Showing 57001 words to 60000 words out of 267381 words
noticing a hoton yake gani. Sau d’aya tak ya kalla, maiyasa ya kasa cire hoton cikin idanunsa, meyasa duk rufe id
anun da zai sai yaga idonta masu d’auke da hawaye.. Maiyasa ta amince da aurensa.. Meyasa hawayenta kawai ya iya noticing.? Shin dole aka mata.? Shin Wacece ita ma.? Shin tasan shirin Mommy Akan auren cewa AUREN WATA UKU zasuyi kuma dalilin auren shine ma
haifinsa ya mallaka masa project. Shin tasan duka wad’ann ta amince da aurensa.? Is she that lowlife.? Wacece zata amince da irin wann wulak’antaccen auren. Does she have any idea who he really is.? Does she even know what she’s getting herself into.? Tamb
ayoyi da yawa Wanda idan ba ita ba babu mai amsa masa. Take yaji zuciyarsa ta soma raya masa ‘Maybe she’s aware of everything.. Maybe kaman yanda Mommy tai deal dakai Akan auren haka itama tai deal da ita.. Mommy zatayi komai dan abinda take so. He knows h
is mother har cinikin auren zatayi. What if wann yarinyar cinikin aurenka tayi da Mommy.? Take yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi. Ji yai ya kuma tsanarta. Ya tsani mutumin da zaiyi komai sabida kud’i da abin duniya. Sauri sauri ya fito daga shower d’in
dan baiso yaci gaba da tunanin.
Yana fitowa ya tadda Dareen har ta kwanta. Ya k’arasa shirinsa kafin ya isa gefe ya kwanta. Saidai kwanciyar sa da kad’an ya soma sinkayo sautin Dareen a hankali kaman na mai kuka.
Ya d’an mirgino yana dubanta, nan yaga
har kaman shesshek’a take. Side lamp ya kunna ya mik’e daga kwamcen da yake “Hey.” Ya furta a hankali.
Jin bata amsa ba ya sanya shi matsawa kusanta ya mirgino da ita, nan yaga hawaye Sun wanke mata fuska. Baison ganin hawaye tin yana yaro. Watak’ila hoto
n yarinyar can da ya gaza b’ace masa a k’wayar ido ma sabida hawayen da ya hango ne cikin idonta. He hates to see people cry.. A nashi tunanin ba abu k’arami bane zaisa mutum kuka. A lokacin yarinta duk irin abubuwan da yai going through baya iya kuka koda
yana son yi. So he believes idan har baiyi kuka lokacin yarinta lokacin da ya kamata ace yayi ba dukda irin abubuwan da ya fuskanta a rayuwa Lallai ba Abu k’arami bane zaisa mutum kuka.
“What’s wrong.?” Ya tambaya cikin kwantar da murya idanunsa tar kan
ta.
Dubansa tai sai kuma ta girgiza Kai “Haidar I don’t know.. Ban sani ba, I.. I just feel like I’m losing you somehow..”
Zuba mata ido yai tausayin ta fal k’irjinsa. She’s right, a kwanakin kaman ya nesanta Kansa da ita. Above all, wann auren shirin ko
yace auren yarjejeniya da Mommy ke yunk’urin yi masa yasa ya d’auke masa hankali da tunani.. He feels like he’s not being fair to her.. Koda ace bai mata irin son da take mishi. She’s still his wife kuma ta cancanci kula na musamman daga wajensa. Hannayen
ta ya rik’e cikin nasa suna fuskantar juna. Yayinda Dareen taketa addu’an Allah yasa tarkonta ya d’anu. Bata isa tace ga weak point d’insa ba tinda tasan shi mutum ne da ba kasafai ake iya karantar yanayinsa ba. What she’s sure about shine shi Mutum ne mai
tausayi wanda ta fahimci haka from his actions, especially towards mutane masu rauni. Yanada tsananin zafi saidai a wasu lokutan tausayin masu rauni da yake dashi yakan rinjayi zafin sa. Da wann takanyi amfani ta tatsa duk wani information gameda rayuwars
a. Ta kula yanzu kaman ya daina sanar da ita abubuwa da dama. Ya fara komawa kaman dai Haidar d’in da ta soma sani daga farko kafin aikin aisiri yai tasiri akansa. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in.
