Showing 12001 words to 15000 words out of 174924 words
shigowa da shi ne ba
zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye
"jita-jita bai ta
ɓ
a wa
nzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a
kan Afeefah amma na
ɗ
auke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ƙaunarta, abin da nake
tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi haƙuri da daukar su har su yi
kwa
ri shikenan na yi laifi...? Ku yi haƙuri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an fa
ɗ
a mishi
abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daa
ɗ
in reaction
na zain
ab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.
"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma
abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kar
iya, tun
fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma
gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu
abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sauƙe mu
raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji ra
ɗ
a
ɗ
in zuciya tun ranar da
uncle ya amince ta zauna da su sai yau.
Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi ha
ɗ
e da rashi
n imani zai
sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce
ta rungumeta ta cicci
ɓ
ota ta zaro ta daga cikin bala'i da ƙuncin rayuwa?
"Afeefah..."
Auntyn ta ƙira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana du
k suka yi shiru tsawon lokaci kan
nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin
ɗ
akin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare
abin hawa ta fa
ɗ
a mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu
Uncle usman da ma ita kara
n kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana
tuburewa, maganganu take gayamishi cikin
ɗ
aci da nuna kaman shi ne ai ya za
ɓ
i ya ba
Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.
"H
aba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da
bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji
magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi ya
nzu ta
haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki
namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".
"A'a Usman ai ka fi ƙaunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da ba
ka
auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun
ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*006*
"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi haƙuri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani
Auntyna ta fa
ɗ
a miki magana ne saboda irin ƙaunar da
take mini amma ni na san gaskiya kika
fa
ɗ
a, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba
da jira har lokacin da ya kamata a ce na
ɗ
auke su
ɗ
in"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokac
in ba su daina zubar da
hawaye ba. Uncle
ɗ
in tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta ta
ɓ
e baki ta ce
"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu
ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare
ɗ
aya a yi
abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sauƙe ki a babur na"
Miƙewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai ha
ɗ
a su ba ta
sauƙa ta shige yayinda ya juy
a ya koma asibitin.
Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta
ɗ
ora girki
marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta
ɗ
an kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne
saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zat
a so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare
Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai
Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata
amma duk da haka sai damun uncle usman take akan magana
n Afeefar har fushi ta yi ta matsa
a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk
da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai ha
ɗ
a su ba don ta matuƙar
jin zafin abin da ta yiwa Afe
efar.
Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran
"Afeefah! Afeefah!!"
Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta,
Auntyn ta
ɗ
ago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya
"Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?"
"A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai
in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daa
ɗ
i, da missing
ɗ
in mu da zai yi sai yayi mishi
yawa"
Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya
da masauki kan a natsa ma maƙota da
abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma
ɗ
inkewa da jama'a nan Afeefah ta
shiga jeka ka dawo.
Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne
zuciyarta, ko Aunty bata
bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko
satan kallon yaran ta yi sai ta ya
ɓ
a mata baƙar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin
son su tamkar jini da tsokarta ta sha
ɓ
uya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi
don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu
duk Aunty bata sani ba.
Auntyn Ta yi matuƙar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan
tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin
da Auntyn ta yi mata musamman na suna
maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka
ta saka kwalli ta shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen
ita suke kira tana miƙawa
mutane abinci daidai ta zo miƙawa wasu mata kenan da yake ta
bayansu ta zo ta ji
ɗ
ayar tana cewa
"Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take riƙo rikakkiyar Mayya
ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su
"
Ɗ
ayar ta ce
"Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma
bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana
ba"
Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsa
yawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta
"za ki gane ta mana wata baƙa marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da
suke manya kaman kwai kin san za'a ga kurwa da kyau... Allah dai ya hana farin ciki komawa
baƙin ciki"
Gabansu ta
zagayo suka
ɗ
an sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu
ɗ
igon walwala idanunta da
suka surke zuwa ja ta
ɗ
an zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin.
