Showing 222001 words to 225000 words out of 267381 words
tsaye ciki rik’eda k’aramin hoto cikin yar k’aramar frame. Ta rik’e hoton cikin hannunta tana maganganu masu firgitarwa. Tana fad’in sai ta kashe matar dake jiki kaman yanda ta kashe Dareen ta b
igeta da mota. Sai na shigo cikin Office d’in hankalina a matuk’ar tashe jin irin kalaman da take. Idan baka mance ba ni dai ban wacece matarka ba balle nasan kamanninta. If you can still recall hoton da aka muku a ranar tariyarku da Ummul shine hoton da k
a saka cikin k’aramin frame ka aje a Office d’inka. Kuma a wann ranar da Anisa takai maka ziyara Office a wann ranar ka aje hoton cikin Office d’inka kafin zuwan Anisa. Haka na nufin nima a wann ranar naga hoton matarka. Na kuma fahimci Ummulkhair da na ta
imaka kake Aure. Sai nai barazana ma Anisa da fad’in zan mik’ata ga hukuma koma na sanar da kai amma sai Anisa ta rokeni da na dubi girman zumuncin dake tsakanin mahaifyarta da mahaifiyarka kar na bata zumunci nayi hakuri ta tuba. Bazata kuma kashe matar H
aidar ba.. Hasalima bata san duniyar da matar Haidar take ba. Tinda ta hadani da girman Allah sai na mata afuwa ban sanar dakai ba. Inata mamakin ashe kaine mijin Ummulkhair. Ban nuna maka na san matarka ba sabida ina so na tabbatar da gaskiyar Anisa akant
a. Kar na bayyanata ta kasheta d’in kaman yanda tace ta kashe Dareen da mota. Sai na soma bibiyar Anisa duk dan nai protecting d’inka da matarka dake gaban mahaifiyata musamman da na fahimci ka saki matarka da juna biyu wanda kaima baka sani ba. Toh a ciki
n bibiyan manufar tuban Anisa da nake na fahimci k’arya take bata tuba ba tana nan akan bakanta na neman Ummulkhairi dan tayi ajalinta. Cikin k’unan zuciya nake sanar da Anisa bazata tab’a cimma burinta akan ahalin Abokina ba, bazan bari ta gansu ba balle
tai ajalinsu musamman da nasan cewa gida d’aya kuke rayuwa kaida Anisa hallaka Ummulkhairi da abinda ke cikinta bazai mata wuya ba tinda she tried once. Tayi k’ok’arin poisoning dinta daga fari... Ni kuma sai nai tunanin zamanta wajen Hajja da abinda ke c
ikinta zaisa Sufi samun tsira da kwanciyar hankali tinda dama Ummulkhair tamkar ‘ya take wajen Hajja su biyun ba bak’in juna bane. Tamkar uwa ce da ‘ya. Sosai na razana da al’amarin Anisa tinda kasan ance kaidin mata yafi na shed’an. Gashi Anisar ta fad’a
ta kashe Dareen da jaririn cikinta a ranar bikin tariyarku da Ummul d’in. Idan kaje ka duba motar da Anisa ta shiga a ranar bikinku zakaga anyi had’ari da motar ta sanar Dani ta aje motar a gida ta rufe ba Wanda Ya sake bi takan motar sabida yawan motocin
dake gidan ba Lallai hankali yakai kan wann motar da aka rufe da bakin k’yalle ba. Kaman yanda aka mance da wann motar kaman haka zata kashe Ummulkhair da abinda ke cikinta kuma a mance dasu a cewarta. Kaji yanda akai Anisa tasan Ummulkhair na Bauchi waje
n mahaifyata ta kuma san tana d’aukeda juna biyu.!” Kuma a jiya da mukayi waya ka tambayeni ban b’oye maka ba. Ce maka nai ina Bauchi na kawo K’anwata da mijinta ya saka asibiti zata haihu. Da ace inada mugun nufi da bazan fad’a maka haka kai tsaye ba Haid
ar. Na fad’a maka haka ne dan bazan so na tashi hankalinka ba dan ka sanar Dani isowarka k’asar kenan daga SouthAfrica. Dama a tsarina shine da zaran Allah Ya sauk’eta lafiya na sanar da Hajja dama Ummulkhair komai kaima kuma na sanar maka asan matakin d’a
uka kan Anisa.!”
Ya dubi Daddy cikin sanyin jiki “Daddy wann itace iyaka gaskiyata duk yanda zaaje. Bazan ce kar D’anuwana yai sharia Dani ba. Amma banida gaskiyar da ta wuce wann.!”
Haidar yaci gaba da girgiza kai cikin tsananin takaici yana duban Hish
am “And you expect me to buy those lies..! Are you that shameless.. Are you that coward..! Don’t you have conscience.?! Why can’t you just admit to the truth.!”
“Enough Haidar.!” Daddy ya dakatar dashi kafin yaci gaba “Ya fad’i nashi sai ka bar ma hukuma
aikinsu suyi bincike su zartar da hukunci.!”
Cikin sanyin jiki Haidar ke duban Daddy. Yana girgiza kai yake fad’in “I can’t believe this Daddy.. Na kasa yarda ka aminta da D’an da ka had’u dashi yau d’aya sama da D’an da ka rayu dashi tsawon rayuwarsa.”
Ya jinjina Kai a hankali still yana duban Daddy “Dama mai zan tsammata.. He’s always been your favorite even before you met him.. A sabida rashin shi ka azabtar Dani shekara da shekaru.. A sabida rashin shi ka kasa kallona a matsayin D’a..” Hawaye suka so
ma gangaro ma Haidar sanda yaci gaba “A sabida rashin sa na rayu cikin duhu ni kad’ai a cikin gidan mahaifina..!”
Wann karon cikin sanyin murya Daddy ke furta “Haidar Ya isa haka.”
Haidar yaci gaba da nuna Hisham jijiyoyin goshinsa Sun mimmike fuskarsa t
ayi ja sosai yake ci gaba da furta “This is the truth Daddy.! Duk a sabida rashinsa ne….!”
A hasale Daddy ya katsesa “Then blame your mother..! Ita ce silar faruwar komai..! She created all this chaos..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar “You s
hould be grateful ka girma kana ganin duka iyayenka biyu. D’anuwanka Ya girma baisan mahaifinsa ba..!” Muryar Daddy ya soma rawa sosai, hannayensa har b’ari suke sanda yaci gaba da nuna Hisham idanunsa naga Haidar “I kicked him out tin yana ciki baizo duni
ya ba.! I kicked my son.. My flesh and blood out of his very own home Haidar..! A sabida haka zan bashi duk wani kariya da yake buk’ata daga yanzu har k’arshen rayuwata Wanda ban bashi a baya ba.!”
Abinda Hisham yake son ji. Anzo daidai gab’ar da yake so
a iso. Ya saki murmushin nasara cikin zuciyarsa. ‘Da kyau.. Da kyau Aliyu Maitama. Ka zab’i turban gaskiya da ka zabi ka bi bayana da mahaifyata.’
Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifinsa. A daidai lokacin Mommy da Hajja Fannah suka k’araso p
arlorn. Haidar ya waigo ya dubi mahaifyarsa. Sai ya isa ya kamo hannunta “Let’s go Mommy.! We are not welcome here.!” Yai maganar yana duban Daddy.
Daddy ya lumshe idonsa kadan ba tareda Ya furta komai ba.
Mommy ta waigowa ta dubi Hisham ta kuma dubi
Haidar. A haka Har suka fice. Suka nufi yanda Sadis ya aje motar.
Mommy ta kula da yanayin Haidar d’in tinda suka fito. Ta kuma ga yanayin rabuwarsa da mahaifinsa. Sai Tai gyaran murya kad’an sanda suka zauna saman kujerun shak’atawa suna jiran zuwan Sadi
s.
“Aliyu kana lafiya.?” Ta tambaya tana dubansa.
Sai ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata. Ya dafa hannunta guda “As long as kina cikin k’oshin lafiya nima ina lafiya Mommy na.”
Ta murmusa tana dubansa sai ta jinjina kai a hankali “Haidar… My Son..”
Y
a d’ago yana duban mahaifyarsa.
Mommy taci gaba “Kai hakuri da mahaifinka.. Kai masa uzuri a wann lokacin. He just met his Son… So zaka iya ganin abubuwa da dama da zaisa kaga kaman baya sonka ko yafi Son sabon D’ansa da basu tab’a had’uwa ba. A’a ko d’ay
a ba haka bane. Yana son duka ‘ya’yansa saidai it is natural mutum yai d’okin sabon abu. Misali kai kanka da aka maka haihuwa just yesterday kaji kana d’aukin wann D’an. Toh kaman haka nake so kai ma mahaifinka uzuri duk abinda zai faru kaji koh.”
