Showing 42001 words to 45000 words out of 174924 words
kin chanza kaman ba ke ba, kullum kina
cikin
damuwa 'yar fa
ɗ
an nan da kike biye ni muyi tayi duk yanzu bakya yi walwala ta kau daga
fuskanki har mommy
ɗ
azu maganan take yi, in baki fa
ɗ
a min ba wa za ki fa
ɗ
awa Sis?"
Kuka kawai ta sakarwa samhar, sai da tayi mai isarta kan ta
ɗ
ago ta kalleta
"Samha
ko na fa
ɗ
a ma ba ku da maganin damuwata"
"Ko Adu'a muka taya ki ai mun taimakeki bare kila akwai shawarar da zan iya baki, idan ba kya
son kowa ya sani ne ma i promise ba zan fa
ɗ
awa kowa ba".
"Samha na kamu da Soyayyar Dr. Sulaiman"
Tsayuwa tayi ta
na tunanin waye Drn Sulaiman sai da yayi clicking a brain
ɗ
inta kan ta yi saurin
cewa
"Wannan likitan dake zuwa duba Mayyar chan?"
Kai ta gya
ɗ
a a sanyaye
"Samha kaman soyayya suke da ita"
"Amma Sulaiman
ɗ
in bai santa bane ba ko? Ina nufin bai san wace
ce ita ba rufe shi take
kokarin yi ta nuna mishi ita 'yar gidan nan ce?"
Samhar ta fada har yanzu tana mamaki, Afeefah ta kai Sulaiman ya ce yana so?
"Da alama kam"
"Toh me kika yanke?"
Ta
ɗ
ago jajayen idanunta tace
"Dole su rabu idan na cigaba da ka
llonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata
ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba
shi zai aurar da kanshi ba ko?"
Kai Samha ke gya
ɗ
a wa
"Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma
ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya
matsayin ta"
A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma
tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta leƙa waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko
abin
ci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake,
bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ƙira su suka nufi
ɗ
akin Afeefar...
***
Tana zaune kanta ha
ɗ
e da ƙafafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an
banko ƙofan
ɗ
akin, suka tsaya suna ƙarewa
ɗ
akin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta
"Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba"
Kayakinta Samha take dagawa tana cewa
"Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo
ya watsa miki ƙasa a idanu duk wa zai saya mata su
bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ƙwalamar dake
ɗ
akin nan? Mommy anya ba
asirce shi tayi ba?"
Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba,
Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta
cike da kwallah.
"Shikenan wallahi tamba
ɗ
e mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace
ku
ɗ
i haka ba tare da ta bashi komai ba?"
Sadiqa c
e tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar
Sulaiman ta bata.
Sameera ta katse ta
"Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tamba
ɗ
e wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan
nan kalar text messages dake ciki na tsantsa
r soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa
ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi"
A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta
kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar bur
in su na kasancewa karkashin inuwa daya.
"Ya isa haka sadiqa"
Mommy ta fa
ɗ
a jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda
kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi
a
mfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma
duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta
matsuguninsu?
"Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa
ɗ
an yau ne shi? A kan
mace? Macen ma Mayya marar
galihu da tushe ha
ɗ
e da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya
ɗ
auke shi? Ni saleem...?"
Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son
masifar hawayenta ya ta
ɓ
a shi ko ta wani
ɓ
anga
re da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan
gwiwowinta
"Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron
fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala'i
n
e a tare da shi..."
Tauuuu sadiqa ta
ɗ
auke ta da mari
"Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya sa
ɓ
a mata? Kin san abin da
ɓ
acin rai daga
gareshi zai iya ja mata?"
Samha da ta janyo jakar da saleem
ɗ
in ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na c
iki tana
cewa
"Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da
ɗ
an uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya
kawo mata a
ɓ
oye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu... Farraku take shirin yi mana
daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan"
"ƙira min sa
leem sadiqa"
Da wayan Afeefar ta ƙira shi, ringing
ɗ
aya ya
ɗ
aga a hankali ya kira sunanta sai ta duƙar da kai
hawaye na gangaro mata jin muryarshi.
"Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka"
Runtse ido yayi da ƙarfi gabanshi na fa
ɗ
uwa, bai shirya
ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba
ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya.
Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sauƙa ya nufi
sashen Boys quaters
ɗ
in yana Adu'ar Allah ya sa kar mom
my tayi mata wani abu, sai kace-
nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara
tana kuka.
Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya duƙa kawai ba tare da ya furta kalma ko guda
ba.
"Saleem"
Ta ƙira sunan
shi ya amsa ba tare da ya kalleta ba
"Ɗago saleem ka kalleni, ka
ɗ
ago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani saƙo da na gani
wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?"
Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji ka
man yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin
furucin
ɓ
atanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi.
"Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y...."
Wani irin mari ta
ɗ
auke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi
don shi yaro
ne mai tsananin biyayya a gareta.
"Maimaita!"
Ta daka mishi tsawa ya sake cewa
"Mommy ina ƙaunarta, kuma aurenta nake buri"
Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi ka
ɗ
ai ba har su sadiqa sun tsorata basu ta
ɓ
a
tunanin za ta iya kai ha
nnunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye
take yi ta sake cewa saleem ya maimaita
"Mommy... Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani
hukunci za'a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy ki
la sai kin cire zuciyar gaba
ɗ
aya daga
kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ƙauna zuwa gareta..."
Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas
abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da S
aleem tunda har zai iya mayarwa mommy
magana sau uku, Mommy ta sake
ɗ
aga hannu zata mareshi sadiqa ta riƙe hannun tana hawaye
"Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin
bar gidan nan ba za ki tarwatsa man
a gida ba"
Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ƙauna da tausayin saleem ne suka sake
mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan
suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta
na aure har mutuwa.
"Saleem!"
Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka
sauya ainun ya
ɗ
ago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da
idanun nashi.
"Saleem!!"
Y
a amsa a hankali
"Saleem!! Sau nawa na kira ka?"
A hankali yace
"Uku"
"Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka
ko? Ka san ni wacece ko?"
"Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake d
ashi a wurina duk fa
ɗ
in
duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da
wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan
kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wall
ahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba
don so bai san rarrashi ba..."
"Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa"
Mommy ta fa
ɗ
a tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya
ɗ
ago
ya kalli mommyn zai yi magana ta
daka mishi tsawa a kan ya mata shiru
"Aure kake so zan
ɗ
aura maka aure da yar
ɗ
an uwana Sabreena da take sonka tun bata san
kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har
Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban
yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka
sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka ha
ɗ
u ban yafe ba ka mata ko da sannu ne... In
har ni na haif...haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya"
A razane yake kallonta, ta share fus
kanta ta dubi Samha
"Je
ɗ
akina ki
ɗ
aukomin akwatin da ya fi kowanne girma"
Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin
irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gaba
ɗ
aya jijiyoyin
kanshi sun
mimmiƙe girgiza kai take yi
"Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa... Ki barta don Allah ko bai
aureta ba ta z..."
Sadiqa ce ta kai mata duka
"Kema asirce ki tayi don ƙaniyarki? Wallahi ta gama zaman gidan nan"
A lo
kacin Samha ta shigo da wani cream trolley.
Mommy ta kar
ɓ
a ta jefa mata
"Na tsani ganin ko inuwar ta ne, ku gaya mata ta tattari duk taeukucenta ba na son ganin ko
ƙ
yallenta a gidan nan kar ma ta dawo cikin dare ta kama wani biya... Har Abada ko magan
a ta
yi wa dana sai na tabbatar ta kare rayuwarta a gidan yari"
Ko gwada roƙon su bata yi ba don ta san ko sama zai ha
ɗ
u da kasa a yanzu mommy ba zata
amince da hakurin ta ba, kuka mai sauti take yi jikin saleem ne ya fara rawa, ba zai cigaba da
sa
uraron kukanta ba ba zai iya ganin tafiyar ta ba, zuciyarshi tamkar zai fashe saboda tsoro da
fargaba in ta fita ina za ta je? Wa ta sani a duk fa
ɗ
in Kaduna? A hankali ya miƙe jiri na kwasar
shi a dafe da gini ya cigaba da tafiya har ya bar
ɗ
akin zuwa lo
kacin da gaske yake hawaye,
hukuncin Mommy tamkar zare mishi farin ciki tayi a wannan rayuwa, tamkar ta kulle shi ne a
magarƙamar da ya fi kowani magarƙama duhu da azaba.
Afeefah ta ha
ɗ
a komai nata, wayar da saleem ya saya mata kawai ne ke riƙe hannun
mommy
kan suka tasa ta gaba har wajen gate, ta jima tsugune a wurin tana kuka kan ta miƙe ta share
fuskarta ta ja akwatin ta fara tafiya.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel...! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abin da take ta nanatawa kenan tana share ha
waye ta yi tafiyan da bata san adadi ba har ta fito
wani babban hanya dake dauke da ababen hawa fiye da cikin unguwar da ta bari, nan ma
miƙawa kawai tayi ta cigaba da tafiya ko biyar babu a hannunta, ta fi awa biyu tana tafiya janye
da trolley
ɗ
in loka
ci lokaci ta kan share hawaye masu zafi dake zuba mata, a daidai wani wurin
ba da hannu ta tsaya ta
ɗ
aga kai ta kalli garin, mutane ne ke ta hada hada kowa harkar
gabanshi yake yi, daidai wutan ya nuna ja motoci suka tsatsaya wani daga gaba yayi kokarin
kin bin doka sai hatsari ya faru a wurin tuni go slow ya wani irin ha
ɗ
uwa.
Tana tsaye har lokacin rike da akwatinta kamkam sam bata san me za ta yanke ba, bata san ya
za tayi ba kaman an ce ta
ɗ
aga kai sai idanunta da suka zama wasu iri tsabar kuka su
ka shige
cikin nashi daidai yana sauƙe glass, kallon seconds biyar suka yi wa juna ya
ɗ
auke kanshi ya
mayar gaba yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta roƙe shi ya taimaka
mata ko da ya ha
ɗ
a ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaim
an ai bai san wacece ita ba idan su
ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake fa
ɗ
a hawaye na silalo mata daidai ya
sake kallonta idanunshi suka sauƙa kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar
wurin.
Juyawa tayi ta ci
gaba da jan trolley
ɗ
in dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin
saleem ma a duniyarta shi ka
ɗ
ai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani
rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta fa
ɗ
i A
feefar tayi
hanzarin sake akwatin ta riƙe ta
"Subhallah! Ki yi haƙuri"
Ta fa
ɗ
a cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai
komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta
"Lafiya Aunty? Ko baki da laf
iya ne?"
Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.
Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a
nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani
tunani ne ya fa
ɗ
o wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa
"Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan ta
ɓ
a jakanki ba"
Bu
ɗ
ewa tayi ta samu
ɗ
ari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki
itama ta shiga mai machine
ɗ
in ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi
"Asibitin dake kusa don Allah"
"Sannu, Sannu"
Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da
lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a h
aka suka isa wani private hospital ya shiga da su har
ciki aka dauƙeta emergency zuwa lokacin bata numfashi.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Are
wabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*018*
Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac
ɗ
in shi ya ƙare, hakan ya
ɓ
ata mishi rai don
baya son bu
ɗ
e glass na mota yana tuƙi, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren
sha biyu ya bar
asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai
ɗ
auki hanyar cikin unguwar su
na Barnawa hold up ya riƙe shi, a dole ya sauƙe glass saboda zafin da yake ji.
Karon farko da idanunshi suka sauƙa a kanta bai gane ta ba sai da ya
ɗ
an yi focusing na
seco
nds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya ta
ɓ
a ceta from poison, wannan yarinya da
saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da
ya mayar da idanunshi wurin suka sauƙa a kan trolley dake gabanta, idanunt
a ya sake mayar
da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi
gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai
ɗ
aga
ba shi da ya tsani kira sau biyu