Showing 54001 words to 57000 words out of 174924 words

Chapter 19 - Haihuwa-Da-Hanji-Complete

fi kowa musulunci a duniya ba za mu nema maka aurenta ba, ba

za.mu ta

ɓ

a hada zuri'a da irin mutanen nan ba, ban da

mu don an ce mata Mayya ba duba da

irin kauyen da tarin jahilci ya musu yawa amma a yadda ta shiga duniya danginta suka watsar

da ita har suke ikikarin yanke duk alaqa da ita, da kuma yadda muka sami wannan gida ba

gidan aure bane, kana da tarin mata

masu nasaba da asali cikakku waenda suke gaban

iyayensu zaune don haka ka tabbatar baka kara tado zancen wata Afeefah ba, a yau ka fara

dubawa cikin sauran yaran da iyayensu suke maka tayin auren su za'a hada aurenka da Munir"

Kawu Ummaru yayi maganan.

Muryar shi na rawa ya ce

"Amma ka..w..."



🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ina so na yi addressing wan

i issue, na yi kokari in share in yi kaman ba komai amma dai na

kasa, wato muna zuwa wani mataki da za'a iya fara cewa Gureenjoh na wulakanci ban damu ba

saboda Allah ya gani ba wulakancin nayi ba, babu yadda za'a yi na fara littafi na yi nisa ki zo ki

ce in tura miki na amsa na kuma tura miki zuwa inda na tsaya, muna groups dayawa dake da

nake posting a maimakon ki cigaba da tarawa ko ki cigaba da bi baki yi hakan ba bayan kwana

biyu na sake yin nisa ki sake dawowa ki ce in kara tura miki daga inda na

tura miki last zuwa

inda na tsaya wallahi ba zai yiwu ba, ba zaman banza nake ba wani lokacin ni na san yadda

nake squizing time

ɗ

ina ina typing, wallahi ba zan tura ba idan za ki jira na gama na ha

ɗ

a

document na tura groups ki gani ki karanta fine, id

an ba za ki karanta ba duka a wurina daidai

ne*

*jama'a kuyi haƙuri da Page nan guntu ne pls, idanuna rufewa su ke da kyar na kai inda na kai

saboda gajiya da bacci*

*021*

"Sulaiman?? Har za ka ja da maganan Yaya a kan yarinyar? Aaa lallai, yo k

o mahaifinka ya isa

ya sauya maganan nan?"

Kawu Zubairu ya katse shi a hasale.

Shiru Sulaiman yayi sai dai idanunshi tamkar garwashi, zuciyarshi yake jin ya wani matse ya

mishi nauyi wane dutse aka

ɗ

ora mai, kawai don kawu bai da hali sai a hana shi

auren Afeefah?

Me laifin ta? Ita me tayi? Har suka shigo Kaduna bashi da natsuwa, da kyar ya kai kowannensu

gida suna ta kushe wannan neman auren nashi haka ya nufi gida ko da ya shigo a parlor ya

samu Umma, ganin yanayinshi kaman zai fa

ɗ

i ta miƙe da ha

nzari ta riƙe shi

"Sulaiman! Menene? Lafiya kake kuwa? Ko wani abin ne ya samu Afeefar?"

Girgiza kai Yayi yana neman inda zai zauna ta ja shi kujera suka zauna tare, Baaba jummai ma

da tun safe take ta adu'ar dacewa ta fito, ruwa ta je ta

ɗ

auko mishi

Umma na tsaye kanshi tana

ta tambayar shi duk ta rikice ta sanshi da masifar migrine in ya fara kuma baya jin magani,

ruwan ya kar

ɓ

a ya sha sossai tamkar zai fasa ihun kuka yace wa Umma

"Umma wai su kawu ba za su nema min aurenta ba, wai ba za su hada

zuri'a da ita ba, Umma

idan kenan kawunka bashi da halin kirki sai aka ce kaima haka kake? Me Afeefah tayi na kin

aurenta? Don Allah ki yiwa Abba magana ya samu Yayanshi zan nemi Afeefah! Zan neme ta

duk inda take ni dai don Allah ya bar ni in aureta a

haka nake son ta"

Duk sun kasa gane inda ya dosa, Abba da shigowan shi kenan ya ce

"Ba da Miyau na ba kam, sai dai kuma idan kai zaka nemawa kanka aure wannan kam zaka iya

amma tunda har Yaya ya kirani ya tabbatar min gidan chan ba gidan neman aure b

ane ba zan

ta

ɓ

a sake tado maganar ba don na san ba karya ya yi ba, da kai aka je ai ba da wani ba kuma

kaima shaida ne"

Idanun da suka sake rinewa sossai ya zubawa Abban yace

"Abba ita wallahi ba haka take ba, nitsatsiya ce kuma tana da tarbiya daida

i gwargwado, Abba

aka auri karuwa da ta tuba ma bare Afeefah? Abba ko ladarta ba za ka bari na samu ba?

Korinta fa suka yi bayan sharri da ƙage da aka lankaya mata a garin"

A yanzu kam hawaye sai da suka zuba mishi.

"Ko ma menene Sulaiman ba a zuri'a

r mu ba, ban ta

ɓ

a sa

ɓ

a maganan Yayana ba kuma ba zan

fara a kan ka ba Sulaiman, ku fara shirye-shiryen auren shi za'a hada da na Munir"

Umma ta

ɗ

ago da sauri ta kalleshi

"Alhj wata

ɗ

aya fa kacal ya saura na Munir yaushe ya gama warke wannan ciwo da za

i yi

aure?"

"Ke kenan kike goya mishi baya yayi abin da yake so ko? Toh shikenan kar yayi"

Yana kai nan ya wuce abin shi.

Baaba jummai kam har hawaye take yi, bayanin abin da duk ya faru yayi musu bayan ya gama

ya kama hannun Umma

"Don Allah umma

ko auren za'a yi min ki taimaka ki saka baki a hada da Afeefah wlh ina son ta,

tausayinta kuma yanzu ya sake kama zuciyata har ina jin kaman zai fashe"

Duk sun tausaya mata, Baaba jummai ta sha kuka sai Allah ya isa take yi a madadin ta, abin da

ya d

ame su ma kasancewar yanzu ba'a san inda ta dosa ba.

"Yanzu ka je ka sha magani ka huta sai ka je ka nemo mana ita in har muka sameta komai mai

sauƙi ne, rayuwar 'ya mace a haka hatsari ne komai zai iya faruwa, imma a yi mata mugun abu

ko kuma ta jefa

kanta halaka"

Duk sun gamsu, Miƙewa yayi ya nufi Sashenshi cike da tunanin ta ina zai fara nemanta?

*****

Saleem a Washegari aka sallameshi ya koma gida, shi ne ma ya matsa saboda ya damu da

halin ko in kula da Mahaifiyarshi ke mishi, ƙannenshi ka

m ba ya kula su bayan ya dawo wanka

yayi ya fito, har kicin ya shiga Talatuwa ta bashi abinci ya zo ya ci kan ya nufi

ɗ

akin Mommy,

sossai yake kokarin danne damuwar da yake ranshi saboda Rayyan da yayi ta ƙoƙari wurin

ganin ya manta Afeefah ya cire ta a

rayuwarshi.

Zaune ya sameta bakin gado tana danna waya, sallamar shi kawai ta amsa amma ko

ɗ

ago ido

bata yi ta kalleshi ba, a gaban kafafunta ya je ya zauna

"Ban ta

ɓ

a tunanin akwai ranar da zai zo da zan yi rashin lafiya har in kwanta na tsawon kwa

na

daya gadon asibiti Mommyna bata zo ta duba ni ba, na san na miki laifi mai girma ne shiyasa na

kasa bari in samu lafiya na nemi a sallameni don in zo in nemi yafiyarki, kiyi haƙuri in shaa

Allahu na cire Afeefah daga raina..."

Ya fa

ɗ

a a raunane

"Du

k kuma abin da kike so zan cigaba da so matukar bai sa

ɓ

awa shari'a ba ko da kuwa zai

cutar da ni ne, ki yi haƙuri Mommy"

Ɗ

agowa tayi ta kalleshi sai zuciyarta ya karye, wani sashe na cewa bata yi mishi adalci ba, wani

kuwa na bata ƙwarin gwiwa a kan a

bin da ta aikata

ɗ

in ai taimakonsu ne gaba

ɗ

aya.

"Zan yafe maka in manta irin rashin kunyar da ka yi min matuƙar ka bi umarnina na karshe a

gareka"

Ta fa

ɗ

a cikin tabbatarwa.

"Mommy ko me kike so ki fa

ɗ

a ni kuma zan cika miki ko da bana so"

"Zan aura

maka Sabreena nan da wata guda"

Da sauri ya

ɗ

ago ya kalleta amma sai harshen shi ya mishi nauyi, uffan ya kasa cewa sama da

mintuna uku kan ya ce da kyar

"Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi"

"Ita ce ma Alkhairin naka"

Kai kawai ya gya

ɗ

a ya miƙe ya

fice fuskar shi babu walwala sam, a parlor ya ga Sameera na

zaune, ido ya

ɗ

an zuba mata ganin ta mishi rama kuma ta yi zuru zuru ga damuwa nan fal a

fuskarta, kaman zai yi magana kuma sai ya wuce abin shi.