Haidar
yai shiru yana sauraron mahaifiyarsa kafin ya jinjina Kai yace “Na gode Mommy.”
Ta jinjina masa kai murmushi saman fuskarta “Ina cikin farin ciki maras misaltuwa a yau d’in. Inaji tamkar na sauk’e wani kaya mai matuk’ar nauyi akaina.. Na nemi yafiyar Fann
ah kuma ta yafe mun. Alhamdulillah.. Ko yanzu na bar duniya Ubangijina Ya cika mun wasu manyan burika nawa. Ya daidaita tsakanin ahalina Ya kuma sake had’ani da Fannah mun fahimci juna ta kuma yafe ni. Sann Ya nuna mun gudan jininka.. jikana. Ba abinda zan
ce sai godiya. Hak’ik’a duk Wanda Ya dogara ga Allah toh Ya isar masa.”
Ya kalleta tausayin ta da k’aunarta tab zuciyarsa. Sai Ya murmusa cikeda jin dadi yana mai danne k’uncinsa tareda ayyana farin cikinsa ganin mahaifiyarsa da yai cikin farin ciki.
**
A b’angaren su Hajja kuwa bayan ficewar su Mommy sai itama tace tafiya zasuyi. Dama ta tsaya ne domin su gana da Kwaise kuma fahimci juna itada Kwaise sun yafi juna dan haka ba zama zatayi ba.
Hisham Ya dubi Daddy sai Ya sadda kai cikeda risinawa yana s
atan kallon Hajja ganin tana binsa da wani irin kallo tamkar kallon tuhuma ko kallon rashin yarda. Ya sadda kai sosai gaban Daddy yace “We.. will go ahead, Sir.!” Yai maganar kaman yanda yake kiransa a Office.
Sai Daddy ya murmusa yace “No more Sir. It’s
Daddy.. Ka kirani Daddy kaman yanda D’anuwanka Haidar ke kirana.”
Murmushi Hisham yai yana kuma sadda kai “Ok.. Daddy.”
Daddy ya jinjina Kai kafin ya k’arada “Come here.” Ya k’arashe yana bud’e masa hannayensa alamun Ya taho su rungumi juna. Aiko Hisham
Ya taho sukai hugging juna Daddy ya dan bigi kafad’arsa kad’an yace “Da kyau my Architect. Baka samu passion din naka a sama ba..It runs in our blood.. After all, your Dad is an Engr.”
Murmushi Hisham yai kafin ya kuma yima Daddy Sallama Ya dubi Hajja ci
keda risinawa yace “Hajja.. Zan jira a waje.”
Bata amsa shi ba sai kallon da ta bishi dashi. Hisham Ya fice yana mai shan jinin jikinsa dan yaga irin kallon da mahaifiyar tasa Tai masa.
Daddy yai gyaran murya bayan ficewar Hisham. Ya d’an tako kad’an “F
annah.!” Ya ambaci sunanta da tausassar murya. Ta d’ago ta dubesa kad’an sai Tai saurin sadda idonta kad’an tana jin zuciyarta na harbawa.
“Thank you.! Na gode da kika yafe ma Kwaise. Na gode da kika yafe mun kika fahimceni.. Sann na gode da kika raini D
’ana cikin aminci ya girma ya zama mutumin K’warai.. Nasan bai zama mai sauki a gareki ba. Amma dukda haka kinyi iyaka kokarinki wajen ganin kin basa tarbiya kuma kin providing masa.. Ina nufin duk wasu d’awanniya da Ya kamata ace nauyi ne na mahaifi.. ci
nsa shansa, lafiyarsa.. Karatunsa da sauransu.. Na gode.”
Ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an “Ka daina min godiya.. Haka ne Ya kamata… Idan ba damuwa ni zan wuce.. Ina so na biya asibiti na duba Ummukhair.”
Daddy ya jinjina Kai “Ok.. Is alright..” Ya fad’i y
ana dan jinjina Kai. Tana shirin mik’ewa yai saurin mik’ewa daga kujeran da yake kai yace “Can I..” Sai ya d’anyi shiru kaman wanda ya tuna wani abu sai kuma ya k’arada “I mean.. see you out.?”
