Showing 120001 words to 123000 words out of 174924 words
/>
ɗ
o jikar Modibbo...
Girman
ɗ
a gado, Ɗan sarkin da ya san Allah, Ɗan sarkin da yayi haƙuri Ɗan jarumi gadon
jarumta Ruwan sanyi mai dafa ganda... Murucin kan dutse b
aka fito ba sai da ka shirya Gobara
daga kogi magani naka Allah, Damisa ba'ai maka kallon banza, sarauta dole in babu ku gari ya
watseee.."
Sossai ya sake kamewa wannan jinin na sake bayyana kanshi da kanshi, takawa yake kaman
ba zai tafi ba cikin sa
rauta har ya isa ga motar sauran sojojin da suke jiran shi da kallon
mamakin al'amarinshi musamman waenda suka san shi su ke Binshi bai cewa kowa komai ba
daga hadiman har sojojin ya shiga ya zauna suka fice daga fadar.
Kai tsaye mai martaba sashen Fu
lani Fa
ɗ
imatu ya nufa dayawa suna mamaki don baya zuwa
sassan matan sai dai su suje amma sun mishi uzuri kasancewar sun san iyaye ne da suke cikin
murnar bayyanuwar
ɗ
an su namiji tilo, wasu daga cikin gulmammu har an fara tambaye
tambayen Meyasa bai je
ga mahaifiyarshi kuma ya bar masarautar? Wasu na ganin barin shi da
Laami
ɗ
o yayi ya tafi ganganci ne.
Tana zaune har lokacin kuka take ta fara jin sanarwan zuwan mai martaba sashen ta, da sauri
ta miƙe tsaye daidai yana shigowa ya tsaya ya zuba mata i
danu yana kallonta chan ya ce
"Fa
ɗ
imatu Me kika aikata?"
Kanta ta mayar ƙasa tana sake sakin kuka cike da tarin nadama da kunyar mai martaba.
"Ashe kukan nan da kike shekara da shekaru ba na rashin
ɗ
a bane sai na yunkurin lalata
rayuwarshi? Me na mik
i da kika za
ɓ
i azabtar da ni da hannayenki Fa
ɗ
imatu? Me na miki da kika
za
ɓ
i gani na cikin ciwo da azabar rashin
ɗ
a tsawon shekaru ashirin da shidda? Me kika mishi da
ko magananki baya ƙaunar ya ji anyi? Kin san zuciyar bafulatanin da aka hasala?? Kin
san yara
nawa ne da zuciya ya dibe su suka tafi tafiya na har Abada sun ki waiwayan baya? Ba sai na
fa
ɗ
a miki ba kin san wanene Bafulatanin mutum... Amma ina so ki san abu
ɗ
aya na gode Allah
da ya amsa min adu'ar dawo min da Sameer ba zan ta
ɓ
a mishi dol
e ya kalleki ba idan baya
so..alhakin mu da kika dauka kuma wannan tsakanin ki da rabbissamawati"
Sossai take kuka tana girgiza kai, mai martaba masoyinta ne in ta ce bai kaunaceta ya
ɗ
aga
darajar ta cikin mata da kwakwarayenshi ba ta yi ƙarya, duk wa
ta kulawa ya bata ya tausaya
mata dukda yana cikin damuwan shima amma ya rarrasheta a lokacin da yake tunanin za ta fi
shi jin zafin
ɓ
atan danta, kwarai ta fishi ita da bata san inda yayi ba bayan nan ita da alhakin shi
ke maƙale a wuyanta na tsawon wan
nan shekarun zuciyarta bai huta ba, idanunta basu tsagaita
da zubar kwallah ba.
"Ranka ya da
ɗ
e ka gafarceni, ka tsaya ka saurari uzurina don Allah..."
Ɗ
aga mata hannu yayi
"Ba ki da uzuri Fa
ɗ
imatu baki dashi..! Babu uzurin da zai wanke bakin cikin da
nake ciki a yanzu
you were the last person i've expected that from, am very disappointed..."
