Showing 81001 words to 84000 words out of 267381 words
tsammaci maganganu irin wad’ann daga bakin bagidajiyar Amaryar Haidar ba.
Ganin t
ayi sakare yasa Ummul kuma murmusawa ta k’araso kusanta “Ni sunana Ummulkhairi.. Watak’ila nasan kin sani Shiyasa baki tambaya ba.” Har lokacin sassanyar murmushi ne saman fuskarta Wanda ba k’aramin tunzura Anisa ya kuma yi ba.
Ganin Anisa tayi Shiru yas
a Ummul katse shirun da fad’in “Yauwa gwara da Allah yasa kika shigo.. Dan Allah ina ne band’aki wllhi tun d’azu nake so na tashi nayi sallan isha amma bansan ta ina zan shiga ba.”
Hararta Anisa tai daga sama zuwa k’asa “Ina Miki kashedi, kar ki kuskura k
i shiga d’akin cen. Dan wann d’akin d’akin Haidar ne.” Ta k’arashe tana nuni da d’akin.
Ummul ta murmusa kad’an “Ok haka na nufin wancan kenan zan shiga.” Tai nuni da d’aya k’ofar.
Takaici ya kuma cika Anisa ganin da gaske Ummul bata d’auketa da zafi ba.
Taja tsaki tana juya ido kafin tasa kai zata fice.
Ummul Tai saurin dakatar da ita “Kinga.” Anisa ta juyo tana dubanta a dak’ile.
“Na gode.” Tai maganar har lokacin kyakkyawan murmushin ne saman fuskarta wanda ko shakka babu k’ok’arin b’oye tashin hank
alin dake saman sa take.
Wani tsakin Anisa ta kumayi kafin tasa kai ta fice a fusace.
Sauk’e ajiyan zuciya Ummul tai tana mai hamdala cikin zuciyarta. Dan da dai tai tozali da mijin da aka aura mata, gwara taita karo da wann figaggiyar. Dan idan fad’a d
a tashin hankali ne zata iya cewa cikinsa ta girma. Amma miji bata san mai zata tarar ba. Bata san wani irin k’alubale zata fuskanta tare da shi ba. Haka zalik’a zuciyarta Sam ya gaza natsuwa dukda kwantar mata da hankali da mahaifiyarsa tai. Ta kuma sauk’
e ajiyan zuciya a hankali kafin tasa kai ta nufi d’aya d’akin hagu da wanda Anisa tai nuni dashi matsayin na Haidar.
Kaman mai tsoron shiga haka ta tura k’ofar. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Sai addu’an neman samun salama had’ida natsuwa take cikin z
uciyarta take. D’aki ne mai matuk’ar kyau da tsari komai na ciki sabo ne dal da alama. Tai tsaye sororo tana duban d’akin dan ita dai bata San ta ina zata fara ba. Abinda ta soma tunowa shine gadon baccinsu ita da ‘yaruwarta Khulsum. Shikenan Sun rabu. Ta
rabu da kowa nata kenan kaman yanda Umma ta umarceta. Shikenan ba ita ba danginta. Wani hali Abba yake ciki.? Yaya yanayin k’arfin jikinsa.? Umma ta mata iyaka dasu gaba d’aya tace ko a waya kar ta nemesu idan har ita ta haifeta. Sai taji k’afafunta Sun ga
za d’aukarta. Nan ta silale wajen kuka na zuwa mata gadan gadan.
**
Kano…
Har ta kwanta wajajen misalin k’arfe shad’aya na dare taji ana buga mata k’ofa. Ta mik’e da kyar tana mamakin waye haka cikin daren nan. Bata kawo kowa ba sai Khulsum tinda ita
ce tazo mata cikin dare irin haka a kwanan baya.
Ta k’araso tana tambayar wanene lokaci guda tana ci gaba da fad’in Khulsum kece nan wajen.
Ga tsananin mamakinta muryar D’anta Hisham taji. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa.
“Hisham.!” Ta furta a hank
ali
Hisham yace “Hajja ni ne.”
Ta bud’e k’ofan tana dubansa da mamaki “Lafiya kai kuma cikin daren nan.. Watau bazaka daina irin wann tafiyar naka ba ko.”
Murmushi Hisham keyi yana duban mahaifiyar tasa “Haba Hajjata tarban da za’a min kenan. Hajja ko
shigowa gidan banyi ba fah balle na sha ruwa balle mujega gaisuwa.”
K’wafa tai tana dubansa kafin tasa kai ta shige tana ci gaba da sababin yanda ya maida tafiyan dare d’abi’arsa.
Hisham ya maida k’ofan ya rufe kafin ya take mata baya yana fad’in Allah y
a huci Zuciyar Mamanshi tuba yake.
Sukai zaune a parlor suna gaisawa bayan ta gama sillesa tas kan yanda ya maida tafiyar dare jiki musamman duba da yanayin hanoyin a yanzu.
Hisham ya tsareta da ido. Shi sai lokacin yake hango rama tattare da ita.
Ta
d’an kuma dubansa “Waima mai Ya dawo dakai ne.? Inji baka jima da komawa bakin aikin ba. Kai da kanka kace kunada babban project a kampanin ku zaka tara hankalinka waje d’aya. Toh me ka dawo yi.?”
“Hajjah..” Ya kira sunanta a hankali.
Sai ta d’ago ta du
besa ganin sosai ya tara hankalinsa.
“Wani abu ya faru ne da bana nan.?”
Tambayar da yai mata sai taji tamkar yana sane da cewa Ummul tayi aure ne kuma ba kowa ta aura ba face D’anuwansa da suke Uba d’aya. Ji tayi kaman d’an nata Ya riga yasan sirrin da
ta jima tana b’oye masa.
Ta girgiza kai a d’an daburce “Mai ka gani.. Kaga ni bacci nake ka katse min. Ko ma meye mayi magana da safe. Tashi kaje ga abinci a kitchen sai kai warming kaci tinda kai ka so zuwa cikin dare. Idan bai maka ba kasha ruwan shayi
dama abinda ka Saba kenan.”
Hisham Ya girgiza kai. Tana k’ok’arin mik’ewa yai saurin k’arasawa Ya rik’e hannunta “Hajjah you look sick. Kinyi ciwo ne sanda bana nan..?”
Ta sauk’e ajiyan zuciya jin ba Ummul ya tambayeta ba wanda ba grin Allah da zai way
e suyi waya bai tambayeta ita ba. Yaso karb’an lambar wayarta ma sai Hajjan ta sanar dashi Ummul batada waya. Yaita mamakin ya za’ace budurwa kaman Ummul ba waya a hannunta.
“Eh.. eh nayi dan zazzabin nan da ake fama dashi. Amma bai wani tsanani ba. Shiy
asa ma ban sanar dakai ba gudun kar ka tashin hankalinka ka d’ago k’afa kazo. naji sauk’i Alhamdulillah.”
Hisham Ya girgiza kai “Haba Hajjah. Har kiyi ciwo ban sani ba.. Hajja a duniyar nan sabida wa nake neman duk abinda nake nema. Hajja sabida kece.. La
fiyarki na gaba da komai da kuma kowa. You are my number one priority kin sani..” ya kuma girgiza kai “Da ace wani abu ya faru dake da bazan tab’a yafe ma kaina ba.” Ya k’arashe fuskarsa fal damuwa.
Sai ta k’ura ma d’an nata ido ganin yanda hankalinsa ya
matuk’ar tashi a sabida ita. Koda duka duniya zasuyi rejecting d’insa zata so shi ta k’aunace shi domin kuwa Hisham d’inta definition ne na d’a na gari a idonta.
Ta d’an dungureshi “Silly. Ba abinda zai sameni da izinin Allah sai naga ‘ya’yanka.”
Ya m
urmusa yana duban mahaifiyar tasa cikeda so da k’auna “And very soon zaki gansu in sha Allah. Dan wann karon na d’au d’amaran neman aure da gaske. Bazan koma ba sai na tabbata an bani ita.” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Zuciyarta yai wan
i irin tsinkewa. Take annurin fuskarta ya d’auke cak. Ta soma k’ok’arin kauda fuskarta dan bata so su had’a ido. Hasalima bata san ta yanda zata soma sanar dashi labarin Auren Ummul ba. Shin da wanne zata fara.? Cewa Ummul tayi aure ko kuma D’anuwansa da b
aisan yana dashi ba ta aura. Shin mahaifinsa tasowa yai daga kabari kokuwa dai yana raye tintinin.
Zata mik’e Hisham yai saurin dakatar da ita ganin gaba d’aya yanayinta Ya sauya tashi guda “Hajja na fad’i wani abu ne da bai dace ba.?”
