Showing 207001 words to 210000 words out of 267381 words
cikin rayuwarta.
A lokacin da Haidar ya cika watanni uku a SouthAfrica a lokacin yake sanar da Mommy shirinsa na dawowa gida. A wann lokacin kuma Aurensu da Ummul ya cika watann
i tara da mutuwa. Haka zalika Ummul ta shiga watan Haihuwarta.
Tinda Mommy ta shelanta labarin dawowar Haidar Anisa ta gaza zaune ta gaza tsaye Angonta zai dawo. Tuni ta fidda Ankon bikinta tsakanin kawayenta. Ko sanar ma Mommy batai ba dan ma kar Mommyn
ta dakatar da ita. Dan a halin yanzu kam ta gama shiri ta kuma lashi takobin zama matar Haidar Maitama. Duk wann bidirin da take iyayen nata kansu basu da labari. A cewarta saidai suga IV musamman Amminta wacce har kawo lokacin basu koma normal da mahaifi
yar Haidar ba. Bazata bari sab’anin dake tsakaninsu ya mata sanadin farin cikinta ba. Gwara kawai idan an gama komai Ammi taga IV.
*
Illahirin ma’aikatan gidan suna kitchen suna aikin abincin sauk’an Haidar. Mommy na tsakani tana directing nasu yanda tak
e so komai Ya kasance perfect. Yayinda Anisa ke zaune gaban make-up artist da ta kirawo Har gida ana tsara mata make-up d’in tarban Angonta Haidar. Ga wata Uwar bridal gown da taci yanda kasan wata amarya. Ranta fari sol kaman yanda rigar tata take. At las
t mafarkinta zai zama gaskiya.
Daga k’ofan d’akin sukaji ana knocking. Anisa sai tsuka take dan a zatonta d’aya ne daga cikin ma’aikatan gidan. A hasale tace “Wai wayene wajen.?! Na fad’a muku I don’t want anything before dinner.. Bazan saka komai a baki
na ba sai Mijina yayi landing.!”
Aka ci gaba da turo k’ofan ana tafe hannu. Cak Anisa ta ja tai turus. Ba shiri ta ture hannun mai make-up zuciyarta naci gaba da bugawa. Ta mik’e a firgice had’ida juyowa tana duban wacce ta shigo. K’iris Ya rage Anisa b
ata kife k’asa ba. Jikinta ya d’auki kyarma ta shiga nunata da dan yatsa “You.!!!”
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*53*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
“Surprise.! Surprise.!!” Ta furta tana duban Anisa daga sama zuwa k’asa murmushi saman fusk
arta.
Anisa ta dubi makeup artist d’in tace ta basu waje. Lokaci guda ta tako zuwa gabanta tana huci take fad’in “Mai kike a nan Leenah..? What exactly do you want from me.?!”
Leenah taci gaba da murmusawa tana duban Anisa “Haba Amarya.. Ai ba’a san amar
e da fushi ba. Kar ki b’ata kwalliyarki..” Ta karada “Kashh kinga Har kin fara jurwaye tun ango bai gani ba.!” Ta kamo bakin rigarta ta soma k’ok’arin gyara ma Anisa kwalliyar tana fad’in “Ki adana guminki Anisa dan ba’a fara wasan ba balle ki jik’e da gum
i.”
Anisa ta kai hannu fusace ta bige hannun Leenah tana huci “I don’t have time for your stupid games Leenah.! Just tell me once and for all Mai ya kawoki gidan nan a daidai wann lokacin.?!”
Leenah ta kuma murmusawa tana duban Anisa sai ta isa ta zaun
e saman sofa ta d’aura k’afa d’aya bisa d’aya “Kar ki damu I’m not here to blackmail you.. Nazo tayaki murna ne. Girlfriend… Ko ince .. Mrs Haidar Maitama.! Oh! Na mance. Soon to be..” Ta k’arashe tana fad’ad’a murmushinta.
Anisa ta had’iyi abinda ya tos
he mata mak’ogoro “Kinga Leenah ki tashi ki fice. Ba Wanda ya gayyaceki.”
“This is where you are wrong Neesah.!” Leenah tace tana dubanta. Sai ta kuma murmuswa “Amma Hajiya Kwaise tasan duk abubuwan da kika aikata..? Ina nufin kin sanar da ita kece kikai
sanadin rufeta a cell..? Kaman yanda bana haufin kece kikai sanadin had’arin motar da D’anta ya kusa rasa ransa ciki.!”
