Showing 75001 words to 78000 words out of 174924 words
wani kyakyawan yaro
da ba za
i wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo
ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana'ar da yake yi kenan a wurin
ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matuƙar ha
ɗ
e ko alamun
dariya babu
kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma
su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini,
wannan yaro ƙarami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da ba
i wuce a ce yana gaban
mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi,
sauƙe glass din nayi muka ha
ɗ
a ido na sakar mishi murmushi
"Yaya sunanka?"
Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda ida
nu da ya tsura min yana
kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na miƙa mishi kaman ba zai kar
ɓ
a ba sai ya
kar
ɓ
a ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.
Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da sh
i
haka na
ɗ
auki mota na koma inda na fara ha
ɗ
uwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman
shi da ƙafa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya ha
ɗ
a kai da gwiwa
Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi
da yanayin sumanshi
na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na duƙa na ta
ɓ
a shi ya
ɗ
ago ya
kalleni da idanunshi da suke a matuƙar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi
da na sauran yara ba don idanunshi na n
una wasu al'amari da na kasa fahimta, maganan
duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na miƙe na je wurin wani mai wankin mota a kusa da
wurin na nuna mishi yaron
"Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?"
"Hajiya yadda kika ganshin nan haka m
u ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya
ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya
ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin
wando idan ya bushe za
i saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda
yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai ta
ɓ
a barin wurin ba sai
wanka ko wanki da ya kan zo nan"
Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin
na koma wurin mota na tafi na je na
sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai buƙata na dawo na bashi ya ƙi kar
ɓ
a a
ƙ
arshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya
samu gurbi a zuciyata, a ranar takal
mina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin
zafin ranar minti minti sai ya
ɗ
an waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba,
har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da
ɓ
angaren mata
abin d
a ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na
sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa
wurinshi a na hu
ɗ
u ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya
kalleni
kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa
"Me ya same ki?"
Numfashi mai nauyi na sauƙe ashe ba kurma bane
"Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana"
Ga mamakina sai ya miƙe ya kama hannuna muka koma inuwa duk
muka zauna bayan nan duk
yadda zan yi yayi magana ya ƙi na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya
kalleni ya ce
"Me kike so?"
Ina mamakin yadda yake magana wane babba
"Kai nake so in taimaka kai nake so in
ɗ
auke daga wannan jujin i
n kaika gidan mu kayi rayuwa
mai kyau, za ka bi ni?"
Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya
ɗ
aya ba zan so rayuwar shi ya ƙare a kan
titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.
Kai ya gya
ɗ
a min na yi farin ciki kwarai n
a kira babana ina mishi albishir don ya san labarin
yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar
kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a
lokacin na je Makka
so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.
Ban barshi cikin ma'aikata ba na kaishi
ɗ
aki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na
dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min
"Na gode"
Murmushi nayi a raina ina ray
a wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za'a yi ba don
bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.
"Ya sunanka?"
"Ban sani ba"
Abin da yace kenan na yi mamaki ƙwarai kuma kaman akwai abinda ya
ɓ
oye min amma ban
bincika ba nace
"Zan saka m
aka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni ka
ɗ
ai ce sai
babana a gidan nan ka
ɗ
aukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan
cika maka shi ka ji?"
Ya kalleni nayi murmushi
"ban kai in haifeka bane? Shekarun
ka nawa?"
Ya
ɗ
aga min yatsu shida nace
"To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba'a kai hakan"
Ya
ɗ
an yi murmushi daga nan na fahimci shi mai
ɗ
abi'ar miskilanci ne tsantsa babana na samu
da shawara shi ya ba da sunan R
ayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki
bana tunanin ya kai shi sarauta..
A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga
ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da z
an kaishi makaranta tare
muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd
Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa
ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga
tashin hankalin da Saraki ne kawai ke
iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na
haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai ta
ɓ
a kirana ba ko zai
yi magana sai dai kawai yayi
na ce ko Aunty ya ce min ya ƙi, Rayyan bashi da lafiya don yadda
yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye
yana ha
ɗ
a gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ƙarami muka fara
ganin
likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo
mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.
Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban
sake
yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya
samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina
da Ciwon ƙoda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ƙodar shi yayi offering mi
ni Mahaifinsu Jannah
ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba'a dace ba, a lokacin da nake jinyar
Baban su Jannah ma ya rasu ga rashin lafiya ga rashin miji na yi ciwo sossai duk Rayyan ne
yake tsaye tsayin daka a kaina ga ƙannenshi Jannah
da Abeeha bai bari na tagayyara ba, yana
mini son da iyakaci kenan ko da ni ce na haife shi.
Saraki ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana ma bata dame shi ba don ko abokai
bashi da su, sannan yaro ne da idan yana abu dole ka kalleshi yana da
jin ƙai ko magana yake
dole ka kalleshi, dalili na ya tafi short service a harkar lafiya don dama science ya karanta a
secondary school, ba'a fi shekara biyu ba na matsa mishi da zancen aure ya nuna akwai wacce
yake gani zai iya aure, magana ta fara ni
sa ranar ya je wurinta babanta ya zo ya same shi ya ce
mishi
"Ina so in ka koma ka tambayi asalinka sai a fara batun neman aure amma ba zan ba da auren
ɗ
iyata wa marar cikakken asali ba"
Wannan magana ya dake shi sossai, wanda ni na
ɗ
an lalla
ɓ
a shi
na tura uncle Musa sai ce
mishi suka yi ba za su bada auren ba basu sani ba ko ba
ɗ
an sunna bane ko an same shi ta
gurbattacciyar hanya, magana ce mai girma a gareshi wanda ya tado ciwon baya da kyar muka
samu ya dawo daidai bayan tsawon wata shidda ba
ya bacci kuma ya ki fa
ɗ
a mini wani irin
mafarki yake ko wa Dr
ɗ
inshi, gashi Rayyan baya ta
ɓ
a zubar da hawaye, tunda ya girma rabon
da in ga hawayenshi kila da wani abu zai ragu a zuciyarshi, daga nan yayi alkawarin ba zai
sake neman aure ba don duk wand
a ya sake kallonshi ya mishi gorin asali sai ya kashe mutum
har lahira.
Afeefah kin ji waye Rayyan, kin ji cewa bashi da cikakkiyar asali sai dai yana da tarin nagarta,
ilimi, natsuwa da sanin ya kamata ga ibada tsantsa, yana da ni matsayin uwa da na
bashi duk
tarbiyar da uwa za ta iya ba yaro daga yarantarshi har girmanshi, ya samu gatan iyaye both
uwa da uba don baban su Jannah har ya rasu bai ta
ɓ
a nuna ko da da second daya cewa ba
shine Uban Rayyan ba, kin ji cewa bashi da cikakkiyar lafiyar kw
akwalwa ba na hauka ba sai na
tsantsar damuwa akan abinda ya shafi rayuwarshi da ciwo a zuciyarshi wanda ya mayar dashi
mai irin zafi da fa
ɗ
an nan, tun yana yaro ba za ki ta
ɓ
a ganin dariyar shi ba sai murmushi shima
sai ya kama, shin za ki iya auren Ray
yan a haka? Afeefah za ki iya yi min wannan alfarmar??
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BO
OK*
*30*
**Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro
wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?"**
Da wani irin amo sautin muryarshi ke dawo mata a sadda yake fa
ɗ
a farkawarta daga shan piya-
piya,
ashe da biyu yake yi mata irin wannan fa
ɗ
an? Ashe shima duniyar ba daa
ɗ
i tayi mishi ba?
Wasu irin ruwan hawaye ne ke bin fuskarta babu kakkautawa, sai taji har gwara ita ma da shi
kaman ƙaddarar ta ya fi nashi sauƙi tunda tana kwanciya tayi bacci lafiy
a ƙalau, kuka kawai take
yi duk yadda mammi ta so tayi shiru ta ƙi, sai da tayi ma'ishi Mammi ta bata ruwa ta sha kan ta
ɗ
ago ta kalli Mammi bata ce komai ba.
"Za ki iya cewa Meyasa ban bashi Abeeha ko Jannah ba ko? Har raina na
ɗ
auki Saraki
ɗ
an da
n
a tsuguna na haifa ne shiyasa har abada na haramta mishi auren 'ya'yana, uba yake a gare su
a yanzu da basu da wani uba shi ya raine su bayan yana jinya na, shi ya basu tarbiya cikakkiya
da har in sun fita ana sha'awar su. Wannan dalili ya sa ko da wasa
wannan tunani bai ta
ɓ
a
darsar min ba don har in mutu bana fata ko sau
ɗ
aya Saraki yayi tunanin don ba ni na haife shi
ba zan iya
ɓ
ata mishi..."
A hankali Afeefah da idanunta suka sauya ainun ta riƙe hannun Mammi
"Ke mutumiyar kirki ce Mammi, kina dag
a cikin sahun 'yan aljanna in shaa Allah... Hakika kina
da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona"
Murmushi ka
ɗ
an kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa
"Mammi ki bar roƙo na kin yarda da ni
ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har
raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so"
Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.
****
Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Salee
m gida bayan yayi ta mishi tuni akan
mahaifiyarshi da 'yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar
wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu'a yana kuma da yakinin
duk abinda yayi farko yana da ƙarshe
musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.
Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta bu
ɗ
e sai
ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya
shiga ya samu wuri ya zau
na, cikin mintuna ka
ɗ
an ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su
snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna
"Barka da juma'a Yaya"
"Barka dai ya gidan?"
Ta amsa da farin ciki
"Lafiya ƙalau ya su Mammi?"
"Alhamdulillah"
Ya fa
ɗ
a yana shan zobo don yana
matuƙar kaunar zobo bayan ya sauƙe cup
ɗ
in ya kalleta
"ba ki da wani damuwa ko?"
Kai ta gya
ɗ
a
"Babu komai Yaya"
Ya ce
"Masha Allah"
Miƙewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota
ya tafi ta dawo ta
na murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai
zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.
Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la'asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya
fita yayi sallah
sai ya dawo ya huta gaba
ɗ
aya, ko da ya shiga yanayin wurin ya
ɗ
an zubawa ido
Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya
ɗ
an ji wani
yanayi da har bai
ɓ
uya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya
ɗ
auke kai sai ta
miƙe ta zo
zata fita muryarta na cracking tace
"Sannu da dawowa"
Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi ka
ɗ
ai tausayi yake bata.
Ɗ
an shiru yayi kan ya ta
ɓ
e baki yana
ɗ
aga Kafada ya isa wurin Mammi
"Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?"
"Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?"
Bai ja zaren zancen ba yace
"Eh, hope baki ji yunwa ba?"
"No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin
you should rest"
Kai ya gya
ɗ
a ya
ɗ
an jingina
da kujera yana lumshe ido
"Ni ko ina son yin wata magana da kai"
Bu
ɗ
e idanun yayi yana kallonta
"Saraki ka tuna kai ka ce in za
ɓ
a maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na za
ɓ
a?"
Ɗ
an shiru yayi kan chan dai ya gya
ɗ
a kai.
"Toh mun samu Mat
a Saraki"
Bai wani nuna ya ji daa
ɗ
i ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya
ɗ
an bu
ɗ
e.
"Baka tambayi wace ba kuma a ina?"
"Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda
ya dace kawai"
"haka za ka auret
a baku fahimci juna ba? Ai ba'a haka dole za ka nuna mata itama macece
kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga
tsakanin saurayi da budurwa"
Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin z
ai iya yin ko abu guda
cikin wanda ta lissafo.
"Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba"
"Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan za
ɓ
a maka wacce na san bata
dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ƙarbar ta yadda take ko?"
Ya
ɗ
an matsa ka
ɗ
an ya riƙe hannunta
"Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda