Showing 204001 words to 207000 words out of 267381 words

Chapter 69 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

29

karonsu da juna ba.

Anisa taja dogon tsaki ta juya Azeema ma Tai shigewarta tana kad’a kai.

Tinda suka iso gidan jikin Abba ba a sake bane. Ya kuma duban Mama Tani yace “Tani wai shin bazai yuwu mu tafi gida a

yau d’in nan bane sai mun kwana gidan sirakanmu. Ni fah sabida naga Ummulkhairi na amince na taho.. Amma ina ganin rashin dacewar hakan. Abin zai yawa ai.”

Dukda k’irjin Mama Tani dake bugawa sai tai k’arfin halin cewa “Haba Malam.. Daga sallamanka asibi

ti sai ka hau hanya.. Ai dai ka jira ka d’anji k’arfin jikin.”

Shiru yai kaman mai nazari sai Ya girgiza kai “A’a Tani.. A Ina kika taba jin Uba yaje gidan sirakansa Ya saki jiki.. Wann ai bai tsari ba… Iyakacin karamci da duk wani taimako mutanen nan Sun

mana. Kuma na shaida Ummulkhair tayi sa’an miji da iyayen miji masu dattaku da sanin darajan d’an Adam. Kinga bazan so ni kuma suga namu rashin dattakun ba.”

Tani ta d’an murmusa “Haba Malam. Kamawa fah take. Ba don jinya da Allah ya jarabceka dashi ba

da hakan bazai kasance ba. Fatanmu Allah ya k’ara maka lafiya su kuma ya biyasu Ida mafificin alkhairi.”

Sai Ya dubeta kaman Wanda Ya tuna wani abu “Na shafe watanni banga Suwaiba ba..”

Wai ance kishi dole saida Mama Tani taji zuciyarta ya d’an sosu. Sai

Tai kokarin kauda tunanin tace “Malam a yau kawai sau uku kai waya da Suwaiba.. Kai hakuri zaka ganta ne da zaran mun koma gida. Kasan Suwaiba da kunya da surkunta bazata iya zuwa nan ta duba ka ba Shiyasa bata zo ba amma ai nakan had’aku a waya tin bayan

da likitoci suka ce zaka iya amsa wayan talho haka ne.”

Abba ya jinjina Kai a hankali sai kuma yace “Ummulkhairi fah.? Kince bata iya fita ko k’ofa sabida junan da take d’auke dashi. Likita yace mai tattare da had’ari ne. “ Ya d’anyi fasali “Amma ai zan

iya ganinta yanzu.. Zan iya zuwa Har yanda take ko Tani.” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa da sandarsa.

Mama Tani ta rasa ta ina zata b’ullo masa. Mai zata sanar dashi gameda Ummul da Aurenta.?

Ganin yana k’ok’arin mik’ewa yasa Tani saurin kamo hannunsa

“A’a Malam ka dakata ka dan huta kaci abinci.. Ai.. Ai nan gidan sirakan Ummulkhairi ne.. Ba.. Ba nan bane Gidanta Shiyasa baka ganta ba.” Ta fad’i cikin k’ok’arin had’o kalaman tanayi tana kauda fuska gefe.

Abba ya tsareta sosai da ido dan yasan matar ta

sa sosai. Ya sani idan tana had’o zance.

“Tani.” Ya kirawo sunanta cikeda kulawa.

Ta d’ago ido a sanyaye ta dubesa “Na’am Malam.”

“Ina Ummulkhairi..?” Ya jefo mata tambayar.

Tani ta d’an sosa keyarta “Tana gidanta Malam. Dan Allah ka kwantar da hankal

inka. Kaji mai likitan nan yace sam shiga tashin hankali ko damuwa ba naka bane… Kaga lokacin sallan la’asar ta gabato barin taimaka maka ka d’auro alwala.” Ta fad’i tana mik’ewa.

Bayan ta masa rakiya ban d’aki ta nuna masa yanda zaiyi nan ta dawo d’akin

tana waya da abokiyar zamanta Suwaiba. Ko shakka Babu matsalan suke tattaunawa.

Sam Tani bataji fitowar Abba daga Band’aki ba sai muryarsa ta saurara yana fad’in “Tani… Mai nake ji kina cewa? Za’a sami Ummul da izinin Allah..? Tani meke faruwa..? Ina Ummu

lkhairi…?”

Ya k’arashe tambayar jikinsa na rawa daga nan yanda yake tsaye. Har sandarsa rawa take.

Murmushin da yafi kama da yak’e Mama Tani tai. Ta k’araso tana fad’in “Wai Har ka fito bakai kirana ba.”

