Showing 114001 words to 117000 words out of 267381 words

Chapter 39 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

28

/>
kanki ne. Let them fight each other. Let them hate each other. Let them go down together… I am warning you kar ki kuskura ki nuna ma Kwaise fuskarki.. You know me Dareen. No body double crosses me. And I have no patience with people who screwed up.!” Ya k’

arashe yana sakin huci.

Ta jinina kanta a hankali “Got it. I won’t go there.. But what about Haidar.. I’m starting to worry.”

“You are useless.!” Ya fad’i yana mai sakin gajeren tsaki kafin Ya katse kiran.

Dareen ta koma ta zauna jikinta duk a mace. Y

anda taga dare haka taga rana dan bata iya bacci ba. Ita dai tafi tunanin mahaifiyar Haidar ta fahimci wani abu gameda Haidar din sann bata zauna ba.

**

A can asibiti kaw wayar Mommy ne Ya tada dashi. Yai gajeren tsaki yana mik’ewa zaune daga nan saman

sofa yanda ya kishingida ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da yai masa nauyi. Gaba d’aya ji yake kaman an masa duka, dan a tak’ure a nan wajen ya kwana. Yakai dubansa gareta Har lokacin idonta a lumshe suke ga nauran oxygen mak’ale hancinta. Ya kuma duba waya

rsa dake ci gaba da vibrating. Har lokacin Mommy ce mai kira. Bai d’aga ba har ya k’arashi ringing. Ya jima baiyi bacci da Ya makara irin haka ba. Ya duba yaga calls da dama ciki Harda na matarsa Dareen Wanda akasarin missed calls daga ita Ya samu. Harda t

ex message ta tura masa wanda bai bi takansu ba. Ya mik’e yana stretching arms d’insa. Ya shafi sumar kansa da duka hannayensa biyu. Nan wayar Mommy ya kuma shigo masa.

Gajeren tsakin ya kuma yi “She won’t stop calling.!” Ya furta a hankali. Tsaban haush

inta da yake ji sai ya jefa wayar a aljihu. Ya d’auki mabudin motarsa ya nufi k’ofa a gaggauce. Har ya isa k’ofa ya kuma juyowa ya dubeta. Har kawo wann lokacin da zaka tanbayesa ya kamanninta yake bazai iya tabtancewa ba. Abu d’aya ya sani shine baida bur

in da ya wuce ta tashi ta amsa masa tulin tambayoyin sa. Dan alk’awari yayi sai ya hukunta Mommy da duk wani Wanda yakeda saka hannu a tarwatsewar rayuwarsa.

Ya furzar da huci kad’an kafin Ya janyo k’ofar Ya kulle.

Yana tafe Mommy na kuma kiransa bai

daga ba har ya shige mota ya soma tuk’i. Abubuwa fal cikin zuciyarsa.

Anisa da bacci Ya kaurace a idonta tin daren jiya ta window ta hango motar Haidar Ya shigo gidan. Ta mik’e da sauri tana lek’ensa. He looks exhausted. She couldn’t believe it wai Haid

ar wajen bagidajiyar cen ya kwana kuma a asibiti. Ta lumshe idonta tana jin zuciyarta na mata ciwo. She couldn’t bear the thought of it.

Suitcase d’insa da dake cikin motar Wanda bai unpacking ba tun bayan dawowarsu daga Cuba 2days back ya bud’e motar y

a Ciro.

Kai tsaye section d’insa ya nufa. Yai tsaye yana k’are ma gidan kallo Wanda a halin yanzu yarinyar ke rayuwa cikin gidan. Tin daga haraban sashen har zuwa parlor a gyare ne. Sai k’are ma gidan kallo yake dan shi mutun ne da baya shiri da k’azant

a. Da yawan cleaning ladies na gidan da ake canzawa sabida shi ake canzawa.