“I have been dealing with so many things lately… That I ev
en lost sight of what’s more important.. I mean you..!” Gajeren murmushi saman fuskarsa ya kuma rik’e hannayenta cikin nasa yaci gaba da fad’in “But I’ll make it up to you.. Just choose a place from the map.. Let’s go for a vacation.”
Surprisingly take d
ubansa “Really, vacation..? Na zab’a duk yanda nake so from the map.?”
Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake jinjina mata kai “Just mention the place.. Any place you have in mind.”
“OMG.! I love you.. I love you so much..” Ta fad’i tana mai fad’awa
jikinsa sabida murna.
“I’ve never been to Cuba. Let’s go to Cuba. Zan duba mana best Resort da sukeda shi.” Ta fad’i murmushi saman fuskarta.
Shid’inma murmushin yai kafin ya jinin Kai “Alright Cuba, Lets explore Cuba then.”
Rungumesa ta kumayi zuciyart
a na raya mata ta mance komai ta daina binciken komai tabi mijinta suje su sha soyayyarsu.
A b’angaren Haidar kaw cikin zuciyarsa yake ayyana wann shine maslaha. A daidai lokacin da Mommy zata kawo masa yarinyar can matsayin mata zata shafa ne taji baya
nan.. Bazai dawo ba sai bayan wani lokaci, zai timing lokacin da zasu fara gudanar da project d’in kafin ya dawo k’asar.
**
Kano
Da tsananin mamaki Hajjah Fannah ta dubi agogo Jin da gaske buga mata k’ofa ake. K’arfe shad’aya na dare har ta gota. Ta fi
to da kyar dan har kawo lokacin bata wani Jin k’arfin jikinta.
Khulsum ta gani tsaye k’ofar gidan ga alamun hawaye saman fuskarta.
“A’ah! Khulsum. Lafiya? Ina kika fito cikin Daren nan..?”
Khulsum bata iya amsa mata ba sai ma wani sabon kukan da ta fa
she mata dashi. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Khulsum suka shige cikin gidan.
Ruwa ta soma kawo mata tace ta sha ta samu natsuwa. Ta d’an dubeta “Khulsum ina Ummul..? Meke faruwa ne wai.. Inji ba wani Abu bane ya kuma faruwa.?”
Khulsum ta saka bay
an hannunta ta share hawayen “Hajja Adda Ummul ta tafi.. Umma ta saida ita.. Tabi Umma.. Ta amince da auren da Umma ta shirya mata.. Ta zab’i tayi biyayya ma Umma bisa auren da ta shirya mata a bayan idon mahaifinmu.. Su d’in basuda wani banbanci da Mama d
a yaranta masu burin ganin bayan Abba..!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.
Hajja Fannah ta dubeta da mamaki “Aure kuma Khulsum. Aure Ummul zatayi.?”
Khulsum ta jinjina mata Kai har lokacin jikinta a mace yake.
Sai Hajja Fannah ta nemi duk wani
ciwon da takeji ta rasa. Taci buri ma d’anta Wanda ko shakka babu shima ya auka ma soyayyar Ummulkhairin. Saidai kana naka Allah na nashi kuma na Allah shine daidai.
Jiki a sanyaye ta dubi Khulsum “Wanene mijin da zai auri Ummul.?”
Khulsum ta girgiza ma
ta Kai tana mai tab’e baki “Bana tsammanin ko ita kanta Umma da ta had’a auren ta sansa.”
Sauk’e ajiyan zuciya Hajja Fannah tai, wani irin batu ne ita kanta Umman nasu bata san mijin da ta nemo ma Ummul ba. Ta yaya haka zai kasance.? Ummul ta wahala a ray
uwa bazataso ta kuma fad’awa wani wahalar ba. Lokaci yayi da za’a dakatar da mahaifiyar Ummul. Idan ahalin su Ummul bazasu iya dakatar da Suwaiba ba zata
nemi taimakon manyan Unguwa musamman mai Unguwa da commette d’insa asan halinda ahalin Malam Isubu ke
ciki ayi k’ok’arin dakatar da Suwaiba tun kafin mai aukuwa ya auku.
Ta dubi Khulsum tace “Kici abinci ki kwanta ki huta na Miki alk’awari in sha Allah zanyi iyaka abinda zan iya dan naga mahaifiyarku bata salwantar da rayuwar Ummul ba da izinin Allah.