Anisa bata bari Leenah takai aya ba ta k’araso ta shiga janyeta tana fad’in ta tashi ta fice ko ta kirawo mata securities.
Leenah ta f
inciki hannunta tana huci itama take duban Anisa wann karon “Kin zata zan barki kici banza ne.? Yanzu ba sai anjima ba zan wargaza duk wani shirinki Anisa. Dan sai na sanar da Hajiya Kwaise wacece ta zuba ma Ummul poison ta kuma d’aura mata blame d’in.” Ta
na ida fad’in haka tasa Kai zata fice Anisa tai saurin fincikota ta maidota baya. Ta marairaice fuska kaman zata fashe da kuka take fad’in “Oh no.. Sorry Leenah.. Please don’t expose me.. Tell me how much money do you want.?” Tana ida fad’in haka sai ta k
ece da dariya tana kuma duban Leenah wacce itama da mamaki take dubanta. Anisa ta dubi Leenah daga sama zuwa k’asa tace “Haka kike so nayi right.? Toh kinyi k’arya Leenah. Bazaki tab’a ganin haka daga wajena ba. Kina tsammanin Mommy zata yarda dake ne.? Id
an bata yarda dake ba a baya meyasa zata yarda dake yanzu Leenah.? Kar ki mance kinada tabon sharrin sata da kikai ma Ummul a idon Mommy. And hello.! Last time I checked, Mommy ta miki iyaka da gidan nan. You might be charged with trespassing sweetheart.”
Shiru Leenah bata ce mata komai ba. Anisa tai murmushin cin nasara “Ko mai zaki sanar da Mommy Leenah kin riga kin makara domin a halin yanzu Mommy ta aminta Dani d’ari bisa d’ari.!” Taci gaba da zagaye Leenah tana fad’in “You can go ahead and tell Mommy
everything Leenah. It’s my word against yours. Kije ki ce mata Ni Anisa ni na canza turaren da ta bani na bama Ummul na kuma zuba guba ciki.! Ni Anisa ni nayi sanadin jefata a cell har ta shafe kwanaki.! Ni Anisa ni nayi sanadin had’arin motan da Haidar y
a kusa rasa ransa ciki dan kawai naga bayan Ummul.! Ni Anisa ni nayi sanadin mutuwan Auren Ummul da Haidar sann zan tabbatar Ummul da abinda ke cikinta basu dawo cikin rayuwar Haidar ba.!”
A daidai nan sukaji an bud’e k’ofar d’akin. A tare suka waigo suna
ganin waye ya bud’e, ba kowa bane face Mommy cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinta ciki ba.
Jikin Anisa ya d’auki rawa sai ta fashe da kuka ta nufi Mommy tana nuna mata Leenah take fad’in “Mommy kisa securities securities Ki koreta. Kin mata iyak
a da gidan nan tin lokacin da ta k’ulla ma Ummul sharrin sata.. Kuma wlhi ni yanzu ba kawata bace babu abinda ya hadani da ita.”
Anisa bata Kai aya ba taji sauk’an Mari maiji da lafiya a k’uncinta. Ta d’ago a firgice tana duban Mommy wacce fuskarta ya gam
a rinewa haka ma idanunta.
Anisa ta dafe k’uncinta bata daina kallon Mommy da mamaki ba. Murya na rawa take fad’in “Mo..Mommy..” Nan ma bata Kai aya ba Mommy ta kuma d’auketa da wani marin. Tana kuma tasowa ta sake Kai mata wani Marin..Sai Anisa ta duk’a
a k’asa tana kuka tana dafe duka b’angaren fuskanta. Ta soma jada baya cikeda tsoron Mommy.
Leenah tasa k’afa ta take k’afar Anisa dake daga zaune tana jan jiki Wanda hakan ya hanata motsawa.
Leenah na k’are mata ma Anisa dake duk’e kasa dafe da fuskant
a tana bin Mommy harma da Leenah da kallon tsoro. Baki na rawa Anisa tace “Waht’s… going on here…?”
Leenah ta katse ta “Hm Anisa kenan. Kin zata ke kad’ai ce kika iya buga wasan.?”
Sai ta murmusa kafin ta saka hannu ta Ciro kwalban turaren da Mommy ta ba
ma Anisa dan ta bama Ummul Wanda bata ma Ummul d’in ba suka canza da mai guba.
Baki sake Anisa ke dubanta tana duban kwalban turaren. Ya akai ya isa hannun Leenah.? Sai ta tuna lokacin da Ammi ta dauketa suka tafi Kano ta bar turaren nan d’aki cikin wardr
obe bata tafi dashi ba. K’ila Leenah ta shigo ta bincika ta samu kenan. Muryar Anisa na rawa ta d’ago hannaye ta had’e waje guda tana duban Mommy “Mommy Kar ki yarda da duk abinda Munafukar nan zata sanar dake.. Wllhi Mommy sharri take mun ni bansan komai
ba. Bakin ciki take mun taga zan auri Haidar.”
“Idan kika sake magana sai na d’aukeki da wani Marin.! Maras mutunci kawai. Ai da Haidar ya aureki Anisa gwara ya k’arashi rayuwarsa a haka.!” Mommy ta katseta tana ci gaba da huci. Lokaci guda Mommy ta k’ar
aso gabanta “Banida lokacin sauraran sauran makircinki bayan Wanda naji da kunnuwana. Abu d’aya zan tambayeki yanzu Anisa, ki fad’a mun ina Ummul take.?!”
Anisa na hawaye take ci gaba da girgiza kai “Mommy dan Allah ki min rai.!”
“Zaki fad’a mun yanda Um
mul take ne ko sai nasa anyi k’asa k’asa dake.!”
Daidai lokacin suka sinkayo muryar Haidar da shigowarsa gidan kenan.
“What is going on here.?.. Mommy did you mention Whereabouts d’in Khairy..?”
Suka waigo gaba d’aya suna dubansa yayinda Haidar yaci ga
ba da shigowa d’akin.
Idanun Mommy naga Anisa dake duk’e tana kuka taci gaba da nunata da yar yatsa “Gata can Haidar.! Anisa ta jima tana k’ulla abubuwa a cikin gidan nan ba tareda mun Kai hankulanmu kanta ba. Anisa da muka dauka shashasha wacce bamu bam
a al’amarin ta mahimmanci… Anisa itace ta k’ulla ta kuma wargaza a gidan nan.!”
Cikin rashin fahimta Haidar ke girgiza Kai yana duban Mommy ya kuma dubi Anisa. Sai ya kara duban Mommy yace “Mommy.. Ban fahimceki ba..”
Mommy taci gaba da jinjina Kai “Yau
zaka fahimci komai Haidar. Kaman yanda watanni k’alilan baya na soma fahimta.” Taci gaba da jinjina Kai “A lokacin da na soma zargin Anisa sai na tafi Kano na dawo da ita gidan nan dan na tabbatar da zargina akanta na kuma Kamata red handed. Na karanci Ani
sa na tsawon watanni yanda na fahimci ita d’in ta jima tana sonka.. Sann duk abubuwan da ta aikata da sunan soyayyar da take maka ne..!”
Da mamaki Haidar ke girgiza Kai “Ni kuma.. Anisa.. Anisa ke sona. Did you hear yourself Mommy..?!”
Mommy ta jinjina K
ai “I couldn’t believe it either har saida na gano abubuwan da ta tapka in the name of tana sonka. Bayan na gano haka sai na nuna mata ina tareda ita d’ari bisa d’ari.. Na nuna mata tanada goyon bayana zan maka umarni da ka aureta.. Nayi wasa da tunaninta
kaman yanda ta jima tanayi da namu. Nan na binciko yanda wann kawar tata take dan ban mance wani rana da suka k’ulla tuggu ma Ummul su biyun har naima kawar tata iyaka da gidan nan.” Mommy taci gaba da jinjina Kai “Anisa itace ta zuba ma Ummul poison a tur
are dan ta kasheta slow dead sann ta d’aura blame d’in akaina.! Anisa itace tai sanadin had’arin motan da ya auka muku kaida Ummul duk dan ta kashe Ummul ta cireta daga cikin rayuwarka.! Anisa ita ce tai sanadin mutuwan Aurenka da Ummul Wanda bana haufi ba
kinsu d’aya da wancan azzalumar da ta aureka ta hanyar sihiri.. Anisa tasan yanda Ummul take tsawon lokacin nan.! Sann..” Sai Mommy tai shiru tana ci gaba da huci “Sann tana saneda cewa.. Ummul is pregnant har ta shiga watan haihuwarta.. Duka Anisa na san
e da wann tsawon lokacin nan.!”
Gumi ne ke gangaro masa tin daga tsakiyar sumarsa har zuwa goshinsa.. Ga jijijiyoyin jikinsa dake kuma mimmik’ewa.. Ya saki k’aramin briefcase din dake hannunsa. Yayinda yaga wani duhu ya gifta k’wayar idonsa..
Anisa ta s
oma jada baya tana hawaye take girgiza Kai ganin Haidar gaba d’aya ya rikice ya sauya mata. Cikin rawar murya tana jan jiki tak fad’in “ No Haidar please.. Haidar..! Haidar dan Allah ka yarda dani.. I did everything out of love… I didn’t mean to harm you o
r Mommy.. Wllhi nayi komai ne sabida ina sonka.. Kuma.. Kuma wllhi ban tab’a had’a baki da Dareen ba… Sann..” Bata Kai aya ba Haidar ya shak’ota da iyaka k’arfinsa yana wani irin huci “I will kill you..! I swear I’m going to kill you.!” Wane irin huci kuru
m yake yana shak’e wuyan Anisa har saida Mommy ta soma k’ok’arin janyesa.
Baza’a kira abinda ke tsartsafowa daga cikin idanunsa hawaye ba saidai ruwan tururin k’unan zuciya.
“Tell me..! Tell me. Where is my wife..?!” Yai maganar gumin dake tsartsafowa ta
ko wani kofan sumar dake jikinsa naci gaba da gangarowa.
Anisa ta soma sosa wuya da kyar tana tarin azaba take fad’in “Zan fad’a maka.. Please let go..!”
“Tell me now..!” Ya kuma fad’i yana fidda huci kaman zaki.
“Ta.. Tana Bauchi…”
Mommy ta dubeta da
mamaki “Bauchi.?”
Anisa taci gaba da jinjina Kai ga gumin azaban da ya wanke umburarren fuskarta da ya sha tafin Mommy ba adadi.
“Bauchi wajen wa.? Mai ya kaita Bauchi.?” Cewar Mommy.
Anisa taci gaba da jinjina Kai daga durk’ushe kaman Marianiyar Ken
yawa “Wajen mahaifiyar Hi… Wajen mahaifiyar Hisham.”
“Hisham..!” Mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki da rud’ani dan tama rasa tuna waye Hisham. Yayinda Haidar yai mutuwar tsaye yana nanata abinda Anisa tace cikin kwanyarsa.
“Waye Hisham kuma.?” Momm
y ta tambaya.
Anisa ta yarfe gumi da hawayen da suka gauraye mata fuska “Hisham Abokin Haidar.. Bansan dalilinsa ba amma ya jima yana bibiyan Haidar da ahalinsa da sharri. Kuma.. Kuma bakinsa d’aya da Dareen tare suke k’ulla komai tin kafin na had’u da Hi
sham.. Hisham has been shadowing Haidar for quit some time.. Tin kafin Ummul ta shigo rayuwarka.”
Kalmar Shadow da Haidar yaji ta ambata sai Ya tuna masa wani rana Ya taba jin Dareen tana waya da wani mai suna Shadow koda Ya tambayeta sai tace Uncle dinta
ne.
Muryar Anisa Ya kuma dakan dodon kunnensa “Sann koda Ummul ta shigo rayuwarka sai akalar yakinsa Ya koma ga k’udirin raba tsakaninku. A cewarsa shi ya fara ganin Ummul ya kuma fara sonta kafin Haidar….Ni kawai.. Kawai nayi tarayya da shine dan na ci
mma burina na mallakan Haidar kamar yanda yake so ya mallaki Ummul.. Kuma ya d’au alwashin raba Haidar da Ummul ko ta wani hali.”
Juyawan da Mommy zatai b’at suka nemi Haidar a wajen suka rasa.
Anisa ta soma k’ok’arin mik’ewa tana Neman gafaran Mommy. M
ommy ta nunata da dan yatsa “Kika kuskura kika motsa daga yanda kike sai nasa an canza Miki kamanni da bugu. Munafuka azzaluma.!”
Leenah ta dubi Mommy tace “Amma ai ni zan iya tafiya..?”
Bata rufe baki ba sai ganin wasu mata guda biyu sanye da Kayan ‘ya
nsanda Sun shigo d’akin ma’aikaciyar gidan na directing nasu.
Mommy ta nuna musu Anisa da Leenah tace “Arrest them.”
Anisa ta saka hannu biyu aka ta kurma ihu tana fad’in “Mommy ki min rai.. You can’t send me to jail.. I’m your niece.. You can’t do this
to me Mommy.. Wayyo na shiga uku ni Anisa.”
Leenah ta katseta “Ba ke kika shiga uku ba Anisa ni kika jefa a uku.. Allah ya isa ban yafe Miki ba. Yau ga yanda bak’in shashancinki da son zuciyarki ya kaimu.. Wayyo ni Leenah guba kawai na kawo ba ni na zuba
ba ma Ummul ba.!”
‘Yarsanda ta tasa k’eyar Leenah tana fad’in “Ki k’arasa bayaninki a station. Move.!” Ta k’arashe tana hankad’eta.
Haka aka tasa k’eyar Anisa da Leenah aka wuce dasu police station.
*
Tinda ya fice yake sharara gudu saman kwalta. Waya
manne kunnensa na hagu. Sadis yake kira. Sadis na d’agawa Haidar yace “I need a plane ticket to Bauchi. Right this instant.!” Bai kuma tsayawa sauraren Sadis ba ya katse kiran yana ci gaba da tururi. Fuskar Hisham kurum yake hangowa. He trusted him. He bel
ieved in him. How could this be possible.? Hisham.! Hisham fah.. Mutumin da ba komai a tsakaninsu face zallan gaskiya, yarda da amana.! Is it a crime to trust someone.? Ta ya haka zai kasance.?! Yaci gaba da girgiza Kai yana ganin abun tamkar dai a mafarki
ne. Not his Hisham. His best friend. Mutumin da ya aminta dashi sama da kowa a duniya ciki harda iyayensa kafin alak’arsa dasu ta gyaru. Ya lumshe idanunsa yana mai kuma Waresu tar a daidai lokacin da ya shigo Company. Securities na gaishesa ko zarafin am
sa su bai ba ya tambayesu ko Hisham yazo Company. Nan suke sanar dashi bai shigo ba gaba d’aya ranan. Haidar ya jinjina Kai kafin yasa kai ya nufi cikin building d’in kaman zai kifa k’asa. Duk Wanda ya gansa basa hanya kawai yake. Yanayi ne da zasuce Sun j
ima basu gansa cikin irinta ba. Ko a zamanin baya da yake samun sab’ani da mahaifinsa bai shiga cikin irin yanayin da suka gansa. Kai tsaye Office d’in Hisham ya nufa. Ya soma takowa cikin Office d’in yana tuno farkon had’uwarsu da Hisham. Motarsa ce ta ts
aya masa a wajen gari Hisham helped him out daga nan suka k’ulla zumunci nan Hisham yake sanar dashi Neman aiki ya kawosa Abuja and he’s an architect. Haidar yace ai kuwa he’s in the right place, because his Dad owns a Construction Company dan haka yasa ma
ransa tamkar ya Sami gurbin aiki k’ark’ashin Kampanin mahaifinsa mai suna Maitama Builders. Nan take yai going through takardun Hisham ya kuma ga ya cancanta hakan yasa babu b’ata lokaci Hisham ya Sami gurbin aiki a kampanin. Hisham yai ta murna harda haw
ayen murna yana fad’in Allah ne ya amsa kokensu shida mahaifyarsa ya turo Haidar cikin rayuwarsa dan ya jima yana neman aiki bai samu ba. Shi maraya ne mahaifinsa ya rasu tun yana k’aramin yaro. Mahaifyarsa ta sha wahala sosai sann tayi d’awainiya dashi tu
n yana k’aramin yaro. Ya gode Allah yanzu zai share mata hawayenta da izinin Allah. Tabbas bazai tab’a mance halaccin Haidar gareshi ba. Ire iren kalaman Hisham kenan Wanda yasa a ko Yaushe yake ma Haidar nasiha gameda bin iyaye. Hisham tolerates Haidar a
cewarsa bayan Hajjarsa baida Wanda ya fiye masa Haidar. Wanda hakan yasa suka k’ulla abota sosai har ta zarce ta koma amintaka. Haidar ya yarda dashi dan hardly ka gansa da wani aboki idan ba Hisham d’in ba.
Haidar ya numfasa had’ida d’aukan wani k’aramin
hotonsu da