Dukda an canza fasalin gidan hakan bai hanasa nufan k’ofan dakinsa ba. Saidai yana murda handle d’in ya jita a rufe. Sai ya lumshe idonsa kadan. Ya mance shid’in bak’o ne a gidan

a halin yanzu. Ya d’anyi gajeren tsaki, ya d’ago yana duban k’ofan d’aya d’akin. He had no other option. Hakan yasa ya nufi k’ofan d’akin. Yai still kaman bazai bud’e k’ofan ba sai kuma ya murda handle d’in had’ida tura k’ofan d’akin. D’akin ma kaman dai

ko ina a gyare yake. Ya tabe baki kad’an dan ba abin mamaki bane dan yaga babu datti yanda yarinyar ke zama tinda ya sani ma’aikatan dake gidan sunfi ahalin cikin gidan yawa amma dukda haka shi zai iya cewa b’angaren nasa bai tab’a kasance masa cikin gyara

da zuciyarsa ta aminta dashi irin haka ba. Suitcase d’insa ya bud’e ya dauki abun buk’ata kafin ya nufi bathroom. Nan ma the same komai a gyare. Idonsa suka sauka kan inners dinta dake shanye a band’akin. Yai saurin janye idonsa sirirn tsaki na kufce m

asa. Sauri sauri ya sakar ma Kansa shower yana mai lumshe idonsa cikin k’ok’arin haramta ma idonsa abinda ya gani. Koda yai wankan ya mance babu towel cikin wann jakan. Ya d’ago kai yana duban bathrobe din dake mak’ale nan cikin bathroom d’in. Ya jima sosa

i yana bin bathrobe din da kallo wai shi Haidar zai amfani da somebody else’s bathrobe. Shi da ko towel d’in matarsa Dareen bai tab’a amfani dashi ba. Ya lumshe idonsa a hankali yana furzar da huci. Akan dole ya d’auki bathrobe din Wanda baida haufi na yar

inyar ne ya zira jikinsa ba don yaso ba. Sanda ya fito daga bathroom din Anisa na nan lab’e jikin k’ofa tana lek’ensa. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa ganin Haidar da gaske wanka yai a d’akin Ummul sann abunda yafi tada mata hankali harda bathrobe d’in Um

mul d’in ta gani d’aure jikinsa. Dan bata mance ba zuwansu shopping tareda Ummul suka sai wann bathrobe din Wanda saida tai masu kauyanci akan bata iya amfani dashi ba. so definitely nata ne. Ji tai kuka na Neman balle mata. Ji tai k’afafunta suna barazana

r gaza d’aukarta. Ta koma da baya a hankali had’ida jingina jikin garu. Ta soma tuhumar kanta anya batai gangancin saka ma Ummul poison din nan ba.? Anya wann ciwo da Ummul take bazai sanadiyan samun kusamcinta da Haidar ba. Ya zama dole ta yi duk yanda za

tai ta tabbata Ummul da Haidar basu samu kusanci ba. Ta lumshe idonta da k’arfin gaske tana Jin bugun zuciyarta na karuwa. Da kyar da iya ficewa daga sashen cikin k’ok’arin maida hawayen da suka gaza Jin lallashinta.

A b’angaren Haidar kaw bayan ya shir

ya nan ya tada sallan asuba da bai ba. Alamu sun nuna a spot din da yai sallah a wann wajen take sallah dan bayan hango Al’Qur’ani mai tsarki da yai saman drawer harda cazbaha a gefe. Ji yai zuciyarsa yayi wani irin tsinkewa sanda ya hango Qur’anin dan shi

dai zai iya cewa rabonsa da ya d’auki littafin Allah mai starki ya karanta tin kafin yayi aure. Sai ya soma wasu irin tunanin da bai zai iya cewa ga abinda yake son tunawa ba. Yaji zuciyarsa ya cika da guilt din da bazai iya cewa na menene ba. Zuciyarsa y

aji na masa d’aci. Yanaji kaman babu komai cikin rayuwarsa face tarin yaudara da k’arya. Yana tsaka da tunanin wayarsa ta soma ruri daga asibiti ake kiransa.

Haidar ya daga kiran suna gaisuwa da Dr. Nan Dr ke sanar dashi sakamakon gwajin turaren Sun fito

shi ake jira.

Haidar ya jinjina Kai yace gashi nan zuwa right away.

Sauri sauri ya nufo waje zai nufi motarsa ya hangi Anisa na zuwa. Bai damu yabi ta kanta ba yaci gaba da tafiya direction d’in motarsa.

Anisa tai saurin cimmasa “Good morning…” Ta

fad’i murmushi saman fuskarta.

