Showing 225001 words to 228000 words out of 267381 words
sako kai ga kuma jariri danyen hai
huwa. Bai kamata su d’au hanya cikin dare ba.
Mommy tace eh gaskiya ne hakan yayi Mama Tani ma duk sunyi na’am da shawarin idan ka dauke Haidar Wanda sam ba hakan yaso ba musamman idan Ya tuna cewa gidan mahaifiyar Hisham Khairy and his Son zasu.
Aka z
o shiga Mota Hajja na rik’eda Ummul suka nufi motar Hisham yayinda Mommy ke rik’eda jaririn. Ga kuma Haidar Ya k’araso da bak’ar Land Cruiser din da Sadis ke ja tin zuwansu garin. A daidai gefen motar Hisham Haidar yai parking. Ga Ummul tsaye tsakiya hannu
nta cikin na Hajja. Mommy na daga bayansu rungume da jaririn.
Ummul ta kalli motar Hisham da tin fitowarsu ke jiran karasowarsu ta kuma dubi Motar Haidar da k’arasowarsa wajen kenan. Sai kawai tasa kai ta nufi motar Hisham.
Daga nan cikin mota Hisham d
a Haidar ke aika ma juna kallo ta tsakankanin glass. Sai Hisham Ya sakar ma Haidar sihirtaccen murmushi alamun shi Ummul ta zab’a tinda gashi ta nufo motarsa. Idanun Haidar suka kad’a sosai sanda yake duban Hisham.
Mommy ta waiga ta dubi Haidar, ta kuma d
ubi Ummul da tuni ta nufi motar Hisham. Sai ta dubi jaririn dake cikin hannunta. Ta kuma duban Haidar. Sai taji tausayin D’an nata sosai. Kawai sai ta nufi motar Haidar da jaririn.
Har ta isa jikin motar Hisham sai ta waigo ta dubi Mommy wacce tuni ta nuf
i motar Haidar. Tausayin Mommy ne taji sosai cikin zuciyarta. Ta dubi Hajja tace “Kiyi hak’uri Hajja.. Zan taho tareda Mommy.”
Hajja ta murmusa had’ida jinjina mata kai “Ba komai ‘Yata Allah hadamu a gida lafiya.. Je ki taho tareda Mommyn ki.”
Ummul ta
jinjina mata kai kafin ta nufi motar Haidar zuciyarta na tsinkewa.
Hisham Ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi.
Ummul tana isa jikin motar Asshe taceda Azeema ta shigo su zauna tare. Aiko kaman jira Azeema take ta shige bayan motar ta zauna tsak
iyar Asshe da Mommy. Sai wage baki take yau gata zaune tsakiyar gogaggun mata wayayyu yan boko.
Ba yanda Ummul ta iya dole ta shige front Seat gefen Haidar.
Su Mama Tani dasu Badia harma da Khulsum suka shige motar Hisham tareda Hajja gaba d’aya suka
dunguma suka nufi gidan Hajja dake nan cikin garin Bauchi.
Koda suka iso gidan, su Mommy na ficewa kafin Ummul Tai wani aune tana k’ok’arin ficewa saiji Tai Haidar ya locking motar.
Ta lumshe idonta kad’an had’ida sauk’e ajiyan zuciya. Ba tareda ta dub
esa ba tace “Ka bud’e min mota na fice.”
Shima a dake yace “And who’s holding you.? Go ahead.. get out.. After all, bani na kawoki cikin motar ba.”
A kufule ta juyo tana dubansa da mamaki “Karma kai tunanin wani abu daban. Sabida Mommy kawai na shigo mo
tar nan.!”
Murmushi yai da gefen baki “Really.. Sabida Mommy.? Toh Mommy ta fice kema sai ki fice.”
Kaman zatai kuka take dubansa “Wai mai keke nema wajena..?!”
A fusace ya matso da fuskarsa dab kusan nata “You..! Ke nake nema Khairy..! You and my Son.!
”
Muryarta ya soma rawa tana girgiza kai “Duk abinda ka mun bai isheka ba.? Kayi AUREN WATA UKU dani.. Kuma ka cika Wa’adin Auren kuma..”
Bata kai aya ba ya katseta “Kar ki sake nanata min wann kalmar. AUREN WATA UKU.!”
Tai murmushi da yafi kama da mu
rmushin takaici. Sai ta d’ago hulan sanyin jaririn dake rike cikin hannunta “Kaga wann shi zai dinga tuna maka da kalmar AUREN WATA UKU..!” Ta k’arashe tana kuma fincikan marfin motar. Har lokacin motar a rufe take ta kuma juyowa a kufule. Sai ta sassauta
murya tace “Dan Allah ka bud’e min na fice.. Please..!” Tai maganar kamar mai shirin kuka.
Har lokacin muryarsa a dake “Khairy.. Look up.. Look here.. Look into my eyes and tell me you don’t love me.. Ki kalli cikin idona ki fad’a mun baki sona..!”
Ka
sa d’agowa tai ta kallesa saima shesshek’ar kukanta da Ya soma jiyowa.
Haidar ya sassauta murya wann karon “You can’t.. Bazaki iya ba.. Because you too love me.! I know you do.! Stop punishing yourself.. Stop punishing me.. Stop torturing our love.. Stop
being stubborn Khairy..! Look, Our life will be good as it was.. I promise you.! Those days.. Those beautiful days kin tuna..?! Ya k’arashe cikin sigan rad’a sihirtaccen murmushi saman fuskarsa.
Katsesa ta da fad’in “Dan Allah ka bud’e min na fice.. Na
rok’eka.” Ta k’arashe tana had’e hannayenta biyu alamun rok’o hawaye naci gaba da gangaro mata.
Hisham na daga gefe yaga fitowar kowa daga cikin motar amma baiga ta fito ba. Duk ya damu. Sai tambayar kansa yake cikin zuciyarsa uban mai Haidar yake mata
da zai kulleta cikin mota Ya hanata fita.
Yana tsaka da tunanin yaga ta fito ta nufi cikin gidan tana matsan hawaye.
Yabi bayanta da kallo Har ta shige kafin Ya maida dubansa ga Haidar da fitowarsa kenan shima daga motar.
Hisham Ya nufosa yana tambay
ar mai Ya ma Ummulkhair.
Dubansa Haidar yake without saying a word sanda Ya jingina jikin mota had’ida folding hannayensa saman k’irjinsa.
Hisham Ya dan furzar da huci ganin irin duban da Haidar d’in ke masa. Sai Ya sassauta murya ya soma fad’in “Look Ha
idar, don’t think otherwise… Ummulkhair kaman k’anwa take a wajena.. Kasan yanda big brothers suke.. So protective.! Ka kira hakan da kulawa na Babban Yaya.” Ya k’arashe yana daga masa gira d’aya.
Har lokacin Haidar bai daina dubansa ba. Ga mamakin Hisham
murmushi yaga Haidar ya sakar masa.
“You are a coward.! Wanda yake aikata laifi sann Ya b’uya a bayan mace. Ta Ya zaka daura nauyin zunubanka akan Anisa. What kind of a coward are you.?!” Ya k’arashe cikin k’unan rai.
Hisham ya murmusa kad’an “You know
what your problem is.. You are being jealous for no reason.. Bazan tilasta maka ka yarda dani ba.. Amma na maka akawari zan wanke kaina.. Dear Brother.!”
Sosai wann karon Haidar ke huci Ya matso da fuskar sa dab kusan na Hisham “You can fool them all you
want.. But you can’t fool me. Zan kama ka a cikin hannuna Hisham ka yarda dani.!”
Hisham Ya dan lumshe ido “Haidar…”
Dakatar dashi Haidar yai “You might be my father’s Son.. But you will never.. Never be my Brother..!” Yaci gaba da jinjina Kai still yan
a duban Hisham d’in “And let me make this clear to you.. You will stay the hell away from Khairy and my Son..!” Bai tsaya sauraron amsar Hisham ba yasa kai ya shige.
Hisham yabi bayansa da kallo muguwar murmushin nan saman fuskarsa.
**
Koda suka isa gid
an sallah sukai kafin suka hadu gaba d’aya tsakar gida gwanin ban sha’awa sai hira ake kowa Ya yafi kowa an zauna inuwa guda. Mai yafi yafiya da zama lafiya dadi a duniya. Gaba d’aya ‘Yanmatan kitchen suka shige sanda sukaga Hajja ta mik’e zata daura girki
. Nan suka karbe ragamar girkin daga hannun Hajja sukace ta huta zasuyi komai.Azeema, Badia harma da Khulsum idan ka d’auke Ummul mai jego dake daga d’aki.