Abba ya girgiza Kai ba alamun wasa “Baki amsa mi

n tambayata ba Tani. Da waye kike magana a waya? Sann meyasa kikace za’a samu Ummulkhair.?”

“Da Suwaiba nake magana Malam. Kuma tambayata take ko kun gana da Ummul tinda tasan kana matuk’ar son ganin Ummulkhairin.. Shine take ce min an sameta a waya nace

za’a sameta in sha Allah.” Ta k’arashe cikin k’ok’arinta na gamsar dashi.

Abba yai shiru kaman mai nazari dan Sam baijin zuciyarsa ta natsu da maganganun Tani d’in.

Bayan yayi sallah Tani ta taimaka masa suka fito parlor yaci abinci Ya sha magani.

Na

n Mama Tani ta soma waige waigen neman Azeema. Ta mik’e tana fad’i ma Abba bari ta nemo Azeema cikin gidan. Dan Sam zuciyarta bai kwanta ba da rashin ganin Azeemar tinda tasan sam ita da Anisa d’iyar k’anwar Hajiya Kwaise had’uwarsu baya dad’i.

Ficewar Ma

ma Tani da kad’an aka soma k’wank’wasa k’ofar.

Abba ya mik’e kad’an daga kishingid’en da yake. Ya bud’e idanunsa yana duban k’ofan yake fad’in “Bismillah.”

Wata budurwa ce ta turo k’ofan da Sallama saman bakinta.

Abba ya gyara zamansa yayinda murmushin

Anisa Ya k’aru tana tambayar Abban ko zata iya shigowa.

Abba ya jinjina Kai yana bata izinin shigowa had’ida amsa gaisuwarta.

Anisa ta risina yawa mutumiyar arziki tana kuma yima Abba sannu da jiki had’ida fatan samun lafiya. Harda addu’o’i ta jero masa

. Abba ya amsa cikeda jin dad’I musamman da yaga yanda yarinyar ke girmamasa sai ta tuna masa da Ummul d’insa.

Anisa taci gaba da risinawa tana fad’in “Abba ni sunana Anisa, kuma k’anwa nake ma sirkin ka Aliyu.. Sann munyi zaman dad’i da Ummul dan ha

r mun k’ulla k’awa ce da Ya zarce Ya koma tamkar ‘yanuwan juna..”

Abba yace “Allah sarki.. Toh.. Ma sha Allah.. Ai ga dukkan alamu halayyanku ne yazo d’aya da Ummulkhair.. Dole kuyi abota.”

Anisa taci gaba da murmusawa tana kuma sadda Kai.

Sai ya dan g

yara zamansa kad’an yace “Amma.. Nace ina ita Ummulkhairin.. Har yanzu ban ganta ba… Ina so naga d’iyata.. Ina so naga yanayin jikin nata.”

Anisa ta waro ido tana dubansa. Sai ta d’an waiga baya kad’an tace “Ban gane baka ganta ba Abba.. Wai har yanzu ba

su sanar dakai ba.?”

Abba ya dubeta da mamaki “Akwai wani abinda Ya kamata na sani ne gameda Ummulkhairina..?”

Anisa ta soma girgiza kai “Abba ai Ummul ta jima bata nan.. Idan ban b’ata lissafi ba mun d’ebe a k’alla watanni shida bamusan yanda take ba..”

Abba ya girgiza Kai cikin rashin fahimta yana dubanta “Ban fahimceki ba yarinya.. Kina nufin b’acewa Ummulkhairi tai baku san yanda take ba.?”

Anisa sai ta fara hawaye murya na rawa take fad’in “Abba Auren Ummul da D’anuwana Aliyu Ya k’are… Ta tafi bab

u Wanda yasan ina ta tafi..”

Daidai lokacin Mama Tani da Azeema suka shigo suka tadda Abba na dafe k’irjinsa ga Anisa duk’e wajen tana kuka.

Mama Tani ta soma salallami ta isa ta tallafi Abba dake k’ok’arin kaiwa k’asa yayinda Azeema ta tafi a guje ta s

hak’o Anisa tana tambayar mai tai ma mahaifinta.

Tani taci gaba da jijjiga Abba tana fad’in “Malam meke faruwa..? Lafiya na Barka.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Malam.!”

Ita kuwa Azeema tuni ta shak’e Anisa tana fad’in sai ta sanar da ita mai tai

ma mahaifinta..

Hayaniyar yaja hankulan mutanen gidan. Mommy ta shigo a fujajan tana tambayar meke faruwa.?

Azeema taci gaba da mak’ura Anisa tana fad’in ko ta fad’a mai tai ma mahaifinta ko itama ta shak’eta sai ta daina numfashi.

Jikin Anisa yaci gab

a da karkarwa. Fad’i take “Mommy ki yarda dani wllhi babu abinda nayi.. Gaishesa na shigo yi Ya tambayeni Ummulkhair ni kuma na sanar dashi bata nan.. Mommy bansan Mahaifin Ummulkhairi baisan meke faruwa ba.. Wllhi iyakacin gaskiyata kenan.”

Azeema ta kum

a yowa kanta tana fad’in “K’arya kike bak’ar munafuka shak’esa kikayi..”

Mommy ta daka musu tsawa da fad’in “Ya isheku dukanku..!” Ta dube Azeema tace “Maza kirawo Sadis a koma asibiti.”

Sai suka sinkayo muryar Abba yana fad’in “A’a ba sai an koma asibit

i ba.. Magana guda nake son ji!” Ya dubi Tani dake hawaye yace “Tani, ina Ummulkhairi..? Shin gaskiya ne Aurenta Ya k’are ta tafi babu Wanda yasan ina take.? Shin wann ne dalilin da yasa na kasa ganin Ummulkhair.? Shin wann ne abinda kuketa b’oye min keda

Suwaiba.? Wann ne dalilin da yasa Suwaiba ta kasa zuwa ta dubani tsawon watannin nan.? Tani mai kuka aiwatar lokacin da nake kwance..? Wane irin Aure Suwaiba da ‘yanuwana sukaima Ummulkhair da zaisa ta guji gida bayan mutuwansa.?”

Sai kukan Tani ya k’aru

yayinda jikin Mommy yai sanyi. Tai k’arfin halin k’arasowa. Ta dubi Abba sai ta dubi Tani.. Tace “Abban Ummul.. Dan Allah kar ka yanke hukunci Har sai ka saurareni… Duk abinda ke faruwa ko ince abinda Ya faru.. Babu wani mai laifi face ni.. Duka laifina ne

…”

Daidai lokacin Haidar Ya shigo. Kafin Mommy ta k’ara furta wani kalma Haidar yai karaf yace “Abba duka laifi na ne.. Ni nayi AUREN WATA UKU da Ummulkhair.! Ni nayi Aure mai k’ayadadden wa’adi da ita. Auren da zai Wanzu na tsawon Watanni uku. Ni na tila

sta mata ta Aureni dan ta Sami damar biyan kud’in jinyarka.! Na saka sadakin Ya zama kudin da za’a maka aiki dashi muddin ta amince da Aurena.. AUREN WATA UKU.. Dan na cimma burina na mallakan wani aiki k’ark’ashin kampanin mahaifina..” Muryarsa ya soma s

haking “It is all my fault.! Duka laifina ne ni Aliyu.. Umma da Mommy duka basuda laifi.. Laifin nawa ne… Da nai irin wann wulak’antaccen Auren da Ummulkhair..”

Cikin tsananin shock Abba ke dubansa. Ya soma takowa yana dogara sandarsa Har ya k’araso gaba

n Haidar Wanda tuni ta sadda idanunsa k’asa.

Abba yaci gaba da girgiza Kai yana ma Haidar kallon k’iyayya “Kai.. Har ka isa.. Har ka isa ka saka rayuwar ‘Yata a matsayin farashi.?!” Hawaye suka soma gangaro ma Abba sanda yaci gaba “Waye kai..? Wa ya baka

ikon wulak’anta rayuwar ‘Yata irin haka.! Ka amsa min waye ya baka dama.!”

Haidar ya rintse idanunsa rad’ad’in da yakeji a zuciyarsa na ninkuwa.

Abba yaci gaba da jinjina kai “Shiyasa ka d’aukoni ka kawo ni nan.? Dan ka goge zumubinka ne.? Ka amsa min.!”

Parlorn yai shiru sai hawayen dake gangaro ma Mama Tani, Mommy harma da Azeema.

Abba yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar dake tsaye gabansa kansa kife. Yaci gaba da nuna Haidar da hannunsa mai rawa “ Ka sani, rayuwar ‘Yata baida farashi.! Gwamma

ace na rasa nawa rayuwan.! Yata tana da daraja.. Tanada k’ima.. Kuma ta wuce ayi irin wann wulak’antaccen Auren da ita. Zan tabbatar maka da hakan.!” Yaci gaba da jinjina kai yana haki da kyar. Lokaci guda ya dubi Tani yace “Ki shige mu tafi bamuda wajen z

ama a wann gidan.!”

Jiki a sanyaye Mama Tani da Azeema suka nufi hanyar d’aki yayinda Mommy ke k’ok’arin shawo kan matsalar amma ko kallo basu ishi Abba ba daga ita Har Haidar d’in balle Ya tanka musu.

A haka suka fito zasu wuce Haidar yai saurin kiran S

adis a waya ya sanar dashi Ya d’aukesu komin dare ya tabbata sun isa kano cikin k’oshin lafiya da izinin Allah.

Bayan tafiyarsu a waje Mommy ta iske Haidar. Ta zauna gefensa su duka biyun ba mai cewa komai.

A hankali Haidar Ya furta “It’s so painful and

tiring Mommy…”

Ta janyosa jikinta tana Shafa sumarsa kadan “This too shall pass”

Haidar yace “Yaushe ne duka wad’ann zasu wuce Mommy.? It’s one challenge after another.”

Mommy ta jinjina kai “Wann sunnar rayuwa ce Haidar. Haka rayuwa ta gada. You canno

t expect life to be hundred percent perfect.. Dole yau idan anyi dariya wataran zaayi kuka… Yau gareka gobe ga waninka.. Tsanani yana tareda sauk’i.. Duka wad’ann zasu zo su wuce.. All you need to do is put your trust in Him.. Ka saka yardarka wajen Allah

shi kad’ai. Da sannu zai yaye mana duka matsalolinmu Ya cika ahalinmu da alkhairi.”

Anisa ta hangesu daga saman bene tana murmushin cin nasaran kauda iyayen Ummul daga cikin picture d’in. Tinda taga Mommy bata nuna mata b’acin ranta gareta ba ya kuma t

abbatar mata Mommy ta aminta da ta d’ari bisa d’ari. Yanzu ta tabbata zatai maganar Aurensu da Haidar dan dama tayi hakan ne dan ta samu ta kauda su a wuce wajen.

*

Koda su Abba suka isa Kano bai gane gidansu ba. Dan tuni an sauya fasalin gidan an d’aga

gini na zamani gaba d’aya gidan hasken lantarki irin manyan fitilun solar d’in nan sun haske gaba d’aya layin. Ya dubi Tani da mamaki ganin ta nufi wann gidan da Ya sauya fasalin unguwar gaba d’aya yace “Nan kuma ina kika kawo ni.?”

Azeema ta d’an dubes

a tace “Abba gidanmu ne fah.. Baka gane ba.”

Rai bace ya dubi Tani yace “Mai nake gani Tani.? Me hakan yake nufi.?”

Jiki a sanyaye Tani tace “Malam mu shiga mana tukuna.. Dare yayi sosai..”

Abba ya girgiza Kai cikin b’acin rai “Bazan shiga ba.. Bazan sh

iga wann gidan da aka ginasa da kudin da aka sayi Ummu ta ba.. Ki shiga ciki ki kirawo mun Suwaiba da duk wani ahalina dake cikin gidan. Ni Malam Isbusu na gama kwana a wann gidan.!”

Tani ta furzar da huci kad’an yayinda Sadis Ya k’araso yana rok’on Abba

da yai hak’uri Ya shiga gidan. Dan motan Sadis d’in ma da fari bai yarda ya shiga ba saida Sadis Ya sanar dashi ba kobon ahalin Haidar jikin motarsa kafin Ya amince Sadis Ya kawosu Kano. Da kyar, har saida Sadis da Azeema suka kirawo ma Abba Dattijan unguw

an da yake jin nauyinsa suka saka baki kafin Ya amince Ya shige cikin gidan. Ya kuma sanar da illahirin ahalinsa cewa basu ba Haidar da danginsa. Ko mai kamannin Haidar baiso Ya sake gani yazo yanda yake. Hakan yasa dole Haidar janye jiki da gidan musamma

n duba da irin yanayin rashin lafiyar da Abban ke fama dashi. Masu lalura irin wann dole lallab’asu ake had’ida guje ma duk abinda zai b’ata ransu.

Haidar ji yake tamkar Ya zama hopeless.. He’s tired and exhausted.. Ji yake Duk wani k’warin gwiwar sa da

k’ok’arinsa sun gama k’arewa musamman yanzu da ya tabbata Abba baya b’angarensa. Ya tabbata koda Khairy ta bayyana zai matuk’ar wahala abubuwa su zo masa da sauk’i.

Furzar da huci ya kumayi a karo na Babu adadi yana duban hotonsu da aka musu ranar aure d

ake aje gefen bedside lamp d’insa an saka cikin k’aramin frame.

Ya d’auki hoton had’ida k’ura ma hoton ido. Cikin wane irin siga yake furta “where are you Khairy..? Do you hate me this much.? Haven’t I suffered enough.” Ya girgiza Kai kad’an “Ya isa haka

Khairy. I’m exhausted..! Please, enough with the punishment. I can’t bear the pain anymore. I can’t Khairy..!” Ya k’arashe yana shafa fuskarta saman hoton. Ya d’an d’auki lokaci yana duban hoton kafin Ya mik’e kaman Wanda aka zaburesa. Shiryawa yai Ya fito

Ya nufi sashen mahaifinsa.

Mommy da Daddy duk suna zaune parlor. Daddy na kallon news channel yayinda Mommy ke k’ok’arin mik’ewa tana fad’in zata shiga ta kwanta nan sukaji sallaman Haidar. Suka dubi juna da mamaki kafin Daddy ya bud’e murya yace “Haida

r.? Is everything all right.?”

Haidar yace “Lafiya Daddy.. I’m sorry na shigo dare yayi.”

Daddy ya girgiza Kai “No.. No problem.. K’araso shigo mana.”

Haidar yaci gaba da takowa Mommy na hankalce dashi.

Ya zauna daga kusan k’afan Daddy. Ya gaida iyayen

nasa. Bayan sun amsa Mommy ta k’arada “Inji dai lafiya.?”

Ya d’an murmusa kad’an “Lafiya Mommy.. Dama wata ‘yar magana na shigo muyi.”

Mommy ta tsaresa da ido “Kuma maganar baza’a iya yinsa da safe ba sai cikin daren nan.?”

Daddy yace “Haba Kwaise ki k

yalesa muji binda yake tafe dashi mana.” Ya dubi Haidar “Ina saurarenka meke faruwa.?”

“Daddy dama akan Kasuwancinmu dake can SouthAfrica ne.. Ina so wann karan na tafi SouthAfrica a maimakon Kai and take care of our Business there.. If that’s ok with you

.”

Daddy yana dubansa yake jinjina Kai “Of course that’s totally fine with me. In fact abu ne da nake matuk’ar so kuma yake cikin tsarina.. But duba da yanayin da kake ciki yasa ban kawo maka wann bukatar nawa ba…”

Da farko Mommy ta nuna k’in amincewarta

a cewarta bata so D’anta yai nesa da ita musamman yanzu da rayuwa ta koma masu tamkar sabuwa. Da kyar Daddy da Haidar sukai convincing dinta da fad’in ba zuwa can zai Ya zauna gaba d’aya ba. Kaman yanda Daddy yake tafiya lokaci zuwa lokaci haka shima zai

yi.. Kuma hakan zai d’an basa dama yai taking break regarding abubuwan dake faruwa.

Da kyar Mommy ta amince ita kuwa Anisa hankalinta ne Ya tashi ganin mutumin da tayi komai dominsa zai kufce mata Ya tafi wata uwa duniyar. Saida Mommy ta lallabeta da fad

’in ba jimawa Haidar zai a SouthAfrica ba sann da zaran Ya dawo maganar bikinsu za’ayi. Kar ku mance Har kawo wann lokacin Anisa da Mommy ne kawai ke zancensu ko Haidar d’in baisan da labarin ba balle akaiga sako iyaye maza cikin maganar.

Idan Anisa ta tu

na tana tare da yarda da amincewar Mommy kawai sai taji Har ta mallaki Haidar an gama hakan yasa ta kuma kwantar da hankalinta dan tasan dik daren dad’ewa dole Haidar ya dawo ya aureta kasancewarta zab’in mahaifiyarsa. Dukda zatai kewar fuskar da take matu

k’ar so amma idan ta tuna Mommy tace da zaran ya dawo sai maganar aurensu ne tinda by then ya mance da batun Ummul sai Anisa ta tsinci kanta cikin annashuwa.

Aka bar Anisa da k’irga kwanaki tin bayan tafiyan Haidar. Daga lissafin kwanaki har ta shiga sat

ittika ta soma k’irga watanni. Hisham na sanar da ita update gameda Ummul da cikinta. Tin bayan da ya warke ya komo Abuja bakin aikinsa sann shi yaima Haidar rakiya har zuwa Airport sanda Haidar d’in zai tafi SouthAfrica.

Hisham ya sanar da Anisa da zaran

Ummul ta haife cikin zai salwantar da abinda ta haifa ya rufe Shafin Haidar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login