Bata damu da rashin amsa mata da bai ba ta k’arada “How’s your patient.?”

Wani irin duba yake mata sann ya girgiza Kansa kad’an yana rage girman idonsa “What patient.?”

Anisa ta dubesa da mamaki dan da alama a yan kwanak

in yana mance abubuwa cikin sauri. Ta ya za’a ce majinyacin da ka kwana kana kula dashi ka mance dashi da safe..? Toh kodai ba asibitin ya kwana ba.? Something is definitely off. Sai ta k’ak’aro murmushin yak’e “I mean your wife..”

Haidar dake k’ok’arin b

ud’e mota Cak ya dakata da abinda yake. Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Don’t… you dare call her my wife.! You don’t have the right.” Ya fad’i cikeda gargadi.

Anisa ta dan kauda fuska tana mai rausayar da ido “Fine, I won’t call her your wife again..”

Ta dan girgiza Kai “ Are.. you leaving already..? I thought you just got here..?” Ta fad’i tana dubansa.

“Why..? Do you have problem with that.?”

Ta girgiza Kai “Mommy ce tace idan ka fito I should let her know because tayita kiran wayarka bata sameka

ba.. And she prepares breakfast for you.”

Tin sanda ta ambaci Mommy yanayin sa yai mugun canzawa. Ya gyara tsayuwarsa sosai yana duban Anisa “Tell her I’m ok.!” Har zai shige mota ya kuma juyowa ya dubi Anisa “No. Go tell her anything prepared by her..Is

contaminated.!” Yana Ida fad’in haka ya bud’e motar ya shige had’i da fuzgan motar.

Anisa tabi bayan motar da kallo tana sakin makirin murmushi. Ta tabbata Haidar zargin mahaifiyarsa yake. A fili take furta “Well done Neesa.! Yanzu ne zaki shana yanzu ne

zaki bak’anta Ummul a idon Hajiya Kwaise. I have to make it looks like Ummul brings nothing to this family but bad lucks. Knowing Kwaise Maitama duk abinda zai shafi mutuncinta da na ahalinta musamman a idon abokan kasuwancinsu zatai komai dan ta kawar da

wann abun.! Kamar haka zata kawar dake Ummul.!” Ta k’arashe tana sakin murmushin cin nasara.

**

Yana isa asibiti Likitan ya nuna masa sakamakon da suka samu cikin wann bakin turaren humra akwai deadly guba da aka zuba ciki Wanda baida haufi shine Ummul

ta shak’a Watak’ila na tsawon kwanaki.

Huci kurum Haidar yake yana hango fuskar Mommy k’iyayyar da yake mata na ninkuwa cikin zuciyarsa. yana tuna sanda Anisa ta sanar dashi musamman Mommy tai ma yarinyar kyautar turaren. Ya jinjina Kansa kad’an kafin ya

daga wayarsa yana dialing layin Hisham.

Hisham yana daga wayar ya soma da “Huh.! Finally you are returning my calls.. I’ve been trying to reach you since yesterday.. Wai ina ka shige ne.?”

“Find me a lawyer Hisham.. A very good one..!”

Hisham ya girgiz

a Kai cikin rashin fahimta “Lawyer kuma.. Mai zakai da Lawyer.. Wait are you having a court case..?”

“Looks like.” Haidar ya bashi amsa Kai tsaye.

Hisham ya dan girgiza Kai “Then what about your family lawyer.. I mean..”

“Wann ahalin ba nawa bane. Ka ne

mo mun Lawyer Hisham .. A very good one.”

Jin Hisham yayi shiru yasa Haidar fad’in “Look, idan bazaka yi bane. Fine zan nema da kaina.”

Hisham yai saurin dakatar dashi “Haidar wait.. What’s going on..? Wai meke faruwa ne.. Tinda ka dawo bamu hadu ba.. Ya

nzu ka kira kana maganar Neman Lawyer.. Waima kana ina ne yanzu.. Zan zo na sameka..” Bai Kai aya ba ya soma sinkayowa ta cikin wayar ana sanar da sunan wani Likita da ake nema a ER.

Hisham yace “Are you in a hospital.? Haidar meke faruwa ne wai.. Mai ka

ke a asibiti.. Waye ba lafiya.?”

