Showing 81001 words to 84000 words out of 174924 words

Chapter 28 - Haihuwa-Da-Hanji-Complete

wani

irin sanyi ta fara jin hawaye na zuba mata dukda ta amince har ranta da auren sai dai tana jin

wani irin ciwo a ƙasan ranta na auren wanda baya sonta bai ma dauketa mace ba, kila ma ko

sunanta bai

sani ba don bata ta

ɓ

a ji ya ambata ba, Abeeha ce ta tsuguna tana tsokanarta har ta

fara kukan auren kenan? Da kyar tayi shiru.

Bayan isha Mammi ta aiko aka ƙirata bayani ta mata akan kwanakin da aka sa auren, bata ce

komai ba Mammi ta ce zata iya tafi

ya a Washegarin aka fara zuwa yi mata gyaran jiki don

mammi sossai ta tashi tsaye Dukda ciwo dake nukurkusarta amma auren

ɗ

an farinta babu

batun zama, shi dai kam ma a satin aka tura shi wani assignment Zamfara ya wuce kuma zai yi

akallah sati uku.

*

***

Ta

ɓ

angaren su mommy fa rayuwar ya juye musu, a hankali suka fara fahimtar abin da rayuwa

ya kunsa barin ma da ta mayar da sunna Tv da kuma Africa tv3 abin sauraro, suna takure sai

dai basu rasa ci da sha ba kuma duka yaran suna zuwa makarantar su

sai dai hankalinsu ba'a

kwance yake ba, ga ayyukan su da suka manta yadda ake su wanki, guga, shara wanke wanke

da girki duk su suke yi idan basa nan suna school haka mommyn ce ke yi dole, ko wani dare

karfe uku baccinta ya ƙare don ciwo ne sossai a ra

nta na abin da aka yi wa saleem, tana roƙon

mishi waraka kuma tana roƙon Allah kar ya kama shi da laifi don ba laifinshi bane nata ne.

Yau da ta ji tana matuƙar kewanshi ta tura Sameera da Samha gidan akan su duba shi, ko da

suka je kaman baƙi haka su

ka tsaya jikin kofan suna knocking kusan mintuna biyar tukuna Gaje

ta zo ta bu

ɗ

e ganinsu ya sa tayi murmushi

"Ah ashe su Sameera ne sannunku da zuwa bismillah"

Sai suka ji wani iri a gidansu ne ake musu iso?

Shiga suka yi suka samu Yaya zaune cikin k

ujera relaxed irin gidan shin nan, zama suka yi

suka gaishe shi ya amsa kan Samha tace

"Wurin Yaya ne muka zo yana nan?"

"Eh yana nan bari na dubo Sabrina ta turo muku shi. Talatuwa..! Talatuwa...!! Kawo musu ruwa"

Su dai banda ikon Allah babu abinda

suke gani wai in fa

ɗ

a ya fi karfinka sai ka mayar da shi

wasa ba kuma baki sai kunne murmushin dole kawai suke yi har Talatuwa ta fito, da tausayi

take kallon su amma ya zata yi dole ta cigaba da aiki da mutanen da suke gidan in tana bukatar

abin rufa

wa kai asiri, ruwan ta kawo musu ta gaishe su suka amsa a sanyaye.

Sun fi mintuna talatin kan ya fito ya zauna yana kallon su itama Sabrina ta zauna gefenshi don

su Gajen duk sun tashi sun yi wuraren da nan ne

ɗ

akunan Mommy da nasu suke a baya,

gaishe

shi suka yi ya amsa

"Lafiya?"

Ya tambaya sai Samha ta fara zubar da hawaye, wai yaya saleem ne ya zama musu baƙo?

Yaya saleem dai da yake matuƙar kaunarsu ne wannan zaune?

"Rashin kunyar taku ne kuka zo har nan ku cigaba ko? Duk wanda kuka dinga yi mat

a a baya

bai ishe ku ba?"

Shiru suka yi don basu san me suka yi ba wani irin tsawa ya daka musu

"Ba Za ku gaishe ta ba??"

A

ɗ

an razane suka shiga gaisheta tayi murmushi tana amsawa har da tambayar su mommy na

lafiya? Suka amsa da lafiya lau.

"Me ku

ke so? Ba na ce zan neme ku ba?"

Ya fa

ɗ

a har yanzu babu walwala a fuskarshi

"Dama mommy ce tace mu zo mu duba kana lafiya?"

"Jinjiri ne ni? Ko idan banda lafiya ku nake jira ku kaini asibiti?"

Shiru suka yi sai Sabrina ce tace

"My S ka daina fushi a

i ba laifi bane don sun ji lafiyarka, ku je ku ce mata yana lafiya yana miƙa

saƙon gaisuwa kuma bai manta da ita ba zai zo idan ya shirya shikenan?"

Sameera ta miƙe ta kama hannun Samha

"Za ta ji, sai anjima"

Ta jata suka fice sai kuka samhar ke yi h

ar suka shiga napep hannun Sameera ta rike

"Sameera har da laifina a mayar da yaya saleem haka, duk ni ce da ban kiraku

ɗ

akin Afeefah

ba da bamu san suna soyayya har mu raba su mommy ta aura mishi wannan fitsararriyar mai

ido a tsakar ka ba"

"Samha k

i daina wannan kukan, komai ya wuce dukkanmu muna da laifi... Ki yi shiru bana so

mu je wurin Mommy kina cigaba da wannan kukan kar hankalinta ya sake tashi, Yaya Adu'a

yake bukata ba kuka ba"

Dukda itama hawaye take sharewa lallai ta yarda duk soyayyar

Uwa ga

ɗ

a tana iya zama

mummunar kaddararshi ko da sanin ta ko akasin hakan, mommy ta zamewa salim mummunar

kaddara sai dai Allah ya bashi ikon hayewa ya bashi ƙwarin zuciyar

ɗ

auka kar ya halaka a haka.

****

A sati uku da suka biyo baya idan ka ga

Afeefah za ka rantse da Allah ba itan ba ce, Caramel

skin

ɗ

inta wani irin daukar ido da sheki yake, tayi wani irin kyau har ta gaji, ba gyaran jiki ka

ɗ

ai

ake yi mata ba sessions ne daban daban a satukan ga karatu, ana koya mata dressing irin na

wayyayy

un matan aure, ana koya mata girke girke na zamani da bata kware ba ana kuma koyar

da ita rayuwar auren da ma auren karan kanshi ha

ɗ

e da dabarun zama da miji, ta

ɗ

an rame

saboda stress amma ta wani irin cikowa tayi kyau masha Allah, ba kananun kudi Mammi

ke

bararwa ba Dukda ba buki za su yi ba sam.

Ko da su Umman Sulaiman suka ji labari su ma ba'a bar su a baya ba, Baaba jummai ta kan zo

ta yini bata shawarari kuma tsaff take

ɗ

auka wasu dai sai dai tayi murmushi don ta san ba dai

Rayyan za ta yiwa b

a don wani abin bata tunanin har abada ma zata yi amfani da shawarar,

mixed emotions take ji akan auren.

Wai ita ce Afeefah za ta yi aure? Ita da ta fara sallamar da zancen aure a rayuwarta saboda

mummunar Ta

ɓ

onta, ko da a da ta yi tunanin auren tayi tu

nanin aure zai zo mata a kaskance

cikin rashin galihu da gata, auren da zata iya zuwa ta cigaba da shan wahala kaman yadda ta

faro a rayuwarta sai gashi ta samu gatan da bata ta

ɓ

a tunani ba, gatan da ko iyayenta suna

raye karshen abin da za su yi mata k

enan, ta kan raba dare tana kuka tana miƙa godiyar ta ga

Allah tana kuma roƙon shi da kar ya nuna mata ranar da za tayiwa waennan bayin Allahn

butulci.

Yau Asabar da wuri ta tashi don sun yi class da mai koya mata girki, gasashen kifi suka yi

talapia

ya ji onion sauce sai irish da aka gasa aka yi ganishing a gefen kifin, a gefe wani hot

beef stir fry jollof Rice ne, a dining suka shirya don ita da Abeeha suna ci Mammi ce dai ba zata

ci ba, bayan sun gama taje tayi wanka yadda aka nuna mata sabon met

hod na yi har da

dauraye jiki da ruwan turare ta fito tana zuba uban kamshi, gaban wardrobe ta tsaya tana

tunanin kayan da zata saka, a hankali ta zaro wani dogon riga mai yanayi da silk material ta

zura yayi mata kyau sossai don A line ne rigar bai k

ai ƙasa sosai ba kuma ƙasan ba a zagaye

ba ana iya ganin idanun sawunta, hula mai butterfly a gaban Goshi ta saka ta

ɗ

an tsaya gaban

madubi sai taga kaman kayan ya mata yawa bata fita classy ba, komawa tayi ta nemi belt ta

ɗ

aura a daidai cikinta sai ya

bata wani kyaun na musamman murmushi ta saki ta

ɗ

auki wayanta

ta fito, daidai Abeeha ma ta fito daga nata

ɗ

akin.

"Ku ne kyau amare"

Ta tsokani Afeefar da kullum aikinta kenan, murmushi Afeefah tayi don tun tana rigima har ta

gaji ta shiga kyale Abeeh

ar.

"Wlh Afeefah kina da kyau, kaman fa wata model haka kika fita, duk kayan da zaki sa yanzu kin

san irin adon da zaki musu su fita daban"

Suna shiga cikin parlorn suke zancen, Afeefah na cewa

"Addah Abee ai ina ga zan saka fashion design cikin ma

farkaina don gaskiya abin na burgeni

bana rabo da kallon fashion show"

"Toh ke madam komai ma kina so? Ke fa kika ce business woman kike son zama na inna naha

don kina son yin ku

ɗ

i"

Ta fa

ɗ

a da dariya.

"Ai duk mace tana bukatar waennan a gani na fa

, kin ga girki ya zama favorite thing

ɗ

ina

saboda wajibi ne a gidan aure, dressing ma wajibi ne in kana so ka burge masoyinka duk ba

laifi bane business kuma shine asalin abin da nake so, ina so nayi ku

ɗ

i na samu na kashewa

marayu da bayin Allah, ina so

nayi kudi na tallafi rayuwar yaran da suke wahala a duk sadda

suka rasa iyaye, gidauniyoyi nake mafarkin bu

ɗ

ewa na wayar da kan mata akan mecece

rayuwa da kuma yakar jahilci a yankunanmu"

Abeeha na dariya take cewa

"Su burge masoyi, a'a ka ga Masoyi

yar Ya Ra..."

Katse wa maganar yayi suka tsaya chak idanunsu a kan Rayyan dake zaune dining yana

karyawa hankali kwance, kuma tsaf ya ji su don daskare wa da suka yi ya sa ya

ɗ

ago firgitattun

idanunshi ya zuba musu yana aika musu da kallo mai kama da ga

rga

ɗ

i....



🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*32*

Idanun ya

ɗ

an tsayar a kan

Abeeha kan yayi baya da su kaman zai

ɗ

auke sai ya sauƙe a kanta

ya

ɗ

an tsayar kan ya janye ya mayar kan abincin shi ya cigaba da ci in his majestic way.

Wani irin bugawa zuciyarta ke yi fiye da misali, ko da wasa bata ji Mammi na maganar zuwanshi

ba d

aga ita har Abeeha kasa gaba suka yi kuma sun kasa baya, ita dai Afeefah tsabar bugun

zuciya har idanunta sun tara kwallah kiris take jira ta sako su, a tare suka juya za su bar wurin

suka ji muryarshi ya ce

"Ku zo nan!"

Wani irin tsalle zuciyar da

ke bugawa yayi, ita dai bata san Meyasa bata iya controlling

heartbreat

ɗ

inta ba in dai akan magananshi ko kallonshi ne ta ajiye akan tsananin tsoron shi da

take ji ne ya janyo hakan, Dukda bai ta

ɓ

a dukan ta ba amma ya sha yi mata fa

ɗ

a, fa

ɗ

an ma

babu ka

man na ranar da ta fara

ɗ

ora idanunta a kanshi a rayuwarta.

Kaman waenda kwai ya fashe musu suka dawo, Abeeha da ta san halinshi ba lallai ma ya kara

magana ba ta ja kujera ta nunawa Afeefah kujeran da idanu, kaman ba zata zauna ba sai kuma

ta zauna A

beehar ma ta ja wani ta zauna ta

ɗ

auki plate a hankali ta yi serving

ɗ

insu Rice

ɗ

in

daban daban Allah ma ya sa shinkafar da tsokar nama suka yi da babu protein za su ci don shi

zallar kifi da irish

ɗ

in yake ci.

Abeeha ta fara ci a hankali kan ta bu

ɗ

e

baki tace

"Sannu da dawowa Yaya"

Kai ya

ɗ

an gya

ɗ

a har lokacin bai

ɗ

ago ba, ita dai Afeefah ko spoon

ɗ

in bata

ɗ

auka ba gashi

tana tsoron magana, kuma kar bata yi ba ya zama laifi da kyar ta ce a rarrabe

"S..sannu da d..dawowa"

Yadda tayi maganan ya

sa ya

ɗ

ago slowly ya kalleta kan ya mayar da kanshi yana kai fork na

karshe baki bayan ya ha

ɗ

iye ya

ɗ

auki ruwa daga fari kal

ɗ

in glass cup dake gefenshi ya sha

kan ya miƙe ya bar wurin, a tare suka sauke ajiyar zuciya Afeefah tace

"Adda Abee Meyasa d

a ya dawo da mu kika sa muka zauna?"

Tayi murmushi tana cin shinkafar tace

"Har yanzu baki san Yaya Rayyan ba, ai ya tsani saboda shi ka ƙi yin abinda ke gaban ka

yanzu da za mu tafi bayan ya kiramu ya kuma san me za mu yi anan muddin muka tafi haka zai

titseyemu ya tsare gida ya ce sai mun fa

ɗ

a mishi dodo ne shi da muke avoiding

ɗ

inshi..."

"Shi dai komai kayi baka burgeshi?"

"Aikam bana tunanin akwai abinda yake burgeshi muddin ba abinda ya shafi Mammi bane"

Ajiye hirar shi suka fi suka cigaba da

cin abinci don hanyar lafiya a bita da shekara dazu sun

tsira gaba basu san me zai faru ba.

Bayan sun gama wurin Mammi suka yi suka samu ma tana waya ne da wata cousin

ɗ

inta akan

boxes da ake ha

ɗ

a mata na auren, ita dai Afeefah a kunyace ta zauna don

yanzu sai take jin

kunyar Mammin na rufeta, bayan Mammin ta gama waya ta dube ta

"Afeefah yaushe ne kuke gama exams ne? Bana so kina yawo cikin rana ana wannan gyaran

jikin"

"Mammi wednesday za mu ƙare"

Ta mayar mata da amsa.

"Da sauƙi, saturda

y ne

ɗ

aurin auren Abeeha ya zancen telan?"

Sai da gaban Afeefah ya fa

ɗ

i ita ta kasa sabo da zancen auren sam, ji take kaman ana

daddaureta ne in aka yi maganar sai ta ga kaman ba gaske ba ita ce zata yi aure, auren ma

Rayyan za ta aura? Ya subhallah w

ani chill take ji yana running over her spine.

"Mammi kin san telan Jannah ne zan ƙirata na ji ko ya gama ha

ɗ

awa ko ni sai in je in kar

ɓ

o"

Hira suka cigaba da yi akan bikin da za'a yi shi ne a yini guda,

ɗ

aurin aure, yini, walima da miƙa

amarya

ɗ

aki

in ji mutanen garinmu suka ce Jollof, ba ana yinshi bane saboda talauci ko wani

abin, ana yin hakan ne saboda sauƙaka zirga-zirga expecially a irin situation na Mammi da bata

bukatar stress ko kadan.

Ranar Juma'a ana yi mata lalle sai ga su Fa'iza da

fauziyya har da Ummusalma matar Sulaiman

da ta sake da ita sossai a yanzu, ga Abeeha da Jannah sai suka zama kaman bridemaids suka

cike

ɗ

akin da hirarraki ana yi ana dariya, Mammi kuwa sai sawa take ana turo musu abubuwan

ta

ɓ

awa sossai hakan yayiwa Afe

efah daa

ɗ

i sai take jin nishadi a ranta na taruwansu ko ba

komai Allah ya ha

ɗ

a ta da tarin mutanen kirki, wani irin kyau lallen nata yayi baƙi da ja ya kar

ɓ

i

hannu da kafafunta duk suma 'yan matan sun yi. Mammi ma tayi ja a yatsun hannu.

Sai dare suka

tafi har Jannah akan sai gobe da sassafe za su dawo.

Rana bata ƙarya sai dai uwar

ɗ

iya ta ji kunya, yau aka wayi garin Asabar kuma a yau ne ake

shirin ƙulla wani babban al'amari mai tarin nauyi tsakanin Afeefah da Rayyan, da misalin karfe

takwas ya s

higo

ɗ

akin Mammin don ta kalli kayan da ita ta bashi ya saka a ranar don rana ce ta

musamman a gareta da ma shi baki

ɗ

aya.

Ɗ

an uban sun Men lace ne fari kal mai shegen tsada ƴar ciki da babban riga ya wani zauna

mishi sak kaman don shi aka halicci yad

in, hula da takalminshi bakake ne haka agogo tsadadde

dake

ɗ

aure tsintsiyar hannunshi zuwa azurfa mai baƙin dutse da ke ƴar yatsar shi, fasalta irin

fita a angon da yayi ma

ɓ

ata lokaci ne sai kamshi kam kaman an yi barin turare, fuskar Mammi

ya zubawa i

do kawai don bai ta

ɓ

a ganinta cikin nishadin da ya ganta a ranar ba sai ya ji wani

abu mai sanyi na sauƙa cikin zuciyarshi, matsowa tayi ta kama hannunshi tana murmushi tace

"Za ka tafi a saurayi ka dawo matsayin magidanci Saraki, ba zan ce komai ba il

lah Allah ubangiji

ya tsare muku hanya daga zuwanku har dawowanku"

Yayi murmushi ya juya zai fita tace

"Saraki...!"

Ya waigo ta

ɗ

auko turarenta ta sake fesa mishi ya fita ranshi fess Dukda wani abu da yake ta ji

na tsungulinshi akan auren.

Ga dum

bin mamakin shi yana fita ya tarar da motoci sun fi sha biyar dauke da tarin ma'aikatan

asibiti da ma 'yan uwanshi sojoji, a hankali ya juya ya kalli Sulaiman da ke mishi murmushi sai

yaji wani abu na mishi yawo a jiki, bai taba zaton za'a mishi irin wan

nan karan ba duba da

gaisuwa ce kawai ke hada shi da kowa, wani iri yake ji a sadda ya shiga gaban motan Sulaiman

suka fara barin unguwar babu saleem, ya nemi saleem a waya har ya gaji baya samunshi ko da

ya dawo gidan ya je mai gadi ya tambaya ya tabba

tar mishi sun yi tafiya da madam, ya tambayi

su mommy yace basa nan suma. Ko jiya sai da ya koma amma bai same shi ba akan basu

dawo ba bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login