Showing 150001 words to 153000 words out of 267381 words
mahaifyarsa “Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..!” Yana ida fad’in haka ta mik’e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa fal damuwan
yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud’ad’ensa kafin wa’adin da ya basa Ya cika.
Yana ficewa Asshe ta mik’e tana tunanin abun yi. Wacece ta d’auke mata hankalin D’a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya p
arlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad’ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad’o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak’i Suwaiba da ita.
Saurin ficewa tai ta nufi nat
a sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata.
Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi.
Asshe ta shafe goshinta tace “How’s my sister doing Anisa..? Yaya ‘yaruwata take.?”
Anisa takai dubanta ga Mom
my wacce Daddy ke rik’e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk’awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa.
Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar “Your sister needs yo
u Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik’a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin
tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d’in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud’e idonta ta gane cewa ita d’in annoba ce kuma had’ari ce ga rayuwar Haidar.. A
mmi only you.. Ke kad’ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud’i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab’a yarda ba.!”
Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b’ullo mata ya wu
ce gaban tasa k’afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d’an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab’a bari Hilal dinta Ya fad’a cikin wann bala’i ba. Nan take t
a sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki.
Anisa tace da mamaki “Ammi yanzu ita Ummul d’in Har tanada ‘yaruwa da Hilal ya k’yalla ido ka
nta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud’ad’ensa.?”
Asshe tace “Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D’anuwanki kobon mahaifinku bazai c
iwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.”
Anisa ta katseta “Ammi you are wrong.!”
Asshe tace da mamaki “Mai kike nufi.?”
Anisa taci gaba “Ammi.. Bana jin Hilal yanada kud’ad’en maida ma Abba yanzu.” Tai maganar kanta staye.
Da mamaki Asshe tac
e “Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?”
“Ammi Hilal ya tura mun kud’ad’en dake account d’insa.!”
Da mamaki Asshe tace “Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?”
Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb’an kud’ad’e wajenta ita kuma tana t
ambayar Hilal.
Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai “Kin kashe ni Anisa..!” Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida masa kud’ad’en ba dole k’arshe zai fad’i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana z
ai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha’inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b’angare na auren da ‘yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn ‘yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana c
ewa ita ce sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba.
Gaba d’aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine
laifi ga d’aya b’angaren.
Anisa na kuka take fad’in “Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had’arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!”
Cak hawayen Asshe suka k’afe “Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b’ata kom
ai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!”
Anisa na kuka take fad’in “Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d’iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I cou
ldn’t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!”
Ta share hawayenta tana huci “But there’s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen M
ommy. Ba ni kad’ai Mommy zata yak’a ba Ammi.. ‘Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne.. ‘Yaruwar da ta rik’eki har kawo Aurenki.. ‘Yaruwar da ta d’aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsay
a a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.!” Tana ida fad’in haka ta kashe kiran.
Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d’aurin goro. Ta d’aura hannu biyu akai tana fad’in ‘ya’yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar
Bata tab’a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba.
Mik’ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije.
Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab’a.
Sa
ida ta Lek’a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d’aga kiran. Babu b’ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran.
Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa
. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe..
Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama “Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?”
Dije ta murmusa “K’walliya munsan
abinda muka sani dai.”
Asshe ta furzar da huci “And we have common enemy here.”
“A’a a’a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.?” Ta k’arashe tana fiddo idonta waje.
“Ina nufin munada mak’iyiya guda d’aya.. Ita ce Suwaiba.!”
Inna Dije ta murmusa
“Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon ‘yaruwa Suwaiba take min ba mak’iyiya ba.”
Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutu
wan tilon D’anki.?”
Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d’in da aka tarbeta dashi “Waye yace miki Dije tana yafiya..?”
Ta kuma gyara zama “Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D’aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son ga
ni ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!”
Asshe ta jinjina kai “Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k’asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da
zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k’asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.!” Ta k’arashe idonta tar cikin na Inna Dije.
Murmushi Inna Dije take tana dubanta “Maiyasa kika kirani.?”
“Kiranki nai mu taru mu had’a k’arfi da k’arfe mukai Suwaiba k’asa. Dan bazan
tab’a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri’arta ba. Bazan bari Alakan D’ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D’ahna ba. Bazan tab’a bari D’ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab’a bari na had’a
zuri’a da Suwaiba ba.!” Ta k’arashe tana huci.
Inna Dije ta murmusa “Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.”
Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D’anta Hilal da kudin da ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata as
iri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud’ad’ensa Har kawo auren da Hilal d’in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so ba face ‘yar Suwaiba.
