Showing 69001 words to 72000 words out of 174924 words
zan mishi magana"
Ledar ta ajiye don ji take ko abin ciki bata sha'awar gani, hankalinta ba'a kwance ba ta tashi tayi
ɗ
akinta ko da ta shiga sai da ta sakawa kofar key don ji take kaman z
ai biyo ta ya cigaba da
fa
ɗ
a.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*FATIMA A MUHAMMAD Sirikata kuma namecyna ina
so in yi amfani da wannan dama in miƙa
saƙon godiya da kuma jinjina bisa irin kokarin da kike yi a kan wannan littafi, haƙiƙa ba ni ma da
kalmar da zan nuna miki jin daa
ɗ
i na da kuma yabawa mai tarin yawa wannan shafin naki ne
kiyi yadda kika ga dama d
a shi... Jama'ar gidan haihuwa da hanji conversation room ina ganin
tarin comments naku sai dai lokaci baya bani dama a kullum na shiga a sha fira da ni amma ina
matukar jin daa
ɗ
i kuma ina yabawa ku sani muddin Aminiyar ango(Fatima A Muhammad) ta
amsa w
allahi kaman ni ce nan na amsa. Ina kuma yi muku albishir gobe public holiday za mu
samu damar jero shafuka biyu in Allah ya yardar mana. Na gode sossai*
*27*
Washegari friday har ta je school ta dawo bata daina tuna irin fa
ɗ
ar shi na jiya ba, ita k
am ba
don mammi ta tabbatar mata da sai ta je ai shi zumunci yake so da ita ba tsiya ba, wanda yake
sonka da arziki kuwa ya gama maka komai da babu inda zata je ai zama lafiya ya fi zama
ɗ
an
sarki.
Ko da ta dawo da
ɗ
akin Mammin ta fara ta duba jikint
a suka
ɗ
an yi hira kan ta wuce
ɗ
akinta aka
biyo ta da abinci, sai da ta ci kan ta shiga tayi wanka da alwala ta zo tayi sallah, a gaban mirror
ta zauna tana kallon kanta a yanzu ko ita ta san ta yi kyau, ta
ɗ
an yi ƙiba skin
ɗ
inta na wani irin
yalki don
man da Abeeha take shafawa ita ma shi ta saya mata kuma skin tone
ɗ
in su
ɗ
aya, ta
sake cika tayi kumatu ka
ɗ
an sai ya mata kyau, kwalli ta zana a idanunta bata cika sakawa ba
amma ta san yana mata kyau kawai dai bata son sakawa ne don yana sa idanunta haw
aye sai
wani ruwa ya kwanta ciki kaman mai, dama gasu da girma masha Allah, lip gloss ta shafa ta
miƙe ta tafi gaban wardrobe.
Abaya ta
ɗ
auko wani blue da adon fari egyptian ne ya amshe ta sossai ta saka farar hula don
farin gyale yake da shi sai t
a yafa gyalen ta yi kyau sossai sai ta ji nishadi a ranta, wa zai ganta
ya ce Afeefar Dutsen-wai ce, Mayya kuma annoba? Wa zai ce tagayyara aka so tayi Allah ya
dube ta ya tallafi rayuwarta? Malamin islamiyyarta na makaranta na cewa Allah zai bu
ɗ
e ma
ba
yinsa kokafofin rahama da sauƙi cikin ko wani tsanani muddin ka saka tsoronshi da tawakalli
cikin ranka, sannan zai bu
ɗ
e maka kofofin arziki ta inda baka yi zato ko tsammani ba ko a
mafarki bata zaci ganinta cikin irin wannan gida tana rayuwa ba, tayi tu
nanin za ta tabbata a
bauta da wahala a kasakance amma da Allah ya ce ba hakan bane ga inda ya kawo ta a yanzu.
Da kyar ta bar gaban madubin wurin Mammi ta nufa.
"Masha Allah Daughter ta tayi kyau tabarakallah!"
Murmushi tayi tana zama gaban Mammin
"Mammi zolaya ta fa kike ina kyau anan? Ko fa powder ban shafa ba"
Mammi za ta yi magana kenan Abeeha ta shigo kaman ta jima da Dawowa don ba da kayan da
ta fita ta shigo ba.
"Afeefah Dr. Sulaiman ya kira yana harabar gidan nan"
Mammi tace
"Abeeha g
obe dai tunda saturday ne ku je ki nema mata waya mai kyau"
Murmushi Afeefah tayi tana Miƙewa
"Sai kun dawo a gaishe su, sannan a kula. Abeeha kar ku jima kin san Yayanku"
Da Toh duk suka amsa suka fice daga parlorn.
Ta jima sossai tana tuna Afeefah
a ranta kan ta sauke ajiyar zuciya tana Miƙewa da kyar cikin
yanayin rashin ƙarfi da cikakken lafiya ta shiga cikin
ɗ
aki.
A harabar gidan kuwa suna fitowa Rayyan na parking, gaban Afeefah ne ya fa
ɗ
i zuciyarta ya
shiga doka wa da ƙarfin gaske, a natse
ya bu
ɗ
e murfin motar ya sanyo jikinshi waje Farar
jallabiya ce da daga ganinta zaka san tana da tsada sai maiƙo take yi kirar Kasar dubai don
tana da wani ado mai yanayi da rubutun larabci daga gefen kirjinshi ka
ɗ
an har karshen hannun
hagunshi, hirami n
e baƙi mai layi layi fari ya mishi wani
ɗ
auri a kai yadda Larabawa suke yi ya
zauna mishi sossai yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano baƙa, hannunshi na daure
da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ƙarshe ke ta d
aukar
idanu.
Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake,
baƙar shade na maƙale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko
Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da y
ake ba ya shige gidan kamshinshi na buso
musu, Abeeha ce ta iya yi mishi
"Sannu da dawowa"
Hannu kawai ya
ɗ
aga mata wai shine amsar ya shige abunshi.
Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan
suna sake g
aisuwa.
Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin
gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ƙasa ta zube tana gaishe da
mahaifiyar shi Umma ta miƙa mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta
zaunar da ita gefenta tana
ɗ
an rungumeta ka
ɗ
an
"Ina ta jin labarin
ɗ
iyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa"
Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daa
ɗ
in irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da
su drinks aka cike musu
gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi
Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake.
Sun jima sossai har aka yi la'asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka
fito shirye don wucewa islamiyya suka y
i sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu
jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da
wani girman jiki a shekaru kuma da ka
ɗ
an za ta iya fin Afeefar kila su yi sa'a da Abeeha, zama
tayi tana ce mus
u sannu.
Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin
Afeefar da bata santa ba amma ta yi matuƙar haddace sunan saboda yawan Ambaton da
Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau
ta fita ko ado ba
ha
ɗ
iye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice.
Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru
ta
ɗ
an yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ƙarshe, Baaba da Umma sun sha kuka
umma ta sake rungumeta tana cewa
"Sannu Afeefah... Sannu! Allah ubangiji ya ƙara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk
wannan wahalhalun"
Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu'a da tayi
ta bin iyayent
a da Aunty zee.
Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe
kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a
ɗ
akin shi a yanzu matsayin
matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani y
ake lokaci ya riga ya ƙure, Dukda
haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga
yanzu.
Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da
ta dinga zuwa mata, har cikin
gida ya dawo dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.
****
Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen
Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado,
da
ɗ
an hanzari ya isa gareta
"Mammi! Lafiya kike kuwa?"
Ta
ɗ
ago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ƙarfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin
murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa ha
ɗ
e da gajiya, a idanunta wani abu mai
wuyar fassara yake
karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu
ɓ
uya ba sam don a
kan Mammi baya iya danne damuwarshi.
"Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana"
A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake
malale tsakar
ɗ
akin.
"Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare
da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma'aikinmu sannan akwai
wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mu
tuwar mutum komai nashi zai tsaya
chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai
ɗ
a
nagari mai mishi Adu'a ashe baka Fatan ka ajiye 'ya'yan da za su yi maka Adu'a bayan baka
nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka
ta
ɓ
a aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin
rashin sanin nagarta da kyaun halinka... Ba duka aka taru aka zama
ɗ
aya ba"
Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam
baya so baya son jin zancen wani aur
e daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san
mummunar ta
ɓ
onshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za'a iya kallon cikin kwayar idanunshi a
fa
ɗ
a mishi kalmar da har abada ba zai ta
ɓ
a mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.
"Mammi..."
"R
AYYAN...!"
A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata ta
ɓ
a ƙira
ba... Gaba
ɗ
aya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce
"Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba?
Kana
so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in
barka ban cika alkawarin da na
ɗ
auka wa rayuwarka ba?"
"Yaaa ilaihil alameen..."
Ya fa
ɗ
a a rikice sai ya miƙe tsaye don wani irin tashin hankali
yake ji, taku biyu yayi gaba ya
juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya tsala ihu ko zai fahimtar
da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.
Zama yayi ya kalleta
"Mammi saboda ke don ke ka
ɗ
ai zan amince da zancen aur
e! Amma ban san kuma ta yadda
zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba
kuma... Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai kar
ɓ
a ne"
Shiru tayi tana kallon shi, ya riƙo hannunayenta
"Mammi kin san yadda na
ɗ
auki alƙawari, na miki alƙawari zan yi iya kokarina a duk abinda za
ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko
wacece zan zauna da ita yadda kike so matuƙar hankakinki zai kwanta,
matuƙar za ki daina yi
min zancen tafiya ki bar ni... Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa"
Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko
babu komai zai tuna da ita ta za
ɓ
ar mishi mata, zai tuna
da ita ya yi mata adu'ar alkhairi a duk
sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi za
ɓ
in nan da kanta ba za ta
bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta roƙi ubangiji yayi mishi za
ɓ
i da kanshi ta san sai ya fi
dacewa duniya da
lahira...
Anan suka bar maganan ya miƙe ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai
yi hannu ta
ɗ
aga sama tana cewa
"Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah
ka sada shi da duk w
ani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ƙiyama..."
Ta shafa.
Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu'ar neman za
ɓ
in Allah, ko sau daya bata yi tunanin
wata mace ba damuwarta kawai Allah ya za
ɓ
a mishi mafi alkhairi cikin mata, ya za
ɓ
a mishi
matar
da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta
kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman
yaro ƙarami da kan riƙe hannunta yayi kuka yayi kuka matuƙa idan an fa
ɗ
a mishi abin da ya
ta
ɓ
a zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da
ƙ
arfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.
Ta
ɗ
auki tsawon sati biyu tana wannan roƙon Alla
hn a cikin uku bisa
ɗ
ayan dare lokacin da
Allah ya ce mu roƙe shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na
ɗ
aya yana neman
bayinshi masu roƙon shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma'a bayan ta
gama nafilfilunta ta kwanta ka
ɗ
a
n saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lalla
ɓ
a
ya dauƙeta ana ƙiran farko na assalatu ta farka a
ɗ
an firgice ta miƙe zaune, a hankali ta saki
murmushi mai kyau kan tayi Adu'a ta miƙe ta nufi bayi don gabatar da Alwala.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Comments
ɗ
in ku shi zai yi determining Page na dare%*
*28*
Tun ƙarfe goma sha
ɗ
aya na saf
e Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani
aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma'a don yana so ya fita da wuri yana so
ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.
A shirye ya fito cikin shigan many
an kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika
son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya
ɗ
in, governors yard ne da aka yi wa
dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito
ɗ
akin Mammi ya fara yi ya sameta
zaune tana a
zkar
ɗ
inta da bata rabo da shi.
"Sannu da hutawa Mammi"
Ya fa
ɗ
a yana zama gefenta
"Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka"
Ya gya
ɗ
a kai
"Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim"
"kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke
ɓ
uy
a ko?"
Murmushi kawai ya
ɗ
an yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta riƙe da tray mai
dauke da plate na abinci.
Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai ha
ɗ
a ta dashi kiyayewa take
saboda yadda bata samun natsuwa a a
rea
ɗ
in da yake gashi abin laifi baya mishi ka
ɗ
an yanzu
ya hau fa
ɗ
a da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray
ɗ
in ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi
dake godiya ya ce
"Ba dai wannan abin za ki ci ba?"
Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci
ne ya zama abu?
"Me yayi?"
Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace
"Kashe ta kike son yi?"
Wani irin fa
ɗ
uwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro
waje tana so tayi magana amma Muryar
rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta
bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind
ɗ
inta ta yadda ko ya
aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.
Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke
razana ta
"Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?"
Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.
"Saraki...! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a