Sai ta girgiza kai kad’an “A’a karka damu.. I can walk myself
to the door.”
Ya jinjina kai kad’an. Har ta fara tafiya Ya kuma dakatar da ita.
Ta lumshe ido a hankali kafin Tai k’ok’arin juyowa.
Daddy yai gyaran murya cikin k’ok’arin had’o kalamansa.
“Em nace ba.. Idan bazaki damu ba ina so na tafi tareda Hisha
m.”
Sai ta murmusa kad’an “He’s a grown Man now.. Kuma Abuja wajen aikinsa ne..”
Daddy ya katseta “Eh haka ne.. Amma ina so Ya zauna tareda mu a can gidana wann karon.. So that.. I can get know my Son better..”
Ta jinjina masa kai kad’an “Duk yanda kai
daidai ne. Kaman yanda kace.. he’s your son.” Tai saurin k’arawa da “Ni zan wuce. Allah bamu alkhairi..” Bata jira amsarsa ba tasa kai cikin sauri. Daddy ya sauk’e deep breath had’ida zama cikin kujera.
A waje ta iske Hisham jikin mota. Yana ganin isowar
ta yai saurin nufan k’ofan motar da zummar bud’e mata. Sai yaga bata shige motar ba ta kafesa da ido sosai. Wane irin kallo da idon da zai iya cewa bai tab’a gani daga gareta ba tin tasowarsa.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*57*
*©
️
Sameena
Aleeyou…✍
🏽
*
Ganin bata shige motar ba yasa jikin Hisham macewa sosai. Cikeda kulawa yace “Hajja ta akwai wani abu ne..? Kodai Daddy ne ya sanar dake wani abu.?”
“Akwai abinda ya kamata ya sanar Dani ne.?” Ta tambaya a dake tana dubansa.
Sai ya dan s
adda idonsa kad’an “A’a… Kawai dai.. Just asking..”
“Hisham.” Ta ambaci sunansa a tsare.
“Na’am Hajjata.” Ya amsa cikeda kulawa.
“Meyasa ka b’oye mana komai idan Har abubuwan da kake fad’a gaskiya ne..? Meyasa ni baka sanar Dani ba..? Anya akwai wani ab
u mai kama da coincidence cikin labaranka.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido sosai.
Sai ta murmusa yana girgiza kai “Hajja ke kika raineni.. Kuma kinsan ni wane irin mutum ne.. Hajja zafin kishi ne kawai ke d’awainiya da Haidar.. Kuma zan tabbatar masa I’
m not after his family.. Hajja ki yarda Dani nayi komai ne sabida Haidar.. Yeah quite alright naso Ummul a baya kema shaida ce Hajja.. Kuma da ace tun a lokacin da na riski labarin Auren Ummul kin sanar Dani asalina da ba wann labarin muke a yanzu ba. Haj
ja b’oye min da kikai Shiyasa Allah Ya hadani da Haidar D’anuwana Har na hadu da ahalina da kuma mahaifina.. You should never have kept this from me Hajjah.. As they say no secret remain hidden forever..” Jikin Hajja yai sanyi sai ta fara tuhumar kanta tan
a jin da gaske itace mai laifi da taita k’ok’arin b’oye masa. Hisham na hankalce da ita yaci gaba “I don’t know who’s the real victim here.. Ni ne victim d’in.. Ko kuma D’anuwana Wanda muka Gina abota mai tsafta tare.?” Yai murmushi mai ban tausayi kafin y
aci gaba “We were so closed Hajja.. We looked up to each other like brothers ba tareda munsan cewa Mu d’in ‘yanuwan juna bane.. Ashe shak’uwarmu da abotan mu ba daga sama Ya samo asali ba Ashe jini ne.. Amma a halin yanzu Haidar baida babban mak’iyi sama D
ani.. Banida zab’i da Ya wuce na wanke kaina daga duk wani zargi..”
Ta d’anyi Jim tana dubansa sai tace cikin sanyin jiki “Amma.. Amma kayi wani furuci da Ya bani tsoro da mamaki a ranar da Ummul zata haihu.. Naji da kunnuwan kana cewa baka damu ba koda z
a’a rasa jaririn matuk’a Ummul zata zama safe.. Kalamai be da ban tab’a jin makamancin su daga gareka ba.”
