Showing 33001 words to 36000 words out of 174924 words
ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta
ka yi wa bayanin da sai ya fi"
Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata
kuka ashe itama aikatau take
yi gidan su Saleem
ɗ
in? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana
cewa Talatuwa
"ko za ki kai ni wurin hajiyar?"
Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she's too
young and fragile kaman she's having a lot a cikin zuc
iyarta.
Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ƙauna da
tausayin Afeefah kaman jikar ta.
Talatuwa ta duƙa gaban mommy bayan ta bar su a waje "Hajiya da ma wai likitan ne yake son
gani ki".
Kan mommy ta yi magana ma
sameera tayi saurin cewa
"Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi"
Samha ta
ɗ
ago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin
daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo.
Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta
kame nagartarshi da kwarjininshi ya
sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama
Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta
gaishe shi itama ya amsa mata kan ya du
bi mommy
"Da ma akan patient
ɗ
i ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin
komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da
kuma low BP da ya addabe ta"
Mommyn ta yi kaman bata san
bata da lafiya ba tace
"Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya,
mutum kullum a maƙale a
ɗ
aki ya ba za'a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta"
Sulaiman ya
ɗ
an murmusa don wannan ba hujja bace a ga
reshi idan kai ka kula da mutum ba
lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai
ke da alhakin leƙa wa ka ji shin yana lafiya?
"Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son int
erracting da kowa ya
fi gane ka
ɗ
aici da rashin magana yana shiga ƙuncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya
kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sauƙi ta
komawa aikinta in Shaa Allah"
Sameera ta riga mommy m
agana
"In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya"
Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara'a take ta
kallonshi.
Mommy ta ce
"Ba na son ka fa
ɗ
awa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma sak
a ido ne a kanta duk
hankalinshi ya tashi, bills
ɗ
in ka dinga turomin zan ke covering"
Ya gya
ɗ
a kai kawai yana kokarin Miƙewa Sameera tace
"Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?"
Ya ce
"No na gode, ai daga gida na fito"
Daga an suka fice suka bar su.
Wayans
hi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya
ɗ
an zubawa Layin salim ido yana nazarin
abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya
san Afeefah bata da lafiya to me kenan? Ɗan shrugging Kafada yayi kan ya dan
na ƙiran salim
yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya
ɗ
aga
"Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?"
"Calm down Captain jikin da sauƙi"
Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mom
myn. Numfashi ya sauƙe bai wani ji
damuwarshi ya ragu ba don ya san da matuƙar wuya su bi ta kanta, roƙon Sulaiman yayi da
akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari.
Yana dan murmushi yace
"ba ka da matsala in shaa Allahu"
"Thank
you so very much Doctor"
"Ɗo not mention"
Daga nan suka ajiye wayar.
"Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim
ɗ
in?"
Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah
ɗ
in.
"Ni ma sai yau nake fahim
tar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su
ɗ
auki
ma'aikatan su da muhimmanci ba"
Ta
ɗ
an juya kai cikin manyanta tace
"ko kuma ita Afeefar ce ba su
ɗ
auke ta mutum ba ba"
Ajiyar zuciya ya sauƙe daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gid
a, ta sauka
kenan yana shirin ƙarasar da motan parking space ta juyo ta kira shi
"Alhj ƙarami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gya
ɗ
a ka kai
mata kila ta iya shan shi"
Ya amsa da
"Toh Baaba Allah ya kaimu dare
ɗ
in"
Ya
ƙarasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai
dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole.
Da misalin ƙarfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi
na
baƙi, skin
ɗ
in shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai
tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat
ɗ
in shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke
zaune cikin kujera ta
ɗ
aga kai ta kalleshi
"An fito kenan bokan Turai
?"
Yayi murmushi yana furta
"Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin"
"A'ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?"
"Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban leƙo ba ashe Baaba kam
tayi ta
baki labarin Afeefah"
Tana murmushi tace
"Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka
leƙa kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka kar
ɓ
a ka tafi mata dashi"
Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan
kitchen
ɗ
in baabar tana side
ɗ
in su bai neme ta bane
saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar
neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da
tsari ta shirya mata kom
ai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar
mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a
sa
ɓ
ani suke.
Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai
nemi iso don
bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi
mudi dake zaune bakin gate da iliya.
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Yayi musu sallamar yana sake miƙa mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi
"Don Allah ku dan yi haƙuri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?"
Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna
suna zazzaro ido, mudi ya ce
"A'a malam sai dai ko in nema m
aka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da
wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada"
Ya ƙarasa cikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gya
ɗ
a kai tabbacin hakan ne.
"Magana ya ta
ɓ
a haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam
mai gadi?"
Yayi maganan yana
ɗ
an dariyar yadda suke reacting.
"Kai dai in ana sallah ba'a magana"
Iliya ya fa
ɗ
a, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen
ɗ
in
"Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wan
ke-wanke zo ki ji da shi"
Sameera da ke shigowa kitchen
ɗ
in ta
ɗ
an yi jimmm kan tace
"Talatuwa ci gaba da aikin bari na je"
Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta
ɓ
ace, sai da ta koma
ɗ
aki ta dubi kanta ta kuma ƙara turare kan
ta fito ta nufi waje, Sula
iman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai
na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman
ke dariya... Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi.
Kal
lon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke
bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta
na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar
shi, ta shiga gaishe shi ya amsa
yana murmushi
"Whats so funny haka Dr.?"
"Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?"
Ta
ɗ
an yi farrr
"Sauri kake haka?"
Ya
ɗ
an duba time a agogon dake
ɗ
aure bisa tsintsiyar hannun shi
"Kusan hakan don kaman
na shiga lokacin aikina"
Ya ƙarasa yana nufar mota, ta bishi suka jera.
"Ai ma kuna ƙoƙari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da
aikinshi"
Ya
ɗ
an yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya bu
ɗ
e booth ya
ɗ
auki ky
akyawar
basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu
ɗ
in kayan ciki da suka nuna suka yi
tu
ɓ
us cike da kayan kamshi, ganin basket
ɗ
in sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta
sake ganin ƙatuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya a
laƙar nan na likita da marar
lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba?
Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da
bugun tara-tara ba, kar dai ta fa
ɗ
a soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ƙw
arin
gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya
bugawa ko ta shaƙe yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ƙwarin gwiwar. Ta
manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da za
ƙ
ewa haka, wayar ƙarya ta ƙirƙira
ya
ɗ
an kalleta
"Ka je Dr zan sameka"
Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ƙarya, shi kam bai damu ba ya nufi
ɗ
akin
Afeefah
ɗ
in a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya
ɗ
an yi ya fahimci maza ne ci
kin
ainihin Boys quaters
ɗ
in don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su?
Sam tsarin bai mishi ba... Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci saleem yayi
hakan ne don ya bata kariya Dukda haka shi abin bai burge shi b
a, ya juya ya kalli main building
na gidan, yanzu duk girman gidan nan a ce babu inda za'a ajiye Afeefah sai cikin maza?
Kimtatar lokaci yayi daga knocking da sallamar shi zuwa yanzu kan ya tura kofan ya shiga da
wani sallama again, ta lalla
ɓ
a ta tash
i zaune ta sanya hijabi tana jingine da gini ƙafafunta na
cikin bargo
"Sannu da zuwa Dr"
Ta fa
ɗ
a cikin sassanyar muryarta da ya ƙara ƙasa sossai.
"Sannu Afeefah ya jikin dai?"
Ya fa
ɗ
a yana ajiye abubuwan hannunshi
"Da sauƙi"
Plate na safen nan ya
ƙ
ara gani a yadda aka ajiye da safe, wani tunani ne ya darsu a ranshi
hakan ya sa ya miƙa hannu ya bu
ɗ
e ga mamakin shi abincin nan na safe ne still zaune cikin
plate
ɗ
in, bata ci ba don ko da Talatuwa ta shigo ta duba ta ta
ɗ
auka ta tafi da shi don ta ka
wo
mata wani mommy ta koro ta akan ba za su yi almubazzaranci ba sai dai ta cinye shi kan a
saka mata wani.
"Afeefah tun safe baki ci komai ba?"
Da
ɗ
an tausayi ha
ɗ
e da zafi yayi maganan ranshi na sosuwa kwarai.
Ta Yi shiru
"Ina za ki samu ƙarfin ji
ki idan ba kya cin komai? Ai ko mai azumi zuwa yanzu dai ya sha ruwa"
Tsam ya miƙe ya nufi bayin ta, ta lumshe ido bayan ya shige chan sai gashi ya fito da bowl
ha
ɗ
e da brush ya bata, ruwan goran da ya shigo dasu ya bu
ɗ
e bakin
ɗ
aya ya dinga zuba mata
ta
na wanke bakin sai da ta gama tsaf ya mayar yaje ya zubar, ya dawo ya tsuguna ya saka
mata peppersoup
ɗ
in da kunun ya ajiye mata a kan kafafunta
ɗ
ayar hannunta na hagu ya miƙa
mata kofin kunun ta kar
ɓ
a ta riƙe idanunta na kallon cikin bowl na psoup
ɗ
in,
sai turiri da kamshi
yake fitarwa.
"Oya ci yanzun nan, ko in baki da kaina?"
Ta girgiza kai ta sanya hannu ta dauki spoon
ɗ
in ta shiga sha, da ka
ɗ
an da ka
ɗ
an yana matsa
mata har ta sha dayawa ta sha kunun kuwa sossai, fruits da ya sayo mata ya kara m
ata da shi.
Ta marairaice
"Zan yi amai fa idan na ci, cikina ya cika"
"kin manta kina tare da likita? Ai aman ma tsorona yake ji Harara
ɗ
aya tak zan mishi ya koma"
Ta saki murmushi karo na farko da har hakwaranta suka bayyana, ta sanya hannu ta kar
ɓ
i
ayaban da ya bare mata.
Magungunan ta ya duba ya ha
ɗ
a Allura yayi mata a canular tana ta wash wash ya ce
"Wato
ɗ
azu ma saboda bakya hayyacinki ne kika manta da raki ko?"
Ta duƙar da kai, wayanta ne yayi haske ya
ɗ
auko ya duba
"Saleemullah ne yayi mik
i saƙo in karanta miki?"
Ta girgiza kai alamun A'a.
"Zan duba anjima"
Ya gya
ɗ
a kai ya shiga Phone ya sanya Layin shi yayi flashing kan yayi saving da
"Dr. Sulaiman"
"kar
ɓ
i, zan zo gobe da safe duk abin da kika ji kina so ko sha'awa just give me a call
za ki samu
kin ji?"
"Toh Dr na gode"
Yayi saurin cewa
"Yanzu kam na wuce wannan matsayin tunda har jinyarki kika saka ni a bati"
Tayi dariya kuma da gaskiyar shi don ta mugun samun ƙwarin jiki, da Allah bai turo mata shi ba
haka za ta kwana don ba
zata iya cin abincin safen ba.
Sallama yayi mata ya fice don ya makara yau kam ainun.
Sameera da ke tsaye jikin Window tun
ɗ
azu ta ƙura mishi ido tana jin zafi a ranta, idan ta
kimtata daidai mintunanshi Arba'in da biyar a
ɗ
akin yarinyar me ya ajiye
shi haka? Har zafi zafi
take ji a idanunta shi kam da bai san ma tana yi ba tuni ya shiga motar shi ya bar gidan.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Ar
ewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*015*
Ta
ɓ
angaren Afeefah Dr. Na tafiya ta janyo wayan, number Dr. Sulaiman shi ne number na biyu
da ya shiga wayanta murmushi ta
ɗ
an yi bayan ta bu
ɗ
e sakon Saleem. Kusan saƙon shin na
ashirin da wani abu kenan a r
anar.
"Ya jikin? Kin ji sauƙi? Kin ci abinci? Don Allah kar ki zauna da yunwa ki ci ko ka
ɗ
an ne, ko
akwai abin da kike so in sa a kawo miki?"
Saƙonnin kenan masu dauke da kulawa.
A yanzu ma emphasizing yake akan ta ci wani abu cike da damuwa ƙarara
a kalaman nashi duk
ya damu, rubutu ta fara a hankali
"Na Ci abinci kuma na ji sauƙi sossai ka kwantar da hankalinka ka ji Ya Saleem?"
Numfashi mai nauyi ya sauƙe a sadda saƙon ya riskeshi matsalar shi ko ya baro Maiduguri ya
dawo Kaduna a yau bas
hi da damar bata kulawa yadda ya dace hakan na damun zuciyarshi
ƙ
warai da gaske.
"Alhamdulillah! Yanzu ni ma zan iya saka wani abu a baki na, na gode Afeefah. Ki kular min da
kan ki sossai in akwai wani damuwa kar ki yi ƙasa a gwiwa wurin sanar min"
Hawaye ne suka cika idanunta, me yasa zuciyarta ba za ta karye a kan saleem ba? Shi ne
mutum na biyu da ya kar
ɓ
e ta a yadda take, bai damu da maganganun mutane ba, ya ba ta
kariya daga cutarwa ya
ɗ
auko ta
ɗ
aga kan titi ya kawo ta gidan su, yana iya ƙoƙ
arin shi wurin
ganin bata zubar da hawaye ba, bata san da me za ta saka mishi ba bata ma da abin saka
mishin da ya wuce Adu'a, har ranta take jin duk abin da mahaifiyarshi da ƙannenshi za su yi
mata in har akwai