Showing 246001 words to 249000 words out of 267381 words

Chapter 83 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

60

nan yanda yake kishi

ngid’e yana maida numfashi.

Lumshe idanunta Tai bayan ta fito daga d’akin tana mai sauk’e ajiyan zuciya. Haidar k’arshe ne Ya kware wajen mantar da ita duk wani b’acin rai da fushi da Ya jefata ciki a baya. A hankali ta furta “I love you.. I love you so

much my bigbaby.”

Ta tadda Baba Ali baccinsa yake Yaa Gumsu na bisa darduma da alama sallah ta ida. Bata ko bari Ummul ta zauna ba ta fatattake ta da ta koma wajen mijinta ta karada idan Baba Ali na nemanta zata kirata a waya. Cikeda kunya Ummul ta fice

ta koma nata d’akin.

Kasancewar bata tadda Haidar a d’akin ba ya bata daman fad’awa bathroom tayo wanka.

Tsaye Tai gaban wardrobe tana nema tufafi mai sauki da zata sauya. Tana nan a haka taji hannun mutum ya zagayeta Ya rungumeta ta baya had’ida manna

mata kiss a dokin wuyarta dake da dashi da dumin ruwan da Tai wanka. Tai wani irin jan numfashi a dan firgice.

Ya kaikaito da ita suna duban juna. A dan shagwab’e tace “Ka bani tsoro.”

Ya d’an Ware ido “Really I scared you..?” Yai maganar yana janyota

jikinsa sosai. Lokaci guda yai kasa da murya “Tell me, ta Ya na baki tsoro..? By… hugging you.. Or.. by… kissing you.?” Yai maganar cikin kashe murya yana kuma shigar da ita jikinsa.

Kaman zata sakar masa kuka tace “ All..!”

Ya kuma shigar da ita jikinsa

yana mai ci gaba da sumbatar wuyarta yake furtawa a hankali “I want you to scare me too.. with your sweet kisses.. Warmed hugs.. And your sincere smile..!” Ya k’arashe cikin kasheta da wani irin salo mai wuyan fasaltuwa.

Cikin k’ok’arin janye jikinta t

ake fad’in Ya kyaleta ta saka kaya.

Ya tsare fuska yana dubanta “Do you need it.?”

Cikeda kunya ta rufe bakinta da tafukan hannu tana zaro ido.

Kashe mata ido yai kafin yace “Zo muje.?”

Ta girgiza masa kai “To where..?”

“To my bedroom obviously.. I h

ave cloths for you there.”

Zata kuma magana ya duk’a gabanta yana mai kwantar mata da gadon bayansa.

Itakam dariya ma abin ya bata ganin Ya duka ya juya mata baya “Wai mai kake ne.. Meye haka.?”

“What..? D’ale mana.” Yace yana nuna mata gadon bayansa.

Murmushi mai bayyana hakwara take. Ta d’an girgiza kai kad’an tana nuni da kanta “Wai ni ce zan d’ale baya.?”

Ya d’ago gira da ido yana dubanta “Oh mamaki kike.? Of course I’ll give my wife a piggyback to my bedroom.”

Itakam dariya da kunya duk sai Ya

rufeta musamman da ta d’ale bayan Haidar d’amas ya nufi bedroom d’insa da ita.

Saida suka isa d’akin ta raina wayonta dan Haidar dai bai aje mata wani kayan sakawa ba kaman yanda yace. Kaman zata masa kuka take tambayarsa ina kayan nata suke.

Ya dan tsu

ke fuska yana dubanta “It’s not.. necessary.. You don’t need it.. You’ll be fine like this..” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda.

Kaman zatai kuka take fad’in ita dai tak’i wann wayon.

Haidar Ya janyota jikinsa yana lallashinta da fad’in yayi alk’awa

rin zasu sharing nasa kayan kafin wayewar gari. Nan kuma suka soma sinkayo kukan Baba Ali.

Ummul ta dubesa tana girgiza kai “Ka gani koh.. Yanzu ya zanyi na fita a haka.. Daga corridor fah nake sinkayo kukan nasa.. Wayyo Allah na nasan zagawa take dashi

dan yai shiru.. Ta ya zan soma fita a haka.?”

Ya kamo hannayenta “Relax Khairy.. You stay here.. I’ll go check on them. Ok.” Ya karshe yana dubanta.

A hankali ta jinjina masa kai. Ta koma tai zaune tana k’are ma d’akin kallo.

A haka Haidar ya shigo da

Baba Ali cikin hannunsa idanun yaron tar a bud’e da alama hira zaiyi. Sai cillasa Haidar yake shi kaw yaron sai k’ekata dariya yake.

Haidar Ya diresa saman gado yana ci gaba da masa wasa. Ya kwanta ringingine ya dora yaron saman k’afafunsa yana cillasa

da k’afafu. D’a da uban duk dariya suke mai cikeda nishadi. Ita kam Ummul sai suka zame mata tv dan sosai suka birgeta.

Ganin Haidar ya shagala da wasa da D’ansa yasa ta fice nata d’akin ta sako tufafi mai sauk’i.

Haidar ya dubeta sama da k’asa sanda ta

turo k’ofan d’akin. Ya dan tsuke fuska yace “Mrs Aliyu, what’s the meaning of this..?”

Ta dan girgiza Kai “Mai fah.?”

Ya mata nuni da bakinsa zuwa kayan jikinta “I mean, do you really have to wear that..?”

Ta dan rausayar da ido dan tasan rigimace kaw

ai irinta Haidar.

Sai Ya dan kashe murya yace “But still.. you look spicy..!” Ya k’arashe yana kashe mata ido. Ya dan bud’e mata hannu yace ta k’araso. Cikin tsanaki take takawa har ta isa garesa. Yai mata masauk’i zuwa b’angarensa guda yayinda Baba Ali

Ke cikin d’aya b’angaren nasa. Ya had’esu gaba d’aya ya rungume. Ya dan lumshe idonsa kadan “Finally we are together.. The three of us.!” Ya fad’i yana sumbatar su biyun.

Sosai ta shige cikin jikin mijinta ga D’anta daga d’aya b’angaren. Mai kuma zata ne

ma a duniyar nan. A hankali take furta kalmar godiya ga Ubangijinta da ya cika rayuwarta da d’imbin albarka.

Haidar ya dubeta yanda Tai lamo gefen kafad’arsa “Mrs Maitama.”

Ta amsa murya a mak’oshi kafin ta dan d’ago ta dubesa.

Haidar yaci gaba “Put hi

m to sleep now.. Let’s have our own time..” Ya k’arashe yana mika mata Baba Ali. Ba musu ta amshesa ta soma kiciniyar basa abincinsa.

Haidar ya rik’e rigar nata yana mai fad’in “Allow me.”

Batai yunk’urin hanasa ba. Batai yunk’urin dakatar dashi ba har y

a saka ma yaron abincinsa a baki da basmala. Haka Haidar yai zaune ya sakasu gaba yana kallon yanda take feeding jaririnsu gwanin bansha’awa. Sosai ya shagala da kallonsu suna k’ara birgesa Har Baba Ali ya samu bacci. Bayan ta shimfid’a Baba Ali Haidar ya

umarceta da ta d’auro alwala tazo suyi sallah. Haka kuwa akai. Ya jasu sukai sallah raka’a biyu kaman yanda yazo a sunnah. Sukai addu’o’i da duk wani abinda Ya kamata suyi. Bayan nan ne fah ta yarda lallai Haidar na buk’atan nasa lokacin. Dukda tsananin so

n kasancewa dashi take a wann daren bai hanata tuno wahalan da ya bata a kasancewarsu ta farko. Haidar ya kula da hakan. Cikin lallama da dabara yake sanar da ita it will be different from the other time. Gently yake biyeda ita. Saida ya tabbata ta mallaka

masa kanta, zuciyarta, ruhinta da gangan jikinta gaba d’aya. A haka yai leading nasu zuwa wata duniya da basu tuna kowa cikinta sai su biyun. Kaman yanda yace zai kasance na daban haka d’in ne ta kasance. Ta yarda yayi kewarta ya kuma nuna mata tsantsan

k’aunarsa gareta. He made sure wann daren zai tabbata na musamman a tarihin rayuwarsu..

A kwanakin soyayya sukaita nuna ma junansu Babu kaman Haidar da gaba d’aya ya sake rikicewa akanta. Idan suna tare basu tuna komai basu tuna kowa sai su biyun wasu l

okutan kukan D’ansu Baba Ali ke dawo dasu wann duniyar.

Sunyi nisa cikin faranta ran junansu suka sinkayo sautin kukan sa. Ummul Tai yunk’urin zame jikinta daga nasa tana fad’in zataje ta duba Baba Ali.

Rik’eta Haidar yai yana kuma shigar da ita jikins

a. A hankali yake rad’a “Do you know why he’s crying..?”

Ta dan girgiza Kai “No.. He’s hungry.. probably..!”

Haidar ya kuma matseta cikin jikinsa “Cewa yake he wants a sibling.”

Cak suka daina sinkayo kukan yaron.

Haidar yaci gaba da rikitata da sal

on k’aunarsa yana fadin “See I can read his mind.. You don’t need to go check on him.. Just stay and give him a sibling..”

Da dabara Ummul ke zame jikinta Har ta samu ta zille masa. Saida ta kai k’ofa taji ya rik’o hannunta. Ya manneta jikin k’ofa had’id

a d’ago hab’arta kad’an suna duban juna “I love you Khairy.. I love you so much.”

A hankali bakinta itama ke furtawa “I love you too.. I love you my sweet.. sweet..!” Bata k’arasa ba Haidar yai karaf yace “Your sweet mons…” Bata bari yakai aya ba tai kara

f tace “My sweetlove..” Ta k’arashe tana mai manna masa kiss a lips d’insa. Daga haka ta zame ta fice cikin sauri tana murmushi ma Haidar da tuni Ya daskare yana shafa lips d’insa.

**

Tarewarsu da sati biyu ake bikin sunan Baba Ali a nan Abuja. Su Mommy

suka hada nasu taron nan gidan Daddy. Ummul tayi waya da yanuwanta duk zasu samu halarta harda Babbar Yayarsu Aunty Salima wacce tuni ta baro yaranta gida wajen Mama Tani dan yaran ne kawai zasu samu halarta banda iyayen.

Sadis ne Ya tafi ya d’aukosu ana

gobe taron sunan. Azeema na gaba yayinda Khulsum, Badia da Aunty Salima ke baya. Aunty Salima tana hankalce da Sadis da Azeema tin tasowarsu Har kawo isowarsu. Ko ba’ace ba zata iya cewa ta fahimci meke wakana tsakanin su biyun.

Sanda suka iso Salima ta

tsare Azeema da ido bayan sunyi Sallama da Sadis Sun nufi cikin gidan.

Salima ta girgiza kai kad’an tana duban Sadis dake kuma waigowa yana satan duban Azeema. Itama Azeema sai murmushi take tana waigawa.

Salima ta tsareta da ido tace “Ke Azeema.. Wai m

eke faruwa ne a nan..?”

Azeema tace “Me fah Aunty..?”

Salima Tai mata nuni da Sadis da tuni Ya nufi mota tace “Shi nake nufi.”

Murmushi Azeema ta saki tana wani juya ido “Laa wai Sadis.. Ba komai fah Aunty Salima.. Kawai mutunci muke.”

Salima ta jinjin

a kai tana fad’in “Eh lallai fah mutunci.. Toh idan Tai tsami munji mun gani.” Ta k’arashe tana take ma Khulsum baya.

Badia kaw dake nan daga waje tin bayan isowarsu tana nan zaune gefen flowers dake jikin k’aton shataletalen dake tsakiyar gidan. Wayar U

mmul take amsawa yanda take sanar da Ummul d’in Sun iso amma Sun sauk’a gidan Daddy. Ummul kaman zatai kuka take fad’in meyasa basu taho sun sauk’a gidanta ba.

Badia tace “Ayya ‘yaruwa kiyi hakuri wllhi tin kafin mu taso Mommy ke ta waya tana fad’in tuni

an shirya mana masauk’i.. Kinsan bazamu iya ce ma Mommy a’a ba.”

Daga d’aya b’angaren Ummul kaman zatai kuka tace “Toh shikenan.. Gobe muma in sha Allah da wuri zamu shigo.. Idan mun zo Zan rok’i Mommy nasan zata amince mu taho tare.”

Badia tace “Toh sh

ikenan Allah Ya kaimu goben. Kinga bara na shige ciki sauk’armu kenan.” Sukai sallama da ‘yaruwar tata a daidai sanda wata k’atuwar b’akar jeep ta shigo gidan.