K
hulsum ta jinjina mata Kai ba tareda ta iya cewa komai ba.
Hajja Fannah dai mamaki ne ya kasa saketa. Sai sak’awa da warwarewa take tana tinanin toh waye mijin da Suwaiba ta kawo ma Ummul Wanda ita kanta bata sanshi ba. A haka ta kwana cikin daren tareda
zullumin idn har auren Ummul ya tabbata batasan ta yanda zata soma sanar da tilon d’anta Wanda ta jima tana binsa da batun aure yana kaucewa sakamon k’azafi da mahaifinsa ya jefasa dashi tin yana d’an watanni uku a ciki. Daga k’arshe Hisham ya samu macen
da take tunanin zasu samu daidaito sai ga kuma abinda ke shirin faruwa. Tabbas Zuciyar D’anta zai karaya.
Washe gari ma Khulsum wajen mahaifinta ta yini dan ko ta kan ahalinta bata kuma bi. A cewarta dukansu basuda banbanci da juna.
*
Washe gari masu
kawo lefe Sun samu isowa gidansu Ummulkhairi. Tin daga bakin layin ake k’irga motocin dake shigowa domin kawo lefen Ummulkhairi.
Su Azeema sukai layi suka jeru nan tsakar gidansu suna duban masu shigo da lefe.
Tin suna k’irga akwatuna har dai suka hak
’ura da k’irge suka zuba ma sarautar Allah idanu.
Azeema ta tab’a Salima tace “Yaya Salima anya wann ba kwari suka saya gaba d’aya ba..!”
Salima ta sauk’e ajiyan zuciya “Ni na ma rasa abin fad’i.”
Gajeren tsaki Badia tai “Mtseww aikin banza.. Wann da ga
ni kasan kayan haya ne ba lefe ba..” Tana ida fad’in haka ta d’age labulen d’aki ta shige.
Azeema ta dubi Salima tace “Kin ganni nan wallhi baza’ayi hidimar nan babu ni ba.. Gwara na shiga a dama Dani dan nasan duk rintsi sai an sallameni da atampa da jak
a da takalmi na samu na yak’an dangin Habibu.
Salima ta tab’e baki “Amma Azeema matsalarki kad’an ce..!” Tana ida fad’in haka itama ta fad’a d’akin mahaifiyarsu. Duk suka zuba tagumi suna Jin yanda hayaniya ke ci gaba da tashi. Zancen guda d’aya ne Ummul
tayi dace.
Azeema kaw tuni ta nufi bakin farandar Umma yanda ake baje kolin kayan lefen Ummul. Sai zuzuta kyaun kayan take tana fad’in ‘yaruwarta tayi goshi..
Umma ta dubeta tace “Kar ki damu Azeema dake za’a tafi kai amarya.”
Azeema ta daka tsalle
tana fad’in “Wllhi Umma ni har zaman d’aki ma sai na mata ai.. Irin wann kayan bajinta kayan alatu haka. Kai ina ma nice mai sa’a irin Ummul..”
Anzo yanda Umma take so. Taji ana ambaton Ummul d’inta da mai sa’a.. Umma ta shiga washe baki tana jin yanda mu
tane ke fad’in K’warai Ummul tayi goshi ita d’in mai sa’a ce.
Haka akaita shigo da zuk’a zuk’an akwatina da sunan lefen Ummulkhairi. Kan kace me labari Ya karad’e unguwa.
Umma naku fah ba’a sama ba’a k’asa, uwar amarya da kanta. Duk magulmatan unguwar m
asu tsegumin Ummulkhairi ta kasa auruwa Sun dawo b’angaren Umma. Mama taga tijara a wann ranan, dan tuni Umma ta amshe girman nata kama daga cikin gida har zuwa wajen mutanen unguwa Wanda a baya suke aibata su.
Uwa uba da sukaga su Hajja Asshe matsayin iy
ayen mijin da zai auri Ummulkhairi dan tuni d’aya daga cikin kawayen Asshe ta soma bada bayanin ko su waye su. Hakan ya kuma sanyar ma kowa gwiwa dan mijin Asshe dai ba b’oyayyen mutum bane a birnin Kano da kewaye. Hakan Ya kuma tabbatar masu Umma dai ba h
ark’ar shan jini ta fad’a ba kaman yanda duk sukai zato a baya. Allah ne ya kashe ya basu. Lokacin su ne yayi.
Azeema sai kallon Hajja Asshe take sanda taji tana yabon surkarsu Ummul. Sai duban dank’ara dank’aran gwal d’in dake zube wuyarta da awarwaron
dake hannunta take. Ga wani k’amshin ‘yan gayu na musamman da matan suke. Dan Asshe ita da K’awayenta suka kawo lefen.
**
Yanda Mama taga rana haka taga dare. Ko asibiti wajen mijinta ta kasa komawa tinda taga an kawo lefen Ummulkhairi. Ta mik’e ta shig
a safa da marwa a d’an tsukikin d’akinta tana neman hanyar da zatabi ta hana yuwan wann aure.
Wani tunani ya fad’o mata. A fili ta furta Dije. Dije ce kawai zata sa wann aure Ya watse.
Cikin sauri ta isa tana bubbuga k’afar Badia wacce tinda Tasi’u Ya
b’ace ta dawo kwanan gida.
“Badia, ke Badia.. Tashi mana..!”
Badia ta mik’e tana mutsuka idanu da kyar “An fara shagalin bikin ne..?”
“Shagalin bikin Ubanki..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa.
Badia taja tsaki tana turo baki gaba “Haba Mama ni wllh
i na zata shagali aka soma inata mafarkin mun tafi Kai amarya an raba mana motoci matsayin tukwici kin wani kama kin tashen.”
Mama ta kuma danna mata harara “Dan ubanki murna kike wann annobar zatai aure bayan ke ga naki auren yana sama yana k’asa. Allah
kad’ai yasan yanda wann macucin mijin naki ya gudu.. Ba abun muyi k’ararsa ba mu tona ma kanmu asiri…”
Badia tace “Mama Tasi fah ba guduwa yai ba. Ni na tabbata yana can yana juya mana kud’ad’enmu sai yayi arziki kaman mijin da zai auri Ummul kafin ya da
wo. Na fad’a Miki ko jiya fah Munyi waya dashi.”
Katseta Mama tai tana mai kuma danna mata wani ashar d’in “Ashe ke babbar shashasha ce. Yacce kika san Suwaiba ce ta haifeki.. Ba dan ina tsoron tonuwar asirina ba ace na saida gadon mijina tun kafin ya mut
u wllhi da na maka k’arar wann d’an iskan mijin naki a Kotu..”
Badia ta shek’e da dariya “Toh ai saidai ki maka k’arar wofi Mama. Dan Tasi dai ba ganinsa zakiyi ba sai Ya zama hamshak’in Mai arziki ya dawo mana da kud’ad’en mu.. Wai baki so muyi arziki k
aman nasu Ummul ne..”
“Idan kika sake kira mun Ummul a nan zan zagi gawa ka k’i kabarin uban nan naki dake kwance. wann aure kuma ba yinsa za’ayi ba dan alwashi na d’auka. Bani wayarki..” Ta k’arashe tana mik’a mata hannu.
Badia ta dubeta sai kuma ta mi
k’a mata “Mama me zakiyi da wayata, ni dai dan Allah kar ki kira Tasi ki zagesa dan nasan halinki..”
Bata amsata ba sai ta mik’a mata nata wayar “Ungo nemo min lambar Dije.. Allah Sa dai bata canza layi ba..”
Badia ta dubeta galala “Mama Inna Dije kike n
ufi ko wa..?”
“Dije k’anwar Ubanku Isubu kira mun ita..”
Badia tace “Mama me zaki fad’a mata a tsohon daren nan.. Sanin kanki ne Inna Dije da Abba harma da ahalinsa sun raba gari tun da jimawa..”
Mama ta jinjina kai “Waye sila..?”
Badia tai k’uri tana
dubanta.
Mama taci gaba “Suwaiba da bakinta ta fad’a cewa ‘Yarta Ummul ita tai sanadin barin Fa’iz duniya dan haka zan kira Dije na sanar da ita komai na kuma kunna mata recording d’in da kikai a wayarki lokacin da Suwaiba ke fad’in Ummul ce tai Sanadin F
a’iz.. Sai muga ta yanda za’ayi ai wann aure tinda naga su ‘yan uwan mahaifin naku an rufe bakinsu da kud’i.. Dije ita kad’ai ce zata saka birki ma wann aure..” Ta k’arashe tana kecewa da dariyar cin nasara. Tana ayyana yanda za’a wayi gari da labarin an
fasa auren Ummulkhairi.
Saidai duk Neman wayar Inna Dije da suke basu samu ba cikin daren. Akan dole Mama ta hak’ura da niyyan washe gari idan Allah ya kai rai zata nemi wani hanyar dan bazata hak’ura ba. Duk rintsi sai ta cimma Dije an wargaza shirin wa
nn auren.
**
Khulsum ita kad’ai ta kwana wajen Abba. Tana zaune gefensa hawaye na gangaro mata. Hannunta saman nasa “Abba.. Abba na Kai hak’uri. Allah ya jarabceka da cuta kaman yanda ya jarabceka da ahalinka. Abba Allah masu imani yake jarabta. Ina ro
k’onsa da ya baka lafiya ya kuma baka ikon cin jarabawa.” Taci gaba da kuka tana mai kwantar da kanta gefe da mahaifinta. A hankali taji kaman Abba na motsi. Khulsum tai saurin d’agowa tana dubansa, sai taga kaman bakinsa na motsi. Ta matsa kusa dashi ciki
n sauri tana kai kunnenta saitin bakinsa dan jin abinda yake son fad’i.
Tai saurin d’aura hannayenta saman nashi “Abba gani a nan. Khulsum ce Abba.”
Amma sai taji kaman yana ambaton Ummulkhairi cikin maganan da bai iya fita sosai.
“Ummulkhairi.!” Khul
sum ta nanata a hankali. Cikin sauri ta dubi Abba “Abba zanyi k’ok’arin dakatar da ita. Bazan bari Umma ta cimma makahon burinta Akan ‘Yaruwata ba. Abba zan dakatar Adda Ummul kaji..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa. Sai kuma ta juyo ta dubi mahaif
in nasu Wanda babu kowa wajensa sai ita. Toh idan ta fice wani abun ya taso fah,.? Ko ma wani abu ya samu Abba.? Kasa ficewa tai sai komawa da tai ta zauna tana tinanin taje ta dakatar da ‘yaruwarta ne ko kuwa ta zauna da Abbanta ne.? A hankali ta lumshe i
danunta tana jin wani abu mai ciwo na tasowa daga cikin k’irjinta. Batajin har abada zata kuma iya kiran ahalinta da sunan ahali. Nan taci gaba da sak’awa tana warwarewa taje ta sanar da Ummul Abba ya ambaci sunanta ne kokuwa ta k’yaleta da makauniyar biy
ayyan da take k’ok’arin yima Umma.
**
Asshe da gogaggun k’awayenta Sun samu hallarowa da Kayan lalle nik’i nik’i. Dan dama sassafe aka taho da Ummul d’in gidan. Umma tace saidai azo gidan mahaifinta a d’auketa kaman yanda yake a al’ada bayan an d’aura a
ure.
Mama ta zuba ma sarautar Allah ido ganin matan nan harda masu algaita suke tafe suna masu rakiya. Sai Asshe ta isa ta kamo hannun Umma suna tik’an rawa tare ta b’alle bandir ‘yan dubu dubu ta shiga lik’a ma Umma. Su Maman Sahal magulmata Unguwa da s
auran ‘yan cikin gidansu Ummul kaw fitowa sukai suna tayasu tik’an rawa sai damben kwasan kud’ad’en da Asshe ke lik’awa suke tsakaninsu da masu algaita.
Mama ta kuma rapka uban tagumi. Ikon Allah yanzu Isubu na kwance gadon asibiti Suwaiba take wann barik
i a cikin gidansa. Idan sunanta Tani wann aure baza’ayi ba. Ta mik’e ta cikin k’ok’arin dakatar da masu algaita tana fad’in irin fashe fashen auren Ummul da bak’in k’addara da yake biyeda rayuwarta. Idan har suna nema ma d’ansu lafiya kar su had’asa da ann
oba. Sai aka maida Tani Mahaukaciya dan babu Wanda ya d’auki zancenta. Iyayen ango kam ma ko kallo bata ishesu ba suka sa aka fito