Showing 117001 words to 120000 words out of 267381 words
me, ban damu Haidar yai aure ko kar yai aure ba in the first place. Dan haka ban damu da sanin halinda Haidar ka iya kasancewa ciki ba balle yarinyar
da kwaise tai masa auren shiririta da ita. Iyakacin abinda yake gaba na shine my business and my company. As long as matsalolinsu bazai affecting d’aya cikin biyun nan ba. Ban damu ba Gimba.!”
Kafin Daddy ya rufe baki Sakatariyarsa ta shigo a birkice tana
nuna masa tablet din dake hannunta “Sir I’m sorry but you need to see this.” Ta k’arashe tana nuna masa fuskar tablet d’in yanda Daddy yaga hoton Haidar an had’a da wani hoto na amarya amma babu fuskar amaryar sai na Haidar. Saman article din an rubuta *S
hahararren D’ankasuwan nan Engr Aliyu Maitama yayi auren sirri ma tilon D’ansa. Kawo wann lokaci Babu Wanda yasan wacece Amaryar ko ‘yar waye. Shin Aliyu Maitama ya aura ma D’ansa ‘yar d’aya daga cikin abokan adawarsa na kasuwanci ne dan ya ceci Kampanins
a?*
“Damn it.!” Daddy ya furta a hankali. Ya juyo yana duban Alhaji Gimba “Ka gani ko.! kaga abinda nake fad’a maka ko. Wann yaron brings nothing to me but trouble.”
Alhaji Gimba Ya girgiza kai yana kallon labarin “Yanzu zaka yarda da batu na da nace da
kai mu tafi asibitin. Rashin nuna damuwarka zai janyo hankalin press garemu. Idan son samu ne yarinyar tana warkewa ka kira koda kwaryakwaryar walima ce tsakanin business partners dinmu ka sanar da Auren D’anka.”
Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad’i
n bazai bari Haidar Ya tarwasta shi ba. A fusce ya fice Alhaji Gimba na take masa baya.
**
A can asibiti kuwa Haidar ne ya k’araso da yan sanda har guda biyu. Hisham na ganinsa da yansanda ya mik’e yana girgiza kai “No.. This is not happening.! Haidar m
ai kake shirin aikatawa.?”
Duk k’ok’arin Hisham na ganin Ya dakatar da Haidar bai nasara ba har saida Haidar d’in Ya kutsa kai cikin recovery room da aka aje Ummul.
Hisham yai wani irin burki zuciyarsa na bugawa sakamakon hango mutum da yai kwance saman
gado. Dukda na’urar oxygen dake saman hancinta bai hana zuciyarsa bugawa sau uku a jere ba. Ji yai Ya kasa jurewa Har saida k’afafunsa suka kaisa gaban gadon. A daidai lokacin da Anisa harma da Mommy suke duban Haidar cikin tsananin mamaki Wanda shigowars
a dakin kenan ga yansanda biye dashi.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*33*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Da tsananin mamaki Mommy ke duban Haidar. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta “Haidar meke faruwa. Why are the police here..? Wh
o are they here for.?”
Haidar da Har lokacin dubanta yake. Wane irin duba da za’a iya fassara sa kai tsaye da duban k’iyayya Ya k’araso daidai gabanta. Ya d’auki dak’ik’ai a haka kafin Ya rank’wafo da kansa saitin kunnen Mommy “Isn’t it obvious? They are
here for you Mommy. Sunzo ne su tafi dake.”
Mommy ta dago cikin tsananin mamaki tana dubansa. Ta girgiza kai cikin rashin yarda tana kuma duban ‘yansandan. Sai ta kuma duban Haidar cikin k’ok’arin tantance shin mafarki take ko kuwa da gaske ne hakan ke f
aruwa. Haidar ne ya kawo yansanda su tafi da ita. D’anta da ta haifa. Tilon D’anta da take duk wani fad’i tashi sabida shi a rayuwarta yau ya kawo yansanda suyi arresting dinta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Bata tab’a tsammanin za’a kawo wann gab’ar
ba. Duk k’iyayya da Haidar ke masu daga ita Har mahaifinsa bata tab’a tsammanin k’iyayyar zai tasiri irin haka ba.
“Aliyu.!” Ta ambaci sunansa cikin sanyin jiki “Ni ce ka kawo ma ‘yansanda su tafi dani.?” Ta k’arashe maganar nata tana nuni zuwa gareta d
a ‘yar yatsarta cikin tsananin shock.
Haidar da Ya kafe ta da ido lokaci guda yake jinjina kai “Remember this is a hospital Mommy. You can’t make a scene here. Ki fita ki tafi tareda ‘yansanda a tsanake.”
Mommy ta kuma girgiza kai tana jin hawaye na k’o
k’arin ciko idonta. Ta tuna shekarun baya lokacin da ta haifi Haidar. Bata raine shi ba haka bata tab’a shayar dashi drop na nononta ba. Ko zai kwana yana kuka a matsayin jariri bata tab’a attempting lallashin shi ba irin yanda uwa keyi ma jaririn ta. Bata
tab’a rungume Haidar yaji d’umin mahaifiyarsa ba. Ta tuna Asshe tasha nusar da ita cewa hakan zai iya yin tasiri tsakanin dangantakarta da D’anta domin kuwa a wann lokacin ake samun bond na uwa da D’ah. Wann shak’uwa soyayya da tausayi dake tsakanin D’ah
da uwa a wann lokacin ake building d’insa. Ba birgewa bane sabida gayu da zamani kice bazaki shayar da D’anki da kika haifa ba wai gudun kar jikinki ya lalace. Kar ki losing figure dinki koh. Toh ki sani wann ba wayewa bane ba kuma birgewa bane. Ba birgewa
bane kice ke bazakiyi d’awainiyar komai ma D’anki da kanki ba sai Nannies. At least ki samu lokaci na musamman tsakaninki da D’anki koda bazaki masa wasu hidindimu na d’abi’a ba. Ke uwa ce mai k’ok’arin k’ulla alak’a mai kyau tsakaninki da D’anki. Mommy t
a dago tana duban cikin idon Haidar Wanda sanda yake jinjiri bata bar shi ya kalli cikin nata idon ba. Bata hango tausayinta ba bata hango soyayyarta ba balle jin k’anta sai akasin haka. Saiga hawaye suna gangarowa daga idon Mommy.
“Haidar ni mahaifiyarka
ce. Ni ce na d’auki cikinka tsawon watanni tara.” Bai bari takai aya ba ya dakatar da ita “Ki aje duk wani bayananki Mommy. Wann labarin da kike bayarwa akwai ayan tambaya akansa a halin yanzu. Kuma kinsan me? Whatsoever you’re hiding sai na binciko sa th
is is just the start.” Ya dubi ‘yansandan “You can take her with you officers.”
‘Yarsandar macen ta soma k’ok’arin matsowa da sauri Anisa ta shiga tsakiya tana hawaye take girgiza kai “Don’t touch her.! Don’t you dare come near her. Do you really know who
you are arresting.?! This woman here is Hajiya Kwaise Maitama. You just can’t arrest her. Kudin zaku iya rasa aikinku gaba d’aya.!”
Haidar ne Ya matso kusan Anisa yana sakin huci Anisa ma na hawaye take dubansa cikeda firgicin yanayin da taga Haidar din
ciki.
“Who the hell do you think you are to interfere.? Get out of the way now. Or else..!” Bai kai aya ba Mommy ta katsesa “She’s my niece, and she has every right to interfere.! Unlike you she’s not ungrateful.. Wane irin D’ah ne zai kawo wa mahaifyar
sa yansanda..?!”
Jinina Kai yake yana duban Mommy “Since you went ahead and brought it up.. Are you really my real mother.? Da gaske kece mahaifiyata kodai sato ni kikai.? Tell me now Kwaise Maitama. Who are my real parents.? Where are they.? Did you kil
l them and kidnapped me.? Answer me now.!” Ya k’arashe idonsa na kuma kadawa.
Mommy ta kasa furta komai sai hawaye dake neman ciko idonta jin danta data dauki cikinsa tsawon watanni tara ta haifosa duniya na kokonto idan ita ta haifesa.
Haidar yaci gaba
da jinjina Kai jin bata basa amsa ba “Of course you don’t have the answer. But I promise you, koda baki amsa yanzu ba zaki amsa a ofishin ‘yansanda.” Idonsa na kanta yaci gaba “Officers take this woman with you right now.!”
Yarsandan ta kuma matsowa Mommy
taci gaba da girgiza Kai “No Haidar. Baka cikin hayyacinka..” Ta dubi yarsandar dake kokarin kamo hannunta ta aika mata wani kallo “You are doing this to lose your job. Do you have any idea who I am.?!”
Yarsandar ta d’anyi gyaran murya “I’m sorry Ma’am b
ut we have the warrant for your arrest.” Ta k’arashe tana k’ok’arin warware mata takardan hannunta.
Mommy zata kuma magana Haidar ya katseta “Ki adana duka bayananki har a isa ofishin ‘yansanda. Zaki sanar dasu yanda akai kika Saka guba a turaren da kika
i niyyan Kasheni dashi ta hanyar gayyato wata mace cikin rayuwana da sunan aure.!”
Mommy ta saki baki wann Karon cikin rashin fahimta “Turare kuma.? Mai.. Ni.. wane irin turare.?!” Ta k’arashe tambayar cikin rashin fahimta yarsandar na k’ok’arin janyota
ta daka mata tsawa da fad’in “I am Kwaise Maitama. You just can’t arrest me.! Idan gayyata ta ofishin ku kuke zan iya tafiya a nawa motar amma baku Kai kuyi arresting dina a k’asar nan ba. Even your superiors sunyi kad’an.!” Ta k’arashe tana sakin huci ta
fito asalin a Kwaisenta.
“And do you think you are above the law.? Just because you are rich and powerful.?!” Haidar ya katseta.
D’aya Dansanda namijin ya tare gaban Haidar yana dannarsa “Calm down Engr. If that’s what she wants let’s do it her way then.
”
Ya dubi Mommy cikin risinawa yace “We are sorry Hajiya. We understand that you are an important figure in the society. Zaki iya zuwa ofishin mu a motar ki tareda rakiyar abokiyar aikinmu guda d’aya. I hope that’s ok with you.” Ya k’arashe cikeda risina
wa.
Takaici ya cika Haidar ganin yanda ikin tsaro ya lalace wai idan kanada matsayi da mukami cikin Al’umma treatment dinka daban ne. Idan kuwa haka ne zai tabbata kudi da influence da Hajiya Kwaise keda shi baiyi tasiri a shari’an da zasuyi da ita ba bec
ause he waged a war on her. Sai yanda k’arfinsa ya k’are.
Haka suka fice salim alim dan Mommy dai bata so taja idon mutane da hankali kanta. Anisa na biye dasu tana hawaye tana ci gaba da rok’on Haidar.
Duk dramar nan da suka gama Hisham na tsaye gaban
gadon ta har dai suka fice gaba d’aya d’akin ya rage saura su biyu Hisham da Ummul dake kwance saman gado ido a lumshe.
Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa. A hankali ya soma furta “You know, when I first met you.. I told myself… Hisham, this i
s the time.. You’ve finally found her… Your soulmate.. The love of your life.. After all the rejections.. All the heartbreaks..” Muryarsa ya tike sanda ya kuma share hawayen da suka Zubo masa “Daga k’arshe ka hadu da ita. But it turned out to be the worse
of all..!” Ya kuma murmusawa yana girgiza Kai “Do you know what’s the funniest thing.. And yet the saddest.. I never got the chance to tell you how I feel about you.. It was all a dream.. Kuma zai tabbata a matsayin mafarki Wanda bazan tab’a farkawa ba.”
Ya hade hannayensa biyu alamun rok’o wasu hawayen na gangaro masa “You are now married to Haidar.. My best friend. He’s like a brother to me you know. Kuma zan iya sadaukar da komai nawa for him if I had to.. Koda kuwa rayuwana ne.. so Please ki daina zuwa
mun a mafarki na.. Please..!” Ya k’arashe wasu hawaye masu ciwo na kuma gangaro masa.
A hankali ya soma janyo k’afafunsa da k’yar cikin k’ok’arinsa na ficewa daga d’akin. Aiko yana ficewa yai bursting cikin wane irin kuka yana mai k’unshe bakinsa. Kai
da gani kasan direct daga zuciya kukan ke fita.
**
Motan Mommy da su Daddy suka gani ya fice daga hospital ga na ‘yansanda biye dasu ya sanyasu cikin tsananin shock da mamaki. Uwa uba da sukaga motar Haidar biye dana su Mommyn.
Daddy ya dubi Alhaji d
ake gefensa “What.. What’s the meaning of this..? Motar Kwaise nake gani tareda ‘yansanda.!” Ya share gumin da yaji na tsartsafowa daga goshinsa “Kwaise da D’anta bazasu tab’a barina ba sai sunga bayana Gimba.!”
Alhaji Gimba ya girgiza kai “Kar kayi magan
a haka Engr. Bamu san abinda ke faruwa ba. Let’s follow them and find out.” Ya k’arashe maganar yana mai sanar da driver da yabi bayan motocin su Mommy.
Girgiza Kai Daddy yake sanda yaga sun nufi hanyar headquarter na yansanda “What.! No way Gimba.. I can
’t be seen there.. Bazai yuwu a haskoni a ofishin ‘Yansanda ba it will be a disaster for our business. Kai kasan hakan.!” Yaci gaba da girgiza Kai yana fad’in karshen zamansa da Kwaise harma da D’anta yazo.
Wani Kayan tashin hankalin shine suna isowa kus
an kofan ofishin suka hangi masu nad’an rahotanni kowa na jefo masu tambayoyi cikin son sanin mai ahalin ke ciki.
Daddy ya shafe fuskarsa da duka hannaye biyu yana girgiza Kai. Sai wani irin huci da yake furzarwa. Ya dubi Alhaji Gimba “Saida nace maka zu
wa police station ba shawari mai kyau bane. Kaga abinda nake sanar dakai. Our company is handling one of the top government infrastructure project at the moment. We can’t afford to lose credibility a idon gwabnati.!”
Alhaji Gimba ya furzar da huci kad’an
dan shima abun na neman fin k’arfinsa. Ya dubi Daddy yace “I’ll take care of the media. Zan tabbata basu publishing wani labari ba. Wancan labarin Auren Haidar da suka daura, I’ll make sure they take it off.. Ka shiga ka samu ahalinka.. Bamu San meke faru
wa ba. Su d’in suna buk’atar ka.”
Da kyar da sud’in goshi Alhaji Gimba ya shawo kan Daddy ya amince ya nufi ofishin yayinda aka barshi nata kokarin ji da Media.
Daddy yana shiga akai directing dinsa zuwa ofishin daukan bayanai yanda akai detaining Mommy
ana koro mata laifukan da ake tuhumarta dashi ga Haidar tsaye a gefe ya kafeta da ido Kai kace shike interrogating din nata.
“D’ansandan yaci gaba “Maiyasa kikai yunk’urin kashe yarinyar.? Shin kinsan turaren da kika bata turare ne mai d’aukeda guba.”
Z
uciyar Mommy yaci gaba da tsinkewa. Shikenan boka ya sakata a uku. Ashe guba ya bata matsayin turaren da zai janyo Haidar zuwaga Ummul. Meyasa ta kasa yarda cewa boka mak’aryaci ne.? Dama da ake cewa boka makaryaci ne bata yarda ba amma yau ta yarda. Wato
ya bata turare mai guba ciki idan Ummul ta shak’a ta Mutu shikenan sai ita kuma tai zaton asirin dake jikin D’anta ne ya karye kaman yanda Bokan yace. Zatai zaton tsafin Boka ne yai aiki. Ashe ba haka bane annamimin guba ya saka cikin turaren Wanda zai aja
lin Ummul shikenan ita kuma ta hau kan aikinsa ne yai tasiri. Kai Kaicon rayuwa cikin b’ata. Gashi nan Boka mushuriki mak’aryaci ya sakata a uku, ya kulleta cikin bala’in da bata san yanda zata wanke kanta a idon mijinta da D’anta ba.
Muryar Daddy suka s
inkayo “Kisa Kwaise.?!”
Mommy tai saurin juyowa tana duban Daddy hawaye na kokarin ciko idonta take girgiza masa Kai alamun a’a.
Daddy ya dubi ‘Yansandan “Would you please, excuse us.?”
‘yansandan suka mik’e cikeda risinawa suna fad’in “Sure Sir, of
course.!”
Haidar dake tsaye gefe jinjina Kai yake yana duban Daddy bayan ‘Yansandan Sun fice “Matarka tayi attempting kashe ni ta hanyar wann yarinyar da ta auro ta kawo cikin gidan da sunan matata.. Shiyasa ta dage sai nazo gidan na zauna tareda yarin
yar. Tayi poisoning d’inta cikin turare sabida motive dinta kawai shine taga bayana. Wann matar ba ita ta haifeni ba.. Kuma yau zata fad’i a yanda ta sato ni.!”
Daddy ya Kai k’ololuwa cikin b’acin rai a hasale ya maida dubansa ga Haidar “Ka daina maganar
shiririta a nan.! Kwaise is your real biological mother. She gave birth to you. She’s your mother.!”
Ya maida dubansa ga Mommy “Tell me Kwaise, meke faruwa a nan.. Meye wann yaron yake fad’a..?!”
Mommy taci gaba sa girgiza Kai tana hawaye “Engr bansan ko
mai ba. Wllhi bansan turaren da na baiwa yarinyar matsayin kyauta akwai guba ciki ba. Why would I poisoned her.. What could be my motive.? You need to believe me. Ina son yarinyar nan like my own. Kowa a gidan shaida ne. Ita kanta Ummul shaida ce.!”
Dadd
y yaci gaba da girgiza Kai yana dubanta “You brought that girl into our family Kwaise. Bansan dalilin ki na dagewa sai kin aura ma D’anki wann yarinyar ba.”
“Her motive’s quite clear. To use her and get rid of me without being detected. Maybe she realises
that I’m no longer useful to her. That I stoped being her weapon. She couldn’t use me to get what she wants. So she decided to get rid of me…” Yaci gaba da jinina kai “When I was a child she used to call me…A useless child. Yes useless.! D’ah maras amfan
i. Haka kike kirana Mommy… Banida amfani cikin rayuwarki.. Yanzu da kika tabbata banida wani amfanin da zan miki.. I couldn’t be what you wanted me to be.. I couldn’t make you proud.! I couldn’t be just like him. Haka ne.?!” Ya k’arashe yana nuni da Daddy
hannunsa har rawa yake jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa.
Daddy ya katsesa “Enough.! I’ve had enough of you and your Son Kwaise. I won’t allow your problems to affect my business in any way.!”
Haidar na huci yake dubansa “Is this about your business aga
in Daddy..?” Yaci gaba da huci yana duban mahaifin nasa “This is about me and my life Dad..!”
“Of course I do not give a damn about you and your chaotic life.!” Daddy ya katsesa da fad’in haka cikin tsananin huci.
Haidar na girgiza Kai cikin rashin yarda
yake duban mahaifin nasa. Ya saki murmushi mai ciwo “Those words ain’t new to my ears. But I want you to keep this in mind. You can use all the power and influence you have. Amma ina mai tabbatar maka, your wife won’t get acquitted until she answers all m
y questions.! Until she pays for all the crimes she’s committed.!”
Bai Kai aya ba Daddy ya daura masa Mari maiji da lafiya su duka suna huci yayinda Mommy tai saurin mik’ewa ta shige tsakaninsu tana kuka sosai.
Haidar na jinjina Kai yake duban iyayen n
asa “All I