Sai Ya dan jinjina Kansa a hankali “K’warai nayi wann furucin.. Watak’ila cikin dimauta da ganin irin yanayin da Ummul ke ciki.. Ya kamata ki min uz
iri a nan.. Sabida zuciya batada k’ashi.. Kar ki mance irin soyayyar da nai ma Ummul.. A lokacin da take yunk’urin haihuwa tsakanin rayuwa da mutuwa take.. Hajja ko kece aka baki zab’i tsakanin Ummul da jaririn dake kokawan fitowa nasan Ummul zaki zaba ba
jaririn ba..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Hajja kema zargina kike kaman Haidar..? Na kasa yarda Hajja.. You raised me yourself.. Kinsan komai akaina.. Ni din tarbiyarki ne kuma rainonki.. Ta Ya Daddy da muka hadu yau d’aya tak zai yarda dani am
ma mahaifiyar da ta raineni ta kasa yarda dani.?”
Furzar da huci kad’an Tai tana kauda fuska gefe. Ta soma girgiza kai “Ban sani ba Hisham.. Ban sani ba ko na tauyeka ta wani waje.. Ban sani ba.. Ko dai nayi kuskure da na zab’i nisantaka da mahaifinka..!”
Sosai muryarta ke rawa sanda take maganan.
“Ban sani ba kodai na gaza.. Ban sani ba Kodai wani abu daban na raina..!” Ta k’arashe muryarta na rawa irin na mai kuka.
Zuciyar Hisham yai wani irin tsinkewa. Hawayen da ya gani na fitowa daga idon mahaifyars
a Ya haifar masa da shiga tashin hankali. A duniyarsa ba abinda baya so kaman b’acin ran mahaifiyarsa. Zaiyi komai sabida ita. Hasalima duk wani fansa da Ya jima yana dauka sabida ita ne sabida soyayyar da yake mata ne Har saida Ummul ta shigo cikin pictur
e d’in.
Saurin k’arasawa yai ya rungumeta “Hajja ki daina kukan nan.. Baki san hawayenki sunfi komai tsada a Duniyar nan ba. I’ll set whole world on fire just for your tears.. Dan Allah Ki daina kuka Hajjata..”
Ta d’ago tana dubansa shima ita yake duba.
Ya kamo hannayenta “Na Miki alk’awari zan wanke kaina Hajja.. Kuma ki yarda dani dan halak kika raina. Zan fito da evidence da zasu tabbatar da iyakacin gaskiyata.” Ya k’arashe yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. Daga nan bud’e mata marfin mota
yai ya taimaka mata ta shige kafin suka d’auki hanyar Asibiti.
**
Suna isa asibiti suka iske ana shirin sallamar su Ummul. Hajja ta mak’ale Ummul cikin jikinta tana fad’in “Ki yafeni ‘Yata na tafi na barki a lokacin da bai kamata na tafi na barki ke kad
’ai ba.”
Ummul ta murmusa “Nasan babban al’amari ne zaisa ki tafi ki barni. Na gode ma Allah da yasa kuka kasance cikin k’oshin lafiya.”
Hajja ta kuma rungumeta tana amsar jaririn. Duk wann abin gaban su Mommy ke faruwa. Sai mamaki suke suna fad’in ashe
Ummul ce zatai sanadin sake had’uwarsu. Mommy ta kuma kamo hannayen Ummul tace Lallai ta cancanci sunanta Uwar Alkhairi kuma element of Union. Gashi dai duk dad’ewa da sukai suka shafe shekara da shekaru suna neman Hajja basu sameta ba sai ta dalilin Ummul
. Tabbas ita d’in alkhairi ce ga ahalinsu. Nan Su Mama Tani suke ta mamakin al’amarin harma da Ummul d’in musamman da sukaji cewa Haidar da Hisham ‘yanuwan juna ne da suka had’a uba d’aya. Mama Tani tace ashe abin duk ahali ne. Mommy ta karada “What a smal
l world.” Addu’a sukai gaba d’aya kafin suka d’unguma suka fito dan tuni an sallamesu. Hajja Fannah ta rok’i alfarma a bar Ummul ta kwana d’aya can gidanta idan yaso washe gari sai su d’auki hanyar kano tinda ga almuru Ya