Showing 24001 words to 27000 words out of 174924 words
kalli hajiyarsu da tunanin za ta yi mata fa
ɗ
a sai ya ga ma kallon shi take da expression
na mamaki a fuskanta.
"Mayya fa ka ce S
alim? Shi ne za ka tura ta
ɗ
akin autana ta fara da ita? Me ya hau kanka da za
ka kawo mana cutarwa gida after all fa
ɗ
i tashi da muka sha don mu ga mun inganta rayuwar
mu?"
Kasake yayi yana cigaba da kallon mahaifiyar tashi bai ta
ɓ
a tunanin zai fuskanci
wani matsala
daga Mommy ba, ya zaci ta san zafin
ɗ
a kuma
ɗ
an wani ma zai iya zama nata musamman idan
ta ji cewa Marainiya ce don ta fi kowa dan
ɗ
anar wahalar da maraici ke janyowa.
"Mommy na
ɗ
auka Afeefah Abar tausayi ce da muddin na ba ki labarinta za
ki kar
ɓ
eta hannu
bibbiyu, ki rungumeta tamkar su Samha wallahi mu ma Allah zai dube mu ya ba mu ladar kula
da ita"
"Dakata Saleem! Dakata min don Allah! Ka kawo yarinya kana ikirarin danginta sun guje ta
saboda Mayya ce da tun tana ciki take cin mai
ta ta ci har uwar da ta haife ta da ubanta ka kuma
yi expecting in kar
ɓ
eta? Ta cinye min ku kenan? Ko ni kake so ta cinye maka? To ba da ni ba
salim... Ba a gidan nan ba maza maza tun dare bai ba tarkatata ka mayar da ita inda ka
ɗ
auko
ta tun muna shaid
a juna je ka fitar min da yarinyar nan a gida ba za mu ta
ɓ
a shiryawa ba..."
Hankali tashe ya
ɗ
an kalli kofar
ɗ
akin Samha kar Afeefahn ta ji ya matso ya riƙe hannun
mommyn.
"Mommy wallahi ba gaskiya ba ne duk fa zargi ne da Ƙazafi irin na mutanen duniy
a, wallahi
Afeefah is innocent mommy ki tausayawa rayuwarta don Allah. Mu ma fa marayu ne ki saka ta
a sawun su Samha idan da
ɗ
aya daga cikinmu ne ake yiwa wannan kazafi za ki iya jura? Za
k...."
A hasale ta katse shi
"Na rantse da Allah zan tsinka ma
ka mari salim ka sake alaƙanta yarana da wanchan Abar, eh
ku marayu ne amma da ba ku ci naman kowa ba uban wa yayi muku Ƙazafi? Bari ka ji ba'a ta
ɓ
a
ya
ɗ
a jita-jitar da bashi da kamshin gaskiya ba. Kafin na hasala na ha
ɗ
a da kai ka je ka fitar min
da yar
inyar nan a gida..."
Samha da har lokacin take hawaye tace
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun ni dai mommy wallahi ba zan iya sake shiga
ɗ
aki na ba"
Sadiqa tace
"Ni dama daga ganinta na ji har ga Allah bata kwanta min ba, sai nuƙu-nuƙu take ashe babu
gaskiya a lamarin ta"
Sameera ta yi kwafa
"Nan ma ba ki ga idanunta bane, duk abin tso..."
"Kun yi min shiru ko sai na sassa
ɓ
a muku? Da ku nake magana ne? Ko na kira sunan dayanku
anan? Kun ga kun yi kama da waenda zan nemi izininku kafin aiwatar da
abin da yake daidai?
Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?"
Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ƙololuwar
ɓ
aci duk mommy ce ta ba su wannan ƙofa amma
ya zai yi?
Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don
saura kiris ya fara
yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce
"Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan
ina za ta je? Musulma ce fa 'yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al'umma
m
ommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan
hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting
ɗ
ina for life please mommy"
Ganin zai kai gwiwar shi ƙasa yana cigaba da roƙon ta ya sa ta riƙe hannunshi suka
koma
zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice
yana roƙonta, Salim a yaranta yana da haƙuri yana kuma da kawaici don da wuya ya roƙe ta
abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matuƙar bukata ko da kuwa buƙata
r ku
ɗ
i ne, yana
tausayinta ƙwarai gani yake har yanzu bata huta da
ɗ
awainiya ba alhali, gidan gadon su ma
'yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar
ɗ
awainiyar karatun
ƙ
annenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na r
ashin lafiya bai ta
ɓ
a gazawa ba tun da
ya riƙe ƙasa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta
kashe mata shi fa? Numfashi mai matuƙar nauyi ta sauƙe ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye
kurwan wanda ya taimaka musu ya ji
tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai
ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?
Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta
"Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharu
ɗɗ
a, sharrudan da zan gindaya
maka
wanda matuƙar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba"
A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya
wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya bu
ɗ
e bakinshi da yayi
masa
nauyi ya furta
"Allah ya isa mommy? Ni??"
Ta gya
ɗ
a kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata
tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai ta
ɓ
a tsallakewa umarnin ta ba.
"Sharu
ɗɗ
an su ne babu ruwanka da abin da y
a shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku
kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka
ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat!
Magana ta fatar baki t
sakanin ku in har ya wuce minti
ɗ
aya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga
cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na
ɗ
ore bane dole za ta bar
gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne"
Ya yi jimmm kanshi ƙasa
duk ya damu kan ya sauƙe numfashi
"Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki"
Yana kai nan ya miƙe ya bar musu parlorn Ranshi na ƙuna, da yana da mata babu abin da zai
hana shi riƙe Afeefah tamkar 'yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a ya
nzu ma bai fidda
tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.
Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta
amince da zaman yarinyar gidan?
"ku yi shiru ku bar ni da sh
i, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga
gidan ba sai wani ya kore ta ba."
Ta miƙe ta nufi
ɗ
akin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa
mata baya wane sarauniya da fadawarta.
Suka sameta zaune ind
a take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin
da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da
fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da
sa
fen a asibiti.
"Ya ma Sunanki?"
Mommyn ta tambaya tana sake ƙare mata kallo.
"Afeefah" ta amsa a hankali.
"Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya za
ɓ
i bijirewa umarni na
a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci?
Zan ja miki federal warning akan yarana don ni
karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan
kina cin ƙasa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa 'ya'ya na suka yi ko da ciwon kai ne
hmmmm"
Ta kara
hmm
ɗ
in da wani irin siga na razanarwa,
"ana magana ba za ki amsa ba?"
Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta
A
ɗ
an razane ta gya
ɗ
a kai.
"Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki
ɗ
auki farantin nan don daga yau a ciki za'a na baki abinci har
Alla
h ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma
almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye.
Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?"
Sameera tace
"Ka
i mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?"
"Eh na fahimta"
Ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi mana ni ki bar min
ɗ
aki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?"
Dole ta miƙe da sauri ta
ɗ
auki kayanta da plates
ɗ
in ta bi bayansu, ta kofan bay
a suka fita suka
miƙa har Boys quaters jin hayaniya da hira ha
ɗ
e da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake
tsorata, isan su varender
ɗ
in Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building
ɗ
in
ɗ
aya daga cikin
su ne ya leƙo ganinta ya sa ya koma da gudu ya
ƙira sauran suka fito su uku. Ba manya bane
chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da
guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me
hajiyar take nufi? A s
ama ta ji muryarta tana cewa
"ke! Ga
ɗ
akin ki nan"
Tq nuna mata wani single room dake kan varender
ɗ
in. Da gaske a waennan garadan za ta
ha
ɗ
a ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye
ɓ
alle mata a take
tana ji hajiyar na cewa
"Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a
ɗ
akin nan kar in ji kar in
gani"
"To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye"
Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.
"Sannu kyakyawa"
Bata tanka ba sai shige wa
ɗ
akin da aka kira
da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da
zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.
Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga
ɗ
aki kuma suka fara gulman
kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ƙarfin gaske d
uk razana suka yi sai kuma a
take suka wani irin zubewa ƙasan ganin Saleem riƙe da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red
babu wanda zai iya cewa ya ta
ɓ
a ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu
ya shiga ba da ƙarar tsoro suna tunanin
me suka yi?
Iliya ke ta maimaita
"Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka.."
Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake ha
ɗ
e fuskan nan tamau, ya samu
hannun kujera ya zauna tare da
ɗ
ora kaf
an shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya
ɗ
an sosa
goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya sauƙar yayi kooking ta ba da sauti tuni
suka maƙale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka fa
ɗ
a wuta sai salati suke.
Ya ce cikin dakakkiya
r murya
"Menene wannan a hannu na?"
Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin
ta tashi bata da hankali ana
ɓ
ata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa
"Abin kashe mutane"
"sunanta n
a tambaya!!"
Ya fa
ɗ
a a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa
"Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta"
"Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?"
Sai kai suke gya
ɗ
awa kaman kadangaru
"Bu
ɗ
e baki za kuyi ku ams
a ni malamai"
Tuni suka cika
ɗ
akin da
"Eh, tabbas! Haƙiƙa hakane!"
"To ku bu
ɗ
e kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon
da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili
ba
aaa..."
Ya miƙe tsaye ya isa inda suke ya
ɗ
od
ɗ
ora bindigar kan kowannen su yace da ƙarfi
"Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??"
Suna zare numfarfashin tsoro da ka
ɗ
uwa suke amsawa a tare
"Mun gane wallahi mun gane, ba za
mu kuskure ba ranka ya dade yallabai"
Ya
ɗ
an matsa baya.
"Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani
ɓ
angare ina da abin
ɗ
aukar video a
ɓ
oye waninku ya gwada sa
ɓ
a doka ta ya gani..."
Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu
bindigar a Goshi ai da gudu iliya da
mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo...! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka
baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna.
Ya
ɗ
an jima tsaye yana kallon kofan
ɗ
akin nata bayan fitanshi kan ya wuce
, yana tsaye a
balcony
ɗ
in shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matuƙar damun shi, ta ya
mommy za ta ha
ɗ
a mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya
mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta b
a zai iya
yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan.
Ringing na ƙarshe ya
ɗ
aga da sallama
"Ya aka yi ne man?"
"I need your advice, ni ne na kawo lu'u lu'u mai tsananin daraja da ƙima sai na rasa inda zan
killace hakan ya sa dole na ajiye a
inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace
da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun
ɓ
arayi da basu kai
ko da shakar numfashi
ɗ
aya ba suna zagaye wannan lu'u lu'u da kallon da ban gamsu ba, idan
ba zan iy
a tafiya da wannan lu'u lu'u ba kuma dole zan tafi wani mataki kake ga ya kamata in
ɗ
auka?"
Ryan ya
ɗ
an yi shiru na seconds kan ya ce cikin dakakkiyar voice
ɗ
in shi
"Dukkan yanki ba'a rasa
ɓ
arayi kuma ko wani
ɓ
arawo yana da uban gida, idan har kai ne
uban
gidan wannan
ɓ
arayi kana da dama da ikon garga
ɗ
i mai zafi irin na asalin maza ba mata ba, ina
mai tabbatar maka daga zarar sun tsorata da gargadin ka ko kallon hanyar da wannan tagulla
take ba za su sake ba"
Lumshe ido yayi
"Na gode"
Ryan ya k
ashe wayanshi.
Ya
ɗ
an sake nazari kan ya saki murmushi ya juya ya je ya
ɗ
auko bindigar ya wuce sashen.
Dariya ka
ɗ
an yayi tuna yadda suke ta zazzaro idanu suka jike jagwaf da gumin tsoro...
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True lif
e story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Don Allah ku yi haƙuri da wannan yau
ɗ
in nan ban zauna ba wallahi*
*012*
Ta
ɓ
angaren Afeefah anan bakin ƙofa ta ci kukanta har bacci ya su
re ta ba tare da ta sani ba,
mummunar mafarki da tayi da Aunty zee ne ya sakata farkawa a razane, fitsari ne kaman zai
zube mata hakan ya sa tayi single kofa guda
ɗ
aya da ta gani a
ɗ
akin sai ta samu madaidaicin
bayi ne, bayan ta gama abinda take ta fito
ne ta fara bin
ɗ
akin da kallon tsanaki don wutar a
kunne tarrr kaman rana.
Matsakaicin
ɗ
aki ne a lailaye yake da farin tiles, fanka da bulbs duk suna aiki daga chan dungu
'yar ƙaramar katifa ce da babu ko shimfidi a kai, sai agogon bango da
ɗ
akin ke
dashi, time ta
kalla ƙarfe biyu na dare har ma da mintuna ashirin da uku, juyawa tayi ta koma bayin ta yo
alwala ta zo ta sake shimfida dankwalinta ta saka hijabinta ta tada sallah, raka'a shidda tayi a
sujadar ƙarshe ne ta saki kukan dake dukanta a kir
ji tana jerowa Allah kirari bayan ta jera
sunayen shi masu daraja casa'in da tara ta bi da salati annabi kan ta fara jero matsalolin ta da
neman sassauci ta yiwa iyayenta da sauran 'yan uwanta da ta rasa Adu'a ta roki Allah ya kawo
mata sauƙin rayuwa ya
warware mata matsalolin ta ya kuma cigaba da bata zuciyar karbar
ƙ
addarar ta a duk yadda ya zo mata. Kusan ƙarfe uku da rabi ta sake kwanciya a