Showing 231001 words to 234000 words out of 267381 words

Chapter 78 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

83

da murmushi yana tarban D’ansa sanda Hisham d’in ya duka yana gaida Daddy cikeda ladabi. Daddy ya kamosa

ya mik’arsa tsaye yana tambayarsa how was his night. Hisham ya amsa yana wani sadda Kai k’asa yawa mutumin arziki. Haidar ya kuma yin murmushin takaici yana kauda fuska. Hisham ya k’araso ya duk’a yana gaida Mommy.. Ta amsa masa da sakin fuska tana fad’in

bismillah ya zauna suyi breakfast.

Hisham ya zauna a kujera mai kallon na Haidar murmushi saman fuskarsa yake fad’in “Good morning bro… I hope I didn’t keep you waiting.?”

Mik’ewa Haidar yai yana fad’in “I’ll.. Go ahead..”

Mommy ta dakatar dashi “H

aidar ka tsaya kaci abinci mana.. You can’t go to work with an empty stomach.”

Haidar ya dan girgiza Kai “Kar ki damu Mommy zanci a Office.”

Daddy yace “Koma ka zauna Haidar..”

Ba don yaso ba ya komo wajen zamansa.

Hisham ya murmusa yana duban Haidar

sanda yake cakalan chips da fork “You shouldn’t be skipping your breakfast Brother.. Because, they say breakfast is the most important meal of the day… Haka ne Daddy.?”

Daddy ya jinjina Kai da murmushi saman fuskarsa “K’warai haka ne. Gwara ka dinga fad’

a ma wann D’auwan naka dan bai son abinci tuntuni.”

Hisham ya murmusa yace “K’warai ni zan bada shaidan hakan.. Dan baida abokin da ya fini..”

Banda murza fork and knife din dake hannunsa ba abinda Haidar keyi sabida takaicin da ya turnikesa. Bai tunani

n zai iya hakurin zama waje d’aya da mayaudari irin Hisham. Washe gari ma Daddy yasa yaran nasa su shirya cikin manyan kaya wann karon. Cikin su biyun babu Wanda yasan nufin Daddy. Bai kuma sanar dasu ina suka nufa ba.. A haka dai suka d’auki hanyar Airpor

t cikin shiga ta manyan kaya.

Basu zarce ko ina ba sai birnin Maidguri yanda sukai rakiya wa mahaifin nasu ya amso aurensa da tsohuwar matarsa a karo na biyu. Saidai amarya bata biyosu Abuja ba ta buk’aci ango ya bari sai daga baya ta tare dan abubuwan k

omai ya faru ne cikin sauri. Ga dangi da bata gama zagawa ba. Taso Hisham Ya zauna nan Maiduguri tareda ita amma sai Daddy ya nuna yana buk’atan Hisham d’in can Abuja kusansa.

Farin ciki wajen Hisham baya misaltuwa. Shidai Haidar bai um bai um um.. Sam b

aijin haushin matar amma yasan D’anta bak’in k’umurcin maciji ne. Snn koda suka dawo gida ya jaddada wa mahaifiyarsa tana tareda goyon bayansa duk abinda zai faru. Mommy ce ta kwantar masa hankali da fad’in babu abinda zai faru da izinin Allah sai alkhairi

domin Auren da mahaifinsa yai ma zabinta ne.

Bayan ficewar Haidar daga wajen Mommy Daddy ya shigo. Duban Mommy yai da murmushi saman fuskarsa. Zatai magana yai saurin daura d’an yatsarsa saman lips dinta. Yai gyaran murya kad’an sanda ya rik’o hannayent

a cikin nasa “You don’t have to say a word Kwaise. Yau d’in ni zanyi maganar.”

Murmushi ne saman fuskokinsu suna duban juna hannayensu cikin na juna. Daddy ya dan sassauta murya kafin yace “Do you know that.. you are the pillar of this family..”

Murmush

i Mommy tai had’ida girgiza Kai kad’an “Kai Engr.. Kar fah ka mance ni fah matar Engr ce so nasan matsayi da amfanin pillar a gini.. I might be the scaffolding that keeps the pillar upright.. But you are the pillar my Engr.”