Aunty Asshe ce ke tsaye daga k’ofan tana duban ‘Yanmatan yanda suke ta k’ok’arin daura girkin sai
raha suke tsakanin junansu suna tuno lokutan k’uruciya sanda suke kwaba girki a gida. Sai Tai tsaye tana dubansu tunanin nata ‘yar dake tsare ofishin yansanda Ya fad’o mata. Tasa bayan hannu ta goge hawayen. Jiki a sanyaye ta shige wajen Mommy da Mama Tani
yanda Mama Tani d’in ta cikata da labarai na barkwanci.
Wayar Mommy na parlor saman kujera yayinda suketa fira saman darduma a veranda. Daddy sai kiran Wayar yake Mommy kam bama ta sani ba tana can Tani ta cikata da hira.
Hajja ce ta fito daga d’aki w
ajen Ummul nan ta hangi wayar sai ruri. Taje da zummar dauka ta kai mata wayar nan taga mijinta ke kira wato Daddy. Zuciyarta yai wani irin yankewa..Sai tai saurin matsawa da baya. Saima ta fice daga parlorn cikin sauri ba tareda ta tab’a wayar ba sabida z
uciyarta da Ya tsananta bugu.
Koda Daddy bai samu wayar Mommy ba sai ya kira na Haidar dake tareda Sadis daga waje saman wani d’an dakali. Nan Daddy ya buk’aci ya hadasa da mahaifiyarsa idan suna tare. Haidar ya mik’e Ya nufi cikin gidan yanda Ya taddasu
gaba d’aya kasan rumfar dake tsakar gidan. Mama Tani da Ummul na daga ciki tana taimaka ma Ummul d’in da wanka. Jaririn kaw na rik’e cikin hannun Hajja shima an masa nasa wankan Mommy tana fad’in a kwantarsa cikin mosquito net d’insa. Hisham tsaye daga g
efen Hajja yana kallon jaririn da murmushi saman fuskarsa lokaci guda yake tambayar “Hajja wai an masa suna kuwa..? Ya kamata dai na samu takwara.”
Muryar Haidar suka sinkayo yana fad’in “Aliyu..!” Gaba d’aya suka juyo suna dubansa.
Haidar yaci gaba daga
nan yanda yake tsaye “Sunansa Aliyu..!”
Gaba d’aya sai murna Ya kacame waje Ya dauka ana Allah Ya raya Aliyu. Another Aliyu in the Family.. Aliyu the 3rd. Hajja Fannah ta mik’a shi ma Mommy tana fad’in Allah Ya raya musu BABA ALI.
Haidar Yaci gaba da
takowa Har gaban Hisham da takaici Ya nuna k’arara a fuskarsa. Yayinda hankulan mutanen dake wajen Ya tafi ga murnan sunan Aliyu da aka sake sakawa cikin ahalin Haidar kaw yai tsaye gaban Hisham da tuni yayi mutuwar tsaye wajen like a loser. Kyakkyawan mu
rmushi saman fuskar Haidar hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa. Ya dan rank’wafo da Kansa saitin kunnen Hisham “He’s named after his Dad.. He will grow up like a Lion.. Just like his Dad.!”
Hisham ya had’iyi abinda yai masa tsaye a mak’oshi yana
ji kaman ya shak’o Haidar amma ba hali.
Haidar yaci gaba “ I had a great Victory.. Like a Lion… I beat you Hisham.!” Yaci gaba da murmushi yana jinjina kai “I won.. You are the loser..” Ya gyara tsayuwarsa Ya tsaya k’yam gaban Hisham Har lokacin da murmus
hi saman fuskarsa. Har ya juya zai soma tafiya sai kuma ya juyo yace “You should change your last name.. You must be eager to bear the name Aliyu Maitama.!” Ya k’arashe still da murmushi lokaci guda ya tsime had’ida sa kai ya bar wajen. Ai Hisham bai kuma
k’ara Minti d’aya tsaye wajen ba ya fice a gaggauce zuciyarsa na masa d’aci.
Ummul ma a sama taji wai Haidar yayi ma jaririnta suna ya kumayi ma Kansa takwara. Takaici ya cikata.. Sabida tsaban gadara ko sanar da ita bai ba yama kansa takwara. Tana Jin s
ai shelan sunan suke a tsakani bata ko bi takansu ba.
Bayan Mommy da Haidar Sun keb’e nan yake sanar da ita Daddy nata nemanta a waya baya samunta.
Mommy tace “Af aiko inaga na baro wayar can yanda nai sallah..” Aiko batai shiru ba Daddy ya sake kiran
layin Haidar.
“He’s calling again.” Haidar yace yana kokarin daga kiran. Ya sanar da Daddyn suna tare da Mommy sann Ya mik’a mata wayar yana mai bata privacy.
Bayan sun gaisa Daddy ke tambayarta ina ta shiga yaketa nemanta duk a dame yake maganar.
Mu
rmushi Tai kafin tace yai hak’uri hira ce tai dad’i.
Daddy yace “Ya kamata ki taho masauki haka nan.. Is getting late already.”
Daidai lokacin Hajja Fannah ta taho da abincin da ta kawo ma Haidar sai ta aje gefen Mommy ganin ba Haidar wajen.
Mommy ta
dubi Hajja Fannah sai tace “Nidai idan ka min izini zan kwana nan gidan Fannah.”
Cak Hajja Fannah ta dakata da abinda take sanda ta jiyo abinda Mommy tace. Bata ida mamaki ba saida ma taji Mommy ta saka wayar a speaker. Tana jin sanda Daddy ke fad’i daga
d’aya b’angaren “Shikenan ni kuma sai ki barni gauro a nan.”
Mommy ta murmusa kad’an “Toh ka k’ara mana kawai Engr… Kaga idan bani nan inada mataimakiya..”
“Aw haka ma kika ce.. Shikenan zan k’ara amma sai idan kece kika samo min matar.”
Mommy ta dan w
are ido “Ina ka taba ji an nemo ma miji mata.?”
Daddy ya murmusa daga d’aya b’angaren “Za’a fara akanki.. Na baki wuk’a da nama Kwaise ta.”
Hajja Fannah da gaba d’aya ta gaza sukuni daga nan yanda take duk’e. K’afafunta Har rawa suke.. tana k’ok’arin mi
k’ewa taji Mommy ta kamo hannunta gam ta hanata barin wajen.
Mommy ta d’ago ta dubeta bayan sun gama waya da Daddy.
“Fannah nasan nayi kasalandan ma rayuwarki.. Amma bakida gidan da Ya wuce gidan Aliyu Maitama. A baya nayi zaton cewa zamana ni kad’ai a
gidan Aliyu Maitama shi zai kawo min dawamammiyar farin ciki Shiyasa nayi duk yanda zanyi naga na rabaku.. Ashe abun ba haka bane.. Sai gashi bayan tafiyarki na rayu ni kad’ai amma Babu farin cikin da naci buri.. Ba abinda yafi komai kawo farin ciki a rayu
war nan kamar ka tsarkake zuciyarka.. Ka zauna da kowa tsakani da Allah.. Shi kuma Allah sai Ya saka maka nutsuwa farin ciki,harma da kwanciyar hankali a zuciyarka..!” Ta kuma kamo hannayen Hajja Fannah “Kaman yanda na zamto silan raba Aurenki da mijina a
baya ina so ki bani dama na zamto silar maida Aurenku a yanzu.!”
Hajja ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Mommy yayinda Mommy taci gaba da jinjina Kai murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Na san bazaki ce a’a ba dan mijina d’aya ne tamk
ar da dubu. Ki yarda Dani.. Ina son mijina.. Ina matuk’ar k’aunarsa… This is the hardest decision of my life.. Amma bazan ja da hukuncin Ubangiji ba. Ina rok’on Allah Ya had’e kawunan ‘yayanmu Ya bamu ikon kyautata ma juna tareda yima mijinmu biyayya.” Sai
suka rungume juna kukan Hajja Fannah na k’aruwa.
Asshe dake kallonsu daga nesa murmushi Tai tana mai goge hawayen da Ya gangaro mata.. A cikin zuciyarta take cewa ina ma ita da nata Abokan zaman zu zamto haka.
Bayan da Haidar Ya dawo wajen Mommy sai T
ai masa tayin abincin da Hajja ta kawo masa. Tab’e baki yai kad’an had’ida girgiza kai “I’m good Mommy.” Ya kuma duban Mommy da kyau “Mommy nace are you sure this place will accomodate you all..?” Yai maganar yana daga ido yana duban gidan cikin wane irin
yanayi.
Mommy ta jinjina kai “Eh mana. K’warai kuwa.. Kaga dukanmu mata ne haka nan zamuyi squatting.”
Da mamaki Haidar ke duban Mommy “Mommy keda kanki kike using word din squat.?!”
Mommy ta kuma murmusawa tana duban gidan “Mamaki kake Hajiya Kwaise M
aitama zata kwana cikin gidan da bai kai darajan d’akunan ma’aikatan ta ba..?” Ta kamo hannayen Haidar cikin nata “Haidar my Son. Shi dan adam bai gane cewa shi ba koman komai bane until life humbles us.. Mu d’auki rayuwa da sauki dan mu d’in daga turb’aya
muke kuma cikinta zamu koma.”
Haidar ya jinjina Kai a hankali “Haka ne Mommy..” sai karada “But Mommy.. Kinaga Khairy da Baby zasu iya kwana a nan..? I mean anyi yawa a gidan.. The place is too crowded.. Plus I don’t like the vibe here..”
Mommy ta sa
ki baki tana dubansa. Sai ta dunguri keyarsa wann karon “Rufe min baki ban son iyayi. Kai a dole kayi D’a ko.. Aiko dukanmu nan daka gani haka dai zamu kwana a nan har Allah ya wayi gari da izininsa. Naga ta yanda zakai kinibibin idan ka bud’e ido ka ganka
Abuja Baba Ali na wajen uwarsa a Kano.”
Ya dan furzar da huci kad’an “Mommy ni fah.. Gaskiya bazan iya komawa Abuja ba tareda an maida Aurenmu da Khairy ba..”
Shiru Mommy tai tana dubansa. Sai ta girgiza kai kad’an “Haidar ni a nawa shawarin. Da ka bar
maganar maida Auren nan ba yanzu ba.. Ummul bata jima da haihuwa ba… Ga abubuwan da suka faru.. Ga iyayenta can gida da zataje ta fuskanta.. Give her some time to recover.. Sai ai komai cikin lumana.”
Duban Mommy ya d’anyi fuskarsa duk a dame “But Mommy..
”
Ta katsesa “No buts Haidar.. This is the right thing to do.. Yanzu ma ni abinda nake so da kai ka kira can station din da Anisa ke tsare ka bada umarnin a saketa.. Kawo wann lokacin nasan ta gane kurenta.”
Ya d’anyi jim yana duban Mommy. Sai Ya shafe f
uskarsa da tafukan hannayensa “Mommy kiyi hakuri.. ba wai bana so a saki Anisa bane.. It breaks my heart seeing Aunty Asshe like this.. Mommy akwai Wanda nake so na kama ne.. Kuma through Anisa kawai zan kama shi.. But I promise you da zaran bincike Ya ka
mmala Anisa will be free.”
Ta jinjina kai a hankali tana dubansa. Sallama yai ma Mommy kafin ya tashi ya fice ya nufi nasa masauk’in.
**
Washe gari kaman yanda suka tsara sassafe Sadis ya kwashesu suka d’auki hanyar Kano.
Tuni Daddy ma Ya tasa kan ‘ya’
yansa Haidar da Hisham suka bi jirgi zuwa Abuja. A Cewar Daddy akwai gabatarwa na musamman da zaiyi a Company gameda ‘ya’yan nasa musamman Hisham Wanda daukacin ma’aikatan Kampanin suka sansa da ordinary employee a baya. A halin yanzu zai koma ne matsayin
D’a ga mai jagorancin Kampanin.
Ba yanda Haidar ya so sabida Daddy dole yabi umarnin mahaifin nasa ya tafi tareda su.
*
Umma na zaune tsakar gida taji Sallama Ya kacame ko ina. Ta mik’e cikeda farin ciki tana ganin masu shigowa. Mama Tani dasu Azeema
ne suka soma shigowa.. Su Azeema dasu Khulsum suka haye jikin Umma suna fad’in sunyi kewarta.
Umma ta dubesu jiki a mace ganin bataga Ummul tareda su ba. Cikin rawar