Showing 132001 words to 135000 words out of 174924 words
zan ko wanka sai an min"
Jannah ta maka mata Harara
"Daa
ɗ
i na dake ragwantaka, kar ki sa in miki adu'ar aure inda za ki
ɗ
or
a tukunya lamba goma"
"Allah ya kiyaye ya kyauta wlh"
Ita dai Afeefah dariya take musu chan tace
"Ni dai kin san Allah duk waennan abubuwan basa burgeni, ni fa na fi so in yi rayuwata ba
takura amma yanzu duk jina nake wani iri wlh"
"za ma ki saba n
e yarinya"
Suna yar hirar su har suka gama suka dawo cikin parlor.
"amma fa sashen nan naku wlh ya ha
ɗ
u ƙarshe, ni kayakin nan ma na kasa tantance irin
masifar tsadarsu ji kujera kaman bread tsabar taushi"
Abeeha tayi maganan Afeefah tace
"Kema kenan
da kuka saba yawace yawace har kasashe ni ko da na shiga bayi sai da nayi
kauyanci, wai ni Afeefah ce cikin masarauta har wani zube min ake a ƙasa abin nan ya kasa fita
a raina"
Jannah zata yi magana sai suka ji sallama.
Dukkansu kofan suka mayar da
hankali wata doguwar matsakaiciyar macece mai cike da
kamala ta shigo sanye da rantsatsen alkhyabba fari tass daga ka ganta ka ga mulki fuskarta
dauke da fara'a bayanta wasu 'yan mata biyu ne sanye da dogayen riguna suma kyakyawa don
duk ruwan Fulani ga
resu.
Kallo daya suka yi mata suka hangi kamanninta da Aliyu kan ma suyi magana kuyangin ta sun
zube suna kirarin da ya sa suka fahimci wacece Dukda Sameer suka ji ake kira.
Dukkansu suka yi yunkurin kaiwa kasa don gaisheta tayi saurin rike Abeeha da
Afeefah ta
ɗ
ago
su kan ta
ɗ
ago jannah duk ta rungumesu
"Barkanku da zuwa 'ya'yana, Maraba lale da isowa masarautar Fombina"
"Mun gode mama"
Suka fada duka da murmushi a sadda ta sake su suka zauna tana rike da hannun Afeefah
Dukda bata ma san wacece
wace ba a cikinsu amma dai duk sun kwanta mata ganinsu hakan
"Sannunku da zuwa"
Aisha ta fa
ɗ
a suka amsa da godiya.
Zarah tace
"Sannunku dai"
Itama suka amsa.
"Ni sunana Ammi ku daina cewa Mama akwai mamar taku Fulani Adama za ku je ku kai mata
gaisuwa anjima, wannan ita ce Aishatu ƙanwar Sameer Yayanku su biyu Allah ya bani kan
ɓ
acewarshi sai wannan
ɗ
iyar wurin Makama cousins suke da su Sameer ko in ce Rayyan
yadda kuka saba fa
ɗ
a. Ina fata za ku dauke ni matsayin Uwa da kuka yi rashi gaba
ɗ
aya.
Allah
ya gafartawa Mammi ya kai haske makwancinta"
Suka amsa da Ameen kan jannah tace
"Ni ce Jannah, wannan kuma Abeeha ita ce kanwata Ga Afeefah ita ce matar Ya Rayyan"
Ammi tayi murmushi tana kallonta
"Masha Allah, Allah ya cigaba da baku zaman
lafiya ya kawo zuri'a masu albarka" kunya ya
hana Afeefah amsawa
"Da ma na kasa haƙuri ne nace dai bara na zo na ganku, Abeeha duk abin da kuke so ko ya
shige muku duhu ku kama sa'ade za ta kawo ku har inda nake ku tambayeni kun ji? Ke kam ma
sashe
na zaki dawo ba da jimawa ba"
Suka yi murmushi ta dubi su Aishatu
"Sai ku zauna nan duk abinda basu fahimta ba za ku iya fahimtar da su da kuma bayani akan
family Dukda sai a hankali za su san kowa"
Suka amsa kan ta miƙe ta fice suna mata sai anjima.
Yadda su Aishatu suka kame haka dukkansu suka kame sai hirar ya koma tsakanin junansu
kawai ita jannah ma waya take da mijinta yayinda Abeeha ke hira da Afeefah suna yar dariya,
kaman daga sama sai ga shi ya shigo. Ko Aisha yau ne suka fara ganin juna
dashi face to face,
zama yayi a one seater ya kame yana kallonsu daya bayan
ɗ
aya, jannah ta fara gaishe shi ya
amsa ta mishi murnan dawowa cikin family Abeeha ma ta gaishe shi.
Zarah ce ta gaishe shi ya kalleta yana son tuna sunan
"Aammm.."
"Zarah"
"Oh Yeah lafiya ƙalau"
Ya kalli Aisha da ta gaishe shi last itama ya amsa, Afeefah ce ta gaishe shi ya
ɗ
an yi shiru kan
ya kalleta sai ya miƙe ya nufi
ɗ
akinshi.
Abeeha ta miƙa hannu ta mistineta, kallon jannah tayi sai jannah ta harareta dole ta miƙe d
on
sun cika ta da lectures kaman me akan Rayyan tun fitansu gida har hawansu jirgi zuwa
sauƙansu magana
ɗ
aya ake babu abinda basu gaya mata ba akan gidan sarauta sai ta tashi ta
kama mijinta a hannu in ba haka ba ta ji a salansa.
Ruwa ta ha
ɗ
a a tray
da cup mai tsananin kyau ta
ɗ
auka ta nufi
ɗ
akinshi, yana zaune bakin gado
dafe da kanshi dake
ɗ
an sarawa ya ji sallamar ta, bai
ɗ
auka za ta shigo ba sai kuma ya ganta
unexpected idanunshi masu shiga jikinta ya kafe ta da su yana yawo lungu da saƙo na jik
in
nata, tana sanye da doguwar riga peach mai roba ya fitar da duk wani shape
ɗ
inta ta
ɗ
aura
dankwalin sai ta sako jelar guda
ɗ
aya ya sauka har kan kirjinta tayi kyau sossai barin ma lips
ɗ
inta dake shining na lip gloss.
Ruwan ta zo ta ajiye mishi ta
na
ɗ
an
ɓ
ata fuska, fuskar yake ta bi da kallo bayan ta ajiye ta juya
zata tafi karab ya riƙo hannunta ya
ɗ
an ja ta tayi baya baya ta zauna bakin gadon gefenshi har
suna gogan juna ya juyo ya kalleta ba tare da ya saki hannun ba.
"Ha
ɗ
e ran nan fa?"
Ya
yi magana yana dan
ɗ
age gira guda alamun tambaya, lumshe ido tayi don maganan ta ji shi
ne har cikin zuciyarta.
Bata san ta narke ba tayi shiru bata ce komai ba. Kuma sai bai ji haushi ba sai ma kyau da ta
mishi yadda take yi da fuskan itama kuma ta j
i daa
ɗ
i da bai mata ihu ba sai ma Ruwan da ya
ɗ
auka ya sha ka
ɗ
an ya ajiye yana dafe Goshi da hannunshi
ɗ
aya har lokacin
ɗ
ayan na cikin
hannunta yana dan motsawa a hankali.
"Ba ka da lafiya ne?"
Ya ji tambayar nata sai ya bu
ɗ
e idanunshi da suka
ɗ
an sa
uya ya kalleta ya
ɗ
aga mata gira
ɗ
aya
"Sorry"
"Kin san Meyasa ban amsa gaisuwarki ba?"
Ta girgiza kai ashe ya san laifin da ya sakata fushin ma.
"Saboda ba haka ake gaisar da miji ba madam..."
Kan tayi wani magana ya ja hannun nata sai jinta tayi ki
rjinshi ya rungumeta ta runtse ido tana
jin zuciyarta na chanza bugu, a hankali ta sa hannunta ta riƙe shi yayi baya baya ya jingina da
jikin gadon ya
ɗ
an lumshe ido.
"Ya kike?"
Taji maganan daga sama, ita dai ta rasa gane kanshi so yake sai ya zauta
ta ko menene?
"Lafiya ƙalau, ina taya ka murnan reunion
ɗ
inka da family... Na kuma ga na
ɗ
i Allah ya taya riƙo"
Ya yi murmushi ka
ɗ
an kan yace
"Ameen, thanks"
Suka yi shiru, ƙoƙarin Miƙewa take ya matse ta
"Your perfume! Yana da daa
ɗ
i"
Tayi murmush
i
"Thank you, gashi na mata ne da na baka"
Dole ya saka shi dan murmusawa yadda take maganan bilhakki.
Sun dan jima haka kan aka kira azahar ya sake ta ta mayar da kanta ƙasa tana wasa da bakin
gyalen ta shi kuma yana kallonta.
"Kin gama exams lafiy
a?"
Tana mamakin yadda sai an manta wani abin shi kuma sai lokacin yake magananshi
"Alhamdulillah"
"Meyasa kika shiga toilet da waya kika jefa ruwa?"
Ta
ɗ
an zaro ido tana mamakin yadda aka yi ya sani shi kuma idanun yake kallo, haka kawai yaji
baya so
su daina maganan Dukda kanshi dake sarawa sai yaji in dai magana da ita ne ko za'a
kwana kaman ba zai gaji ba, sanyin yanayinta, kamshinta, murmushinta da ma maganarta
kashe shi suke.
Bayani take mishi amma Bakinta yake kallo har ta gama bai ji komai
ba, jin ana shirin shiga
sallah ya miƙe ya nufi bayi bai ce komai ba, ta girgiza kai ta dauki tray
ɗ
in ta fito dayake
ɗ
akinshi akwai dan hanya tsakanin shi da parlor da hakan yasa tana gab da bayyana parlor ta ji
Zarah na cewa Aisha
"Aisha kina gani
n Ya Sameer zai yarda ya aureni? Wlh tun ranar da ya cecemu na kamu da son
shi da na fahimci shine Yaya Sameer wanda nake da alkawarin aure dashi tun yaranta sai na ji
na sake kara sonshi kalleshi kiga yadda yake komai cikin wani irin aji da natsuwa...ba
ki ji kishin
da Naji ba da na kalli matarshi"
Aisha tayi dariya
"Zai aureki mana kin taba ganin inda aka yi alkawarin aure aka karya shi a zuri'ar nan? Kuma ai
na ga matar tashi tana da sanyi bare ma dolenta ta ga kishiya har da kwarkwarori ma idan
yana
so sarkin gobe fa take aure"
"hakane kam duk kishi na shiyasa nake dannewa sanin a auren sarki iya ruwa ne fidda kai
kowacce ta iya allonta ta wanke ne, yanzu haka ba za'a rasa ma waenda suka nemi ha
ɗ
in aure
dashi ba ta wurin mai martaba daga ba
yyanar shi zuwa yau"
Sossai maganganunsun ya daki Afeefah, bata san wani irin yanayi ta shiga ba ko motsi bata yi
ba sai da ta ji ya bu
ɗ
e kofa ya fito sai ya tsaya yana kallonta tayi kokarin danne abinda ke taso
mata ta fita parlorn ya bi bayanta ya f
ice masallaci ita kuma kan ta isa dining ma kuyanginta sun
kar
ɓ
a...
"Ba Za mu isa kuyi sallah ba?"
Ta tambayesu tana danne yanayinta kwarai da gaske don for the First time a rayuwarta taji
zafin wani duk abubuwan da ake mata a baya tana kokarin shany
ewa kuma tana kokarin ta ga
bata tsani kowa ba amma yanzu ji tayi bata son sake kallon Zarah a inda take, har
ɗ
aci
ɗ
aci
take ji akan harshen ta maganan son da take yiwa Rayyan ke ta kai koma a ranta...
"Kar ki damu yanzu za mu tafi ma ai"
Kai ta gya
ɗ
a suka miƙe suna mata sai anjima tace
"Na gode sai anjima"
Suka fice ta nufi
ɗ
akinta ta samu bakin gado ta zauna tana dafa kirjinta dake zafi zafi, duk
ɗ
an
farin cikin da ta samu a tare da shi ya kau.
Bata motsa ba sai da aka mata sallama ta ba da izin
i aka shiga sai ta kalli wata mata ce babbar
mace rike da wani tray a hannunta wata kuyanga na binta a baya da akwati
"Barka da wannan lokaci ranki ya dade"
Nauyi taji na matar tace
"Ina yini?"
Matar ta kalleta lallai wannan ba tashin masarauta ba c
e.
"Fulani Fa
ɗ
imatu ce ta aiko mu shirya ki mai martaba na son ganinku gaba
ɗ
aya"
Kai ta gya
ɗ
a matar ta shige bayi ta ha
ɗ
a mata ruwa mai kamshin gaske ta mata iso cikin bayin
ita dai ba don su jannah sun ce mata kar tayi musu a duk abinda ake sakata ba d
a zata ce
musu ba sai ta yi wanka ba yanzu tayi wani amma kuma da ta shiga ruwan yadda aka hada shi
ya mata daa
ɗ
i da ta fito kamshi duk motsinta haka yake tashi.
Turaren kolecture suka bata mai bala'in kamshi ta shafa ko ina na jikinta kan ta shafa lo
tion
ɗ
inta, da kansu suka shirya ta cikin atampha riga da zani da ya zauna mata sossai suka bata
gyale ta yafa bayan sun daura mata dan kwali suka hada gyalen da
ɗ
an kwalin suka yi pinning
yadda ba zai dinga zamewa ba kan suka
ɗ
ora mata wani cream colou
r Alkyabba da yayi mata
mugun kyau kaman ka sace ta ka gudu.
Ta kara turaruka Dukda kamshin ma da take ya isheta, kan suka fito gaba
ɗ
aya ta samu su
Abeeha a parlor
"Masha Allah Kin ga yadda kika yi kyau uwargidan Ciroman fombina kuma Yariman matasan
fombina?"
Sai ta
ɗ
an yi murmushi kadan don uwargida da aka ce ya tuna mata kalaman zarah..
Suka fice gaba
ɗ
aya aka musu jagora har babban parlorn mai martaba sun samu kowa na nan
na kusa kusa dangi da ya kamata a ce sun sani.
Gaisuwa aka yi Mai marta
ba ya gabatar da Uncle Musa da su Uncle sanusi matsayin dangin
Rayyan tunda su suka rike shi tun barin shi gidan har kawo yanzu, yayi musu godiya marar
iyaka kan ya nuna su Abeeha matsayin 'ya'yanshi don ya ce a yanzu basu da maraba da su
Aisha a wurins
hi sai ya nuna Afeefah don Ammi dake gefenshi duk ta nuna mishi su dama
kuma ya riga ya gaisa da su Uncle kan zaman duk Ciroma yayi introducing nasu.
"Ga 'yata Afeefah ita ce matar Ciroma, ina fata za mu cigaba da zama anan cikin zaman lafiya
da ha
ɗ
in
kai yadda muke tafiya, ina marabtar ku da shigowa wannan masarauta matsayin 'ya'ya
masu daraja, duk wani abu da kuke so za ku iya zuwa kai tsaye wurina dukkanku matsayin uba
nake a wurin ku kaman yadda na dauke ku duk 'ya'ya na"
Godiya duk suka yi Afee
fah dai na matuƙar takure kuma zuciyarta bugawa yake kaman zai fito
tana jin idanu sun mata yawa a jiki amma bata iya ta
ɗ
ago ba har sarki ya sallami Matan suka
fice
"Afeefah!"
Ta ji muryarshi ya kira sunanta sai taji wani iri, sunanta a bakinshi dab
an take jinshi chak ta
tsaya ya matso har tana jin kamshinshi da ma numfashin shi dake fita a hankali...
"Ba na son duk abin da za'a baki a gidan nan ki ci! Idan ma ya baki sha'awa za ki iya fada min
in nemo miki amma kar ki ci komai daga kowani banga
re a gidan nan ina fata kin gane?"
Kanta ya ƙulle ta
ɗ
ago ta kalleshi amma ganin idanunshi a kanta ya sa ta
ɗ
an gya
ɗ
a kai.
"Ki amsa min da bakinki, bana son jin cewa kuskure ne ko akasin hakan... Ba kuma na so ki
fara tunanin dalili hope am clear?"
"
In shaa Allah"
Kai ya gya
ɗ
a ya juya ya koma ita kuma tayi gaba ta samu su Jannah, aka fara raka su sashen
Fulani Adama duk inda ta wuce kirari ake mata.
A ƙasa duk suka zauna tana kame cikin kujera suka gaisheta ta amsa tana
ɗ
an murmushi
"ƴa ta Afeef
ah sai ga ki gidan sarauta, ina fata za ki ba da ha
ɗ
in kai wurin ganin an zauna cikin
aminci kin ga nan ba kaman normal gidaje ba"
Tayi murmushi tace
"In shaa Allahu Mama"
"Sannan za ki yi haƙuri da tsare tsarenmu anan, duk muma haƙuri muka yi muke
zaune lafiya
ina fata in kin ji labarin alkawarin zarah da mijinki ba za ki ji haushin mu ba kar ki ga kaman
daga dawowanshi ne aka bashi mata, kin san mu anan al'adar mu in aka haifi namiji da shekaru
biyu ko uku ko ma biyar daga an haifi mace to za'a
yi mishi alkawari wanda sai in mutuwa ce ta
karya, kin ganni nan tun ban yi rarrafe ba nake matsayin matar mai martaba haka ma Uwar shi
Ciroma amma kin ga duk muna zaune ne lafiya cikin amana da kula da juna"
Ta Yi mugun ƙoƙari da ta iya danne hasala
n da ranta ke yi tayi murmushi
"Eyyaaa Allah ya ba mu ikon zama lafiya na gode".
Sai kallonta Fulanin take har suka tashi suka fita ta sa aka bi su da kyautarta na maraba a
ƙ
warya rufe da faifai...
Su Jannah maimaita maganan suke da damuwa ita dai ba
ta ce musu komai ba har suka shiga
wurin Ammi suka gaisheta
"Afeefah kina lafiya kam?"
Ta gya
ɗ
a kai basu jima sossai ba don su Zarah suna wurin suka mata sallama itama kyauta
sossai ta basu a ƙwarya suka nufi wurin Fulani Ameenatou kadaran-hadaran su
ka gaisa ta basu
kyautarta suka nufi wurin Amarya Fulani Salimah itama suka gaisa kan suka nufi sashensu
alkyabbar kawai take so taji ta cire ta huta gashi ana ta kiran la'asar, suna zuwa kuwa ta zame
kayakin tas ta
ɗ
auki karamar riga marar nauyi mai ha
nnun singlet dogo ne sossai silk Brown ta
saka yana da tsagu gefe da gefe har wurin gwiwa ta hau gado ta kwanta kawai bata motsa ba.
Maganganun da ta riska yau kawai a gidan ta ji ya sire mata, bata san ta fashe da kuka ba
zuciyarta na squeezing yana
mata zafi ta ma rasa me ke damunta.
Ta Yi kuka har tayi bacci a haka sai Magrib ta farka ta dauki hijabi ta saka bayan ta wanke
fuskanta idanunta dai har lokacin sun dan kumbura kuma sun yi ja ta fito parlor ta samu su
Abeeha suka
ɗ
an yi hira ta ci abin
ci ka
ɗ
an kan ta ce musu za ta kwanta kanta na ciwo daga
haka ta shige
ɗ
aki.
Abeeha tace
"Addah jannah baki kula Afeefah na da damuwa ba?"
Tace
"Na kula Abeeha ko nima ina taya ta damuwa ace daga zuwa yau an fara mata zancen zata yi
haƙuri mijinta a
ure zai yi, na san zai iya yi probably tunda dama haka tsarin su yake amma
kuma bai kamata ana fada mata ba gaskiya."
"Gaskiya sai Naji da ma bamu zo