Showing 135001 words to 138000 words out of 267381 words

Chapter 46 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

77

fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k’addara mai kamanceceniya musamman a b’angaren abinda ya sh

afi alak’arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad’o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata.

Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba.

**

Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k’are

cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k’are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak’ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b

’oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b’oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab’a sanar da kowa ga yanda ya b’oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida

kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k’arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d’in Anisa. Watak’ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Sh

i Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d’insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik’e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab’a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last

abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai. Ya isa ya janyo wan

i drawer. K’asan drawer d’in ya daga tile guda sai ga wani bak’in tulu an rufe samansa da jan kyalle. Dama shi yake ajiye da wann tulun Wanda hakan yasa ya rik’e Dareen a tafin hannunsa. Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i dukda da ita da sunanta

da sumarta da na Haidar aka had’a akai asirin amma batada say dan bata san ina Hisham ya b’oye tulun ba. Shiyasa a kullum take bin Hisham a sannu dan Dodon tsafi ya sanar dasu duk randa wann tulun ta fashe asirin zai karye sann Haidar zai rabu da ita zai n

una bai ma tab’a saninta ba. Koda Hisham yaji haka sai yai wuf ya d’auke tulun ya b’oye dan ya samu ya rik’e Dareen cikin hannunsa ta dinga yin duk abinda ya Umarceta. Wann dalili yasa Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i sabida Tulun na wajensa ya

masa b’oyo mai nisa kaman yanda Dodo ya sanar da ita. Hakan yasa Dareen ke bin Hisham a sannu gudun kar ya fasa wann tulun ya karya asirinta na kasancewa matar Haidar.

Sauri sauri ya fito daga gidan nasa tulun rungume cikin hannunsa.

Dareen na tsaye h

araban gidan tana faman safa da marwa ta hangi Hisham na zuwa. Tai tsaye Cak tana dubansa k’irjinta na bugawa.

Bata Ida razana ba saida ta hangi hannun Hisham rungume da bakin tulun da Dodo ya k’ulla aurensu da sumarta da sumar Haidar ya rufe cikin wann

tulun ya kuma tabbatar mata matuk’a wann tulun na nan yanda yake aurensu da Haidar babu abinda zai samesa sai mutuwa ce zata raba.

Ta nufo Hisham cikin rawar jiki tana fad’in “Finally ka zab’i ka dank’a min ajiyan makullin aurena da Haidar.!” Tai maganar

murmushi saman fuskarta.

Dakatar da ita Hisham yai da fad’in “Stay right there.!”

Dareen taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Cikin rawar murya take furta “Hi….Hisham.. What’s going on..?”

Murmushi Hisham yake da gefen baki “You are no longer

useful to me.. Kuma kinsan abinda nake da mutanen da basuda sauran amfani wajena.. I dispose them.. Just like this..” Ya k’arashe yana k’ok’arin sakin tulun.

Dareen ta zaburo tana k’ok’arin yowa Kansa “No Hisham don’t do this.. Please kar ka aikata min h

aka.. Kar ka tsinka igiyan aurena da Haidar.. Wllhi I truly love him..!”

Dariyar rainin hankali Hisham yai “Love.? Did you just say love.. How is that relevant.? Ta ya zakiyi soyayya da mutumin da bashi a hayyacinsa. bai san dake ba ko ince baisan da Aure

nki ba.? Ko kuma nace idan ma ya sani auren na fluctuating cikin kansa.”

Dareen ta girgiza Kai tana hawaye “Watak’ila baisan ya akai Aurenmu ba amma nayi alk’awarin kare wann auren till my last breath. You can’t break our marriage Hisham.”

Ya kuma murm

usawa har lokacin bak’in kwaskon na cikin hannunsa “Na tuna miki yanda akai kuka hadu ne.?”

Ta kasa cewa komai sai hawaye dake gangaro mata.

Hisham yaci gaba “Wani rana ne a airport. Zamu tafi wani construction work Lagos muka hadu dake a jirgi. Tinda n

aga yanda kike kallon Haidar na tabbata kin kamu da sonsa. Kinyi ta k’ok’arin shige masa amma sai kika lura bazaki samu chance dashi ba. Har dai kaman kinyi giving up. Ni na sameki nai Miki proposing idan kina son Abokina da gaske. Kika kuma tabbatar min z

aki iya komai dan kawai ki mallakesa. Na baki zab’i cewa zaki mallakesa amma zaki min aiki a jikinsa. Zaki zame min tamkar spy wacce zata dinga nado min komai na duk abinda yake ciki a rayuwarsa domin Nima na cimma burina Kansa. Dani dake muka had’a k’arfi

da k’arfe. Ni na nemo Miki sumar Haidar muka had’a da naki sumar muka Kai gaban dodon tsafinku aka k’ulla aurenku da Haidar kaman yanda Dodon ya buk’ata. Ya kuma tabbatar mana duk yanda Haidar yake zai bayyana matsayin mijinki.. Zaki bayyana masa matsay

in matarsa.. Haka ne.?”

Taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Hisham yaci gaba da murmusawa “Kiyi gaggawan b’acewa daga cikin rayuwar Haidar. Dan idan kika jira na fasa kwaskwon nan Haidar sai ya kusa kashe ki da hannayensa kafin ya mik’a ki ga hukuma.”

Dareen na huci take dubansa “Na ranste da Allah baka isa ba Hisham. Baka isa ka rabani da abin kaunata Haidar ba.!” Ta k’arashe tana kokawan k’wace bakin kwaskon daga hannun Hisham.

A daidai lokacin Haidar ya k’araso. Hisham na hangosa yaci gaba da kokaw

an k’wace kwaskon daga hannun Dareen yana fadin “Allah ne ya toni asirinki mushirika. Ni dama na jima da fahimtar ba tsakani da Allah kike zaune da abokina ba. Kuma yau sharrinki zai koma kanki dan sai na fasa wann kwaskon da na ganki dashi. Yau Haidar za

i fahimci gaskiyar abinda naita nusar dashi akanki.!”

Aikaw garin kokawan k’wace kwasko ya fad’i k’asa ji kake tasss ya fashe. Sai ga bak’in hayak’i na tashi. Dareen ta saki k’ara tana soshe soshe yayinda Haidar ya Kama Kansa da yai wani irin sara masa.

Ya duk’a nan wajen yana rik’e Kansa had’ida sakin k’ara da bai san yana yi ba. Nan ya kwanta wajen tamkar sumamme. Hisham yayo Kansa a guje yana jijjigasa yayinda Dareen ta k’araso tana haki ta dubi Hisham dake jijjiga Haidar Wanda da alama ya sume. Ta nun

a Hisham da yatsa “This is far from over Hisham. Ko ince shadow ka tsammaci dawowa ta dan nice zan dawo maka a matsayin Shadow.!”

Murmushi Hisham yai mata da gefen baki “Kafin ki dawo na Miki alk’awarin na d’auke abinda nake son d’aukewa daga wajen Haida

r. Bazaki sameni cikin rayuwarsa ba.!” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda.

Da baya da baya ta dinga tafiya har ta shiga gidan a guje ta soma tattara ya nata ya nata.

Hisham ya d’auki Haidar ya shigar dashi cikin gidan ya kwantar sa saman kujera. B

ayan ficewar Dareen.

Bayan shud’ewar wasu mintoci Haidar ya soma bud’e idonsa da sukai masa nauyi yana jin kaman abin da a kullum yake ji ya masa nauyi a k’irjinsa anyi lifting masa. Wani cunkushewa da yake ji zuciyarsa da kwanyarsa suna masa sai yaji kam

an an d’aga masa Abu mai nauyi da aka ajiye cikin k’irjinsa.

Tilon abokinsa Hisham ya gani zaune gefensa yana danna masa towel saman goshinsa.

Hisham na ganin Haidar ya bud’e ido ya sakar masa murmushi yana hamdala “Alhamdulillah Haidar ka tashi.!”

Sos

ai Haidar ya mik’e yana k’are ma Hisham kallo “Meke faruwa Hisham. What just happened.?”

Hisham bai Kai ga basa amsa ba ya hangi hotonsa da na Dareen mak’ale a parlorn ta mak’alk’ale cikin jikinsa. Ya juyo yana duban Hisham zuciyarsa na bugawa da sauri d

a sauri. Sai ya mik’e ya isa jikin hoton yana kallo sosai. A hankali komai yake dawo masa. Tin daga had’uwarsu a airport da irin shige masa da taso yi bata samu k’ofa ba. Dan har wajen aikinsu a Lagos ta bisu. Da tsanar da yai mata. Ya kuma tuna Tabbas yay

i zaman aure da ita auren da bazai ce ga yanda aka k’ulla ba. Auren da wani lokaci Ya tuna da ita wani lokaci Ya mance da ita.

Idonsa naga hoton yake furta “Ya akai na k’are da auren yarinyar nan Hisham.?”

Hisham ya mik’e yana mai furzar da huci. Ya dan

tako kusan Haidar d’in su duka biyu suna kallon hoton kafin Hisham yai gyaran murya “Tambayar da na jima ina maka Haidar. Ka mance.?” Hisham yaci gaba “Tun a fari ban San ya akai haka ta kasance ba Haidar. Sanin irin k’iyayyar da Kai ma yarinyar a haduwar

ku ta farko a airport. Ka tuna.? Ganinka kawai da ita nai matsayin matarka bansan ya akai k’iyayyar da Kai mata ya rikid’a ya koma soyayya ba. Soyayyar da har ta kaiku ga aure. Auren da bayan ni ko iyayenka baka sanar masu ba kuma nima ka haneni na sanar m

asu.”