Inna Dije ta sauk’e ajiyan zuciya “Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri’arki zab’i d
’aya kike dashi a nan.”
Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wane zab’i kenan.?”
“Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!”
Asshe ta d’ago da mamaki tana duban Inna Dije “Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar
da Suwaiba ke fad’i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!”
Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad’an daga cikin kujeran “Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda
nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak’i iskan ‘yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi i
rinta gogaggun mata saman fuskarta.
Asshe tai shiru kaman mai nazari. Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d’aya. Zataja layi ma D’anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zais
o mahaifinsa yasan cewa ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa kud’ad’en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk’awari baya tab’a sab’awa musamman tsakaninsa da ‘yaruwarsa. Yana k’aunar ‘yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fit
ar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d’aure Hilal.
Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k’asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai.
“K’warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na n
ufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.”
Inna Dije ta jinjina kai “Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma
yarda da sakin jiki Dani. A sauk’ak’e zamu kaita k’asa.”
Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai da yanda zasu gudanar da komai.
**
Bayan kwanaki uku da faruwan wann al’amari Tani ta shak’i iskan ‘yanci. Duk a tunanin Umma Inna
Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud’ad’ensa harda tara.
Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk’awarin zama da kowa lafiya.
A b’angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe
tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak’a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad’in “Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud’ad’en yayi amfani dasu wajen d’aukar ma surkar Haidar L
awyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d’in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d’aga koda k’adarata..”
Katseta yai da fad’in “Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud’ad’en.”
Ya dubi Hilal “Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud’ad’en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d’aukes
u matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk’uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud’ad’ena.” Yana ida fad’in haka Ya mik’e ya fice yana sab’a babbar riga.
Hilal ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud’esu ya dubi Amminsa cikin
mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa.
Kafin yai wani magana ta dakatar dashi “K’warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud’ad’en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Ku
ma nasan ko mai zai maka bazaka tab’a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba ‘yar Suwaiba.! Ka nemi ‘yar gidan ko waye ka aura amma ba ‘yar Suwaiba ba.!”
Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa “Kinyi haka ne dan ki d’aur
eni Ammi..? Sabida haka kika zab’i taimaka masu.?”
“Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark’an Suwaiba da zuri’arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai
na sa kud’i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi ‘yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda ‘yar Suwaiba ehe.!”
Ya girgiza Kansa “Kiyi hak’uri Ammi.. You don’t have to go this far.. Kimarki ya wuce
haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.
K’arshe dai Asshe ciwon k’arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar.
*
*
Abuja..
Yau kwanan Haidar ak’alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk’ufa addu’a gareshi da rok’ar masa sauk’i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Umm
ul ke kwana wajensa.
Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na’urar nasara Sun masa k’awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido.
Mommy taci gaba “A lokuta da dama mukan mance wasu ni’imomin da
Allah yai mana na d’an lokaci ne ba mai tabbata ba… Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman ‘ya’ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a’a shekaru n
awa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk’e nauyin da aka d’aura maka na hakkoki..?” Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni “Ina rok’on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haida
r a gaba.. Ina rok’on Allah Ya tashi kafad’unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib’icin Al’amaransa..” Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata “Ina rok’on Allah Ya nuna mun zuri’ar Haidar kafin na bar wann duniy
ar Ummul.. He’s all I have.. I can’t lose him..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k’ok’arin k’arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar zai tashi cik
in yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D’ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.!”
Ta d’ago tana duban Ummul wacce itama d’in Mommyn take duba hawaye fal idonta.
Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata “Na fad’a zan k’ara fad’a, kin amsa sunanki
Uwar alkhairi.. Kinzo da d’imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.!” Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d’ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba “I entrust my son to you.. Ple
ase take care of him.. Be patient with him.. Don’t let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri’a ta gari.”
Sai Ummul ta sadda idonta k’asa cikin jin nauyin Mommy.
Mommy ta murm
usa kad’an tana dubanta kafin tace “Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak’on sa yana jirana a reception.”
Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik’e ta nufi bathroom.
Koda Mommy ta mik’e sai ta nufi jikin gado
n Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta “My handsome Boy. Allah ya baka lafiya.” karanto masa addu’o’i samun sauk’i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k’auna kafin ta fice.
Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Hai
dar.
A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud’esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had’arin da sukai.
Ya tuna sanda motar ta sauk’a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da
yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na’urar dake hancinsa lokaci guda ya furta “KHAIRY.!”
A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom.
Haidar na jin an tab’a k’ofa ya kuma lumshe idonsa kif.
Ummul ta
kai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen.
Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan