Showing 18001 words to 21000 words out of 174924 words
shi
ɗ
ewa, bai hana ta ba ya barta tayi kukan sossai har tana ajiyar
zuciya kan ya
ɗ
auki ruwa ya miƙa mata, sai da ta jima tana kallon hannun nashi kan ta sanya
hannu ta kar
ɓ
a ta sha sossai kan ta sauƙar tare da gintsewa cikin hannunta tana sauƙe
numfashi ta sake ƙura wa bango idanu.
"Ya Sunanki?"
Ta ji tambayar ya zo mata, kallonshi ta yi yana da tausayi haka yana da sanyin hali duk da
khakin sojojin da ta ganshi da shi ba irin wanchan
ɗ
ayan ba da ko a mafarki bata fata ta sake
ganinshi don
kila sai ta sume.
"Afeefah"
Ta furta a hankali
"kina da suna mai daa
ɗ
i Afeefah".
Shiru ta yi.
"Ko za ki kwanta ki huta? Ko in samo miki abin da za ki ci?"
Nan ma shiru tayi, a hankali kuma ko me ta tuna tace
"Eh"
"Eh wa wanne kenan? Kwanciya k
o abinci?"
Da wasa yayi maganan hakan ya sa ta sake kallonshi kan tace
"kwanciya"
"duk biyu dai Afeefah, yanzu kwanta ki na hutawa ni kuma zan je in samo miki abincin kin ga ina
dawowa ke kuma kin gama hutawa sai cin abinci ko?"
Ta gya
ɗ
a kai
"yauwa A
feefah"
Kwanciya tayi shi kuma ya fice.
Ya fi awa
ɗ
aya da fita kan ya dawo, ya samu wani baccin ya
ɗ
auke ta yadda kuma fuskanta da
idanunta suka sake suntuma suka tabbatar mishi da ta sake wani kukan fiye ma da na
ɗ
azu.
Sossai ta bashi tausayi adu'ar
samun sauƙi a ko ma menene dake damunta ya yi mata kan ya
ajiye babbar ledan da ke hannunshi ya fice, office na Ryan ya koma sai dai ya samu a rufe
girgiza kai yayi kan ya juya ya koma nurses station inda ya roki a duba mishi Drn da Ryan yayi
referring
ɗ
inta to don ya san ko mutuwa za tayi ba zai sake duba ta ba. Ganin Dr Sulaiman ya
sa ya nufi office
ɗ
in nashi.
Dukda Captain Saleem zallar soja ne na ƙasa wato land army sai dai tarensu da Ryan ya sa
kusan duk wadda ya san Surgeon General Ryan Moh'd
Khamis ya san Salim, Salim shi ne
ƙ
wallin abokin Ryan don shi ka
ɗ
ai ke iya tolerating mur
ɗ
a
ɗɗ
iyar halinshi da zafin Ranshi sam
Ryan ba shi da hayaniya kuma ba ya shiri da mai hayaniya, ba ya dogon magana kuma ko da
ido yana so idan yayi magana ka fahim
ce shi bare kuma in ya bu
ɗ
e baki ya furta ko za ka mutu
ba zai maimaita ba, yana da saurin fushi kullum a hasale yake ga ko in kula a koma menene
matukar ba shi ya so yin abu ba babu mai mishi dole, sarauta da ƙasaitarshi wane sarki don har
wasu kan tam
bayi ko shi
ɗ
in jinin sarauta ne?
A kofan office
ɗ
in yayi knocking aka bashi izinin shiga ya sanya kai, Dr Sulaiman ya miƙe ya
bashi hannu suka gaisa kan ya zauna yana dubanshi yace
"Dr. Ka san yanayin aikin namu tafiya ce ta kama ni babu zato, zan ta
fi Kano kuma zan kwana
biyu ban san ko za ka iya sallamar ta a yau ba samu in mayar da ita kar in tafi kuma aiki ya
riƙeni in kasa dawowa da wuri".
