Showing 69001 words to 72000 words out of 267381 words
Toh amma rayuwar Haidar ake magana a nan.” Ta shiga gi
rgiza kai tana mai furtawa a hankali “A’a.. A’a bazan bari hakan ta kasance ba.. Haidar’s life is at stake here.. Bazan bari a kai masa ajalinsa ba.. I need to do something immediately.. I need to come up with something… I just.. Can’t sit back and do noth
ing.. Amma me zanyi..?”
Batakai aya ba wayarta ta soma ruri Hajiya Kwaise ke kira.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU.!*
*21*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Jikin Asshe Ya kuma yin lak’was dan gani take kaman Kwaise ta riga ta san komai. Cewa Aj
alin D’anta zata kai mata matsayin makarin asirinsa.. Har wayar ta kusa tsinkewa kafin Asshe ta iya tattara daidai gwargwadon natsuwan da yazo mata a wann lokacin. Murya a raunane ta d’aga kiran “Aunty Kwaise..”
Daga d’aya b’angaren Mommy ta kaste ta “Ass
he duk yanda za’ai Amaryar wata uku ta iso Abuja a gobe.. Asshe a yanda na hango tsananin k’iyayya a idon Haidar Ya kuma haifar min da tsoron rasa D’ana. I can’t afford to lose him Asshe. Haidar shi kad’ai ne D’ah na zanyi komai zan sadaukar da komai nawa
dan na kub’utar dashi da ahalina daga sharrin shed’aniyar can. Asshe bana so a sami wani mishkila. Ki kula da matar wata uku da kyau tamkar k’wai a hannun yaro tinda kinsan amfanin ta wajenmu. Rayuwar d’ana tamkar yana had’e ne da nata rayuwar. Har sai lo
kacin da zata karya wann asiri da aka jefesa dashi. We need to make sure ta iso a gobe cikin k’udurar Ubangiji.”
“Amma.. Amma.. Aunty Kwaise..”
“Asshe Babu wani Amma.. I cant afford to lose my son completely… Just do as I say.. The house is set. Everythi
ng is ready. Isowarta kawai ake jira na rik’e Haidar a gida kaman yanda yake bisa yarjejeniyar mu dashi. Engr ma cikin satin nan zai tafiya, Business trip. Akan Auren Haidar na hana kaina bin mijina tafiyar da zai d’aukesa makonni kinga kuwa na shirya ma w
ann aure. Na shirya karya asirin da akai ma Haidar.” Mommy ta k’ark’are wayar nata tana kuma jaddada ma Asshe lallai lallai kar a samu wani matsala.
Asshe Tai sakare tana duban wayar. Zama Tai gijif cikin gado zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Shikenan..
Ta faru ta k’are wai anyiwa mai dami d’aya sata yanzu mi zatayi..? Ba tada ikon canza komai a halin yanzu. A dole ta nad’e Ummulkhairy ta kaita ma Yayarta Kwaise. Yanzu ita meye abinyi. Anisa ce ta fad’o zuciyarta. A fili ta furta “Anisa.. Anisa zata taima
ka min na aiwatar da komai ba tareda Haidar Ya cutu ba sann ba tareda ‘Yaruwata ta fahimci komai ba. Lallai zaman Anisa a can shine kawai rufin asirina. Toh amma idan Anisa taje ta tafka wani shashancin fah.? Kuma kenan zaki sanar da Anisa komai.?” Ta soma
girgiza kai a hankali “A’a Anisa doesn’t need to know about everything. Kawai umarni zan dinga bata daga nan.” A hankali ta shiga jinjina kai kafin ta nufo k’asa.
Nan Asshe ta tadda Inna Dije ta titsiye Umma sai ta fito mata da Ummulkhairy ta tafi da it
a. Umma sai kuka take tana rok’on Mama Dije ta rufa mata asiri kar ta tona mata Auren Ummul ya mutu tun a daren aurenta kafin tafiyarta. Cikin gunjin kuka Umma taci gaba “Dije ki dubi girman Allah ki rufa mun asiri.. Wanda kika tona min ma Ya isheni
wllhi.
. Yanzu idan auren Ummul Ya Mutu Tun a daren yau da wani idanun zan kalli mutanen unguwarmu da dangi baki d’aya… Dije idan kina ma Allah kar ki d’auki Ummul.. Kar ki tafi da Ummul..”
Kaman daga sama muryar Asshe ya katse su “Babu yanda za’a tafi da Ummul
domin kuwa a halin yanzu mutum d’aya keda iko da Ummul shine mijinta..!”
Gaba d’aya suka juyo suna dubanta, daga Umman Har Mama Dije.
Asshe taci gaba da sauk’owa daga bene cikeda k’asaita. Ta k’araso gaban Inna Dije dake tsaye gaban Umma wacce ke duk’e k
aman mabaraciya tana Koke Koke.
Dije ta zuba ma Asshe idanu. Su duka biyun suna duban juna. kowacce tana sak’awa cikin zuciyarta.
Murmusawa Dije Tai tana kuma duban Asshe da kyau “Da gaske..? Bayan duk abubuwan da kika ji… Kin amince a kaima D’anki ajal
insa..? Oh! D’an ‘yaruwarki..? Haka ne..?!”
Asshe ta murmusa tana ma Dije irin duban da biri yake ma Ayaba “Ko mai zai faru a halin yanzu.. Ummul tana k’ark’ashin ikon mu ne.. Sadaki D’anmu Ya biya Wanda Ya tabbatar da wanzuwan igiyoyi Har guda uku da suk
a mallaka masa cikakken dama da iko akan Ummul. Duk wani abinda zai biyo baya, hukunci zai zamana yana wajenmu.!”
Sosai Mama Dije ta tsareta da idanu tana ji akwai wata a k’asa. Dan ta tabbata wann aure ba auren Allah da Annabi bane.. Duk yanda akai akwai
wata shiryayya. Idan auren tsakani da Allah ne bayan duk abinda ta sanar ma Asshe a gaban Suwaiba wacce take mahaifiya ga Ummul ba yanda za’ai Asshe ta amince akaima D’ansu mace irin Ummul.
Umma harda sujudusshukur tayi dan farin ciki. Ta shiga d’aga han
naye sama tana mik’a ma Allah godiya “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Allah abin godiya.. Allah gatan bawansa.. Kai amma dai annamimi baiji dadi ba.. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko fah ana Muzuru ko ana shaho sai yayi.. Kuma wllhi idan rana ta fito taf
in hannunki bata isa ta rufesa ba Dije..! Tani ma ta buga Dani ta barni balle ke..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye harda rangad’a gud’a.
“Bada garaje ba Suwaiba..!” Muryar Asshe ya dakatar da ita.
Umma ta waro idanu waje dafe da k’irji tana duban Asshe.
Sai kuma ta soma girgiza Kai “A’a dan Allah.. Ki rufa mun asiri Hajja Asshe.. Ki dubi girman Allah kar ki bari mak’iya suyi dariya.. Wllhi duk abinda kikaji daga bakin Dije ba komai bane face sharrin mak’iya..”
Asshe ta dafa Umma tana murmushi “Kin yarda
cewa aure rai ne dashi..?!”
Umma ta jinjina kai tana duban Asshe.
Asshe taci gaba “Bazai Mutu ba sai kwanakin Sa ya k’are.. Haka ne..?”
Nan ma a sanyaye Umma ta jinina Kai.
Asshe ta juya ta basu baya daga Umma har mama Dije lokaci guda tana taka parlo
rn nata a hankali take ci gaba da fad’in “Bari muce auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..!”
Dummm! Haka k’irjin Umma ya buga. Jiri ne taji na neman aikata k’asa. Ta dafe garu tana furta “Ban ban.. Ban fahimceki ba Hajja Asshe.. Mai Kike nufi da ce
wa auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..?”
Assshe ta juyo tana dubansu “Ina nufin zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal.!”
Dije ta gyara tsayuwarta sosai tana duban Asshe makirin murmushi kwance saman fuskarta. Cikin zuciyarta take furtawa ‘Eh
Lallai.. Da alama yanzu ne wasan zai d’au zafi.. Bari dai mu gani..!’
Muryar Umma ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.
“Ban.. Ban gane tsawon watanni uku kacal ba.. Me kike nufi Hajiya Asshe..? Me kike nufi da auren Ummul zai rayu ne na tsawon
watanni uku kacal..? Ki min magana dan Allah.. Ki sanar Dani mai kike nufi..?!”
“AUREN WATA UKU..! Ina nufin AUREN WATA UKU kawai mukayi ma D’anmu da ‘yarki.. Bayan wata uku.. ‘Yarki zata dawo gareki.. Sai ki shirya mata wajen zama bayan wata uku..!”