****

Ta

ɓ

angaren Afeefah ta tashi Washegar

in jikin da kwari sossai, wanka tayi ta saka kayanta ta

samu wuri ta zauna don bakunta ne fal cikinta da kuma tsoro, har yanzu Mammi bata san

wacece ita ba shin wani abu zai chanza in ta san wacece ita? Anya shi ma Rayyan ya san

wacece ita kuwa? Tunanin

da yake ta kai komo kenan a ranta har ta ji an tura kofan an shigo.

Ɗ

aga kai tayi tana amsa sallamar Abeeha.

"Alhamdulillah jiki yayi sauƙi sossai Aunty Abeeha"

Ta amsa mata bayan ta jefa mata tambayar yaya jiki, Zaro ido Abeeha tayi

"Lallai Afeefah

ni ce Auntyn taki? Kin ga kirani Abeeha na bana wani son Aunty na san ko da

zan girme ki ba zai wuci da shekaru biyu ba"

Afeefah ta

ɗ

an yi murmushi

"Toh ai ko da kwana

ɗ

aya ne kin cancanci na ce miki hakan bare har shekaru biyu"

"Ni dai bana so na b

ar miki"

Ta fa

ɗ

a da dariya, Afeefah ma tayi murmushi

"Kin karya kuwa?"

Abeeha ta tamabaya don ita ta tafi lectures 6 yanzu kenan dawowanta 9

ɗ

in nan.

"Eh sun kawo min har nan na karya, ina dai so in je in duba jikin Mammi ne kuma ban san ta

inda zan g

anta ba"

"Nima chan nayi daga nan, na fita duk kuna bacci. tashi mu je"

Miƙewa Afeefah tayi Abeeha na cewa rigarta ya mata kyau tayi murmushi tana mamakin saukin

halin Abeehar da saurin sabon ta.

Sai kallon gidan Afeefah ke yi tana ƙara yabawa abin d

a ya fi burgeta yadda ko ina kalkal sai

kamshi da sanyin Ac ke tashi, ga nan chandliers design daban daban masu kyau kowanne da

kalar hasken shi da tsaruwarshi, silifas

ɗ

in kafafunsu mai taushi kaman ka nitse ciki take ta jin

daa

ɗ

in shi don duk basa yaw

o kafa banza a cikin gidan da lofas

ɗ

in su masu kyau itama kuma

har

ɗ

aki aka kai mata saboda sanyin tiles,

ɗ

akin Mammin suka tura da sallama suka shiga.

A kan kujera suka samu Mammi gabanta fruits ne masu low potassium tana sha shima kuma in

portion n

e akwai yawan da ba zai yiwu ta sha ba, Daga kan gadonta Rayyan ne yana cikin

bargo Dukda ba bacci yake ba idanunshi lumshe yana tunanin maganan da Mammi ta gama

fa

ɗ

a mishi yanzu, numfashi ya

ɗ

an sauƙe ya bu

ɗ

e idanunshi ya kalli inda suke a lokacin

Afee

fah ta kai ƙasa Mammi na ce mata

"Tashi! Tashi a ƙasan nan Afeefah ga kujera zauna ko ki zauna bakin gado ina ke ina zaman

wannan sanyin"

A bakin kujera ta

ɗ

an dosana tana gaishe da Mammin, Mammin ta amsa cike da kulawa tana

tambayarta jiki ta ce ta

ji sauƙi, Abeeha ma ta gaisheta tana tambayar karfin jikinta duk adua

suka dinga yi wa Mammin tana amsawa, sam Afeefah bata kula da Rayyan ba Mammi da ta

kosa ta ji Afeefar daga ina take kuma ina danginta tace

"Afeefah ki yi haƙuri da tambayana, ba wa

i zan tambayeki bane saboda mun gaji dake ko muna

so ki tafi ba, yana da kyau ne tambayar saboda mu san asalinki mu san me ya rabo ki da

danginki, in kika duba yadda wannan zamani ya zama har wasu tsoron taimakon suke saboda

dayawa an fi janyo su inuwa

su tura mutum rana. Idan har baki shirya sanar da mu ba kuma za

mu hakura mu cigaba da zama dake har ki ji kin gamsu kina son sanar da mu

ɗ

in. Na yi ta

tambayar Saraki bai ce min komai ba"

Afeefah ta

ɗ

an muskuta gabanta na tsananta fa

ɗ

uwa ta ce

"Mamm

i don Allah ki daina ba ni haƙuri, ya zama dole in sanar da ku wacece ni! Ina tsoron saka

ki cikin damuwa alhali ba lafiya ce ta ishe ki ba don labarina bashi da daa

ɗ

i, bashi da abin

burgewa ko karsashi, babu abin da ke ciki sai tarin baƙin ciki, kuka da

damuwa, Mammi Sunana

Afeefah kamal na bu

ɗ

i idona ne kawai na tsince ni gaban kakata wacce ta haifi babana...."

A hankali ta cigaba da basu labarinta tun daga farko har ƙarshe, ta gaji da kuka a kan labarinta

hakan ya sa a yanzu ta danne kwarai bata yi

kukan ba sai idanunta da suka rine matuƙa gaya,

bayan ta gama ta

ɗ

ago ido tana kallon expression na su Mammin gabanta na fa

ɗ

uwa zuciyarta

na duka da ƙarfin gaske....



🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatim

a Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*22*

Ga dumbin mamakinta dukkansu biyu kuka suke yi, Abeeha kam ma da sauti yayinda Mammi

ke zubar da hawaye, ko kan tayi wani yunkuri Mammi ta miƙe ta iskota

ta

ɗ

ago ta sai ta sanya

ta jikinta ta rungume tana shafa bayanta, wannan dalili! wannan

ɗ

umin jikin shi ya saka Afeefah

fashewa da sassanyar kuka mai sauti.

Sun fi mintuna goma a haka tana wannan kukan, tuna komai take yi tamkar yanzu ne ya faru ji

take duk mace-macen yanzu ne suke dawo mata sabo, taji tana kewar mahaifiyarta da Aunty

zee, wannan tausayi da kauna da ta gani daga Mammi sai ya tsaya mata a rai ta ji itama tana

ƙ

aunar matar tamkar mahaifiyarta.

Rayyan da tun kan tayi nisa ya lums

he idanunshi bai bu

ɗ

e ba sai da ya ga kukan na yawa, duk

tsikar jikinshi jinshi yake a tashe, ko da ya miƙe zaune sai da ya ji kanshi ya sara ya

ɗ

an runtse

idanunshi ya bu

ɗ

e kan ya ja tsaki ya sauka daga gadon, ya taka ya dafa kafadar Mammi da har

lokac

in take rike da Afeefah.

Mammin gabanta ya fa

ɗ

i tuna yana

ɗ

akin ta tuna labarin Afeefah sai tayi sauri ta saki Afeefah ta

waiga tana kallon yanayinshi, idanunshi ya sauƙe kasa a hankali yace

"Mammi please ki bar kukan nan, you are sick already kukan n

an bashi da amfani, dole ne sai

mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune ka

ɗ

ai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na

nan dayawa Mammi..."

Yankewa maganan yayi ya

ɗ

ago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sarƙe cikin nata,

sama da seconds

hu

ɗ

u yana kallonta kan kawai ya juya ya bar

ɗ

akin.

"Saraki.! Saraki....!!"

Bai juyo ba ya fice, ta duƙar da kanta tana ambatar sunan Allah... Chan ta sauƙe numfashi ta

waigo ga Afeefah da tunda taji sauƙar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta y

a

tsaya chakk, ha

ɗ

a idanun da suka yi ya matuƙar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a

gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma'anar kallon nashi ta

kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta.

"Lallai Afeefah k

in ga rayuwa, haƙiƙa na ka

ɗ

u da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika

cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk

jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma

sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa,

Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin

gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu um

arnin cigaba da

kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da

hawayen baƙin ciki Afeefah... Sannu! Sannu da juriya"

Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka,

Abeeha

ta taho ta

ɗ

ago ta tana riƙe hannunta

"In shaa Allahu ba za mu ta

ɓ

a kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ƙi ka dole wani

ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ƙirani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa

Allahu ni ba zan ta

ɓ

a guda

r ki ba"

Sossai take kuka, a ranta Adu'a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ƙarshe

ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da

ɗ

a mai ido?

Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa A

llah.

Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta miƙe tayi sashen Rayyan don duk yana cikin

ranta tun

ɗ

azu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu

a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi ra

ɗ

a-ra

ɗ

a a waje, jin ha

nnunta ya sa ya bu

ɗ

e idanun da suka

sake sauyawa ya zuba mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login