Haidar yai shiru kaman mai nazari dan yasan duk anyi haka.

Idonsa ya kada sosai yake duban hotonsu da Dareen yana tuna irin rayuwar da sukai Wanda sai gashi yana son tuno Abu ko tambayarta wani Abu sai ya kasa ko ya mance “How is this possible Hish

am.?”

Hisham ya girgiza Kai kad’an “Baka a hayyacinka ne Haidar.. Kaga wann..” Ya k’arashe yana nuna masa bakin tukunyar da ya fasa.

Haidar ya tako yana duban abun da mamaki. Abun da shi bai tab’a believing ma anayi ma mutane ba balle yayi tasiri akansa

.

Hisham yaci gaba “Kwanaki uku kenan bamu hadu da Kai ba. Naje asibiti wajen d’aya matarka dake kwance asibiti a tunanina zan sameka can ban sameka can ba. Hasalima Likita ya sanar Dani ka d’auki matarka kun tafi babu Wanda yasan ina kuke. So sai nayi t

unanin nan gidanka ka kawota maybe ka had’ata da matarka Dareen. So da nazo sai na tadda Dareen rik’eda wann kwasko da kake gani tanata wasu sunbatu more like rituals, kaman ma yare take dan ban fahimci mai take cewa ba. So sai jikina ya bani wani Abu ba

daidai bane. Musamman yanda taketa ambaton sunanka ga yare tanayi ga kuma wann tukunyar cikin hannunta. Koda ta ganni ta razana sosai nan na fahimci my hunch was right. Shine kaga ina kokawan fasawa har Allah ya taimakeni nai nasaran fasa wann kwaskon Wand

a ko shakka babu na tsafin ta ne.”

Hisham ya numfasa dan har lokacin Haidar bai iya cewa komai “ Ka gode ma Allah Haidar da ya maida mata sharrinta kanta.” Yai maganar yana mai dafa Haidar d’in.

Haidar baice komai ba sai komawa parlor da yai ya zauna s

aman kujera ya k’ura ma waje guda ido. Har lokacin bai dawo daidai ba da alama.

Hisham ya dafasa kad’an “Is not easy.. Abinda kake going through ba abu bane mai sauk’i Haidar. Ace ka zauna da mace ak’alla tsawon watanni shida ba tareda sanin ya akai ka au

reta ba akwai tashin hankali… Amma na maka alk’awari zata biya abinda ta aikata maka abokina. I’ll look for her yanda ta shiga ta fita.. we can’t let her get away with what she did to you..!” Ya mik’e yana jinjina Kai alamun tabbatarwa. Lokaci guda yasa ka

i ya fice da zummar neman Dareen. Kai kace da gaske Har zuciyarsa ya damu da Haidar d’in ne.

Haidar ya bisa da kallo har ya bace masa ba tareda yace komai ba. Ya jima zaune wajen yanata kallon hotonsu shida Dareen. Bazai ce ga abinda yake ji ba. Saidai

wann nauyin da a kullum k’irjinsa ke masa yaji kaman anyi lifting abu mai nauyin. Like he’s free from captivity. Amma freedom da bazaice ga makomarsa ba. Jiki babu k’wari ya mik’e ya fice daga gidan ba tareda ya jira dawowar Hisham ba.

A b’angaren Hisham

kaw ficewa yai cikin k’ok’arin cimma Dareen dan yasan ta yanda zai bullo mata kafin tai gangancin b’ata masa shirinsa. Saidai koda ya fita bai cimma Dareen ba ga wayarta bata shiga. Yaita buga tsaki yai saurin dawowa ga Haidar dan ya samu yaji ina yakai U

mmul ya b’oye. Saidai yana dawowa yaga wayam babu Haidar babu dalilinsa.

Ya buga tsaki yana naushin kujera da hannunsa “Damn you Haidar.! Damn you.!” Yayi duk abinda zaiyi ne dan ya gano yanda Haidar ya b’oye Ummul amma da alama Haidar ya fice ya tafi ba

tareda ya jira dawowarsa ba. Bayan duk abinda yai ma Haidar d’in still yai zab’i yaita yin abubuwansa ba tareda ya sanar dashi ba. Haka ya dinga tsaki shi bai cimma Dareen ba bai kuma tadda Haidar ba. Ficewa yai yana dialing layin Anisa.

**

A b’angaren

Haidar kaw koda ya k’araso gidan zama yai a veranda dake nan wajen gidan. Bai bi takanta ba bai nemeta ba sai zama da yai ya daura hannayensa saman k’afafunsa Kansa kife tamkar maras lafiya ko Wanda ke cikin yanayin damuwa.

Ta window ta hangi motarsa. T

ai mamaki Jin bataji shigowarsa ba yau d’in. Tai saurin mik’ewa ta yafa mayafin doguwar rigarta ta nufo waje. Nan ta gansa zaune ya kifa Kansa ga tsuntsayen da yake basu abinci Sun kewayesa amma ba abincin yake basu ba.

Sosai taji mamakin ganinsa haka sa

i ta soma takowa cikin sand’a kaman mai tsoro ta k’araso Sallama saman bakinta. Amma sai taji shiru bai amsa ba. Ta d’anyi gyaran murya tace “Ka mun izinin…. Zama.?”

Nan ma shiru bai amsa ta ba. Sai dai kawai tai ta maza ta zauna daga can gefe dashi tana

satan kallonsa ganin bazai amsata ba.

Har lokacin Kansa a kife yake. Bai d’ago ba bai ce da ita komai ba. Ta dan sha jinin jikinta sai ta soma kallon yanda tsuntsayen suketa kewayesa alamun suna jira ya basu abinci.

Ta saki murmushi a hankali tace “Kam

an dai… Kai suke jira..” Yanda tai maganar zaka fahimci k’ok’ari take ta had’a kalaman saman harshenta.

Nan ma shiru bai ce komai ba. Ta d’an k’ara satan kallonsa still yana nan yanda yake. Ta maida kallonta ga tsuntsayen “Bari ni na baku…. idan zakuci n

awa.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Har lokacin yana nan yanda yake.

Mik’ewa tai tana satan kallonsa har lokacin yana nan yanda yake. Ta tafi ta dauko sauran abincin da Haidar ya kawo mata na ranan da ya gabata. Ta k’araso a d’arare tana watsa masu

sai suka fara tashi sama suna guduwa.

Ta d’anyi rau rau da ido tana kallonsu “Kaga ni basa son na basu.. dan Allah ka amsa ka basu.. Kaga guduwa suke..” Tai maganar kaman zatai kuka tana duban Haidar Wanda sai a lokacin ya dago fuskarsa yana dubanta.

Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i gani da tai fuskar nasa cikin wane irin yanayi da zatace bata tab’a ganinsa ciki ba. Ga idanuwansa Sun kad’a sunyi ja sosai. Duk sai jikinta yai sanyi. Ta sadda nata idon a hankali tana tuhumar kanta mai ma ya kawot

a yanda yake.? Wata zuciya tace ta haka ne kawai zaki iya fahimtarsa idan har kina son sanin wanene shi.

Wata Zuciyar ta gargad’eta ‘Anya baki tafi da nisa ba Ummul.?’ Sai ta soma k’ok’arin janye jikinta da nufin barin wajen amma sai taga hannayensa sama

n nata. Ta d’ago a d’an razane tana dubansa. Shid’inma ita yake duba. Wann karon fuskarsa ya zama pale sosai tamkar ta marassa lafiya.

Batasan ya akai ba sai ji tai ya rungumeta sosai cikin jikinsa had’ida kwanto da Kansa saman kafad’arta.

Zuciyarta y

aci gaba da harbawa. Har lokacin Haidar na nan rik’eda ita idanunsa a lumshe. Yayinda jikin Ummul ya gama yin sanyi. Kaf nauyinsa ya d’aura mata saman kafad’arta. Ta kasa katab’us ta kasa koda motsawa Haidar kaw bai saketa ba. Sun jima sosai a haka kafin t

aji yana sassauta rik’on da yai mata. Ya soma k’ok’arin mik’ewa tsaye fuskarsa a matuk’ar tsare kaman ba shine ya gama rungumarta ba. Kauda kansa gefe yai kad’an yayinda Ummul tai k’asa da fuskarta cikin sanyin jiki.

Saida ya mik’e tsaye sosai ya zira h

annayensa cikin aljihun jeans d’insa kafin ya dubeta “Let’s go.”

“Na’am.!” Ta fad’a a dan daburce had’ida dagowa tana dubansa.

“Pack your things we are leaving..” ya fad’i yana nufan mota.

Mamaki ya cika Ummul. Allah mai iko.. Toh kodai Addu’arta ne suk

a fara karbuwa.. Allah yasa haka ne. Allah yasa Zuciyar Haidar ne ta karkata ga mahaifyarsa kaman yanda take ta addu’a. Cikin sauri ta mik’e tai yanda yace.

Tana karasowa yasa hannu ya bud’e mata front Seat ta shige a d’arare. Tana addu’an Allah yasa ba w

ani wajen zai kaita ba.

Ita dai addu’a kawai take cikin zuciyarta tinda suka baro wann gida dake tsakiyan daji a cewarta. Ganin sun nufi gari yasa hankalinta ya soma kwanciya. Bata Ida mamaki ba saida taga sun doso wani dogon gini mai d’aukeda ‘yansanda t

in daga waje.

Suna isowa yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login