Du
niyar Umma ya shiga juyawa sama na koma mata k’asa… Ta girgiza kai tana jin hankalinta na neman gushewa da gaske. Cikin rawar murya Umma ke furta “Amma.. Amma meyasa haka Hajiya Asshe.. Shin wani irin aure kukai ma D’anku da ‘Yata… Meyasa na wata uku kawai
..?”
“D’an ‘Yar uwata yana aiki ne k’ark’ashin Kampanin Mahaifinsa. Mahaifinsa zai basa wani k’wangila ne na tsawon watanni uku kawai idan yayi aure.. Bayan wata uku zai gama wann kwangilar.. Daga nan kuma bamuda buk’atar ‘yarki dan kwangilar ta k’are.. K
in fahimta..?” Ta k’arashe tana duban Umma sosai.
Umma na girgiza kai cikeda rashin yarda take duban Asshe “Amm.. Amma.. Amma.. Bamu yi haka dake ba.. Wann zalunci ne.. ‘Yata ta jima, ta d’auki lokaci batayi aure ba.. meyasa kuka zab’i cutar mun da ‘ya..
Ummul.. Ta wahala a rayuwa, ta fuskanci k’alubale na gujewan manema.. Ta fuskanci k’alubale da dama.. Bata cancanci irin wann auren ba.. ‘Yata ta cancanci aure na gaske.. Aure mai d’orewa ba mai rabewa ba.. Shin Auren Kwangila kukaima D’anku da ‘yata..? Ha
jiya Asshe kin cuceni.!”
“Ban cuceki ba hasalima taimakon ki nayi.. Idan baki mance ba sadakin ‘yarki shine kud’in jinyar mijinki.!”
“Wani irin taimako ne wann..? Wane irin taimako ne haka.. Wann zalunci ne ba taimako ba..”
A zuciye Asshe ta katseta “Ka
r ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D’ana auren cikan buri da ‘yarki ko kuma keda kika cuceni kika sakani a tsaka mai wuya, nai jagoranci wajen aura ma d’an ‘Yaruwata wa
nn ‘yar taki mai lullub’e da Illan asiri da farar k’afa.. shin ki fad’a mun… Tsakanin mu biyun waye ya cuci wani..? Rayuwan d’ana yana tsaka mai wuya a nan.. Idan Haidar Ya Mutu ‘yarki ce Sila.. Shin banyi adalci ba da nace zata zauna na tsawon watanni uku
..?!”
Umma taci gaba da hawaye tana duk’e wajen.
Asshe taci gaba “Ki gode ma Allah.. ‘Yarki bazata fuskanci tozarci na mutuwan aure a daren aurenta ba.. Ki gode ma Allah bayan duk abubuwan da kikayi ‘yarki zata zauna k’ark’ashin Inuwan aure na tsawon wat
anni uku.. Ki gode ma Allah bazaki fuskanci dariya da gori harma da wulak’anci idan har auren ‘yarki Ya Mutu a daren yau ba.. Domin kuwa duk wani Sirrinki da naji sai na bankad’e.. Kuma Kinsan me..?” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Umma dake duk’e tana
hawaye “Zaki amar da duk wasu kud’ad’en da na kashe wajen nema ma D’an ‘Yaruwata auren ‘yarki. Kaf ko kobo bazan bari yai ciwon kai ba.. Kin shirya biya.?” Ta k’arashe tana tsare Umma sosai da ido.
Inna Dije ta k’arada “Daga nan kuma sai kiyi bankwana da
Mijinki Suwaiba bayan kin rasa yaranki. Dan bayan abinda Ya faru ki sani zan d’auke D’anuwana na masa jinya bazan barshi tsakanin mata guda biyu da Babu Allah cikin zukatansu ba..!”
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Dije da Asshe “Dan All
ah.. Kar ku jefa rayuwata cikin garari.. Kuji tsoron Allah.. Kuji tausayin rai.. Ku tuna kuma iyaye ne.. Kuma burin ko wace uwa ta kai ‘yarta d’akin miji.”
“Kar kiyi mana maganan zama iyaye a nan.. Domin kaw baki tab’a zama uwa ga ‘ya’yanki ba Suwaiba.. K
uma yau zaki fara girban duk abinda kika shuka..!” Dije ta k’arashe tana sakin huci.
Asshe ta gyara tsayuwarta “A tsakanin watanni ukun ma inada sharud’a.. Dan Kinsan a daren nan zan iya kashe auren ‘yarki Suwaiba haka ne..?!” Ta k’arashe tana duban Umma
kannare da idanu.
Umma ta share hawayenta tana kuma jinjina kai a hankali kaman marainiyar mage.
Asshe ta jinjina kai “Shradina shine bazakiyi magana da Ummul ba har na tsawon watanni Uku. Ina nufin iyakacin wa’adin zaman da zatai da D’anmu. Keda had’u
wa da ita kuma sai kwangilar D’ana Ya k’are randa Ya cika aikinsa ya warware auren.. Ni kuma zan d’auko ‘yarki da kaina na kawo miki ita cikin mutunci. Kin amince..?”
Umma ta d’ago a raunane tana duban Asshe jin da gaske dai Auren wutin gadi Ummul tayi ba
kaman yanda taci mata buri ba. Sann ga wasu dokoki da sharud’a Wanda aka gindaya na datse alak’arta da ‘yarta “Dan Allah kar kiyi haka.. Kiyi hakuri… Kar ki rabani da Ummul.. Wllhi Ina son ‘Yata..”
“Na zata kinfi so tayi aure tayi nesa dake… Ko ba haka b
ane..?” Asshe ta katse ta.
Umma ta kuma rintse idanunta tana hawaye.
Muryar Inna Dije ya katseta “Burinki Ya cika Suwaiba.. Mata mazan ‘yarki tayi aure.. Amma aure mai gibi.. Wanda bada jimawa ba angulu zata koma gidanta na tsamiya..” Ta murmusa kafin t
aci gaba “Inama zanga Tani na bata wann babban Albishir..!”
Umma ta shiga d’ago hannaye daga duk’e tana rok’on Dije “Dan girman Allah ki rufa mun asiri Dije.. Kar abinda Ya faru yau ya fita ko ina.. Dan Allah Ku rufa mun asiri.. Wllhi na amince zanyi duk
abinda kukace.. Amma kafin nan dan Allah ku barni nai Sallama da Ummul.. Ku barni nai Sallama da ‘Yata..!”
Dije da Asshe suka dubi juna kafin Asshe ta jinina kai “Kinada minti talatin kacal kiyi Sallama da ‘yarki.. Sann ki aje wann a ranki.. Kaman dai yau
nan da watanni uku zaki sake had’uwa da ‘yarki.. Watak’ila had’uwa ta Har abada..”
Umma ta shiga jinina kai tana godiya. Jiki Babu laka ta mik’e ta nufi sashen da aka aje Ummulkhairy.
Umma tana shigewa Dije ta juyo tana duban Asshe duban irinta gogaggu.
Dukansu biyu suka tsare juna da idanu. Kai da gani zaka fahimci wann ta naima wann kallon biri ne waccan tanai ma d’aya kallon ayaba. Ko wacce irin duban da take ma juna kenan.
Dije ta murmusa tace “Kin d’auki kasada mai girma ma d’anki dukda na sanar d
ake ga abinda Ya samu nawa d’an.. Meyasa..? Meye dalinlinki..?”
Asshe ta murmusa irinta gogaggun wayayyu “Aw.! Baki yarda da hujjata bace..? Cewar auren kwangila na tsawon watanni uku mukai da ‘yarku.?”
Murmushi Inna Dije Tai “Kar kiyi zaton wayewarki za
isa ki shashashantar Dani kamar yanda kika shahsantar da Suwaiba.. Ni ba Suwaiba bace.. K’ar nake kallonki.. Dan haka Ki sanar dani meye asalin dalilinki.. Dan babu wanda zaiji abinda na fad’a Ya kuma amince D’ansa ko wani nasa yai tarayya da Ummul.. Bayan
jifa na asiri dake jikinta ita d’in barazana ce ga rayuwarsa.. Anya akwai wacce zata amince wani nata Ya zauna da Ummul matsayin matar aure..? Ko da yake ba d’anki da kika haifa bane.. D’an ‘Yaruwarki ne.. Tabbas akwai banbanci.!” Ta k’arashe shu’umin mur
mushi saman fuskarta.
Asshe ta murmusa “Jifa na asiri..? Toh kodai kece kikai jifan.. Dan idan Har Zan amince D’an ‘Yaruwata ya auri ‘yarku mai tawaya na asiri.. Bana jin akwai wacce zata tona ma ‘yar D’an uwanta asiri irin haka.. Kaman dai yanda kikai ma
Ummul.. Da ni dake dukanmu ‘Yanuwa ne ga iyayen Ummul da kuma Haidar.. Haka ne..?”