Badia ta soma tafiya kenan taji wata murya na babban mutum mai cikeda kamala na mata Sallama.

Ta waigo cikeda girmamawa tana amsawa. Dan idan dai bai kai Abbanta a shekare ba zaiyi kusansa dukda hutu da jin dad’i na b’oye tsufa.

Bayan ta gaida mutumin sai Ya k’arada “Allah sa dai ‘yar gidan ce ke.?”

Ta d’an girgiza kai kad’an “A’a ni ba ‘yar g

idan bace. Amma ciki zan shiga yanzu.”

Ya murmusa yana jinjina kai “Toh da Allah idan kin shiga kimin iso wajen Maigidan. Dan nayita neman layinsa bana samu.”

Ta d’anyi jim sai tace “Toh.. Wanene zance.?”

Mutumin yace “Kice Alhaji Gimba ne.”

Ta jinjina

kai tana mai amsawa kafin ta shige.

Alhaji Gimba yabi bayanta da kallo murmushi saman fuskarsa yana jin wani abu na fuzgarsa.

Koda Daddy ya fito ya tadda Alhaji Gimba tambayar da Ya soma yi ma Daddy shine wacece wann yarinyar da Tai masa iso.?

Daddy ya

d’anyi jim sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Bansan wacece ciki ba amma dai ina tsamman d’aya daga cikin ‘yanuwan Matar Haidar ne..” Sai Daddy ya dan girgiza kai “Amma meke faruwa..? Allah yasa dai lafiya.?”

Alhaji Gimba yai saurin girgiza kai “Lafiya

sai alkhairi.. Kawai dai.. Naga iri gidanka ne abokina.”

Da mamaki Daddy ke dubansa. Sai Ya girgiza kai kad’an yace “A’a Gimba.. You can’t be serious. Bazaka mana haka ba.”

Alhaji Gimba yace “Wllhi I’m serious Abokina.. Ai kasan ban tab’a zuwa maka da ma

gana makamancin wann ba. Ba irin k’ok’arin da bakayi ba ganin na sake aure Tun bayan da na rasa iyalina amma banyi ba. Yau nazo maka da irin batun da kake son ji kana nema ka k’aryatani.”

Daddy ya girgiza Kai “Ni ba k’aryataka zanyi ba amma matar d ka d’a

uko d’in ne ban tsammaci haka ba. Bayan kasancewarta k’aramar yarinya ka fad’a mun ta Ya zamuje muna zubda gwiwoyin mu a yanda Haidar keyi. Ta ina zamu fara jera kafad’a muna surkunta a yanda Haidar keyi.?”

Alhaji Gimba Ya murmusa yace “Abokina kenan. Nag

a dai ba haramci cikin abinda nake son aikatawa sai alkhairi in sha Allah. Sann Tafiyar Haidar daban namu daban.. Kaman yanda kaje ka nemo ma Haidar haka zaka tafi a nemo min matuk’a na samu yarda da amincewar yarinyar.

Daddy ya girgiza Kai yana fad’in “G

askiya Gimba ni baza’ayi wann kayan kunyan dani ba. Kaje can ka nemi aurenka ba hannuna.”

Alhaji Gimba Ya dan dara yana kuma fad’in lallai sai Daddy ya shige masa gaba a neman auren da yake.

Washe gari ta kama ranar taron sunan Baba Ali da Kakaninsa na

Abuja suka shirya. Sann ranar mutanen SouthAfrica wato Hisham da Anisa ke dawowa gida Nigeria.

Hisham Ya kaikaito Ya dubeta sanda jirginsu Tai landing a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport. Shu’umin murmushin nan nasa ne saman f

uskarsa “Mai ciki. Tashi ki daina baccin haka mun iso.”

Wani Uwar harara Anisa ta watsa masa tana jin kaman wani haraswan zata kuma dan tayi amai cikin jirgin yafi sau uku.

Huci take tana fad’in “Na tsaneka Hisham..! Allah ya isa fyaden da ka dinga mun.

!”

Hisham yaci gaba da murmushi yana shafa hab’arsa “Daga baya kenan… Na Miki na k’arfi sau d’aya amma duka sauran da yarda da amincewarki akayi..!” Cikeda gargadi yaci gaba “Kuma bari kiji na fad’a Miki wllhi kikayi gigin cire cikin nan ko kika bari wan

i abu ya samu cikin nan..!” Sai ya girgiza Kai yana dubanta “I don’t know what I might do to you Anisa.!”

Murmushin takaici Anisa take tana dubansa “I can’t believe I’m three months pregnant with your child Hisham. A monster like you bai cancanci zama ma

haifi ba.!”

Murmushi Hisham ya kumayi yana dubanta kafin ya sakalo hannunta cikin nasa “You won’t do anything foolish Anisa..! You will face them and act cool..!” Ya k’arashe yana mai finciko hannunta suka nufi arrivals.

Can ya hangi Mota mai d’aukeda p

late number na Company d’insu. Ya rik’o hannunta yana fad’in our ride is here.

Babu wata wata suka shige bayan motar Hisham na kuma jero ma Anisa warnings. Tana fad’in yayi kad’an ya sakata yin abinda batai niyya ba. Haka akaita shera gudu dasu sai masifa

suke tsakaninsu sam bama su kula da waye driver din nasu ba dan p cap ne akansa.

Saida akai nisa sukaga driver ya canza hanya ya d’auki wani hanyar.. Hisham ya fara fad’in “Lafiya..? Wane hanyar kake bi.. Hey who are you.. Why can’t you turn back..!” His

ham ya k’arshe yana k’ok’arin fizgoshi saidai tuni driver d’in ya murda AC din motar take wani abu kaman hayak’i ya gauraye cikin motar. Suka soma tari gaba d’aya idan ka d’auke driver d’in da hancinsa ke rufe da nose mask..

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA

UKU..!*

*62*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Suna zaune gaba d’aya parlorn Hajja a sama, hira suke na yaushe rabo cikeda nishad’i. Ga gidan tuni Ya soma cika sakamakon taron da zaayi da yamma. Dan har wasu dangi daga Maiduguri Sun samu hallara. Ko

da Haidar Ya Lek’a yaji hayaniyar mutane sai bai haye saman ba yai zamansa a parlorn k’asa. Wayarsa ya Ciro Ya tura mata sak’o.

Ana tsaka da hira sak’on Haidar ya shigo ma Ummul.

_I’m hungry_

Ta karance sak’on sai ta soma waige waige. Ta tura masa reply



_Where are you_

Ya mayar mata da amsa

_Downstairs.. Waiting for you_

Mik’ewa Ummul Tai da zummar barin wajen Salima tace ina zata suna tsaka da hira. Ummul ta d’an juya ido tana mata alama da k’asa.

Badia tai gyaran murya tace “Haba Aunty Salima sai k

in mata tonon silili ne. Wajen Oga Haidar zata.”

Salima ta jinjina kai “Haka kuma. Toh a dawo lafiya..”

Murmushi kawai Ummul tai tasa kai ta fice. Tana ficewa kuwa Salima ta dawo kan Azeema tana fad’in sai ta fad’a meke tsakaninsu da Sadis d’in can. Nan

Badia ta saka baki tana fad’in itama ta kula tsaf da su biyun. Azeema kaw sai cewa take ita ba komai tsakaninsu fah sai mutunci.

Ita dai Khulsum kallonsu kawai take jikinta duk a sanyaye ba tareda tasan dalili ba. Bata san meyasa ba amma haka kurum taji t

unaninsa Ya zo mata. Tinda ya koma makaranta bata sake ji daga garesa ba. K’ila ma Ya mance da ita. Saurin kwaban zuciyarta tai da fad’in ‘Toh ke ina ruwanki dashi.. Meyasa zakiyi tunaninsa Har haka.. Ya mance da ke kema ki mance dashi.’ Saurin mik’ewa Tai

ta bar wajen cikin k’ok’arin kawar da tunanin.

A parlor Ummul ta iske Haidar. Sanye yake da jampa ruwan k’asa harda hula. Ya turo hular saman fuskarsa had’ida kishingid’a cikin kujeran. Tai tsaye tana dubansa murmushi saman fuskarta. A hankali take takow

a Har ta iso kusansa. K’amshin ta ne yai masa Sallama. A hankali yasa hannu Ya janye hular. Ya bud’e lumsassun idanunsa yana dubanta. Tayi kyau cikin leshi golden brown color. Dinkin sosai yai mata kyau Ya zauna jikinta kaman wacce bata jima da haihuwa ba.



Ya bud’e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login