Showing 165001 words to 168000 words out of 174924 words
da ama
na tsawon
shekara da nayi a gidan nan baka ta
ɓ
a hantara ta ba, wlh baka min komai ba ni ban ga laifinka
ba ko da ka zarge ni saboda ina da tambarin tun farko manne a goshina"
"Na kasa amincewa da cewa Allah ne me kashewa kuma mai raya wa, hankali na y
a tashi ainun
don bayan mun binne zainab kin dawo mun kore ki sai muka muka je asibiti da su Suhail za'a yi
musu riga kafi a kuma ba mu madarar da ya kamata su cigaba da sha anan ne likitan ya ji
maganan da muke yi da Hamdiyya da maiyya ce ta kashe zain
abu yayi saurin taka mana birki
ya kuma shiga yi mana bayanin abinda ya faru da zainabu wanda bamu sani ba, ya ce mata
dayawa suna samun wannan matsala na Postpertum ko a samu ta
ɓ
uwar mu'amala ko irin
ciwon cikin wasu kam ma har a zaci sun haukace ne, c
iwon cikin nata bamu farga da wuri ba
sai da ya mata illah kwarai muka koma a sannan babu abinda za su iya ta rasu. Hamdiyya
kuma dama ta jima tana yi mata hassada tana jin haushin yadda ta samu ciki ita tana zaune
hakika ta yi yunkurin illa ta cikin tu
n kan su zo duniya Allah na kare su har ta haihu tana ganin
kaman za ku ha
ɗ
u ku kwashe dan abinda na mallaka da ke da zainabu ga yarana da farin cikin
samuwar su bai
ɓ
oya mini kuma dama ta jima tana sanyawa ranta ba sonta nake ba na aureta
ne kawai don
in haihuwa a yanzu da bata haihu ba matata ta haihu ta gama amfani kenan zan
iya sakarta kowani lokaci hakan yasa ta ƙarfafa hassadarta a kanku musamman ke tana amfani
da baƙanta miki tana kuntatawa Zainabu.
A ƙarshe tayi sanadin da kika bar gidan nan
anan ta fara rainon azaba ga yarana ba tare da na
sani ba, duka zagi tun basu san kansu ba, ta bar su da yunwa ta bar su cikin ruwan wanka duka
don ba ita ta haife su ba Allah ne ke kare su ban sani ba, a ranan da na san duk abinda take
kullawa na shig
a masifar tashin hankali marar misaltuwa musamman in na tuna abinda na yi
miki daga nan jinina ya hau na samu matsalar shanyewan jiki, a takaice Hamdiyya ta tattara
komai ta sayar akan ba zata iya zama da ni ba ga jinya, ga rainon ƴaƴan da ba nata ba kum
a
bata da damar haihuwa, ko sati ba'a yi ba na samu labarin mota ta ka
ɗ
e ta ta rasa kafafunta ta
kuma rasa rabin fuskarta duk kudin yana tafiya a jinyar da har yau bata warke ba. Ku
ɗ
in da
Zainabu tayi ta ajiye miki a asusu da su na tsira sai waenda abok
an arziki kan kawo da shi nake
aika yaran nan su sayi abinci su ci ko makota su basu, bana iya yi musu komai ko wanka sai dai
su je su watsa"
Sossai Afeefah ke kuka, Allah sarki rayuwa amma Hamdiyya ta cika azzalumar matar uba kuma
ko a yanzu ta ga
ishara, Rayyan Aisha ta kira don Afeefah ta kasa daina kuka hankalinta ba
karamin tashi yayi ba shi ya kira aka dauki uncle Usman yace a koma cikin Kaduna dashi a
kaishi asibiti zai kira Sulaiman kan su juyo.
Su Suhail na rungume da Afeefah suka fito
zuwa mota yan unguwar na zuwa su gaisheta suna
ta mamaki har wasu na tambayar ko Afeefahn Aunty zee ce ta gya
ɗ
a musu kai, Rayyan ya
zubar da dukiya don duk wanda ya nuna ya gane ta aka gaisa sai ya mishi kyauta daga nan
suka nufi Dutsen-wai.
"Afeefa
h!"
