwarki nazo d’auka..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi.
Cikin azama Khulsum ta rik’e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye “A’a
Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije..”
Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud’e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d’an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje.” Daga haka ta fad’a mota kayanta.
Khulsum ta kuma s
hare hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad’in “Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak’ila rad’erad’in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d’aya bamu San Wacece ita ba
a halin yanzu.”
Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba “ Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.?”
Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud’e m
ata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d’in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta ‘Kiyi hak’uri ‘Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Al
lah ya k’addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d’abi’a da halayya. Munsan matsalan
mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk’i a rud’eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak’ik’anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auk
a ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K’anwata..’ Ta k’arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata.
A daidai gate d’in wani gida mai matuk’ar kyau da tsari motar tai horn.
Khulsum da tuni ta d’ale acab’a tabisu a ba
ya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada ‘yaruwarta ayi tsafi da ita ba.
Driver na Ida parking Ya f
ito ya bud’e masu k’ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban Umma wacce ta koma mata tamkar bak’uwa.
Umma ta dafata tana murmushi “Ki saki jikinki Ummul d’ita. Ban kawo ki yanda za’a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki b
urina shine rayuwarki ya cika da d’imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Kinga nan gidan.. Gidan da za’a share mana hawaye ne.. Gidan da za’a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k’arshe Ummul.. Taho
muje..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje.
Umma ta juyo tana dubanta “Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k’yale ’yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da
ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji.”
Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta “Umma gidan da za’a cika mana buri fah kikace… Umma Ashe har akwai mahaluk’in da zai cika ma wani mahaluk’i burinsa..? U
mma idan kinga burin d’an adam ya cika ya bar duniyar nan ne..”
Bata Kai aya ba Umma ta hanb’are mata baki “Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina
shine na ganki a d’akinki dik rintsi.. Koda k’arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana..”
Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta
take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi “Ummul d’inmu ta iso..!” Ta fad’i kyakkyawan murmushi saman fuskarta.
Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad’ad’a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k’araso ta run
gumeta tana fad’in finally sun had’u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba.
Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Me
ke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki.
Jikin Ummul sai rawa yake yayind
a Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta.
*
A b’angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b’angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k’ofan wajen a bud’e Ya sanyata nufan
k’ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand’a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand’an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta n
a tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk’e huci da take.
Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard’e. Yana binta da kallo mai d’aukeda alaman tambaya.
Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duba
n juna ba.
“Ina ‘yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?”
Hilal ya girgiza kai kad’an “Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.?”
Gajeren tsaki tai had’ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tar
e gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa “Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b’angare na.?”
Ya d’an girgiza kai ganin har lok
acin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad’in