Showing 9001 words to 12000 words out of 174924 words

Chapter 4 - Haihuwa-Da-Hanji-Complete

komawa ta sake bingirewa da bacci"

Afeefah tayi murmushi

"Toh shikenan na wuce makaranta"

"kar

ɓ

i"

Ta matsa ta kar

ɓ

i

ɗ

ari

biyu da yake miƙa mata

"Sai kin dawo a mayar da hankali"

Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da

tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.

Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa

ba koyaushe littafi na

hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu

programs na makarantar, bata da ƙawa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams

ake don haka yau revision ƙarfe sha biyu suka tashi t

a nufo gida cikin natsuwa.

Sai dai ta samu babu kowa, ta kar

ɓ

i key a maƙota ta shiga sai da ta zare uniform

ɗ

inta ta sauya

da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta

ɗ

aura

dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta

ɗ

ora mu

su tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata

ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san

suna da dangin nesa nesa ta

ɓ

angaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba

ko daukar ta da muhim

manci Dukda ita kanta Aunty zee

ɗ

in ba ta su take ba abinda ke gabanta

ma ya fi karfinta.

Tana sauƙe faten doyar sai ga su sun shigo

"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"

Aunty zee ta leƙo kicin

ɗ

in tana tambaya

Dariya Afeefah tayi

"Aun

ty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"

Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta miƙawa Afeefahn, Afeefah ta kar

ɓ

a ta shiga saka

mata kan tace

"Eh Afeefah ban jin daa

ɗ

i ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ƙani"

Wan

i irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee

ɗ

in sai ta hau hawayen

murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta

a duniya?

Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace

"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle

ɗ

inki da ma

ɗ

ayar Auntyn taki da suka tasa

ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana

yasa"

Tana murmushi ta ƙarasa saka mata ta dauka mata zuwa gind

in bishiyar dake ba da iska mai

ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa

a cin abincinta.

Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term

ɗ

in don Aunty

tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee

ɗ

in ba, ko

tsinke in ta ga zata

ɗ

aga za ta kar

ɓ

e duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta

yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan

ba ko ta wani

ɓ

angare, kishiyar Aunty zee

ɗ

in ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa

ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani ha

ɗ

u da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko

hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar

bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba

tunda babu abin da ya ha

ɗ

a su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan

so bata damu ba sam.

Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta

dawo

gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da

safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta

"Aunty ki taya ni murna"

Result

ɗ

in ta miƙa mata

"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah uban

giji ya sa ki fi haka ya dafa miki a

dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi

kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"

Kai ta gya

ɗ

a tana ta dariya.

****

Aunty zee

ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta

tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa

Aunty zee

ɗ

in hira ka

ɗ

an kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka k

oma sati hu

ɗ

u

kenan.

A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah

ɗ

in tana da matuƙar buri a kan rayuwar

Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda

ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya ci

gaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba

ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar

hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah

"Wai kuwa kin san kamanninki har ya

ɓ

aci da Yaya Aisha?"

Afeefah ta

ɗ

ago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin

Aunty zee

ɗ

in

"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"

Miƙewa Aunty zee ta yi ta shiga

ɗ

aki ta

ɗ

an jima sossai kan

ta fito da wasu hotuna hannunta, a

lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da

cikinta har ya turo sossai ta zauna.

"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokac

in

bikinta ne da babanki"

Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na

ɗ

an rawa ta sanya ta kar

ɓ

a hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta

da bata sani ba zaune sanye da zani da rig

a tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke

ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar

ta irin na mamanta ne, baƙin fatarsu mai sheƙi, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su,

karamin bakinsu da fa

raren hakwaransu hatta dimple guda

ɗ

aya da maman nata ke dashi a

gefen hagu itama tana da shi.

Ra

ɗ

a

ɗ

in maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici?

Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iy

ayenta take tunawa sai

taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk

duniya idan da za'a ce me take buƙata ayi mata ko da abu na ƙarshe ne za ta za

ɓ

i su yi rayuwa

na har abada amma ake mata Ƙazafin kashe su, anya

zuciyarta za ta ta

ɓ

a warkewa? Anya za

ta iya yafewa masu alhakinta?

Ɗ

ago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee

"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda

kake yi in ba hakan ba ta ya zan za

ɓ

i wannan ra

yuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan

hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin ku

ɗ

i ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba?

Yanzu wannan pure soul

ɗ

in ni na kasheta ko?"

Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta

san fitan su

ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwo da ra

ɗ

a

ɗ

i...



🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-G

ureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku yi ta Adu'a mu ƙare a haka ina jin karsashin typing, ina jin daa

ɗ

in comments

ɗ

in ku Allah ya

bar ƙauna*

*005*

Hannunta ta riƙe cike da tarin tausayinta da kuma ƙaunar da take jin tana mata fiye da ƙima ta

shiga cewa

"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ƙage ne kawai da Ƙazafi irin da jahilai daga cikin

al'ummar mu, ƙarancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a

ƙ

arƙarorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntu

ɓ

e

bawa yayi sai an

fa

ɗ

i dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.

Afeefah Kowacce rayuwa akwai ƙalubale ciki ke kuma ta ki kalar ƙalubalen kenan, amma fa na

fa

ɗ

a na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai

ubangiji, duk

kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ƙare ne ko da sanadi ko babu

dole babu maƙawa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ƙaunar da

kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga

kina zub da hawaye ko kin ƙuntatawa kan ki

saboda ƙaddarar da ba ke kika

ɗ

orawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara

ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassaƙa

ba su isa su hana ki to

ho ba"

Jikin Aunty zee kawai ta fa

ɗ

a tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta

ɗ

ago

"Na miki alƙawari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki ta

ɓ

a kuka a

kaina ba"

"Allah ya amince hajiya ta"

Dariya Afeefah ta s

aki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar

'yar kasuwa don tana so tayi ku

ɗ

i saboda wani dalili nata. Ƙaurin kamawar leda da suka ji ya sa

ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta

"Aunty

alele na so yayi mana buƙulu"

Aunty zee na dariya tace

"Hira ta yi daa

ɗ

i ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"

Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ƙasan guda biyu da ledar ya ƙone nan ta zuba musu tare da

Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zau

na suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan

sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata

"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"

Murmushi ta saki kan ta kar

ɓ

a tana godiya.

Wasa wasa cikin Aunty zee ya shig

a watan haihuwa, ta

ɓ

angaren Afeefah tana nan tana

ƙ

oƙarin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta

ɗ

auki na

ɗ

aya kuma 3rd term

nan suna ƙare ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a

bakinta ba kam

an baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa

saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee

ɗ

in ta shigar da Afeefah cikin business

ɗ

in ta, wani

lokacin ta kan aike ta ita ka

ɗ

ai ma kasuwa wurin customers

ɗ

inta kuma ta zo ta raba w

a clients

ɗ

inta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki

duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar

da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma k

o nan gaba zata iya anfani da

kayanta idan buƙatar hakan ta taso.

A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi,

hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu

kasanc

ewar tun da abin ya fara mijin ya ƙirata, ta fi kowa shiga damuwa an ƙarbe ta zuwa

ɗ

akin

haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ru

ɗ

ewa babu abin da take tunawa vividly

sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ƙarshe daga ita har babyn s

uka koma wannan abu ba

zata ta

ɓ

a mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya ka

ɗ

a a yanzu Allah ka

ɗ

ai

ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.

Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes

ɗ

in da su

ka kar

ɓ

i haihuwar suka fito suna musu albishir

na ta samu 'yan biyu mace da namiji fa

ɗ

in kalar murnar da suka yi

ɓ

ata baki ne. Karo na

barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin

sha'awa kaman ta Ha

ɗ

iye su, s

am bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta

"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"

Da sauri ta juyo tana dariya

"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"

Ta

ɗ

an saki murmushi.

"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"

Ta furta hawaye na ganga

ro mata Dukda tana sauƙa sai da ta ji

ɗ

uminsu kan wannan

wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman

mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe

ta da ganin ƙwant

a? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta

ba don ko yau ta fa

ɗ

i ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a,

bata san daa

ɗ

in haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman

ta rabu da

baƙin ciki har abada matukar suna kusa da ita.

A hankali Afeefah take kokarin

ɗ

aukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn

"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike

ɗ

aga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki

ɗ

aga

su?"

Yadda tak

e maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta

kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da

hankali ba don Aunty zee ta amsa mata

"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce d

a zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata

iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"

"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya ta

ɓ

a su bare

wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"

Da sauri Afeefah ta

mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta

ɗ

ago ta kalleta

"Me kike nufi Hamdiyya?"

"Gaskiya nake fa

ɗ

a Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya

koma baƙin ciki ba"

Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi

wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi

Aunty zee ta

ɗ

ora mata yaran duk biyu a kan kafafunta

"Afeefah ga su nan ƙannenki ne, ki riƙe su yadda kike so"

Juyawa ta yi ga hamdiyya

"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan ta

ɓ

a zuba ido ki

tozarta

ɗ

iyata a

gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daa

ɗ

in su ko? To wallahi zan iya za

ɓ

ar

Afeefah sau dubu kan in za

ɓ

e su sau

ɗ

aya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"

"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"

Ko

kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe

da kuka mai ƙarfi tana yunƙurin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son

abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ƙwarai wurin ha

ɗ

e kawunansu ba zai

so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin

farin ciki tsantsa.

"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya ha

ɗ

a ku?"

Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta

"

Ka yi haƙuri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk

ɗ

aya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama

nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"

"Zainab!"

Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daa

ɗ

i

"Gori kika yi mata?"

"Amma dai ka fi kowa

sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan ta

ɓ

a yi mata ba

don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login