Girgiza masa kai
tai “Hisham kaje ka kwanta dare yayi.” Tana fad’in haka ta mik’e ta shige d’aki ta barsa nan wajen yana sak’e sak’e. Fatansa Allah sa dai lafiya ba wani abun bane ya faru. Jiki babu wani kuzari Ya mik’e Ya nufi nasa d’akin.
**
Washe gari Inna Dije bata
Ida warwarewa ba sai a cikin mota bayan Sun d’auki hanya sunyi nisa. Ita kad’ai sai layi take dan baccin bai saketa ba. Haka Asshe da Anisa suka turata cikin mota. Ko zarafin Sallama da Ummul basu barta tayi ba.
Saida sukai nisa Abadan kafin Inna Dije t
a ida warwarewa. Ta dubi Asshe dake gefenta da mamaki tana kuma duban cikin motar.
Asshe ta karyi goron dake hannunta dan galibi idan zatai tafiya mai tsawo da goronta cikin jaka. Ta murmusa tana duban Inna Dije “Barka da safiya K’awalliya.”
Inna Dije ta
kuma dubanta da mamaki sai lokacin take tuno duk abubuwan da suka faru.
Asshe ta murmusa had’ida mik’a mata goro “Karb’i ki karya kumallo.”
Inna Dije kallon mamaki kurum take ma Asshe Har lokacin. Ta dubi goron da take mik’a mata “Kin bani k’waya cikin
dare yanzu zaki had’a min da goro ki k’arasa kasheni. Makira algunguma.!”
Asshe ta dara kad’an “Haba K’awalliya wasa fah ake bugawa. Da sauran lokaci ai ba’a gama ba. Kika sani ko anjima ki lallasa ni.”
Inna Dije tace “Ina muke..?”
Asshe ta kuma karya
r goronta “Kar ki damu mun kusa isa gida nasa a shirya Miki karin kumammalo mai kyau gudun kar kiyi mutuwar bakin al’muru.”
Inna Dije ta girgiza kanta Wanda Har lokacin nauyi Ya mata “Yanzu sabida rashin imani naki Asshe shine kika bugar dani ko sallan a
suba banyi ba kika nad’oni kika saka cikin mota.. Toh ina jakan kayana.?”
Asshe ta tab’e baki “Buhun tsummokaranki zakice. Wari suke min a mota nai watsi dasu. Kar ki damu sabbi suna jiranki idan mun isa. Yanzu bari a samu waje a tsaya kiyi sallah tinda k
in dawo hayyacinki.”
Inna Dije sai kallon mamaki take ma Asshe dan ta fara zarce tunaninta.
Koda suka iso Kano kai tsaye gidan Asshe suka nufa. Inna Dije ta samu ta saka abu cikinta sann tai wanka aka bata tufafi ta canza.
Asshe ta k’araso tana duban
ta lokaci guda tana tinda ransa Suwaiba ta soma zuwa gidan.
Murmushi ta sakar mata ganin ta shirya tsaf “Ko kefa K’awalliya. Kin ganki kuwa..”
Inna Dije ta d’aga mata hannu alamun dakatarwa “Ke ni fah ba Suwaiba bace. Babu wani makircinki da zai bani ts
oro. Bazan bari na sake fad’awa tarkonki ba. Mijina baisan nayi tafiya ba a nasa tunanin ina tare ne da d’a uwana. Ni ba ballagaza bace kaman Suwaiba.”
Asshe ta murmusa “Ashe duk kanwar ja ce.”
“Mai kika ce.?” Inna Dije ta katseta.
Asshe ta kuma murmusa
wa “A’a K’awalliya cewa nai idan kin gama Hilal sai ya kaiki masaukin ki.”
Zata fice kenan Inna Dije ta janyota. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kinyi kuskure tinda kika kaini naga gidan. Watak’ila kin lashe wasan a wann karon. Amma ki kiyayi karawa na g
aba. Abun bazai miki da kyau ba. K’walliya.” Ta k’arashe harda kashe ma Asshe ido.
Sai Asshe ta murmusa su duka biyun suna k’are ma juna kallo.
“Kar ki damu na Miki alkawarin babu had’uwa na gaba. Dan kafin wann lokacin zan tabbata ‘yarku ta fice daga
rayuwar D’anmu. K’awalliya.” Asshe tace tana mai ficewa. Lokaci guda ta kira Hilal Tai masa umarni da yakai Inna Dije Asibitin koyarwa.
