Showing 174001 words to 177000 words out of 267381 words
Not again.” Ya fad’i yana kame Kansa kad’an. Sai kuma ya dubeta a fusace “Maybe he pushed me into becoming this monster.. Don’t you think.!”
Sai ta girgiza Kai tana dubansa “A’a saidai idan hakan d’in ka zab’a. K’walla suka ciko idonta tana
dubansa. Ta rik’o hannayensa cikin nata “Shin zakaci gaba da rayuwa a bayanka ne.? Meyasa zaka bar kanka rufe cikin kurkuku.. Wann k’uncin da kake ji cikin zuciyarka ba komai bane illa kasa karb’an k’addararka da kayi. A wasu lokuta Allah yakan saka mana
jarabawar mu su zamto mutanen da suke da alak’a ta jini damu. Mutane mafi kusanci damu. Bamu ke zab’an ahalinmu ba, kuma hakan Rahamarsa ce.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba. Allah ya jarabci salihan bayinsa Annabawansa da ahalinsu. Kaman Annabi Ibrahim (A
S) Allah ya jarabce shi da Babansa. Kaman Annabi Yusuf (AS) Allah ya jarabce shi da ‘yanuwansa. Kaman Annabi Yaqub (AS) Allah ya jarabce shi da ‘ya’yansa. Kaman Annabi Nooh(AS) Allah ya jarabce shi da D’ansa. Kaman Annabinmu fiyayyen halitta(SAW) Allah ya
jarabcesa da Uncles d’insa. Duka wad’annan Annabawa masu daraja sun fuskanci jarabawa daga cikin ahali. Ashe lallai muma zaa jarabcemu daga cikin namu ahalin. Wad’ann k’alubale da jarabawa suke k’arfafa imaninmu..Sann Allah shike shiryar da Wanda yaso..” D
aga haka bata kuma cewa komai ba taci gaba da tattare kayyakin da take.
Haidar ya koma ya zauna had’ida zuba mata ido ba tareda ya kuma cewa komai ba. A hankali yasa tafukan hannayensa ya shafi fuskarsa.
**
Koda suka dawo gida maganganun Anisa suke ya
wo a kwanyarta, tayi k’ok’arin ta yakice tinanin amma ta kasa. A lissafi saura kwanaki uku kacal ta cika watanni uku da aure. Hakan na nufin alk’awarin da ta d’aukar ma mahaifiyarta yana gab da cika. Ya kamata ta waiwayi gida. Tana buk’atan sanin wani hali
ahalinta ke ciki. Musamman majinyacin mahaifinta. Tinanin kalaman Anisa suka ci gaba da dukan kwanyarta. ‘Shin Mommy ta tab’a tambayarki wani abu gameda ahalinki.?’ Tai saurin rintse idonta ta mik’e da zummar ficewa taji muryar Haidar daga bathroom yana k
iranta. Ta isa jikin closet din kafin ta d’anyi gyaran murya ta amsa. Haidar yaci gaba “Could you please pass me my towel.”
Ta shiga bin closet din da kallo tana duban yanda komai yake cikin tsari. Nan ta hangi towel d’in dan sama kad’an anyi folding an j
erasu cikin open shelf cabinet. Ta ciro towel din mai dan girma tai knocking a k’ofan bathroom din “Ga.. Gashi nan na kawo maka.”
Muryarsa ta sinkayo “The door is open.. you can come in.”
Ta zaro ido waje jin abinda yace. Sai ta soma girgiza kai ita kad’
ai “A’a.. A’a kawai ka karb’a.” Ta k’arashe tana mai tura hannunta dake rikeda towel d’in ta tsakanin k’ofar. Bata ankare ba saiji tai ya had’e da hannunta Ya janyota cikin bathroom d’in.
Ummul ta rintse idonta sosai sai ta fashe masa da kuka. ta shiga du
kan k’irjinsa “Mai kake aikatawa ne.. Dan Allah ka… k’yaleni na fice. Please..!”
For the first time da taji sautin dariyarsa. Cak ta tsaya da abinda take still ta kasa bud’e idonta.
Haidar murmushi yake Har hak’waransa na bayyana “Okay.. Open your eyes
now.. You are here already..!”
Ummul ta mak’e kafad’a tana kuma dukan k’irjinsa “A’a nidai bazan.. bazan bud’e ba.”
“Okaaaay.. Let’s see now..” “Trust me, I’m gonna make you open those eyes.” Har lokacin murmushi mai sauti mai bayyana hak’wara yake. Ab
inda Ya jima baiba na tsawon lokaci.
“Wai.. Mai kake k’ok’arin aikatawa.?”
Bai amsata ba yaci gaba da niyyansa.
A yayinda Ummul ke k’ok’arin zillewa bata ankara ba sai ji tai Haidar Ya janyota sun fad’a cikin jacuzzi tub d’in a tare.
Ummul ta ja num
fashi tana mai fiddo kanta waje had’ida shafe ruwan da Ya jik’a mata fuska.
Ta kafesa da ido baki a ture kaman zata fashe da wani kukan.
Haidar ya kashe mata ido daya “See. I told you zansa ki bud’e idonki.”
Ta soma k’ok’arin mik’ewa yayi saurin kamo
hannayenta “Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik’e.”
Baki a ture tace “Ba kaine ka jik’ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..”
“Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba.
.”
Ta d’an hararesa baki a ture “Kuma na riga na shirya.. kasa na jik’e gaba d’aya.”
Ya dan tab’e baki kad’an had’ida lifting shoulders d’insa “Shikenan sai ki sake wani wankan.” Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya “Let’s bath.. Together..”
Tu
rasa tai da duka k’arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d’insa da hannunta “Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka..” Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dari
yar.
“Don’t worry, I’ll get you next time.” Ya k’arashe yana mai mata alama da yatsarsa.
Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad’ad’ kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab’e yanda take sinkayo sautin. K’iris Ya rag
e Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen.
Tana ficewa ta d’auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad’in “No way Hisham. I can’t wait till that day.. I’m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She’s dr
iving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak’eta.”
“You will not do anything foolish.”
Ta katsesa “Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad’i ba. They were having a good time.” Ta saki kara tana fad’in “It’s so irritating.. Ka gane we can’t
let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!”
Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa “Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Ha
idar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.!” Ya k’arashe idanunsa ba kuma kad’awa in rage.
A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d’akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kw
anyarta da kunnuwarta. Ta saki k’ara kad’an tana durk’usawa wajen. A hankali take furta “I hate you.. I hate you Ummul.!”
*
Koda Ummul ta koma nata d’akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe
ido a hankali tana sauk’e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d’auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d’an man leb’e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sa
nn bai cika duhu ba ya k’ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k’abilar fulani da ta d’auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d’aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosa
i ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d’aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d’in kawai take hangowa a dun
iyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare.
A b’angaren Haidar kuwa bayan Ya d’auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa.
Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo.
Daddy ya d’ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k’ara k’arfin gani ga wad’anda shekaru Ya d’an ja masu.
Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d’anyi sa
nyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya.
Sun d’auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d’insa yace ya zauna.
Haidar ya k’arisa ya zauna.
Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin H
aidar yai k’arfin halin cewa “Daddy.. Barka da dare.”
Daddy ya amsa masa had’ida jinjina Kai.
Sai Haidar ya aje folder d’in saman table din Daddy.
Daddy ya girgiza Kai kad’an kaman Wanda yake avoiding k’wayan idon Haidar d’in “What’s this for.?”
Haida
r yai clearing throat d’insa “Yarjejeniyar project d’in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.”
Daddy sai Ya d’ago yana dubansa sosai wann karon.
Haidar sai Ya mik’e kansa a kife “I..
I’m sorry idan ban kasance wann d’an da kake fata da buri na zama ba..”
Ya soma k’ok’arin ficewa daga study d’in mahaifinsa ya dakatar dashi.
“Aliyu.!” Daddy ya ambaci sunansa.
Ya d’ago Ya dubi Daddy.
Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran “Koma ka za
una.”
Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife.
Cikin tsawa da fad’a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad’in “Ni kake ce ma ka aje aikinka..?” How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje
aikinka.? Kai har ka isa.?!”
Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse “I’m sorry.. But I can’t do it Daddy.!” Ya fad’i k’walla suna ciko idanunsa. Cak mahaif
insa ya tsaya yana dubansa.
Haidar yaci gaba da girgiza Kai “I can’t destroy you.!”
Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d’in sosai cikin tsanani shock.
“My plan was… To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind
of monster you created in me.. But then I couldn’t.. I couldn’t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak’a mai rauni cikeda tarin k’alubale.” Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad’an wann karon “I just want to be free from this
prison. I.. I don’t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own..” Muryarsa yaci gaba da rawa “I.. I’m sorry Daddy.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an dake fata da burin samu
ba.. I’m sorry idan ban kasance wann D’an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..”
Baikai aya ba Daddy dake ta k’ok’arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak’ale masa a
ido.
Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa “Aliyu, my son..”
Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D’ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba.
“Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajen
ka ba.?”
Shiru Haidar baice komai ba.
Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b’angaren da Haidar d’in yake ba “Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven’t been a good father to you.. And
I treated you badly..” Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa “Fad’an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d’in ban sauk’e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za
’a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank’a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar… Bazan iya ba..!” Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy.
Haidar ya mik’e jikinsa a matuk’ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke z
aune bisa. Duk’awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin Kansa na kife yana d’igar da hawaye.
Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d’in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya.
Daddy ya
rik’e hannayen Haidar tsam cikin nasa “I’m sorry son.. I’m sorry.. Please forgive your Dad…”
Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk’e gaban Daddy hannayensu cikin na juna.
Mommy da ta nufo k’ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D’ansu da matarsa din
ner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d’in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al’ajabi. Rana mai d’inbin tarihi.. K’afafun Mommy suka kusan gaza d’aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k’uncinta.. Sai Mommy
ta fad’i k’asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab’a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa l
allai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d’auko daga fari ta
rik’e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk’i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b’ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira.
Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d’akinta ta maida k’ofa ta rufe ta fad’a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k’wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gi
danta da ahalinta.
Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik’eda hannayen Daddy gam cikin nasa “Daddy ka daina bani hak’uri. We are all human beings.. We make mistakes. What’s important is that we learn from those mistakes.” Yaci gaba da jinjina kai a han
kali “Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should’ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad’a masa ‘A rayu
wa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood.’ Sai Haidar ya mik’a hannu ya d’auko folder d’in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da sir
aran hawaye saman fuskar Haidar yake fad’in “Daddy I can walkway from this Business because it’s my choice.. But I can’t walkway from you. Do you know why.?”
Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai “Because you are my Fathe
r.. Allah chose you for me… We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance.” Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi “Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn’t walkaway
from me either. Sabida ni d’in D’anka ne.”
Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad’in “Allah ya maka albarka Aliyu.”
**
A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya
karad’e ko ina tamkar ba dare ba.
An shirya teburin gwanin ban sha’awa ga barbecue stand daga gefe.
Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanya
r murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau.
Yana k’arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had’ida rank’wafo da kansa kusan kunnenta “You look.. Gorgeous.!” Ya fad’i
cikin sigan rad’a.
Ummul ta soma k’ok’arin turesa daga jikinta tana ‘yan waige waige “Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?”
Bai saketa ba ya kuma rad’a mata “So what.! Can’t I hug my wife.?”
Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana ams
a waya. Ta kuma duban ma’aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand.
Kaman zatai kuka tace “Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..”
Juyawa yai ya dubi kitchen staff d’in. Sai ya dan murmusa “Is that problem.? fine. Zo muje.” Bai jir
a amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma’aikatan ke gashin naman.
Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d’in.
Ma’aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad’in ita fah bata iya
amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi.
Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab’a ganin ya faru gidan ba. Basu tab’a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwa
n Ummulkhair gidan Alkhairi ne.
Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k’araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misalt
uwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad’ai.
Haidar na fad’in ta mik’a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta