Showing 6001 words to 9000 words out of 174924 words
wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikint
a gefe ta tsaya tamkar jiƙaƙƙiyar kaza da ta
rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
Ku
ɗ
in da ta wullo mata a wulaƙance ta sanya hannu ta
ɗ
auka ta juya tana jefa singallin
kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje
, ko da ta dawo zaune ta tadda
zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan
ɗ
umamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da ta
ke tsoron ji ita
ɗ
in dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin ra
ɗ
a
ɗ
i ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani
ba ba kuma ta tunanin za ta sauya
ɗ
in abu ne da ta riga ta s
ani a kullum idan har za a raba
abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya fa
ɗ
i ƙas.
Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi
take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta d
a shi ba ta kuma da
wanda zai ba ta babu mai
ɗ
igon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda
ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.
Sauƙar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ƙarar azaba a firgice ta miƙe daga durƙuson
da ta
yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta
ɗ
aile, daidai
lokacin inna larain take fa
ɗ
ar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shes
sheƙa ta
fara roƙon su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina mur
ɗ
a suke,
yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ƙafafu ta ham
ɓ
are ta ba tare da ta ko damu da raunin ƙunar da ke
ji
kinta ba.
"Ba za ki ta
ɓ
a samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin
ɗ
aura mini abincin rana."
Jiki a sa
ɓ
ule ta miƙe ta nufi wurin murhu, a haka cikin ra
ɗ
a
ɗ
in gangar jiki da zuci ta fara aikin.
Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanuka
n mawanki kowa ya nufi
ɗ
akinsa
don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ƙarfin miƙewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar
dake dawainiya da rayuwarta.
Ɗ
an sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta ha
ɗ
e da tukunyar ta
kan
kare ƙasan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula
inna Larai dake mata garga
ɗ
in kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta miƙe ba don ta
ƙ
oshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ƙarasa ta kwalfi ruwa t
a afawa cikinta. A
gindin randar ta ra
ɓ
e cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a
cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.
"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sure ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta
tare da kiran sunanta.
"Lafiya kike bacci a nan?"
Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai
maganar da muryarta yayi kama da wacce ta sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta.
Sanyin farinc
ikin sanya mace guda da ta rage mai ƙaunarta kaf fa
ɗ
in duniya a idanunta, tashi ta
yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ƙarewa fuskarta da ma
jikinta kallo n
e ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi. Dama me neman kuka ne aka
jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta
ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da
ƙyar Afeefah
ta yi shiru kan matar ta bu
ɗ
e jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar
mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ƙwarewa, matar ta
ɗ
ibo
ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da k
awu ya fito shirye da alama kasuwa
za shi..
"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ƙarfin ƙaddara ba.
Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ƙarƙashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka,
a yau za ka iya fa
ɗ
uwa k
a mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"
Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar
Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi
ɓ
acin
ɓ
acina kuma ki daina
ha
ɗ
a yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko
ɗ
aya ba, ban kuma shirya mutuwa ba.
Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah
ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya
sake kallon ta.
"Af! Idan ƙarshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Miƙewa tsaye ta yi a zuciye.
"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a saman dami,
idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tash
i mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta
Aunty zainabu da ita ka
ɗ
ai ce ƙanwar mahaifiyarta ta so kar
ɓ
ar ta sai dai kakarta ta ƙi har ma ya
kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau
ɗ
aya ta ta
ɓ
a zuwa ta duba ta a gidan
kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo
sau biyu sai dai bata ta
ɓ
a wuce awa
ɗ
aya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani
kauye gaba da su sossai ta
ke.
Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a
yanayin da ta sameta ya matukar
ɗ
aga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su fa
ɗ
o ta saisaita ta miƙe da sauri ta shige akurkin
ɗ
aki
n nata. Wani
tunani da ya
ɗ
arsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika
idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ƙarewa
ɗ
akin kallo cike da tausayawa ta duƙa gangarta
tare da dafa kafa
ɗ
arta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da
tunanin da zuciyarta ke yi.
"Sau tari ƙaddarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko
akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sauƙi.
Mu tafi."
Taya ta tayi suka ha
ɗ
a yar G
hana most go
ɗ
inta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu
da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ƙeya suka bi su da shi don
yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.
Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya m
atuƙar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa
bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya ha
ɗ
u da bata ta
ɓ
a
shiga mota ba a rayuwarta don bata ta
ɓ
a barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata
san akwai titi kwantacce
irin hakan ba sai da suka
ɗ
auki titin cikin garin Anchau daga kauyensu
chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty
zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sauƙa ba ma su isa t
asha ba don
Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sauƙa
suka yi ta
ɗ
auki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan
ƙ
arfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai d
ai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida
da take da tarin shuke-shuke.
A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta bu
ɗ
e karamin frigde
ɗ
inta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na
ɗ
ora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai
ta
kura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gya
ɗ
a tana yaƙe dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa
Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ƙi tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka
shiga yi tare tare har suka gama,
shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"
ɗ
auka ki koma ƙasan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.
Aunty zainabu dai na ta kokarin ha
ɗ
a na
mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin
abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har
yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai
har yanzu babu wani laba
ri na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.
Tana ƙoƙarin kai loma yana sallama, ta amsa ya
ɗ
an yi turus yana kallonta gabanta ne ya
ɗ
an
fa
ɗ
i don ganin fuskanshi ya
ɗ
an sauya ko da ta gaishe shi da kalma
ɗ
aya ya amsa kan ya nufi
ciki yana kiran za
inabu...
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls
bear with me ku riƙe wannan as na
chan anjima
ɗ
in tunda Its already friday.*
*004*
A wurin ta cigaba da zama jiki a sa
ɓ
ule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har
ya
ɗ
uri ruwa saboda ƙuna daga gefe zuwa ƙasan idanunta, Allah ya t
aƙaita ma bai ta
ɓ
a idanun
ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"
"Eh Aunty na gama"
Ta fa
ɗ
a a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle
ɗ
inki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya dub
a miki wannan ƙunar
kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta miƙe ta shiga parlor zuwa
ɗ
akin da ta ajiye mata kayanta
daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu
idan ba mayar da ita inda kika
ɗ
auko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ƙira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta
ɗ
aga mishi murya ba sai yau.
Kuka
ta fara
"Haba Usman na fa fa
ɗ
a maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah
ɗ
iyar
yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa
ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don All
ah ka kalleta da kyau ka
ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."
Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan
Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar
nan ba, ko kwanan nan ta ci
kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki
ɗ
auko ta ki kawo min
cikin gida?"
Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan ta
ɓ
a yarda Afeefah zata yi maita ba,
babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ƙare idan ko don ka zauna da mutum kwana ya
ƙ
are ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa
makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan
iya sake mayar
da ita gidan labaran ba wallahi"
Numfashi mai karfi ya sauƙe
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"
A lokacin Afeefah ta sulale ta maƙale jikin gini kama
r kadangaruwa ta chusa kanta cikin
kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi
amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta
kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty
zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta
ɗ
ago kai
"Aunty don Allah ki yi haƙuri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina
hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta
dalilina ba zan iya
yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye
"bawa baya ta
ɓ
a wuce ƙaddarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face
ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan ta
ɓ
a iya sake barinki ki zauna wur
in
'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ƙuna a wurin kan suka dawo.
Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai
babu wanda
bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke maƙotaka tana saya kuma ta
sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna
ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afe
efah interview
da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba
termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba
tela akan zai
ɗ
inka kan su gama sayayya, sayayya so
ssai ta yi mata da saida tayi ta zub da
hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar
yadda zata so mahaifiyarta.
Da kaya sossai suka dawo niki niki, a
ɗ
akin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango
n
an ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu
ɗ
an dama suka tafi da su kasuwa aka
rarrage mata yadda zai ƙarbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.
Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da
uncle us
man, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo,
natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don
babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta m
alamai
sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen
shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka
islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar sabo
da yadda Aunty zee
ɗ
in ke
nuna ta matsayin
ɗ
iyarta.
Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag
ɗ
inta, fuskanta ya fito fess
a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin
ɗ
inta
har
wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango
Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga
ɗ
akin uncle usman ta samu
ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta
ɗ
an duka ta gaishe shi ya amsa ci
kin natsuwa
"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana