Showing 102001 words to 105000 words out of 174924 words
iri da kyar bacci ya
ɗ
auketa. Chan cikin dare sai ta fara jin kaman numfarfashi a
ɗ
an
tsorace ta farka ta miƙe zaune sai ta ji kaman daga ka
n gadon da yake kwance ne da sauri ta
miƙe tsaye ta tafi ta kunna hasken
ɗ
akin ta nufi gangar shi.
Ya ha
ɗ
a zufa yayi sharkaf sai juye juye yake kaman mai mummunan mafarki, numfashinshi na
seizing kaman mai ciwon asthma hankalinta ne ya tashi bata san
ta riƙe hannunshi ba tana
jijjigawa
"Ya Saraki! Ya Saraki ka tashi..!"
Duk ta ru
ɗ
e saboda yadda yake yin kaman zai mutu, da karfin gaske ta jijjigashi hakan ya sa ya
bu
ɗ
e rinannun idanunsa ya zuba mata yana sauke numfashi a hankali hankali, hawaye ne
ke
bin idanunta suna diga a duk inda suka samu zarafi kama daga gaban hijabinta har kan
hannunshi dake cikin nata.
"Mummunan mafarki kake? Sannu ka ji? Bari na kawo maka ruwa"
Duk ta rikice tsabar yadda ta ganshin ya dameta, da sauri ta nufi frigde
ta kawo mishi ruwa da
kyar ya miƙe zaune ya
ɗ
an yi tapping wayanshi ya kalli time karfe biyu, lumshe ido yayi ya bu
ɗ
e
a kanta tana miƙa mishi ruwan, bai san me yasa ya kar
ɓ
a ba ya dai tsinci kanshi yana shan
ruwan yana jin wani abu dake tsaye mishi a ma
koshi na sauƙa a hankali, sai kuma ya ji cikinshi
na murdawa yana jin amai na taso mishi rabon shi da abinci tun jiya da daddare don ko
karyawa bai yi ba rashin lafiyar mami ya riskeshi, ruwan ya miƙa mata tana daga tsaye tana
kallonshi har lokacin idan
unta na cike da kwalla.
Ƙ
oƙarin sauƙa yake daga gadon ba tare da ya ce uffan ba sai jiri ya kwashe shi ya tafi zai fa
ɗ
i
da wani irin hanzari ta riƙe shi
"Ya Saraki baka da lafiya...! Jikinka zafi sossai me kake so in kawo maka?"
A karye take maganan,
kaman ba zai yi magana ba yana tsaye tana dafe dashi Dukda ya
tabbatar in fa
ɗ
uwar ne
ɗ
an tiny body
ɗ
intan nan bai isa riƙe shi ba a hankali yace
"Amai...!"
Kalma na farko da ya furta kenan tun bayan Ameen da yake ta cewa in an yiwa Mammi Adu'a.
"Amai
za ka yi? Sannu mu je bayin ko in kawo maka abu ka yi daga nan?"
Shiru ya mata sai ya yunkura zai cigaba da tafiya nan ta gane bayin yake son zuwa da
taimakonta ana tafiya ana hutawa suka shiga bayin, sai da ya dafe jikin sink ya kalleta ya kalli
kofa.
"In fita? Za ka iya?"
In ba don halin da yake ciki ba za ta iya rantsewa ya Harare ta, bata ƙara magana ba ganin ya
zuba mata idon da suke sake firgitata da bata tsoro ta fice da sauri sai da ta rufe kofa ya lumshe
ido.
Kai tsaye kitchen nasu taje
ta ha
ɗ
o tea mai kauri ta dawo
ɗ
akin gadon da ya jajjanye bedsheets
ɗ
in ta gyara ta tsaya daga gefe kaman security, ganin ya jima bai fito ba ta yunkura ta nufi bayin
tana shirin yin knocking yana bu
ɗ
e kofan da sauri ta matsa baya, ya kalleta ya dauke ka
i ganin
bashi da ƙarfin jiki ta matso ta kama hannunshi bai hanata ba har suka isa kan couch ya zauna
yana jinguwa tare da riƙe kanshi da kaman zai fashe yana cewa
"Asshhhh!"
Kaman zata yi kuka take jera mishi sannu.
Tea din ta
ɗ
auko
"Ya... Saraki!
"
Ta fa
ɗ
a a rarrabe, ya
ɗ
an bu
ɗ
e ido ya kalleta yana jin sunan na mishi wani iri har a cikin jikinshi
"ka sha tea ka ga cikin ka babu komai sai ka sha magani Don Allah..."
Ya lumshe ido kawai fuskar nan tamau, hawaye ne ya zuba mata ta
ɗ
an ja Shesheka s
ai ya
bude idanun yana kallonta ya zubawa hawayen idanu haushi yake ji, takaici yake ji Meyasa shi
ba zai yi kukan kaman kowa ba? Meyasa take da arhar hawaye a sadda shi yake nema?
Zuciyarshi zafi yake mishi ra
ɗ
a
ɗ
i da kuna yake mishi.
Hannu ya miƙa m
ata don yana da buƙatar yin Sallar isha don bai yi ba kuma ba zai iya samun
karfi ba matukar ba abu bane ya shiga cikinshi, da sauri ta miƙa mishi ta koma gefe tana share
fuskanta wanda ta rasa me yasa hawayen nata suka ki tsayuwa muddin ta kalleshi sai
ta ji suna
zubowa tsabar tausayinshi.
Kurba bai fi hudu yayi ba ya ajiye, ta dubo magungunanshi ta ajiye mishi ya kalleta tace
"Don Allah Ya Saraki ka sha ko zaka samu sassauci...!"
A karye tayi maganan yayi shiru
"Wanne ne zan cire maka?"
Ya sake
yin shiru
"Ya Saraki...!"
"Get out of this room..!"
Yayi maganan a kausashe ta girgiza kai za tayi magana ya ce
"Nowww!"
Da ƙarfi yayi magana yana zaro mata idanu...
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fat
ima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*39*
Kuka ta sakar mishi mai sauti ya kawo idanu ya zuba mata yana mamaki a ƙasan ranshi, ganin
ta ƙi fita ya sa bai bi ta kant
a ba ya
ɗ
auki maganin ya hadiye ya tura mata taje ta
ɗ
auka ta
mayar inda ta samu ta sake ja ta tsaya, Miƙewa yayi ya isa wurin Sallarshi ya tada sallah.
Bayinshi ta shiga itama tayi Alwala ko kan ta fito ya idar da isha nafilfili yake yi itama ta fara
nafilfilin sai uku da wani abu taji ta gaji shima yana zaune ne kanshi da yake jin kaman zai fashe
jingine da jikin gado, Miƙewa tayi taje ta kwanta a inda ta kwanta da farko nan ƙasa tana
kallonshi zuciyarta cike da tarin tsantsar tausayinshi tana kuma
mamakin irin karfin halin da tayi
har bacci ya sureta bata sani ba.
Karfe biyar da rabi ya bu
ɗ
e idanunshi ya miƙe yaje yayi alwala, har ya wuce ta kaman yayi
fitanshi ya kyaleta sai ya tuna irin kulawar da ta bashi a daren na jiya da irin yadda tayi
ta zubar
da hawaye akan damuwarshi, ko da Abeeha ce ba zai barta ana sallah tana bacci ba,
tsugunawa yayi don bashi da wani ƙarfin magana ya sa hannu ya
ɗ
an ja hijab
ɗ
inta firgigit tayi
ta tashi tana kallonshi don baccin dama rabi da rabi ne inda bata s
aba ba, Miƙewa kawai yayi
ya fice bai ce komai ba.
Da sauri ta miƙe taje ta yi Alwala ta zo ta gabatar da sallah, bata tsaya doguwar Adu'a sossai
ba ta miƙe ta gyara
ɗ
akin tsaf ta share ta saka turaren wuta kan ta fice zuwa babban kitchen,
duk abinci
n da aka ci jiya a wurin makoki order ne daga manyan restuarants yau kuma a gidan
za'a girka don haka tana bukatar ganin me zasu yi Dukda ba wasu mutane ne na waje ba
kadan da suka Kwana duk na gida ne.
Pepper soup ne na cowtail da bread sai tea da su
ke zubawa flasks flasks daga nan ta wuce
wurin Abeeha ta samu idanunta biyu suka gaisa take tambayarta jikinta ko da Abeeha ta
tambayi
"Ya Yaya Rayyan?"
Bata wani damu ba ta ce
"Ya fita masallaci"
Murmushi Abeehar tayi
ɗ
an ka
ɗ
an Allah sarki ta je ta
kulan dashi kenan.
Shi kam daga masallaci mota ya
ɗ
auka ya fice asibiti su jannah sai ganinshi suka yi, da sauri ta
sauƙo ta zo ta riƙe shi zata fara kuka ya rabata da jikinshi ya ja hannunta zuwa bakin gadon ta
zauna.
"Menene na kukan? Uhmm? Lafiy
ar ki ya kamata ki yi focusing a kai mun riga mun yi rashi,
haƙuri kuma ya zame mana dole ki bar kukan nan"
Kai ta gya
ɗ
a tana share hawayen dake silalo mata, bata jin tausayinsu kaman yadda take jin
nashi don yana maganan ne kana jin yadda
ɗ
aci dake shi
mfide bisa zuciyarshi ke hauro wa har
kan harshen shi.
Ya gaishe da matar uncle Mansur dake
ɗ
akin
ɗ
ayar cousin
ɗ
insu ya gaishe shi ya amsa suna
ƙ
ara yi mishi gaisuwa.
Sai da yaje wurin bills aka tabbatar mishi mijinta ya biya komai ya dawo ya nemi da
su zo su
koma gida tunda ta ji sauƙi, tattara wa suka yi ya
ɗ
auko su har gida ya shiga ciki ya duba
Abeeha a lokacin Afeefah bata nan, ko da zasu fara kuka ganin juna fa
ɗ
a ya hau su dashi dole
suka yi shiru ya gaisa da iyayen da suke ciki kan ya miƙe y
a nufi sashensu har lokacin kuma
kanshi kaman zai rabe amma juriyarshi ya hana shi kwanciya.
A tsakiyar parlorn suka ha
ɗ
u ta fito daga
ɗ
akinta sanye da doguwar riga mai fa
ɗ
i sai karamin
hijab da ya shiga da kayan, ganin shi ya sa ta dake tare da danne
tsoron ta ta furta
"Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?"
Da
ɗ
an hanzari tayi maganan ganin zai wuceta.
"Lafiya"
Ya amsa kan ya wuce ya shige
ɗ
aki, zama tayi don ta san kila yanzu wanka zai yi sai da ta
ɗ
auki awa kan ta miƙe ta nufi dining ta ha
ɗ
a mishi
tean ta
ɗ
auki bowl ta dibi pepper soup
ɗ
in ta
ha
ɗ
a a karamin tray ta nufi
ɗ
akin, ya yi wanka manyan kaya ne a jikinshi kaftan baƙar yadi mai
taushi da ya sake fito da ainihin hasken fatar shi sannan ramarshi ma ya bayyana, a kan couch
yake zaune yanzu m
a yayi relaxing sossai idanunshi a rufe, waya ya gama yi da likitarshi bata
nan ta samu labarin rasuwa hankalinta ya tashi roƙon shi take akan ya samu ya zubar da
hawaye yayi leting damuwarshi fita ko ka
ɗ
an ne in ba haka zai iya samun matsala ya dai mata
shiru ne amma bai san ko zai iya ba yana son yin shima ko zai samu sassauci amma taurin
ranshi na dayawa, kuma hakan na da alaƙa da training da ya samu a farkon rayuwarshi.
Shigowar ta bai sa ya bu
ɗ
e idanu ba har ta ja
ɗ
an table ta ajiye mishi tray
ɗ
in ta tsuguna
"Ya Saraki..!"
Har ranshi ya ji sunan, bai san Meyasa duk ta kirashi hakan sai ya ji kaman an kirashi ba kuma
dole zuciyarshi take motsawa ta wani
ɓ
angaren kuma sai yaji kaman Mammi ce ta ƙira shi, dole
ta sa ya bu
ɗ
e idanu ya kalleta ta
sauƙe nata ƙasa don ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba
ko a yana ƙalau ma bare yanzu da suke a birkice.
"Ga abin kari nan na kawo maka, Don Allah ka ci ka samu ka sha magani."
Idan dutse ya tanka to ya tanka, jin shirun yayi yawa ta
ɗ
aga i
do ta kalleshi yana lumshe da
idanun abin shi.
"Don Allah dai ka ci Ya Saraki! Ko babu daa
ɗ
i ka lalla
ɓ
a ka ci ko ka
ɗ
an ne a yanzu ba mu da
wani majingina bayan kai, ko da ni bana buƙatarka su Adda Abeeha suna da buƙatarka bare ma
dukkanmu kaine bangon
mu a yanzu ba za mu so ganin komai ya same ka ba a wannan ga
ɓ
ar
da bamu warke raunin tafiyar Mammi daga rayuwar mu ba.."
Muryarta ya shiga rawa hawaye ya shiga silalo mata.
Sunan Allah yake ƙira a hankali
"Ya Allahu!"
Kalaman sun dirar mishi da wani
rauni da baya tunanin ya ta
ɓ
a jin irin raunin zuciyarshi na rawa
sossai, yadda ta furta cikin kuka ya sa yaji idanunshi kaman za su iya kawo ruwa muddin ta
cigaba da irin waennan kalaman cikin sanyin murya da Salon karya zuciya.
"Ki je zan ci!"
Ya f
a
ɗ
a a hankali, bazata taji kalaman kuma hakan ya sakata jin daa
ɗ
i tunda ya yarda zai ci ta
miƙe ta kawo mishi magungunan shi kusa kan ta fice sai da ta fita ya bu
ɗ
e idanu ya zubawa
kofan da ta rufe sama da seconds goma kan ya
ɗ
auke ya mayar kan abincin
, ya kuwa sha
pepper soup
ɗ
in mai yawa ya sha tean tare da magani ya ajiye ya miƙe ya koma kan gado ya
kwanta don jiri yake gani a cikin maganin akwai na saka bacci ko da bai so ba dole baccin ya
ɗ
auke shi dama ya saba ko da zai sha da daddare baya iya
bacci amma in da rana ne yana yi
ba tare da mugun mafarkin shi ba.
****
"Malam Labaran Haƙƙin uba zuwa ga 'ya'yansa yana da matuƙar muhimmanci musamman a
musulunce, wannan haƙƙi yana tattare da nauyin kulawa, tarbiya da tabbatar da rayuwa ta gari
ga 'ya'ya ciki sun ha
ɗ
a da:
Samar da halal
ɗ
in haihuwa wannan ba sai na yi dogon jawabi ba na san ka fahimta ya kasance
an samu wannan yaro ta hanyar aure kaman yadda addini ya tanadar.
Alhakin samarwa yaro suna mai kyau da ma'ana wadda bai sabawa Addin
i ba.
Ciyarwa da sutura uba na da nauyin ciyar da 'ya'yansa da matansa daidai gwargwadon iko,
hakanan da saya musu sutura da tufafi daidai gwargwado.
Ga babban wato ilimi da tarbiya, koyar dasu abubuwan ibada sallah, azumi da sauransu. Samar
musu da il
imin zamani da horo da zai sa su zama masu amfanar da kansu da al'umma.
Ka ga tarbiya a kan hali ba karamin alfanu yake da shi ga yaranmu ba dole ne akanka ka basu
horo a kan gaskiya, amana, girmama manya da kyakyawar mu'amala da mutane.
Suna da alhaki
akanka na basu kariya da tsaro hakan ya ha
ɗ
a da hana su mu'amala da
miyagun abokai ko dabi'u kaman su shaye-shaye, fasikanci da sauran su.
Malam Labaran uba kan zama abin koyi ga
ɗ
a wajen addini, hali da mu'amala ina so ka yi
nazari a iya tunanin ka mat
sayinka na uba kuma miji me ka sauƙe a cikin waennan?"
Inna Larai ta numfashi
"Wallahi malam liman ina ga bayan hakkin farko na samar da su ta hanyar aure babu abin da
Malam Labaran ya sauƙe ciki ko haihuwa aka yi mutumin nan baya ragon suna."
Inna A
sabe da kanta ke ƙasa tace
"Mun samu tawaya sossai saboda rashin ilimi da rashin sani gashi mun lalata rayuwar
'ya'yanmu"
Malam Labaran yayi shiru jikinshi a sanyaye kenan shi fa Allah zai kama da laifi? A hankali yace
"Toh malam liman wani hanya za
mu bi mu gyara abin da muka
ɓ
ata tun farko? Hakikanin
gaskiya ina samun abin da zan iya rufawa kaina asiri da gidana amma son zuciyata ya sa nake
kyashin sayowa in kawo, kowa ta kanshi yake kaman rayuwar bariki hatta sutura wannan na
manta rabon da in s
aya ma kowa a gidan, Dukda ina kallonsu da suturu da ma wasu ababen
ƙ
awa amma ban ta
ɓ
a tambayar ina suka samu ba sai ma fata nake in ga nasu in kwace ko in
sace...kaico kaico da wannan rayuwar jahilcin"
Hawaye ne ya zubo mishi don sai a yanzu yake fahim
tar irin illar da jahilci yake dashi, ga yaran
duk sun lalace ya tabbatar babu mai auren su a tunaninsu Afeefah ce ba zata auru ba saboda
yadda tayi tambari a garin sai gashi ta auri wanda kaf kauyen basu da kamarsa, haƙiƙa yayi
matukar nadamar abubuwan
da yayi tayi a baya na tsantsar rashin ilimi.
"Hanya
ɗ
aya ne jal kuna raye lokaci bai ƙure ba, ayi Adu'a a nemi yafiyar waenda aka zalunta
babban hanyar shine a nemi sani akan addini."
Nasiha ya cigaba da yi musu mai ratsa jiki sai gashi duk jikins
u yayi wani irin sanyi, inna Larai
dake fama da azabar kafa kawai ta kama kuka, lallai Allah mai girma ne kuma baya abu kan
kuskure hassada da bakin ciki akan rayuwar Afeefah ya ja ta jefa kanta da kanta ga halaka.
Anan aka saka kawu Labaran mayar das
u dakunansu, inda ya nemi zai dinga zuwa daukar
karatu masallacin da malam liman ke koyawa kowani bayan Magrib haka zai yi kokari ya ga ya
sauke duk wani hakkinshi amma bai san inda zai ga Afeefah ba.
"Za ta zo ne! Dole zata neme ku don ku ne dolenta"
Kanshi ya duƙar ba tare da ya yarda da zata zo
ɗ
in ba don su ka
ɗ
ai suka san irin cutarwan da
suka yi mata.
****
Samha ce zaune da Abeeha bayan Magrib tana
ɗ
an janta da hira yayinda jannah ke kwance
akan gado idanunta a lumshe Afeefah tayi sallama
ta shigo
ɗ
akin.
Idanu suka hada da Samha, sai tayi kaman bata santa ba ta
ɗ
auke kai ta nufi wurin jannah
"Addah jannah sannu, ya jikin? Akwai abin da kike bukata ne?"
Ta girgiza kai
"Babu, bacci ma zan yi yanzu ki huta da zirga-zirgan nan haka pleas
e tun safe kece nan ke ce
chan baki huta ba"
Afeefah ta
ɗ
an murmusa kadan Dukda ta gajin iya gajiya rabon da tayi irin wannan wahalar ma
tun Dutsen-wai, ita ce kitchen ita ce kaiwa mutane abinci da sauran dai duk wani zirga-zirga da
za'a rike mutum a g
ida a yayin hidima ko ta aure ko ta mutuwa.
"Shikenan