Ta kalleshi ya riƙe hannunta ya sa hannu yana share mata fuska yace
"kuka sam bai kamace ki ba, ko don zafin da nake ji a nan ya kamata ki sassauta"
Ya ƙarasa yana nuna zuciyarshi. Ta gya
ɗ
a kai ya ce
"Na san burinki shi ne ki yi ku
ɗ
i, ba kuma don w
ani abu ba sai don ki tallafawa al'umma
musamman na ƙauye irin cikin kauyen ku da ake rayuwa kara zube babu neman ilimi, babu
sana'a ana rayuwa irin rayuwar dabobbi ko zamanin da chan baya, ina so in sanar miki cewa na
ba da wannan gudumawa na bu
ɗ
e miki
Center na farko ina fata ya zama farkon buduwar tarin
alkhairanki... Ina adu'a Allah ya sanyawa gidauniyarki daga na farko har na karshe albarka ya
dafa miki ya kuma isar miki da ladan... Akwai Center da aka gama bu
ɗ
ewa a Dutsen-wai da
Sunanki a yau za
'a yi taron kaddamarwa a cikin wannan plaza akwai kayan aiki da malamai na
Musamman da zasu ke koyawa mata sana'o'in dogaro da kai kaman su
ɗ
inki da sauransu
akwai kuma makaranta islamiyya da malaman da muka yi hiring na musulunci da za su tsaya
tsayin
daka wurin ganin sun koyawa matan wannan kauye da ma mazan addini akwai kuma
babban masallacin juma'a a kusa da wannan plaza shi kam na Mammi ne ina Fatan duk Sallar
da za'a yi ciki ladar ya isa gareta. Ba ni da alaka da kula da wurin daga yau duk naki n
e ga
takardun da ma komai da komai na plaza
ɗ
in kyauta ne na musamman zuwa gareki"
Jikinshi kawai ta fa
ɗ
a don ta gigice ta rasa ma wani irin abu zata yi, kuka kawai ta saka mishi
yana ta aikin rarrashi za tayi godiya ya manne Bakinta da nashi yana kis
sing passionatly sai da
ya tabbatar ta daina hawayen kan ya saki yayi pecking goshinta
"Anything for you my baby girl ki sani wannan
ɗ
in mafarin nasararki kenan a rayuwa, duk wanda
ya baƙanta miki a da a yanzu yana a karkashin kafafunki, na ji daa
ɗ
i da
kika nufi saka musu da
alkhairi bayan sun bi ki da sharri amma ki sani wannan yunkuri naki na basu ilimi makami ne
mai girman gaske a duniyarsu ladar ki sai a wurin ubangiji"
Daidai nan suka isa cikin Dutsen-wai ita ke kwatanta musu har kofan Gidan Kawu
Labaran.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
"Last Page na zuwa anjima in shaa Allah. Wlh j
iya na yi gajiyar da ban san adadi ba ina bu
ɗ
e
ido da niyyar typing idon na rufuwa ganin ba zan iya ba yasa nayi bacci and yau ma same thing
zan lalla
ɓ
a in ba ku shafin karshe in shaa Allah. Na gode da haƙuri da ni*
*59*
A gaban gidan ta tsaya ta ƙ
ura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna
baƙar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na
raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da
kyar t
a hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni'imomin Allah a gareta sai ta furta
Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ƙara ta
ɓ
ar
ɓ
are musu wane
wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushew
ar ginin ƙasan
dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga
da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai
da suka ha
ɗ
a idanu, Chakk ya tsaya yana ƙare mata ka
llo kaman yadda ita ma take ƙare mishi
kallo.
Sanye yake da jallabiya baƙa har da hula ta
ɓ
ani ka ji hadisi da chasbi riƙe a hannunshi sai wani
littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gaba
ɗ
aya ya lalace, shi karan kanshi bai
gane ta ba sai d
a yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata
wankin inji ne, kaman bata ta
ɓ
a sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace
"Ka..kawu"
Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu d
a kayan tsubbu da
komai.
"Af...Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?"
Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta
ɗ
aga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube
gwiwowinshi ƙasa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, na
ta dai bata san
me take ji ba don abubuwa ne suka ha
ɗ
e mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a
gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana
nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta b
a ta wani
ɓ
angaren tana jin babu
daa
ɗ
in yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman ku
ɗ
in
guzuri.
Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa riƙe amana da zumuncin
ɗ
an uwanshi yake yi wa
kuka, kunya mai tsanani da ba zai i
ya cewa ya ta
ɓ
a jin irin shi ba yake ji na
ɗ
iyar cikinshi.
"Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na
zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ƙima, na wargaza natsuwarki
har ya kai
na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da baƙar zuciyata... Ina kallo
matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da
kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min Ƙashin kifi, an zo neman
aurenki
har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son
zuciya irin tamu... A ƙarshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba,
mecece sana'ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da
ku
ɗ
i sun kuma nemi auren
kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta fa
ɗ
a min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na
ci arziki na fa
ɗ
a hannun 'yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke
fa
ɗ
a, a ranar na tabbatar harkar shan jini da
maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa
ya rufe ni a kullum Adu'a ta shi ne yadda zan ganki kafin ƙasa ya rufe min idanu Afeefah...."
Sossai yake kuka ta mayar da kanta ƙasa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha
hawaye suke shi kuwa Ray
yan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa.
"Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?"
Zuwa lokacin makota duk ana maƙale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu
yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankal
inta kansu ba yayinda duk suke kuka.
Hannun kawu ta riƙe tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace
"Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na
duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji... Tsoro
nake ji kar ku ƙi kar
ɓ
a ta.."
"Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin
yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don
Allah, Don darajar Allah ki dubi girma
n shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah"
Kai take gya
ɗ
a wa ta kai hannu ta share mishi fuska
"Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gaba
ɗ
aya"
Inna Asabe ta rarrafo
"Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah"
Ta kallesu sai t
a ga inna Larai na ja da duwawu kafa
ɗ
aya kam babu gaba
ɗ
aya kuma ba sanda
bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da
kukan ya taho ya
ɗ
aga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike d
a
kamshi ya fara
ɗ
auke mata hawayen fuskarshi babu
ɗ
igon walwala.
"Am sorry"
Ta fa
ɗ
a a hankali.
Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za'a iya shimfida musu su
zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kall
on Rayyan.
"Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?"
Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ƙasa ko wannan ka
ɗ
ai ya isa
ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana
wurin idan ba don
haka ba me ha
ɗ
in kifi da kaska?
Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun
daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan
sun rabauta don ilimi shi ne g
inshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da
yayi musu matuƙar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za'a ci ma
wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya
yinshi y
a ga an ci wani abu ko da sau
ɗ
aya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi
mata fa
ɗ
a ganin da gaske ranshi ya
ɓ
aci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da
ita har kawo yau
"Allahu Akbar... Allahu Akbar kabiran lallai shi mahaku
rci mawadaci ne kuma mai haƙuri shi
yake dafa dutse... Yanzu Afeefah har 'ya'yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta
sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma'ar da babu
irinshi a wannan gari? Allah mai girma
Allah mai yadda ya so"
Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji.
Kallon Inna Larai tayi tace
"Kawu me ya sameta?"
"Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai
da kyar muka hada
kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a
dole take yawo a haka da ja da duwawu"
Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da
iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron k
usan duka jama'ar garin suna
ɗ
akin taron barin ma
fankoki dake ka
ɗ
a su ya sa sai nishadi suke.
Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta za
ɓ
i inganta rayuwarsu
ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama mu
su komai, da ya zo wurin kiran
suna sai ya ce
"Wannan
ɗ
in ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman
Matasa na ƙasar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??"
Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan
garin ido suka zuba mata
suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta miƙe ta haura
podium
ɗ
in ta kar
ɓ
i mic
"Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata
ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsari
nsa daga
sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai
ɓ
atar da
shi, wanda kuma ya
ɓ
atar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta
da gaskiya sai Allah, shi ka
ɗ
ai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina sha
idawa cewa, Annabi
Muhammad bawansa ne manzonsa
ne. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum
warahmatullah"
Duk suka amsa, ta
ɗ
an sauke numfashi
"Ba gixo ba kuma ba mafarki ba haƙiƙa ni din ce Afeefah kamal wacce
kuka fi sani da Annoba
ko kuma Mayya a wannan gari, haƙiƙa na jure abubuwa dayawa daga gare ku 'yan uwana,
yayyena, Ƙannene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata
da gudu. Abar tozarta wa da wulaƙanta wa, Abar muzantawa
a cikin al'umma sa
ɓ
anin a yanzu
da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa
inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daa
ɗ
i zuwa wacce ta
zama mai cike da buri da alfahari. Da na
zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan
kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun
ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da
koma baya a wannan
ɓ
angaren
iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na
sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al'ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in
wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa
wa
ta mace ko wani yaro