A karshe dai ba'a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afee
fah
Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ƙyar aka fita
da ita a gidan zuwa maƙota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata yi ba
duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai
ta tuna Aunty zee da ta yarda
da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da
za'a yi sai ya fi haka, chan kuryar maƙociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar
Aunty zee ba amma ta ji hannu ya ta
ɓ
a
ta firgita ta yi ta miƙe tsaye tana girgiza kai
"Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi haƙuri ban ta
ɓ
a cin naman
mutum ba wallahi..!"
A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta
"Ya isa A
feefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke"
Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee
ɗ
in.
Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta
ya
dda ko kuzarin ta
ɓ
a yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta ta
ɓ
a su abu ya faru haka Aunty zee
ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai
"Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen
Afeefah ne amma ka ga yadda
take baya baya da su ko ta
ɓ
a su sai na yi da gaske take yi!
Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta
ɗ
auki alhakinta dayawa
kuma ni kam ta daina burgeni sam"
Shiru yayi chan ya ce
"Ki yi haƙuri zan yi mata magana, amma ki di
nga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar
Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka
ɗ
auka
kafin Allah ya ba mu"
"Wallahi na fi ƙaunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na
cikin ha
ɗ
ar
i don Allah zan roƙe ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda
ka fara mata, ka dubi maraicinta ka riƙe ta kamar yadda za ka riƙe suhail da suhaila".
Hannayenta duk biyu ya riƙe
"Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan c
igaba da iya ƙoƙarina a kanta"
"na gode sossai Baban 'yan biyu"
Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa.
Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle
ɗ
in kan ja Afeefar jiki ko ma
ya bata babies
ɗ
in da take matukar so ta riƙe, yau s
atinsu na biyu kenan a duniya.
Tsaki Aunty zee ta
ɗ
an ja ka
ɗ
an karo na ba adadi hakan ya saka Afeefah dake jijjiga suhaila
yayinda Auntyn ke ba Suhail Mama ta kalleta ganin tana ta yamutsa fuska ya saka Afeefar
katse shirun nasu
"Aunty lafiya kuwa?"
Ta sake jan wani tsakin karo na barkatai kan ta furta
"Wlh Afeefah ciwon ciki ne ke
ɗ
an matsa min tun haihuwar nan kullum sai na yi shi kaman
ƙ
a'ida"
"Sannu Allah ya ba ki lafiya, babu maganin da suka ba ki a asibiti?"
"Akwai fa ina sha amma kaman ban
a sha"
"Sannu"
Haka tayi ta jera mata duk ta saka kanta a damuwa domin sam bata so taji wani na ciwo a
gidan sai gabanta yayi ta fa
ɗ
uwa fargaba ya bi ya rufeta har sai an furta mata yayi sauƙi.
Shigowar Uncle da karbar babyn da yayi daga hannunta ya
sa ta yi musu sai da safe ta shige ta
bar su nan parlor.
Chan cikin dare sai ta ji kaman ana motsi da ƙarfi, sai kuma ta ji bugun kofar
ɗ
akinta a razane ta
farka tana salati jin Muryar uncle ya sa ta dirko da hanzari ta zo ta bu
ɗ
e kofar
"Afeefah ki zau
na da yaran nan idan sun yi kuka ki ba su madara zan kai Auntynki asibiti ciwon
ciki ya tasar mata sossai"
Tuni ta rikice hawaye har sun fara zarya a idanunta.
"Toh uncle"
Ta fa
ɗ
a tana bin bayanshi, shi ya riƙo Aunty zee da ke tafiya da kyar Afeefah na
ta bin su tana
share hawaye har zuwa kan babur ya hau ta kwanta jikinshi suka fice tana ta jera mata sannu
da Allah ya bata lafiya. sai da taje ta rufe kofa kan ta dawo kan yaran ta zabga tagumi cike da
damuwar ciwon Auntyn.
Yaran sam ba su da rikic
i daman, tun tana tagumi har bacci ya sure ta a kansu ƙiran Sallar
farko da kukan suhaila su ne suka farkar da ita, ta tashi ta ha
ɗ
a musu NAN1
ɗ
in su da ake basu
saboda abinci ya ishe su, ba zallar nono Auntyn ke ba su ba, sai da ta saisaita ya zama da
dumi
cikin tsafta ta fara ba su don suhailar na koshi sai suhail ma ya tashi bayan ta gama ta fice taje
tayi alwala ta zo ta fara sallah sai da ta idar tayi Adu'a ciki har da roƙon Allah ya ba Auntynta
lafiya kan ta miƙe ta bar sallayar zuwa tsakar gid
a.
ƙ
oƙarin
ɗ
ora musu breakfast ta fara a natse take aikin Dukda hankalinta rabi na ga su Uncle da
suke asibiti rabi na ga 'yan biyu kar su farka bata ji kukansu ba har ta gama ha
ɗ
a abinda zata
buƙata ta
ɗ
ora kan ta shiga sharar tsakar gidan.
Ta gam
a ha
ɗ
awa tana ƙoƙarin kwashewa kenan ta ji ana bubbuga kofa ba irin bugun hankali
ba, jikin kofar ta isa sai ta ji kaman surutai dai ba na mutum
ɗ
aya ba, bata bu
ɗ
e ba ta shiga
tambayar waye ne?
"Ki bu
ɗ
e mana ai za ki gani!"
Muryar hamdiyya da ta ji ya
sa ta bu
ɗ
e kofar sai dai me za ta gani...!
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Jama'a kuna manta cewa na rubu
ta True life story a jikin labarin nan, Meyasa na yi kyauta ne
kam? Saboda ina so mu ƙaru da ilimin dake ciki, na tabbatar daga page 1 zuwa yanzu kun
zaƙulo darusa masu dumbin yawa kuma ko ban kawo gyara ciki ba kun san amsar hakan.
Wallahil azeem ban ƙ
ara komai a labarin Afeefah ba, ban ce babu ƙari ba akwai amma sai a
gaba yanzu duk abinda kuka gani a gaske ne ban chanza komai ba, please bear with me
🙏
*
*007*
Wasu gungun matasa ne
ɗ
auke da makamai suna ƙoƙarin Hanka
ɗ
a hamdiyya su rufta mata ai
da wani irin hanzari ta mayar da kofar ta rufe jikinta na wani irin
ɗ
aukar tsuma, hankalinta sai ta
ji yayi wani irin tashi tsoro da fargaba suka rufe ta, ko kafafunta ta kasa motsa su daga inda
take tsaye... Ƙuuuuu haka cikinta yayi wani irin ƙara a sad
da ta ji kukan uncle ha
ɗ
i da
maganarshi daga bakin kofan
"Ki bu
ɗ
e ki ba ni yarana...! Kin riga kin cuce ni kin raba ni da uwarsu rabuwa ta har Abada a
yanzu ba zan iya sake
ɗ
aukar raba ni da su ba, in kuma su ma kin cinye kurwarsu ne kaman
uwarsu nim
a duk ki ha
ɗ
a da ni ki cinye Afeefah..."
Sossai yake gunji daga jin muryarshi zaka san baya cikin hayyacinshi ne.
Tsurewa ta yi tana jin kaman ta zauce ko kunnuwanta ba sa ji da kyau. Tamkar sauƙar aradu ta
ji wani da kaman yanzu ya iso a gigice yana fu
rta
"Da gaske ne Usman Zainabu ta rasu?"
'Zainabu ta rasu!'
Ko kan kalaman su gama shiga kwakwalwanta sai ji tayi uncle na amsawa
"Zainabu ta tafi ta bar ni. Sai da aka garga
ɗ
e ni amma na ƙi saurara saboda ta ba ni yaƙini a
kan yarinyar, ashe ba hak
a ba ne kai duniya...! Ashe wanda ya maka rana za ka iya masa
dare? Afeefah ta yi mana shigo shigo ba zurfi, lafiya ƙalau muka kwanta da zainabu daga ciwon
ciki farar
ɗ
aya muna zuwa asibiti sai ga kiran hamdiyya take sanar min ta yi mummunar mafarki
a k
an zainabu, sai na sanar mata muna asibiti bata da lafiya ta tsorata tace gata nan zuwa
Dukda dare ne haka ta bi gidan wani malami ta