Dr Sulaiman ya bu
ɗ
e file
ɗ
inta ya sake dubawa sossai kan ya
ɗ
ago yana kallon Salim ya shiga
cewa
"A g
askiya cap. Sallama ba zai yiwu yau ba yarinyar jininta yayi ƙasa sossai matuƙa kuma ka
san hatsarin hakan, ga damuwa dake dukar zuciyarta shiyasa take ta complain ciwon kai da
kirjin dole tana buƙatar kulawar likita atleast na kwana uku zuwa hu
ɗ
u".
Aji
yar zuciya salim ya saki.
"Dr Sulaiman ko za ka taimakeni don Allah ka kula da ita har na dawo?"
Murmushi Dr Sulaiman yayi
"Kar ka samu matsala In shaa Allah zan kula muku da ita, akwai wata tsohuwa dake mana aiki
gida zan
ɗ
auko ta ta zauna muku da i
ta har ku dawo"
Godiya sossai salim ya mishi kan ya fice.
Ko da ya koma
ɗ
akin ya samu ta farka abinci ya sa ta ci yana
ɗ
an janta da wasa yana mata hira
har ta ce mishi ya isheta bayani yayi mata a kan bayan Magrib zai bar garin akwai mai zuwa ta
zaun
a da ita har ya dawo in shaa Allah yana fata kan ya dawo ya samu ta yi sauƙi samu ya
mayar da ita gida Fatan hakan ba zai haifar mata da matsala ba?
Ta amsa da "uhmm" a ranta take raya a yanzu ko
ɓ
ata ta yi
ɓ
at a duniya babu mai neman ta
bare ya damu da
wanzuwar ta ko akasin hakan, yanzu haka aka tambayeta ina za'a kaita bata
sani ba don ko giyar wake ta sha ba za ta tunkari wurin uncle ba dolenta dai shi ne kawu, Nan
ma kuma bata san abin da za ta iya riska ba Shikenan ta koma Square Zero?
Wasu irin
zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata.
"Afeefah!"
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*009*
Captain Sal
im ya ƙira sunan nata cikin tausasawa, ta
ɗ
aga ido ta kalleshi.
"Akwai wani matsala ne?"
Ta girgiza kai.
"Na gode sossai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
Yayi mata murmushi, bai bar
ɗ
akin ba sai ga dattijuwar matar ku
ɗ
i masu kauri ya fitar y
a ba
dattijuwar saboda sayan abinci ya nuna mata kaya kala biyu dogayen riguna da ya siyo da man
shafawa, macline, brush, turare da soson wanka ya roƙe ta da ta kula da ita don Allah har ya
dawo, kaman kar ya tafi haka ya fice a
ɗ
akin domin haka kawai y
a tsinci kanshi cikin tsantsar
tausayinta da har yana so ya yiwa zuciyarshi yawa.
Baaba jummai macece mai faram-faram da saurin sabo duk yadda Afeefah ta yi shiru sai ta
saka ta magana har da murmushi, tana kula da ita sossai sossai, bata maƙe ku
ɗ
in d
a salim ya
bata ba ta kan sayo musu kayan daa
ɗ
i ta bajo musu tana cewa
"Ke 'yannan sa hannu maza ki ga mu ci kin ga ko mutuwa muka yi yanzu za'a
ɗ
auke mu da
nishi saboda nauyin mu ina amfanin kana da shi baka ci ba? Maza-maza sa hannu"
Dole Afeefah t
ake murmushi kuma ta biye wa Baaba ta ci sossai dare idan an gama duba
Afeefar kan su kwanta bacci za ta shiga ba ta labarin aurenta da ma rayuwar da tayi har ma da
irin kishin su na da chan baya da kissa kala kala da kan kashe Afeefah da dariya, kan kwa
na
biyu ya zagayo har ta fara manta tarin damuwarta, duk Sallar ta kuwa bata ta
ɓ
a mance iyayenta
da Aunty zee ba ta kan kai wa Allah kukanta musamman cikin dare akan ya gafarta musu yayi
musu rahama (Tana roƙon duk wanda ya zo across wannan littafi ya n
ema musu rahama domin
Allah
🙏
)
Kaman yau Dukda safiya ce bayan sun gama karyawa da doya da miya ha
ɗ
e da shayi da duk a
bakin asibitin Baaba ke sayo musu ta dubi Afeefar da ta
ɗ
an yi shiru tana tunani tsoron ta
ɗ
aya
dawowar salim ina za tace ya kaita?
Ina ta nufa? Ya zata yi?
"Wai 'yannan kin kuwa san abin da ke ƙara ba ni mamaki ma a wannan zamanin?"
Afeefah ta girgiza kai tana
ɗ
an kakaro murmushi don ta san zancen baaba bai ta
ɓ
a wuce kan
ta
ɓ
ar
ɓ
arewar tarbiya a wannan zamani ba.
"Mu a lokacin mu
ina mace ta isa ta ƙira ko mai irin sunan mijinta? Kai ko bayan ya mutu ko kun
rabu mu kam ba ma iya kiran sunan ko da kuwa da kuskure amma ki ji mace yanzu gatsal tana
cewa Ummaruuu a gaban yara ma da iyayenshi ko nata kai ko a gyalen su"
Dariya Afeef
ah ke yi sossai tace
"Yanzu Baaba ko sakin ki yayi ba za ki iya ƙiran suna mai irin nashi ba?"
"Eh mana! Ai da kunya 'yannan"
"Tabb baaba ba dai irin sakin wannan zamani ba, komai fa akwai silar chanzuwarshi Baaba bai
wuci mazan ma na da na yanzu ba
ɗ
a
ya ba ne shiyasa ake ganin bambanci"
"za dai ki kare su ni dai na fa
ɗ
a miki ki kiyaye, kin ga maza suna matuƙar son a ba su girma,
idan za ki ba namiji girma toh tabbas mutuncin ki ma zai zama daban ne a idanunshi ko da
kuwa ya auri wata ne"
Tana murmu
shi sossai tana tuna wato gidan kawu Labaran ban da rashin tarbiya har da tarin
jahilci da suke dashi, daga mu'amalar iyayen har ta 'ya'yan gashinan dai gashi nan yo idan ta
ciwo shi ai sai dai a ji suna dambe da mata...
Fuskanta
ɗ
auke da murmushi tan
a sake jinjina rayuwar da don baaba jummai na sake bata
labarin yadda maƙota sai ya hukunta
ɗ
anka baka sani ba idan ma ka sani ka je har gida ka
mishi godiya amma yaran yanzu ko kanwarka ce ka mari yaronta gabanta sai ta maka Allah ya
isa a gaban yaro t
o me yasa ba za'a lalace ba? Haka batun ƙarfafa zumunci Meyasa zumunci
ba zai yi ƙarancin ba yara suna 'yan pendo da
ɗ
an kawu amma idan wanchan sun fi ku
ɗ
i sai ka
ga yana nuna bai san yayyunshi cousins ba ko ya fi karfinsu uwa kuma ta kasa kwa
ɓ
a saboda
tana ganin hakan ce daidai daga mutum mai ku
ɗ
i ne level nashi ya fi karfin talaka ko da kuwa
cikin umma
ɗ
aya ne.
Turo kofan yayi bakinshi
ɗ
auke da sallama a kanta idanunshi suka soma sauƙa, ajiyar zuciya ne
ya kufce mishi ba tare da ya san dalili ba m
urmushi na yalwatuwa a fuskar tashi ganin ko da
suka hada idanu murmushin bai kau daga kan fuskanta ba, fara'a na yi mata kyau ya ayyana
hakan a ranshi maganan Baaba ne ya yanke mishi tunani
"Bawan Allah sannu da dawowa, lale maraba"
Ya saki murmushi
ya
ɗ
an rankwafa ya shiga gaisheta ta amsa cike da kulawa tana tambayar shi
aikin da sanya mishi albarka, Afeefah ya duba da ta
ɗ
an duƙar da kai tana kallon yatsun
hannunta
"Na shigo kuna ta raha me yayi miki daa
ɗ
i haka Afeefah?"
Ta
ɗ
ago tana murmushi
"Ni da Baaba ne, barka da dawowa"
Yana zama gefen gadon tuni
ɗ
akin ya cike da sassanyar kamshin shi ya ce
"Yauwa ya jikin? Hope kin samu lafiya?"
Ta gya
ɗ
a kai tana dorawa da
"Alhamdulillah na gode"
Da Baaba suka cigaba da hira akan jikin nata ita dai
sai murmushi bata magana har Dr.
Sulaiman ya shigo, sai da suka dan sake hira kan ya miƙawa salim takardar sallamar ta
"My patient is good to go, kawai dai ta kiyaye sa damuwa a ranta and gaskiya ku kula da ita
sossai da sossai Dukda SG Ryan yayi mug
un ƙoƙari a kanta babu wani traces na guba a jikinta
amma don Allah ku sake kula, ke kuma Afeefah ki saka a ranki komai yayi zafi maganinshi
Allah. Manzon Allah S.A.W ya ce; "Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana
nan madawwami a cikin
Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha
guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwadar ta a cikin Wutar
Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani karfe,
to karfensa na
nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana
madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109)".
"Allahu akbarr" Baaba jummai ta zabga kabbara Afeefah dai kanta ƙasa zuciyarta na sake shiga
ci
kin tsantsar nadamar wannan yunkuri da tayi da ta mutu ta shiga ukunta.
Godiya sossai ta musu haka salim yayi wa Sulaiman da Baba godiya murmushi kawai Sulaiman
yayi yana shaida wa Baaba akwai driver waje zai mayar da ita gida sai ga Baaba na hawayen
ra
buwa da Afeefah Dukda zaman nasu na kwana biyu ne amma sanin ranar sake ha
ɗ
uwa sai
Allah, Afeefar ma sai ta kama hawaye, a duk sadda ta ga wani ya kaunace ta Saboda Allah ta
kan ji son shi fiye da yadda shi ya kaunace ta don masu hakan a gareta basu da y
awa, bata yi
shiru ba ko da Baabar ta tafi sai ma zuciyarta da ya tsinke, tsoro da fargaba suka lalla
ɓ
o suka
rufe ta.
Daram! Haka zuciyarta ya buga a sadda Salim ya
ɗ
auki 'yan kayanta yana furta
"Mu je ko Afeefah?"
Jiki a sa
ɓ
ule ta sanya kafafunta
ƙasa ta shiga takawa har ta wuce shi yana riƙe mata da ƙofa
bayan ta fita ya ja kofan a bayanta ya rufe suka jera a tare har motar shi, ya bu
ɗ
e mata gidan
gaba ta shiga ya bu
ɗ
e baya ya ajiye kayanta kan ya zagaya ya shiga ya ta da motar suka fice
daga
cikin asibitin, cikin natsuwa yake tukin kan ya
ɗ
an kalleta
"Anchau muka nufa ko?"
Kamar mai karyayyen wuya haka ta gya
ɗ
a kai gabanta na dukan tara-tara, bata fata Uncle ya
raba ta da su suhail bata fata su tashi a hannun kishiyar uwa, daga shi har ya
ran wani irin
tausayinsu take ji har
ɓ
argonta bata ga laifin uncle ba don ta tabbatar dole mutuwar Aunty zee
ta jijjiga shi fiye da ƙima tana fata da adu'ar Allah ya sa ya sassauto ya kar
ɓ
eta kar ya kore ta.
Salim ya gya
ɗ
a kai shima, motar ya
ɗ
auki sh
iru na seconds kan yace
"Afeefah!"
A hankali ta amsa
"Na'am"
"Na san kowa abinda yake fa
ɗ
a miki jarrabawa, kaddara haƙuri. nima ba zan chanza ba don
akan hakan Allah ya halicce mu haƙuri kuma da kaddara ibada ne kaman yadda ya halicce mu
don mu bauta
masa, idan kika ga na wani Afeefah sai kin yi hamdala wani jarabawar shi
'ya'yanshi, wani za ki samu jarabawarshi Mata ne, wani talauci, wani dukiya hatta Mahaifiya ta
kan iya zama mummunar jarabawar
ɗ
a, kaman yadda rayyan ya fa
ɗ
a kuma Sulaiman ya ba ki
har hadisi, da kashe kai shine mataki mafi sauƙi a yayin da duniya ta yi wa bawa tsanani da ba
za mu tarar da miliyoyin mutane ba a raye, akwai wani hadisi da Manzon Allah S.A.W ya tashi
tsoratar da masu yunkurin kashe kansu da ko tunanin aikata hakan
ka yi to ka yi gaggawar tuba
ka tsarkake zuciyarka daga shaidan. Ban san irin naki ƙalubalen ba amma ina sake jan
hankalinki da ki kiyaye dokokin Allah ki duƙufa da Adu'a In shaa Allahu komai yayi farko yana
da ƙarshe kinji ƙanwata?"
Kai ta gya
ɗ
a mis
hi a hankali cikin sassanyar Murya tace
"Yaya Salim hakika ba ni da bakin gode muku, kun ceceni daga azabar Allah da baku zo ba a
lokacin da ban san a yanzu wani hali nake ciki ba. Na gode Na gode Allah ya yaye maka naka
matsalolin ya saka maka da gidan
Aljanna"
Ya amsa da Ameen yana
ɗ
an murmushi.
Kaman yadda ta zata isar su Anchau kai tsaye gidan uncle suka yi, ko da ya tura yaro yayi
mishi sallama da uncle ba'a jima ba sai gashi ya fito idanunshi na sauƙa kanta yayi mugu-
mugun
ɗ
aure fuska bai ts
aya ma salim ya gama bashi haƙuri da koro mishi jawabin da ya sa bai
dawo da ita kan lokaci ba ranar ya shiga karta musu rashin mutunci yana kwashe mata albarka
duk yayi wani irin susucewa, sai jefanta yake da munanan kalamai da suka zama tamkar rurin
g
arwashi a zuciyarta, ya shiga tuna mata Alkhairin Aunty zee a rayuwarta da mugun
sakayyarta, ya kuma yi alkawarin muddin bata bar mishi kofan gida ba wallahi shi zai kawo
karshenta yayi ajalinta.
Kokarin bashi hakuri salim ya shiga yi ganin tana wani
irin kuka amma ina tuni ya soma tara
musu jama'a babu arziki suka koma mota, ta ha
ɗ
a kai da gwiwa tana ƙara fashewa da wani
kukan mai ta
ɓ
a zuciyar duk mai saurare.
A hankali salim ya ja motar sai da suka yi nisa sossai yayi parking tare da jingina bayan
sa da
jikin kujerar ya lumshe idanu yana sauraren kukan nata da idan har ka ji ka san duniya bata
yiwa mai yinsa daa
ɗ
i. Sai da tayi ma'ishi bai ce mata komai ba da kanta ta
ɗ
ago ya miƙa mata
ruwa ta fita ta wanke fuskanta ta dawo ta sha ka
ɗ
an kan ta mi
ƙ
a mishi ba tare da ta kalleshi ba
ya sa hannu ya kar
ɓ
a.
"Ki yi haƙuri Afeefah!"
Ta gya
ɗ
a kai
"Yanzu ina kuma kike da shi da zan kai ki?"
Hawaye ne ya sake cike idanunta a sadda take furta
"Akwai kawuna a Dutsen-wai"
Cikin dasasshiyar muryarta da
ya dishe saboda kuka.
Motar ya ja tare da miƙa hannu ya kunna musu ƙira'a domin zuciyarta