**
Cikin sand’a Umma ke takowa ta nufi k’ofan d’akin Abba tana addu’an Allah yasa kar ta tadda Dije.
Ai kaw tana t
ura k’ofan a hankali taga Babu kowa sai Abba dake kwance shi kad’ansa.
Tai k’uri tana dubansa sai taji hawaye na neman ciko idonta. Rayuwarsu na baya taketa tunowa da yanda burin son ganin ta aurar da Ummul ko ta halin k’ak’a ya rufe mata ido. Ta share h
awayen da suka zubo mata tana neman afuwan mahaliccinta cikin zuciyarta. Cikin sand’a tamkar mai tsoron kar wani ya ganta ta shigo d’akin. A d’arare ta zaune gefe dashi. Tana hawaye take furta “Abban Ummul ka yafe mun. Na tapka kuskure mai girma. Kuma nasa
n ni ban cancanci yafiya ba.. Amma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Saida tai mai isarta kukan da ba sauti kafin taci gaba “Bazan gushe ba Ina maka addu’an samun lafiya mijina.. Hak’ik’a duniya makaranta ce kuma naga izna akan hakan. Duk abubuwan da na
aikata Sun dawo gareni harda tukuici. Kaico na.. Kaicon irin wann rayuwa. Kaiconki Suwaiba.!” Ta k’arashe tana toshe bakinta dan kuka ne na gaske ke zuwa mata.
Shigowar Khulsum kenan ta hangi Umma zaune gaban gadon Abba tana shesshek’ar kuka.
Khulsum
Tai saurin k’arasowa ta raba tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta.
Umma ta d’ago jiki a sanyaye tana duban Khulsum wacce itama d’in ita take duba saidai babu d’igon annuri a fuskarta.
“Khulsum..!” Umma tace cikin tsananin rawar murya.
Khulsum ta girgiza
mata kai “Umma me kikeyi a nan.. Dan Allah ki tashi ki fita kafin Inna Dije ta shigo ta taddaki. Dan yau ta sanar Dani zasu dawo tareda ‘Yaruwata wacce kikai mata auren rashin galiho. Inna Dije tace bazata bari aci amanan mahaifinmu dake kwance ba. Tace ba
zata dawo ba sai tareda ‘Yaruwata wacce kika rabamu da ita sabida son zuciya irin naki Umma.” Khulsum ta k’arashe hawaye na gangaro mata yayinda Umma ma ke hawaye tana jinjina kai. Dan a halin yanzu ita dai kam tasan batada wani hujja ko kalamai da zatai a
mfani dasu dan ta wanke kanta. Ta kuma san sai yanda k’arfin Dije ya k’are wajen ganin ta rabata da ahalinta.
“Umma dan Allah ki tashi ki fice.. Bamu neman wani tashin hankali a nan..” Khulsum ta sake fad’i cikin rawar murya.
Jiki a sanyaye Umma ta mik’
e sai ta ajiye ‘yar kular da ta shigo dashi na abinci Wanda ta kawo ne ma Khulsum d’in.
Duban foodflask d’in Khulsum Tai ganin Umma takai k’ofa tai saurin dakatar da Umma kafin ta d’auki kular ta mik’a mata “Kin mance wann Umma. Idan dan Abba kika kawo b
aici.. Idan kuma sabida ni kika kawo kiyi hak’uri nima bana buk’ata. Ci na ko shana bai tab’a damunki ba Umma. Abu d’aya ne damuwarki a gidan duniyar nan shine ki aurar da ‘Yaruwata.” Tai murmushi mai ciwo “Auren da kikai ikirarin kin rabu dani akan shi Um
ma.. Wacce Har zaki mata irin wann kalami bana tunanin akwai sauran damuwar da zakiyi da ita Umma.. Haka ne.?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata.
Har lokacin Umma bata iya cewa komai ba sai hawaye.
Khulsum ta share hawayen da suka zubo mata kafin t
a kuma nuna ma Umma k’ofa “Idan Inna Dije tazo nan ta sameki Umma kinsan abin bazai kyau ba. Ki dubi girman Allah ki duba jinyan da mahaifina ke ciki dan Allah ki fita ki tafi Umma..”
Umma ta jinjina kai tana hawaye ta nufo waje. Khulsum tai saurin bin
bayanta rik’eda kulan abincin tana k’ok’arin dakatar da ita.
Daidai lokacin motar Hilal tai parking..
Aiko Inna Dije tana hango Umma da Khulsum tai saurin fitowa ta nufosu.
Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Saida tai ma Umma tas kafin ta jany
o Khulsum tace maza su shige wajen Abba.
Khulsum ta kaikaito ta dubi Umma tana kuma sharan k’walla.
Haka Umma taci gaba da tafiya kaman kazar da k’wai ya fashe ma.
Hilal da akai komai gabansa bayan Umma yabi da mota dan sosai ta basa tausayi. Ya fit
o ya gaida Umma bayan yayi parking gefen kwalta. Umma ta ganesa d’an wajen Hajiya Asshe ne da ba yau suka fara had’uwa ba. Hilal Ya rok’eta ta shiga mota ya kaita gida. Da fari k’in amincewa Umma tai saida Hilal yai da gaske dan ta kula idan har bata shiga
n ba bazai k’yaleta ba.
Yai saurin bud’e mata backseat ta shige kafin ya dawo mazauninsa Ya shige had’ida tada motar.
Har k’ofan gida yakai Umma kafin Ya juya. Maimakon ya koma gida sai ya koma asibitin.
Room number d’in Abba ya tambaya a reception s
uka sanar dashi. Ya isa yai knocking. Har lokacin Khulsum kuka take bayan Inna Dije ta sanar da ita sab’anin halinda ta baro Ummul ciki. Cewa da gaske Suwaiba ta saida ta ne ma wasu irin mutane marassa imani balle mutunci. Ba yanda bataiba ganin k’ok’arin
ta dawo da Ummul amma mutanen sunce kudi suka sa sukai sayi Ummul. Ko Kotu za aje bazasu iya kashe auren Ummul ba tinda tak’ama suke da kudi . Yacce kasan zamanin cinikin bayi haka aka saida ‘yaruwarta a wulak’ance.
Knocking d’in ne Ya d’auki hankalinsu.
Inna Dije ta mik’e tana tambayan wanene. Ga mamakinta Hilal ta kuma gani.
Ya sakar mata murmushi yana gaisheta had’ida tambayarta mai jiki. Ta amsa tana tambayarsa lafiya. Ko wani mantuwa ne Asshen Tai.
Hilal Ya girgiza kai alamun a’a. Sai ya k’ara da
“Em.. Da Allah dama nace.. Emm yarinyar nan da na gani d’azu..” Dan shi dik had’uwar da suke da Khulsum kusan sau uku bazaice ga sunanta ba.
Inna Dije ta katsesa “Wace kenan..?”
Hilal yace “Emm.. K’anwar Matar Haidar.” Dan ya tabbata ta haka kawai za’a
ganeta.
Jin haka yasa Khulsum lek’owa tana dubansa dan taso d’ago muryar. Ai kuwa shi d’in ne dai.
Ta galla masa harara cikeda takaici musamman da Inna Dije ta sanar da ita yanda sukai da danginsa akan ‘yaruwarta Ummul.
Hangota da Hilal yai sai ta s
akar mata murmushi Ya d’ago mata hannu alamun gaisuwa.
Inna Dije da Tai k’ebebe bakin k’ofa tace “Toooh mai kake nema wajenta.?”
Hilal Ya rasa abun fad’i. Sai ya soma ‘yan kame kame “Em.. Dama akwai wani sak’o ne da zan bata.. Idan hakan na matsala.”
Ta dubeshi a dak’ile, sai Ta juyo ta dubi Khulsum, ta kuma duban Hilal “Minti goma. Minti goma na baka. Kuma kar kuyi nisa Ku tsaya bayan lambun d’akin nan yanda zanke hango ku ta window ehe..” Ta dubi Khulsum tace “Zo kije ina kallonku ta window.”
Har lo
kacin hararsa kurum Khulsum take. Kaf danginsu ta tsanesu.
Suka jera suna tafiya har suka isa zuwa wajen wani dogon kujera na shak’atawa. Hilal Ya nuna mata kujeran “Bismillah..”
“Kaga Malam ba zuwa nan nai dan na saurareka ba. Zuwa nai na baka sak’o ka
fad’a ma azzaluman danginka. Ni UmmuKhulsum ‘yaruwarta sai na raba wann auren k’etar da sukai ma d’ansu da ita. Ka fahimta.!”
Hilal ta girgiza kai kad’an