Katsewa magananshi yayi jin sanarwar isowar Fulani Adama, da kuka ta shigo
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah mun gode maka ya Allah da ka share mana hawa
ye ka
amsa adu'ar mu ashe Magaji na raye? Ashe muna da rabon sake ganawa? Mai martaba
sashen ka nayi don wannan babban abin murna ne sai ake sanar min kana nan ashe... Ina
yake? Ina Sameer in ga yadda ya sauya ya zama mutum cikakke?"
Har yanzu idanun
shi da suka sauya suna kan Fulani Fa
ɗ
imatu kan ya janye ya kalli Fulani
Adama yace
"Alhamdulillah yana nan lafiya Fulani, a yanzu ya tafi abinda ya kawo shi wato tseratar da
kanwanshi."
"Alhamdulillah! Ashe rayuwa ya inganta Soja ne ashe?"
"A sojoji
n ma ba laga-laga ba. Na bar ku lafiya"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta kalli Fulani Fa
ɗ
imatu tana murmushi
"Barka na taya ki murna Fa
ɗ
imatu"
"Ai ke ce uwa a gareshi Fulani ke ya kamata mu taya murna.."
"Kwarai kuwa! Gashi ya zo a ga
ɓ
ar da matarshi m
a ta isa aure gwara da muka jinkirta aurar da
zarah ashe alƙawari zai cika"
Kai ta gya
ɗ
a bata iya tace komai ba don a gigice take, ta sake murmushi tana ta kallonta kan ta
juya ta fita, zubewa Fulani Fa
ɗ
imatu tayi kan kujera bata zaci lamarin zai kai ha
ka ba, kuruciya
ne da buƙatar uwa na ganin ta ba abinda ta haifa kariya ya sa ta aikata bata zaci abin zai zama
mata haka ba sam, tun daga ranar take nadama har yau.
Ko motsi bata sake yi ba sai ga Fulani Aminatou itama murna ta zo tayi mata bata kai
ga fita ba
sai ga Fulani Salimah itama ta mata murna duk amsawa take amma tana sane da wanda ya kai
ciki da wanda bai kai ba Dukda duk yanzu ba sune gabanta ba.
Duk rubibin da ake
Madaki da Makama suna zaune ne tamkar a kan ƙaya fata kawai suke sarki
ya ce ya sallame
su su samu su ke
ɓ
e aiko Galadima na sanar da tashin Fada kai tsaye su biyun ganawa suka
nemi yi da Fulani Adama.
"Balki ki sanar da su ba yanzu ba da kifi ya riga ya ru
ɓ
e su bari sai ya daina wari za mu
tattauna"
Da sauri amintacci
yarta bilki ta amsa
"an gama Allah ya baki yawan rai"
Tana kai nan ta fice taje ta kai saƙon suka kalli juna suka juya suka tafi babu mai uhm bare uhm
uhm.
****
Shi kam Rayyan komai ya watsar suka shiga kokarin ganin sun tsara yadda za su kubutar
da su
Aishatu cike da hikima irin ta squad
ɗ
in tasu na musamman da aka turo wannan aiki, lokaci
lokaci ya kan yi tsaki ka
ɗ
an har dai aka gama kuma akwai alamun nasara don sun samu haske
sossai daga ƙiran da aka yi na biyu.
Bayan sun gama zaman ya nuf
i
ɗ
akinshi kai tsaye wanka yayi saboda gajiyar da yake ji ainun
jikinshi, ya fito ya shirya cikin kayan baccinshi ya nufi gadon ya kai kwance kaman jira ya fara jin
ta jikinshi, emptiness da bai san na menene ba ke ratsa shi ji yake gadon yayi mishi fa
ɗ
i
ƙwarai,
shafa cikinshi yayi da bai ci komai ba tun safe da tana nan da ta fara mishi puppy face tana
roƙon shi ya ci wani abu wane cikinta ne tsintar kanshi yayi da
ɗ
an murmusawa a fili yace
"Yarinyar ta cika tsoro"
Yana maganan yana tuna idanunta in
ta ji muryarshi ko idan yayi mata tsawa. Daga karshe da
ya ga ba zai iya bacci ba dole ya tashi ya sha coffee ya koma ya kwanta ya janyo wayanshi ya
tafi numbern ta da ya kar
ɓ
a da safe kawai ya yanke bin shawarar zuciyarshi na ko muryarta ne
yaji ya dan
na wa ƙira.
Tana kwance tun tuni ko shirin bacci bata yi ba, takardu ne gabanta amma ta kasa karatu sai
tunaninshi take ya je lafiya? Ya ci abinci? Sun fara aikin? Ta rasa natsuwa duk adu'arta na
salollin yinin akan Allah ya kare mata shi ne ya bashi
sa'a a duk abinda ya sanya gaba, tana
nan tana juye juye a kan gadon sai ga ƙiran shi bata san Layin ba don bata dashi.
"Waye ke kirana ƙarfe sha
ɗ
aya?"
Tayi tambayar tana sake kallon lokaci kaman ba zata
ɗ
aga ba ta zo dagawa ya yanke, ya sake
ƙ
ira k
aro na biyu dole ta
ɗ
aga ta makala a kunne bata yi magana ba shima sai bai yi ba suka yi
shiru suna sauraron numfashin juna, chan tace
"Waye ne? Meyasa ake kira a irin wannan lokaci?"
Ya tsinci kanshi da wani kalar murmushin da bai fi second biyu ba,
ashe ta iya tsiwa shi ne take
yi wa puppy eyes na tsoro.
"Idan babu abin fa
ɗ
a zan kashe don ina da abin yi..."
"Ba ki iya sallama ba?"
Daram gabanta ya fa
ɗ
i tayi saurin Miƙewa zaune tana sake riƙe wayan da kyau Ya Saraki ne,
tuna abin da ta fa
ɗ
a da
farko yasa tayi saurin cewa
"Kayi haƙuri ban san kai ba ne Assalamu Alaikum warahmatullah"
Ya amsa sallamar
"Me kike yi ba ki yi bacci ba har wannan lokaci?"
Ta kalli takardun gabanta tana mamakin yadda ya ƙirata har yana
ɗ
an magana Dukda maganan
kama
n za'a yi kaman ba za'a yi ba yake jefowa.
"Abu nake yi ne shiyasa ban kwanta ba."
Shiru yayi idanunshi a lumshe yana sauraron muryarta.
"Abin babu suna?"
"Karatu!"
Ta amsa suka
ɗ
an yi shiru ita dai har hannayenta sun ha
ɗ
a zufa nervousness da kyar t
a fitar da
abin da ke ranta kan yayi magana ta ce
"ka isa lafiya?"
Bu
ɗ
e idanunshi yayi ya zubawa wuri guda Mammi ce ke fa
ɗ
o mishi a duk sadda motsin yarinyar
nan ya shige shi sai ya rasa Meyasa yake tuna Mammi, yanzu haka abinda yaji Allah ne kadai
ya sani. Mammi ce ka
ɗ
ai duk inda zai je sai ta tabbatar da isan shi lafiya, ita ce yake yawan jin
wannan kalmar daga Bakinta ba wata ba.
Jin shirun yayi yawa tace
"Hello!"
"Lafiya! Ki ajiye abin da duk kike ki kwanta"
Ta amsa da Toh
"Kar ki kashe!"
Chak ta tsaya da yanke call din ya
ɗ
an kausasa murya
"Ke kika ƙira ne da za ki kashe?"
Ta ha
ɗ
e lips
ɗ
inta shi dai ba'a yi mishi ba za'a zauna dashi a wanye lafiya ba.
"Afuwan"
Ta fa
ɗ
a chan ƙasa a hankali da ya saka shi sake lumshe idanu.
Miƙewa ta
yi da wayan a kunne ta tattare duk takardun ta saka a speaker kar yayi magana bata
ji ba ta shiga uku ta chanza zuwa kayan bacci ta kashe wuta taje ta hau gado.
"Na gama."
Duk motsinta yana ji.
"Ba kya alwala ne idan za ki yi baccin?"
"Manta wa na
yi!"
Bai ce komai ba taje tayi alwalan ta zo ta zauna tayi Adu'a ta shafa duk yana jinta kan ta kwanta
tayi shiru.
Bacci ne ya ci karfin idanunta don bata saba hira ba saboda bata yin baccin da safe ko rana ta
riga ta saba tun chan. Cikin Muryar bacci
tace
"Sai da safe ya Saraki"
Ya ja numfashi a hankali don Muryar ya isa inda bai kamata ya isa ba, yana sauraron komai har
tayi bacci kan ya katse ƙiran ya ajiye wayan kan kirjinshi da kyar baccin ya
ɗ
auke shi cike da
tunanunnuka.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Masu tambayar daga farko a yanzu za ku yi haƙuri ku jira a ƙarasa don
abin da ya saura babu
yawa sossai a ha
ɗ
a doc ayi distributing gaba
ɗ
aya because pages almost 50 ba abu bane mai
sauki in ta forwarding please bare with me*
*46*
Kwanakin da suka biyo baya sun zo mishi da tarin ayyuka ha
ɗ
e da zirga-zirga ta yadda ma
wani
daji suka koma suka yi camping don dai ganin an ceto su Aisha a hannun waennan Ƴan
garkuwa da mutane, inda yake ko service babu hakan ya sa ya manta rabon da su yi waya ko
da Abeeha ce kuwa bare Afeefah da sau biyu ya ta
ɓ
a kiranta gashi har an ci t
sawon sati uku
suna abu
ɗ
aya ba su ƙare ba, sun yi namijin kokari duka team
ɗ
in wanda suka hada har da
taimakon wasu airforce, polisawa da 'yan sa kai da ake cewa Hunters a cikin sati na hu
ɗ
un
suka samu gagarumar nasara bayan kubutar dasu sun kubutar da
dayawa daga cikin waenda
abin ya ritsa dasu kuma sun samu nasarar hallaka dayawa daga cikin miyagun.
A yau da ya kasance Juma'a suka iso cikin garin Fombina zuwa masarauta, kai tsaye aka musu
iso don an san da isowarsu kuma an shirya musu tarba na mu
samman, ko bai nuna ya san
Aishan ba ma itama daga ita har Zara da yake a tsorace suke har lokacin ba tantance kowa
suke yi ba sai da suka gansu tsakiyar masarauta kai tsaye sashen Uwar
ɗ
akinsu Fulani Adama
aka yi dasu ta fito ta rungumesu tana hamdala
nan suka saki kukan da ya gama cin su a rai.
Shi kam Rayyan na cikin baƙin fada inda sarki ya nemi da su koma masaukinsu su huta kafin ya
gana da su ko zuwa dare don yanzu yana ta samun baƙin taya murna daga kananan
hukumominshi da na shuwagabannin ru
gagen dake kewaye da Daular fombina, Rayyan ya
tashi zai bi bayansu Laami
ɗ
o yayi gyaran murya ya furta
"Ciroma!"
Chak ya tsaya, ya dawo da baya ya koma zaune
"Allah ya baka yawan rai!"
"Bisa tsarin umurnin da na yanke, ka shigo kenan Sarkin gida zai m
aka rakiya zuwa sashenka
an tanadar maka duk wani abin da zaka buƙata ka je ka huta iyayenka na bukatar ganawa da
kai."
Da wani irin hanzari ya
ɗ
ago ya kalli mai martaba sai kuma ya mayar da idanun ƙasa ganin duk
idanun manyan fada na a kanshi, Miƙewa
yayi
"Na barku lafiya!"
Daga haka ya fice sarkin gida yayi saurin mara mishi baya, a wajen ma dogarai shidda ya gani
sun rufa mishi baya kuma ya san sune aka yi assigning don kare lafiyarshi haka kawai yaji
kaman an takura shi.
Sashe ne na musamman
tsararre ya ji furnitures da komai da komai masu tsada da
ɗ
aukar ido
amma shi bai wani burgeshi ba tunda ba tatse
ɗ
in shi bane,
ɗ
akuna hu
ɗ
u ne a sashen ya nufi
wanda sarkin gida ya nuna mishi shine nashi ya shige ba tare da ya ce mishi komai ba yayinda
sauran dogaran suka kafe a bakin mashigar sashen.
Komai kuwa akwai ko da ya bu
ɗ
e wardrobe kaya ne kala kala kawai gasu nan, manya da
kananu Dukda ya san idan ba a cikin sashenshi ba a yanzu saka kananun kaya ma yayi yawo
da su a cikin masarautar ya ha
ramta mishi, kayan jikinshi ya zame ya shiga wanka ya jima
sossai kan ya fito ya shirya cikin karamin three quater baka da wata karamar riga fara ta kama
shi ta fitar da surarshi na cikakke kuma karfaffen namiji, wayanshi ya zara ya fito parlor sai ya
s
amu an cika dining
ɗ
in da kuloli na alfarma wanda ya san abinci ne ciki.
Gyaran murya yayi da hanzari dogarin dake dab kofa ya fa
ɗ
o ciki ya zube ƙasa
"Allah ya ja da zamanin Ciroman fombina, Allah ya kare gabanka da bayanka ubangidana, gaba
salamun ba
ya salamun naka fa
ɗ
a ne namu cikawa...."
Hannu ya
ɗ
aga mishi
"Daga ina aka kawo wannan?"
Ya jefa tambayar yana
ɗ
ora kafa
ɗ
aya kan
ɗ
aya a lokaci daya yana dan karka
ɗ
awa idanunshi
zube a kan screen
ɗ
in wayanshi
"kuyangin Uwar magajin sarki ne suka s
higo dashi ranka ya dade...."
"Ku tattara ku fitar min, daga yanzu ban amince a shigo min da abincin ko wani sashe ba don
ba na buƙata!"
Cikin ba da umarni yayi magana hakan ya sa dogarin sake zubewa
"An gama sadaukin maza..!"
Da wuri yaje ya fara t
attare wa shi kam yana zaune shiru don ya gwada Layin Afeefah bai shiga
ba na Abeeha kira daya ya mata bata
ɗ
aga ba kuma bai sake kiran ba.
Damuwar shi yadda mai martaba ya ba da umarnin dawowanshi kenan ya san ba zai taba
amincewa ya tafi ba amma kum
a idan ya zauna kaman bai yi adalci ba, bai kamata kawai su
Uncle Musa su ji cewa ya dawo gida ba dole yana bukatar komawa da su su san asalinshi ya
tattauna da su da tsara yadda za'a tafiyar da rayuwar su Abeeha da yake jin banda aure babu
wanda ya isa
ya ce zai karbi riƙon Abeehar don kawai ya dawo gida har yanzu shi a jinin Maami
yake kallon kanshi kuma a hakan yake so ya tabbata don haka dole ne ma ya ga sarki.
Time ya kalla karfe tara ne kwata kwata da mintuna ashirin, Dukda baccin da ya tarar m
ishi dole
yaje ya ga sarki ya san karfe goma zai koma turakarshi don fara shirin tafiya masallaci, Miƙewa
ya yi ya koma
ɗ
aki ya shirya cikin wasu navy blue kaftan da ya sha
ɗ
inki irin na sarauta, ya saka
hular da ta dace da kayan ya zura takalmi ya fito
hannshi riƙe da waya amma sai ya tattaresu
ya goya a baya ya fice daga sashen dogaran na ganinshi suka rufu za su bi shi ya juyo ya kalli
shugabansu.
"Sunanka?"
"Gaab
ɗ
o ranka ya dade" (Joy yake nufi)
"sauran su zauna kai ka biyo ni"
Yana kai nan y
a juya da sauri Gaab
ɗ
o ya bishi har turakar mai martaba duk inda ya ratsa
hadimai za su zube suna kwasar gaisuwa kai kawai yake
ɗ
aga musu, sai da aka sanar da
isowarshi kan ya shiga, ya ci sa'a mai