Daddy yai murmushi mai bayya

na hakwara kad’an kafin yace “Lallai na yarda ke matar magini ce. Amma a wann ahalin you are both the scaffolding and the pillar Kwaise..

Behind every successful man is a woman. Do you think I'd be Aliyu Maitama that I am today if it weren't for you..?” Y

aci gaba da murmushi yana dubanta “Hak’ik’a Allah Ya gama min duk wani gata da Ya bani mace ‘yar aljannah irinki. Thank you for everything Kwaise.. Allah ya miki albarka..”

Ta sadda idonta kad’an tana mai amsawa da Ameen mijina.

**

Washe gari sassafe a

station ya musu. Idan kaga Anisa sai ta baka tausayi. Ta fice a hayyacinta ta shiga makarantar ta natsu. Ga mahaifinta yace ba ruwansa ya cire hannunsa akanta sann idan Asshe ma ta taka k’afa taje yanda Anisa take a bakin Aurenta. Asshe tanaji tana gani a

n mata farrak’u da ‘yarta kaman yanda tai ma Umma da ‘yarta Ummulkhair a baya. Tabbas sharri d’an aike ne. Duk yanda ka tura shi zai dawo gareka.

Hisham dai Ya gama k’ulle Anisa cikin case din ko ta ina. Sam bai bar wani k’ofa da zargi zai hau kansa ba.

K’arshe Daddy da Haidar suka buk’aci belin Anisa Daddy ya bada umarni da a rufe case din gaba d’aya .. Saidai ana tsaka da processing release papers d’in Anisa sukaji sauti daga bayansu na fad’in “Bada garaje ba. Babu yanda wann macuciyar zataje har sai

ta biya kisan yar mu da tai.!”

A tare Daddy da Haidar harma Hisham suka waigo suna duban mutanen da suka shigo station d’in.

Daddy ya girgiza kai yana dubansu cikin rashin fahimta “Su waye ku.?”

Mutumin yace “Mune iyayen Dareen da ‘yarku ta kashe.!”

S

abon tashin hankali da ba’a saka masa rana.

Ga dai iyayen Dareen Sun bayyana Sun kuma d’au alwashin sai an karb’ar ma ‘yarsu hakkin kasheta da akai wanda hakan ke nufin ba ranar fitar Anisa daga gidan kasu babu kuma ranar rufe case. Sann ba ranar yanke h

ukuncin shari’a har sai angano gawan Dareen.

Anisa ta amsa laifin ta na cewa ita ta bige Dareen da mota sabida soyayyar da take ma Haidar dan ga shaida an samu a gidan Aliyu Maitama motar da Anisa tai amfani dashi ta bige Dareen.

A halin yanzu case ake

na kisan Dareen Wanda duk wani evidence yake pointing zuwa ga Anisa. Itace prime suspect. Ita keda babban dalilin kashe Dareen sabida son da take ma Haidar kaman yanda ta tassama kashe Ummulkhair.

Allah sarki Anisa dole ta baka tausayi dan ba wanda zai

fiddata daga cikin wann masifa da take ciki sai Allah. Ta saduda ta koma ga Ubangiji. Shi kawai take ambata da ya kawo mata d’auki.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*59*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Safiyar ranar Alhamis Haidar ya fito ciki

n shirin fita Office. Can wajen motoci ya hangi Hisham na zab’en motar da zai d’ale. Saida ya hangi fitowar Haidar kafin yai murmushi ya isa jikin farar SUV da Haidar ke hawa time to time ya dafa motar yana duban Haidar murmushin nan nasa saman fuskarsa “H

ow about this ride.. Baka tunanin zai dace Dani..? Dear brother..!”

Haidar baice dashi komai ba ya nufi motarsa. Har ya isa jikin motar ya d’ago yana duban Hisham da murmushi saman fuskarsa “Bazaka tab’a zama kaman Haidar Maitama ba, no matter how hard

you try.. Kasan dalili..?” Ya tsare Hisham sosai da ido “You are nothing like me.!” Yana ida fad’in haka ya saki murmushi kad’an kafin ya juya zai shige motarsa. Sai kuma ya juyo kaman Wanda ya tuna wani abu. Ya dubi Hisham yace “Make sure you don’t lose t

rack of time.. You don’t want your Boss to arrive first before you.!” Ya k’arashe yana nuni da agogon dake daure hannunsa. Lokaci guda yasa kai ya shige mota yaja motar ya fice daga gidan.

Takaici ya cika Hisham. Ya bigi tayar motar da k’afarsa guda tsan

ar Haidar na kuma ruruwa cikin zuciyarsa musamman idan ya tuna yana sama dashi wajen aiki. Da takaicin Haidar ya nufi Company. Yana tafe hanya Daddy ya kirasa ya sanar dashi ya zama in charge bazai Sami shigowa company ba ranar. Haba nan fah kan Hisham ya

kuma fashewa yana jinsa sama da Haidar.. Alla alla yake ya isa Company ya nuna ma Haidar kasawarsa tinda gashi Daddy shi ya k’ira ya bar masa ragamar komai a hannunsa. Yau sai ya wulak’anta Haidar ya k’ask’antar dashi a company. Allah yasa ya Riga Haidar i

sa ya wulak’anta sa.

Haidar kaw bai isa Company ba Daddy ya kirasa yace ya juyo zuwa gida. Ba musu ya dawo ya tadda mahaifin nasa.

Farar shadda mai dankaran kyau da tsada Daddy ya basa yace ya sauya shiga zasu wani wajen. Ba musu Haidar ya amsa yai ya

nda Daddy yace duk a tunanin Haidar Maiduguri zasu sake komawa tinda bai jima ba sukaje suka amso auren Daddyn.

Wann karon ma airport suka nufa saidai ga mamakin Haidar maimakon Maiduguri wann karon Garin Kano suka nufa. Suna isa Sadis ya isa ya d’aukosu

. Shidai Haidar sai aika ma Sadis kallon tuhuma yake yayinda Sadis ke ta faman k’unshe dariyarsa dan shima Sadis d’in cikin shiga ta manyan kaya yake.

Haidar bai ida Shan mamaki ba saida yaga Sadis ya dire su k’ofan gidan su Ummulkhair. Ga tsirarun muta

ne da basu shige a k’irga ba zaune k’ofar gidan. Can ya hangi mahaifinta yayi shiga ta manyan kaya shima. Kan Haidar ya kuma d’aurewar.. Toh kodai bikin radin sunan little Haidar ake bacin haka bai tunanin Abba zai barsa ya tako k’ofar gidansa balle har y

a basa wajen zama.

Haidar ya saci kallon Daddy da mamaki sai yaga Abba ya mik’e ya nufosu ya tarbi Daddy suna masabaha. A hankali Haidar ya janyo Sadis ya rage murya sosai yace “Now you tell me.. What is going on.?”

Sadis ya murmusa “Baza’a ji a bakina

ba Ango.”

Haidar ya girgiza kai “Ango.?”

Sadis yace “Kashh.! Ka jini da sub’utan baki.. Kaga gashi can Daddy na mana alama da hannu.. Mu k’arasa.”

Jiki ba wani k’wari Haidar ya soma takowa da jagorancin Sadis dan gani yake kaman Abba zai fatattake sa ka

man dai yanda ya saba.

Ga mamakin Haidar baki har kunne Abba ke nuna masa wajen zama “Bismillah Aliyu.. Taho ka zauna.. Ga Imam din ya k’araso.”

Haidar ya zauna bugun zuciyarsa na k’aruwa. Bai k’arasa Shan mamaki saida yaji da kunnuwansa Daddy na nemar

masa da a sabunta aurensa da Ummulkhair.

Abba yai na’am da batun a take Daddy ya fiddo sadaki ya bayar aka samu cika cikan aure. Sadaki siga da kuma shaidu nan take a sabunta Auren Haidar da Ummulkhair cikin abinda yai saura na wancan Auren.

Tuni Sadis

ya mik’e yana rabon goro da alawa.

Tsananin shock ya hana Haidar furta koda kalma har saida Abba ya mik’a masa hannu sukai masabaha ya kuma tayasa murna sann ya jaddada masa amanar ‘yarsa Ummulkhair a karo na biyu.

Daddy ya tabbatar masa in sha Allah z

asu rik’e amana dan Ummulkhair ‘ya ce wajensa kaman Haidar.

*

Koda Abba ya shigo gida sai yasa aka masa kiran Ummulkhair. Kanta a k’asa ta k’araso ga Abba. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yai gyaran murya kad’an “Ummulkhair.”

“Na’am Abba.” Ta furta a

hankali.

Abba yaci gaba “A yau na maida aurenki da mijinki Aliyu kaman yanda na Sami yarda da amincewar ki.. Ki sani ke ‘Yata ce banida burin da ya shige na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Burin ko wani mahaifi shine rayuwar yaransa ya ingan

ta. In sha Allah zaki kasance cikin aminci kaman yanda kika kasance mai biyayya a garemu. Na jarabta mijinki ta hanyoyi da dama a lokacin da baki nan kuma Tabbas Aliyu yaci jarabawa dan na gamsu da hankalinsa tarbiyarsa dattakunsa da kuma irin k’aunar da y

ake Miki. Hak’ik’a bani tunanin akwai wani Wanda ya cancanci zama mijinki sama da Mahaifin D’anki. Allah ya muku albarka ya albarkaci zuri’arku ya kuma zaunar daku lafiya.”

A hankali ta amsa da Ameen Abba.

Abba ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Gameda maga

nar tarwarki gidan mijinki mahaifiyarki ta buk’aci da an dan bada lokaci ki Sami k’arfin jikinki jariri Aliyu ma ya dan yi kwari. Tuni nayi magana da mahaifin mijin naki ya kuma samu mijinki da batun kuma an samu daidaiton fahimta. Ina fata hakan kema ya m

iki.”

Ta kuma sadda kanta kad’an “Duk yanda kukayi daidai ne Abba.”

Ya kuma murmusawa cikeda Jin dadin biyayyarta a garesa shi mata albarka ya kuma kafin ya sallameta.

Cikin gida ya kacame da guda da murna. Ga murnar radin suna ga murnar sabon Aure. Mu

rna ta ko ina sai son barka.

Saidai Sam Amarya Ummulkhair bata bari Angonta ya sakata a idonsa ba har ya Kama hanyar Abuja a washe gari. Koda shima din bai nemi ya ganta ba.

**

Isowarsu Abuja Kai tsaye company ya nufa dan yasan can zai Sami Hisham.

H

isham sai cika yake yana batsewa. Haidar yanaji yana bada umarnin kar a bar kowa ya shigo ya damesa yanda kasan shine shugaban kampanin. Haidar bai tsaya sauraron kowa ba ya tura k’ofar ya shige. Idon Hisham naga computer din dake gabansa ba tareda ya dub

i Wanda ya shigo na ya soma fad’a yana fad’in waye ya shigo masa office ba izinin sa. D’agowar da zai suka had’a ido da Haidar.

Murmushi Haidar ya sakar masa sai yace “Tuba nake Mr CEO, na shigo ba tareda izini ba.”

Murmushi Hisham d’in ma yai kafin ya n

una ma Haidar wajen zama “Welcome brother. Bismillah have a seat.”

Haidar ya girgiza Kai kad’an “Ba zama nazo yi ba. But thanks anyway..Nazo ne na baka wann.!” Yai maganar yana saka hannu a aljihun sa. Sai ya Ciro goro da alawa na Aure. Tinda Hisham yaga

haka zuciyarsa ke tsinkewa.

Haidar ya aje masa goron da alawan saman table d’insa.

Hisham Ya girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “What are.. we celebrating, Brother.?”

Har lokacin murmushi ne saman fuskar Haidar “Ka tayani murna. Jiya an maida aure

na da matata UMULKHAIR.! Don’t you think is enough reason for us to celebrate.?”

Kaman sauk’an aradu haka Hisham yaji batun. Ya saki baki da hanci cikin tsananin shock yana duban Haidar.

Sai kuma Haidar ya janye alawan. Sosai Ya matso da fuskarsa kusan

na Hisham. Ya rank’wafo suna duban juna cikin ido. Murya a dake yake furta “Goro shi ya kamaceka dan na tabbata kana jin d’aci a ranka fiyeda dacin goron nan. !” Ya sakar masa murmushi yana jefa candy din a bakinsa ya kashe ma Hisham ido guda sann yaci g

aba “Enjoy the bitterness of those kola nuts.” Daga haka sa kai yai ya fice.

Har lokacin Hisham bai dawo daidai ba. Ya kasa yarda da abinda yaji. Wai dama tafiyar da Haidar da Daddy sukai ba tafiya bace ta kasuwanci. Tafiya ce ta Auren Haidar d’in. Lalla

i ma Daddy yama raina masa hankali.. Shi yana nan yana k’ababa yana murnan Daddy ya fara sakar masa ragamar company Ashe munafuntarsa yai.. Ashe ya tafi ne dan ya karb’ar ma d’ansa Auren Ummul d’insa da yai komai dan ya tabbata ya rabasu da Haidar d’in. Ya

ci gaba da huci yana jinjina kai. A zuciyarsa yake furta ‘You don’t want to play fair Haidar.! Idan haka kake so.. I can play dirty as well.. Yanzu wasan zai fara kawai ka jira ka gani.’ Ya k’arashe zancen zucin nasa yana sakin huci idanunsa na kuma kad’aw

a. Sauri sauri ya fito daga Office d’in ya nufi elevator. Wata staff tai saurin dakatar dashi sanda zai shige elevator din “Em excuse me sir. That’s Mr Haidar’s private elevator.”

Huci Hisham yake yana dubanta “Ke kinsan ni waye.? Kinsan da waye kike mag

ana.?!” Yanda yake mata maganar cikin tsananin tsawatarwa ya janyo hankulan sauran mutanen.

Hisham yaci gaba da huci yana furta “I am Hisham Maitama.! I own this company.. I can fire you right this instant if I want.!”

Sai ta soma basa hakuri tana neman

hanyar tsira. Yaci gaba da duban mutanen wajen kaman wani zararre “Sunana Hisham Aliyu Maitama. The Eldest Son of Engr Aliyu Maitama. Did you all get it.! Ni ne Hisham Maitama. Hisham Maitama.. Everything here is mine. I own this company.! Dukkanku ku saka

wann a cikin kawunanku.!” Yana ida fad’in haka yasa Kai ya shige cikin k’unan rai.

Shi d’ayansa yana driving yana buga steering wheel yana furta “Damn you.! Damn you Haidar.! Damn you..!”

Waje ya nema yai parking yana maida huci. Sai k’ullawa da sak’aw

a yake yana neman ta yanda zai b’ullo ma al’amarin. Dan Alk’awari Ya dauka bazai taba saduda ba. A fili Ya futa “ANISA.!” Anisa dai ita kad’ai ce card d’in da zai sake amfani da ita. Kai tsaye motarsa ya shige ya nufi jail din da Anisa ke tsare.

Sosai A

nisa taji mamakin wai Hisham Ya kawo mata visit.

Hisham Ya tsareta da ido yanda ta rame tai duhu duk ta fice hayyacinta kaman wann Anisa ‘yar gayu da Ya sani ba.

Ta dan rausayar da ido had’ida furzar da huci. Wanda saida tai wann d’abi’ar nata ma Hisham

Ya tabbata ita d’in ce.

“Mai ya kawoka wajena.?” Ta tambaya tana dubansa.

Hisham Ya murmusa “Alkhairi.!”

Ta dan girgiza Kai kad’an “Kai har akwai wani alkhairi tattareda kai Hisham. Bayan duk abubuwan da ka mun. I’m in this situation because of you.”

Hisham ya dakatar da ita “No Neesa. You are in this situation because of your stupidity. Kinga duk ba wann ba.. Idan Har kika amince da batun da nazo Miki dashi ki yarda dani you’ll be set free..”

Tai murmushin takaici “Now I understand everything. Kai

din ka jima da sanin Haidar d’an mahaifinka ne. Kaidin fansa kawai kake nema kan Haidar da Aunt dina Shiyasa kai amfani dani. Shiyasa ka b’oye min komai naka baka sanar Dani cikinka ba kaman yanda ni na sanar dakai nawa. Ashe amfani Dani kawai kake dan ka

cimma burinka.” Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Kayi amfani dani a karo na farko bazan bari ka sake amfani dani ba Hisham.. Dareen was right kaman yanda kai amfani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login