“You ask too many questions Hisham.. You know what.! Calling you is pointless.”

Hisham bai bari ya katse wayar ba yace ya sanar dashi asibitin da yake gashi nan tafe.

**

Sanda Hisham ya iso mamaki ne ya cikasa jin Haid

ar k’arar mahaifiyarsa zaiyi. Bai tsaya a nan ba har sai ya tabbata an gark’ame ta a gidan kasu.

Hisham yaci gaba da girgiza Kai cikin rashin yarda “No Haidar.. You are insane.”

“You are the one who’s sick in the head if you think I’m going to let that w

oman get away with everything she’s done..!” Haidar katse Hisham cikin karaji.

Yau d’in ran Hisham a bace yake sosai da abokin nasa. Ya sani yana hak’uri da Haidar yana masa uzuri a lokuta da dama sann yana nusar dashi kan mahimmanci iyaye amma bai tab’a

tunanin Haidar zai tafi da nisa irin haka ba.

“Ce mun kake na nemo lauyan da zai tsaya maka ka kulle mahaifiyarka Haidar..? Haidar mhaifiya fah..! Shin kasan matsayin mahaifiya a wajenka.?!”

“Kar ka sake ambaton wann matar da mahaifiyata domin mahaifiy

a ta gaske bazata tab’a yunk’urin halak’a D’anta ba.!”

Girgiza Kai Hisham keyi “Ko meye mahaifiyarka tai maka matsayin ta da darajar ta ya wuce duk yanda kake tunani.”

“Well I don’t give a damn.!” Haidar ya fad’i cikin karaji.

Daidai lokacin d’aya daga

cikin Likitocin da sukai ma Ummul surgery a jiya yazo wucewa. Hango Haidar da yai ya k’araso suna gaisawa had’ida tambayarsa jikin matarsa.

Bayan Likitan ya shige Hisham ya dubi Haidar da mamaki “Matarka akaima aiki..? Wai Dareen ce a kwance a asibiti.?”

Haidar ya d’ago yana duban Hisham sosai “Not Dareen, actually.!”

Cikin rashin fahimta Hisham ke girgiza Kai “Wait.. If not Dareen, then who.?” Ya kuma girgiza Kai “Wait a second. Haidar don’t tell me aure ka sakeyi secretly ba tareda sanin iyayenka ba.?”

“Throw that question to Kwaise Maitama. Ina ganin itace tafi cancanta ta baka wann amsar..!” Yai maganar yana sakin huci yana ci gaba da takowa kusan Hisham “Kasan dalili.?” Su duka biyun duban juna suke. Haidar na sakin huci yayinda Hisham ke binsa da k

allon mamaki. Haidar yaci gaba “Well that woman da na girma na sani matsayin mahaifiyata ta kawo wata mata cikin rayuwata dan tayi amfani da ita ta kasheni. Wann matar da kake ta k’ok’arin karewa Hisham ta sa nayi signing agreement dan kawai ta cimma burin

ta akaina.” Hawayen zafin zuciya na gangarowa daga idonsa guda yake ci gaba “Kasan dalilin da yasa wad’ann mutanen suka amince na jagoranci project d’in.? It’s because I signed the marriage agreement Hisham.! Kasan dalilin da yasa na tafi Cuba.?” Hawaye su

ka ci gaba da zubo masa yayinda jikin Hisham yai matuk’ar yin sanyi.

Haidar yaci gaba “That’s the reason Hisham. Wann shine dalilin.!” Ya jinina Kansa yana ci gaba da duban Hisham da ya zama speechless “Tell me Hisham. Wace irin uwa ce take ma D’anta ha

ka. Tell me.. Wad’ann mutanen su suka haife ni..? Tell me akwai iyayen da zasuyi ma d’ansu irin wann k’iyayyar..? Tell me..! Answer the damn question.!” Ya k’arashe idanunsa na kuma rinewa Kai kace zai shak’o Hisham d’in ne.

Cikeda tausayawa wann karon H

isham ke dubansa. Jiki a sanyaye yake waigawa dan ya tabbatar babu idon mutane kansu ganin Haidar d’in ya fice a giya. A hankali yake furta “Calm down Haidar.. Just try to calm down please.” Ya k’arashe yana kamo Haidar d’in had’ida zaunar dashi saman kuje

ran dake gefensu.

Haidar ya had’e duka hannayensa biyu a shafe fuskarsa da tuni ta koma jazir.

Hisham ya zauna gefensa yana k’ok’arin digesting maganganun. Tausayin abokinsa ne fal zuciyarsa. He couldn’t believe Haidar yayi going through duka abubuwan da

ya sanar dashi. Shi yana ta murna Mahaifin Haidar da Haidar sun soma samun jituwa tinda gashi har ya amince ya basa jagorancin project d’in da suka jima suna fad’i tashi akai ashe ba haka bane. Ashe sun tilasta masa signing yarjejeniyan aure ne. Ya kasa y

arda da abinda yaji. Marriage is a serious commitment abinda kullum mahaifiyarsa ke sanar dashi. Ya za’ace iyayen mutum sun masa irin wann auren.? Ya kasa yarda da abinda yaji. Sosai tausayin abokinsa ya cika zuciyarsa. Sun d’auki lokaci a haka kafin Hisha

m ya soma fad’in “I’m sorry Haidar. I didn’t know kayi going through duk abubuwan da kace. Kai hakuri Haidar.”

Haidar ya dubesa sai ya dan girgiza kai “Na riga na gama yanke hukunci. I’ll have that woman arrested. Ta haka ne kawai zan San komai. Duk wan

i k’ulli dake rufe.”

Hisham ya zuba masa ido sai ya d’an girgiza Kai kad’an “No Haidar, ka nutsu kai tunani akai. Wann al’amari ne da ya danganci ahali. you can’t involve the authorities.. I mean it might turn out to be a scandal..”

“Well I don’t give a

damn. Wann ahalin ya riga ya lalace.!”

Hisham ya girgiza Kai “No Haidar. Wann Abu ne da zai shafi rayuwarka. Ba rayuwar ahalinka kawai ba..” Yai maganar cikeda nuna kulawa.

“My life is already a circus Hisham.” Haidar ya basa amsa Kai tsaye.

Hisham ya d

’an lumshe ido had’ida girgiza Kai “No Haidar. You have no idea what you are talking about.. Haidar na taso not knowing wanene mahaifina. Ban San me ya faru a shekarun baya ba. Bansan menene tsakanin mahaifina da mahaifiyata ba.. Bansan meyasa ta b’oye min

shi ba. Iyakacin abinda na sani shine ta sanar Dani ya Mutu. Ko danginsa tak’i ta nuna mun. Rashin sanin mahaifina da asalinsa yayi affecting dina Haidar. And I am the one paying the price. Rashin sanin asalina ya janyo min setback da dama a rayuwa. Ka

yarda dani.” Ya k’arashe cikeda kulawa. Ya d’ago yana duban Haidar sosai “Haidar bana so irin abinda ya sameni ya sameka. Please mubi komai a hankali.”

Girgiza masa Kai Haidar yai “At this point ban damu ba Hisham.! I’m so tired of everything.!”

Rufe ba

kin Haidar keda wuya suka hangi Mommy da Anisa na fitowa daga mota.

Haidar ya kafe Mommy da ido yana jinina Kai. Lokaci guda yake fad’i ma Hisham “Don’t let that woman escape. I’ll be back soon.” Yana ida fad’in haka ya nufi motarsa cikin sassarfa. Hisha

m na bin bayansa yana tambayarsa ina zai je shi amma inaa ko zarafin amsa shi Haidar bai samu ba sai ma fuzgar motar da yai ya bar wajen.

Hisham ya dawo da baya yana girgiza Kai yasan shawo kan Haidar ai abu cikin lallama ba k’aramin aiki bane.

**

A ca

n company kuwa Daddy ya dubi Alhaji Gimba Ya kuma girgiza kai “Ni Aliyu Maitama ne zan d’auki k’afa na tafi asibiti duba yarinyar da Kwaise taima Haidar auren wasan yara da ita Gimba.? What for..?”

“Because she’s family. D’anka yana aurenta.. Inaga ta can

canci muje mu dubata.” Alhaji Gimba Ya basa amsa kai tsaye.

Daddy ya kuma girgiza kai “If it were up to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login