Dije Tai shiru tana duban Asshe. Ta kula su duka biyun Sun k’ware a iya buga wasan. Tabbas kuskure kad’an zatai gaban matar nan ta sha k’asa.. Koda wasa bazata bari hakan
ta kasance ba. Gwara ta gyara d’amararta da kyau.
Murmusawa Dije tai tace “Af! K’warai haka fah.. Magana ake na gwaggwani da Innoni.. Wanda yafi nuna kula ga nasa.. Tabbas shi zai d’auki kambin.. Mai zai faru idan na tafi na samu ‘yaruwarki na sanar da i
ta ga abinda kika shirya ma D’anta… A bayan idonta..?” Ta k’arashe tana tsare Asshe da idanu ga muguwar murmushi saman fuskarta.
Asshe ta d’an d’auki lokaci tana dubanta. Dukda bugu da zuciyarta keyi bai hanata tattaro natsuwarta ba dan bata so ta bama D
ije k’ofan da zata d’ago rauninta. ta murmusa tace “Wai ance da D’an gari akanki gari.. Kin tab’a jin an shiga gari yak’i Anci yak’in ba tareda taimakon D’an gari ba..? Ina nufin kinada masaniyar wace irin yarda ce tsakanin ‘yanuwa biyu.?” Ta k’arashe tan
a tsare Dijen da idanu itama..”
Su dukansu biyu suna duban juna. Asshe ta murmusa ganin Dije bata bata amsa ba. Ta k’araso ta dafa Dije kad’an “A shawarce “Kowa ya tsaya a masarautarsa , Ina nufin kiyi yanda kikaso da Suwaiba harma da D’anuwanki.. Kar ki
shiga tsakanina da ‘Yaruwata.. Dan nasan bazaki so yin wasa da wuta ba..”Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Dije ta murmusa “D’iyar mak’eri bata shakkan wuta.. Hasalima ta saba wasa da wuta.. Kiyi tunani kan abinda na sanar dake. Domin kuwa kaman yanda
kika amshi bak’oncina cikin gidanki ba tareda kin gayyaceni ba. Toh ina mai tabbatar Miki zan kai ziyara ma ‘yaruwarki ta birnin tarayya.. Ina nufin mahaifiyar surkinmu.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Shiru Asshe tai zuciyarta na kuma bugawa. Lall
ai wann matar babbar barazana ce a gareta. Dan tabbas idan ta tafi ta samu Kwaise ta sanar da ita abinda ke faruwa toh fah tata ta k’are. Sosai tai nisa cikin duniyar tunanin yanda zata b’ullo ma wann Dijen wacce ta zamto babban threat a gareta.
Inna Dij
e ta gyara zaman mayafinta “Kiyi tunani da kyau.. Ni zan tafi.. Dare yana yi.. Amma kafin na tafi ki zuba mun lambobinki a nan.. Sabuwar k’awata..” Ta k’arashe tana duban Asshe da ta zama deep in thoughts.
Asshe ta dubeta irin duban baki kai ki shiga jer
in matsayin kawayena ba.. Sai kuma ta murmusa abinka da gogaggiya “K’awa..? Oh haka ne… Ta bayan fage..!” Ta k’arashe maganar tana Shafa kwantattun gwalgwalan dake zube wuyanta zuwa kunnuwanta da hannayenta. Dije sai dubanta take tana jinina barikin matar
nan. Watau bazata fad’a mata matsayinta da baki ba saidai yanayin shigarta da suturan dake jikinta Ya tantance hakan.
Lokaci guda ta d’auki wayarta ta mik’a ma Inna Dije “Zuba min lambobinki a nan..”
Inna Dije ta murmusa kafin ta dubi wayar kaman zata a
msa sai kuma ta tabe baki tace “Baki tunanin ban Saba da rik’e irin wayoyin nan naku ba.. K’awa..!” Ta k’arashe tana juya mata gajiyayyar wayar dake rik’e hannunta harda d’aurin robber ring jiki.
Asshe ta murmusa tace “Gashi Ba hand sanitiser kusa, bara
na sanar dake da baki sai ki juye a naki wayar.. Ya Miki..”
Dije ta jinjina kai “Kar ki damu.. matuk’a bazaki lank’wasa harshe ba.. Anyi alimantari an samu na zama cikin Al’umma.. Kar ki mance lambobin gaske zaki bada dan idan