Showing 153001 words to 156000 words out of 174924 words
/>
ɗ
u tunda kana da halin hakan kuma kana da lafiya, abu daya zan roka
daga gareka Ya Saraki kar ka daina so na don Allah zuciyata fashewa zata yi".
Yana shafata tana sake yin lub jikinshi ya shiga furta
"Afeefah ki yarda da ni, babu wata kishiya da
zuciyar Ryan zata iya yi miki a soyayya domin ke
ɗ
aya jal ta sani kuma ke ka
ɗ
ai ta aminta da ki ja ta duk inda kike so, da ke ka
ɗ
ai ta aminta a
matsayin Abokiyar rayuwa ba ni da yadda zan yi ne da babu dalilin da zai sa in amince da batun
zarah amma
ba zan iya watsawa mahaifina ƙasa a ido ba alkawari ne da aka yi tun ban san
kaina ba, amma in har za ki cigaba da wannan kukan komai zan iya yi ciki har da barin wannan
gid..."
Ɗ
agowa tayi ta ha
ɗ
e lips
ɗ
insu da kanta sai da ta bashi kyakyawar Kiss ka
n ta kalli idanunshi
hannunta na a fuskarshi shima idanunshi zube cikin nata da suke a rine tace
"Kar ka ce komai, ni da kai duka karkashin ikon mai martaba muke dukkanmu uba ne shi a gare
mu da magana kawai zai yi mu cika, sannan aure ba haramun bane i
dan yana cikin ƙaddararmu
ina roƙon Allah ya ba ni haƙuri da juriya ya kuma kawo mana ta gari wacce za mu ha
ɗ
e kai mu
zauna mu kula da kai gaba
ɗ
aya, don haka Allah ya nuna mana lokaci ya bamu zaman lafiya
gaba
ɗ
ayanmu"
Ta ƙarasa tana komawa kan kirjinsh
i ta kwantar da kanta tana mayar da hawayen da suka cika
mata ido.
Matseta yayi a jikinshi kawai bai ce komai ba, sun jima a haka don bacci ne ma ya
ɗ
auketa shi
kam bai iya yayi baccin ba damuwar da ta shiga ya tsaya mishi ainun ya san ba komai bane s
ai
zallar soyayyar da take mishi, lumshe ido yayi kawai sai ranar da take ba Mammi da Abeeha
labarinta ya fa
ɗ
o mishi the way she was deeply hurt nd depressed anya ta chanchanci raba
farin cikinta guda
ɗ
aya jal da wata? Yayi adalci kenan idan ya iya ha
ɗ
a
jiki da wata mace ba ita
ba? Numfashi ya sauke mai nauyi ya mirginata kwance ya ja mata bargo kan ya sauka ya dauki
shirt ya saka ya nufi kitchen.
Breakfast ya samar mata bayan ya gama ya kai har kan gado ya ajiye kan ya shiga shafa kanta
zuwa fuska
rta cikin tattali da kulawa har ta bu
ɗ
e ido, murmushi ta mishi ya mayar mata
"Tashi ki ci abinci Bo
ɗɗ
i"
Miƙewa tayi zaune tace
"Brush tukuna bakina babu daa
ɗ
i"
"Ba dole ba na tabbatar through out jiya baki ci komai ba"
"kaima ai na ajiye maka baka ci
ba i was disturbed"
"Toh ba fushi kika yi da Sarakinki ba..!"
Yayi maganan cikin muryarta ta saki dariya ya
ɗ
auketa zuwa bayi tare suka yi brush suka dawo
tana bashi yana bata har suka koshi.
Wanka ma tare suka yi abin su yana ta takalarta tana ture
shi, suka fito ta shirya shi kan suka je
ɗ
akinta ya taya ta shiryawa.
"Bari na je nayi gaisuwa na dawo"
"Ki bar gaisuwan nan babu inda zaki a sake bata miki rai a banza"
Idanu ta ware
"An ta
ɓ
a fushi da iyaye ne Ya Saraki? Iyaye musamman uwa ita ka
ɗ
a
i ce take mantawa da
kanta yayin da take yiwa danta Adu'a ita a wurinta idan danta yayi nasara itama ta yi, Na san ka
rasa Mammi ka kuma tabbatar babu zafi da ciwon da ya kai na rashin mahaifiya. Ciwo ne da
baya ta
ɓ
a goguwa har abada, zaka yi fata za ka
yi adu'ar ko da ganinta sau
ɗ
aya ne a yayinda
kasa ya rufe idanunta a sannan kuma babu halin hakan, Uwa garkuwa ce ga dan da ta haifa,
Ya Saraki in na ce maka ga kalar kukan da nayi na maraici ba zaka yarda ba, duk ra
ɗ
a
ɗ
in da
zan fada maka akwai ba z
aka fahimta ba wani lokacin Allah ya sanya albarka daga bakinsu
kawai kake nema ba zaka samu ba, Allah ya umurcemu da kyautata musu iya iyawa a sadda
suke raye ni ka ga ban samu wannan damar ba, ko sanin su ban yi ba tsakanina da su Adu'a
ashe ba zaka a
mfani wannan damar ba? Don Allah Ya Saraki ka sake tunani akan hukuncin da
zuciyarka ke aikatawa, Allah ya sasanta tsakaninku cikin sauƙi"
Shiru yayi ganin kaman zata
ɓ
ata mishi rai ta tashi ta fice tana ce mishi sai ta dawo ya bita da
kallo kawai bai c
e komai ba.
Sashen Ammi ta fara zuwa suka gaisa ta
ɗ
an jima suna hira da Zarah da Aisha kan ta wuce
sashen Fulani Adama.
"Barka da safiya Mama!"
Tana hakimce ta amsa idanunta na scanning Afeefar ciki da bai kallon da ya sa taji duk ta
tsargu kan ta
amsa.
"Lafiya ƙalau, shi mijin naki kam isar shi ta kai ya share sama da watanni a Masarautar nan bai
ta
ɓ
a zuwa inda muke ba sai dai mun ha
ɗ
u a hanya ko? Uhm ko da shike ba ke ya kamata na
yiwa zancen ba mai martaba ne ya
ɗ
aure mishi kugu dole"
Shiru
tayi don bata san me zata ce ba, kiran hadimarta tayi
"Ke Rahane kawo mata abin ta
ɓ
awa"
"Ai mama da ta barshi yanzu na karya kenan na fito"
"Dama na lura baki ta
ɓ
a cin komai na
ɓ
angaren nan ba, ashe kema baki daukeni uwa ba
kenan... ai shikenan sai ga
isuwar ma a barta kawai Allahn da bai bamu 'ya'yan ba yana sane da
mu, na ji labarin babu abinda bakya ci a sashen Fa
ɗ
imatu nan ne ba zaki ci komai ba? Yayi
kyau"
Bata san Meyasa take mata maganganu haka ba, duk sai ta rikice ma tana tuna garga
ɗ
in
Rayy
an akan kar ta ci komai na gidan kuma dai tana cin na Ammi, wani zuciyar yace ta
gudarwa kanta matsalar Fulani Adama ta ci kawai ai Rayyan ba zai sani ba kuma ma kindirmon
da aka kawo mata fari tas kwance a ƙwarya yayi matukar bata sha'awa don haka ta ja
nyo ta
dauki ludayi ta shiga sha, sai da ta sha dayawa ta ture tayi godiya kan ta miƙe ta bar sashen.
Yinin ranar suna tare da Rayyan yana sake nuna mata ita ka
ɗ
ai ce tauraruwar zuciyarshi yana
cika ta da kauna don ko girkin rana da dare ma ba ita tay
i ba, bayan sun gama cin abincin dare
tana kwance kanta akan kafafunshi suna ma kallon wani movie ne yana wasa da gashinta ya
shiga jin hannunshi na jikewa musamman in ya kai ga goshinta, shafa goshinta yayi yana kiran
sunanta ta amsa
"Lafiya kike zufa
haka? Duk irin Ac dake aiki a parlorn nan?"
Tace
"Nima ban sani ba kawai dai cikina ke dan murda min kadan kadan ba sossai ba"
"Mp ne? Amma ai bakya ciwon cikin priod pain tashi mu gani ko mu tafi asibiti?"
Ta girgiza kai
"Ba wani sosai bane ba fa za
i daina Yaya"
Ganin ta ƙi tashi ya sa ya kai hannunshi yana shafa mata cikin a hankali.
Mutsu mutsu ta fara duk ta kasa kwanciya wuri guda ita ka
ɗ
ai ta san azabar da take ji wanda
rashin son tada mishi hankali yasa take ta daurewa, yana kula da motsin
ta sai gani tayi ya
ɗ
agata ya kai hannu ya kunna hasken parlorn tarrr, ganin idanunta ya tabbatar mishi da ba
ciwon wasa take ji ba.
"Tashi mu tafi Asibiti"
Ya miƙe yana riƙo ta bata yi musu ba ta miƙe tsaye sai dai abin da taji yana bin kafan ta ne
yasa
tayi saurin kallon wurin shima ganin yadda ta razana sai ya kai idanunshi wurin.
"Jini??"
Yayi maganan a
ɗ
an rikice kaman kuwa ana jira su gani cikin nata ya shiga kartar da bai yi ba
da farko, damke hannunshi tayi tana jin azabar na shirin kash
eta tuni ta fita hayyacinta a rikice
ya
ɗ
auketa suka fice daga parlorn da gudu Gaab
ɗ
o ya je ya bu
ɗ
e mishi mota ganin yadda suka
fito ko tukin ba zai iya ba yana rike da ita a baya yana shafa cikin yana mata sannu sai juye juye
take tana zub da hawayen d
a bata san suna ma zuwa ba, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba
jinin da bai san daga ina ba kuma na me na ta wanke su sai sannu yake maimaita mata kaman
ya taya ta kukan a haka suka isa asibiti aka yi emergency da ita don har ta fara sumewa.
A masar
auta kuwa Ammi na zaune da su Aisha aka kawo musu labarin dukkansu hankalinsu ya
tashi suka miƙe tsaye suna tambayar
"Me ya sameta?"
Babu wanda ya san amsar sai kiran me martaba da Ammi tayi tuni ya bata umarnin tafiya suka
fito a ru
ɗ
e sai ga Ameer tar
e da shi da wasu securities suka bi bayan su Afeefar cike da adu'ar
Allah ya sassauta koma menene ya bata lafiya cikin gaggawa..
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureen
jo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Don Allah ku yi min uzuri na so in bi comments in amsa kowanne amma na kasa, bana jin
daa
ɗ
i ne kar ku yi expecting biyu gobe in na iya na yi
ɗ
ayan ma Alhamdulillah!*
*56*
A
feefah ta matuƙar jiggata kan aka samu aka shawo kanta da kyar, shi dai ba zai ce ga abin da
yake yi musu a
ɗ
akin ba yana tsaye ne kawai saboda matsayin shi na likita kuma mai muƙami
da ba zasu iya kora ba, hannunshi na rike da nata yana tsaye kyamm idan
unshi na zube kan
fuskarta wani irin ciwo ne wannan lokaci
ɗ
aya? Me ya sameta? Babu kalar sake saken da bai yi
ba.
Kalaman da ya ji likitocin suke yi cikin harshen turanci cike da ƙwarewar aiki ya ƙara daure
mishi kai ya jefa shi cikin tunani da damu
wa lokaci
ɗ
aya.
"Sir da ka je ka sauya wannan kaya saboda duk sun yi stains, za tayi bacci sossai kila sai zuwa
midnight ta farka sai a sake running wasu tests"
Wani likitan ya fa
ɗ
a bayan ya dafa kafa
ɗ
ar Rayyan da ya jima cikin duniyar tsoro, mamaki d
a
ka
ɗ
uwa.
Hannunta ya zame yana kallon kayan da aka kawo za'a sauya mata da wasu towels da za'a
goge mata jikin da ya
ɓ
aci Dukda mata ne kar
ɓ
a yayi suka fita, shi ya goge mata jikin tas ya
sanya mata kayan asibitin riga da wando ne kan ya gyara mata
kwanciya ya duba tafiyar ruwan
har lokacin fuskarshi Jajazir, kwakwalwarshi ya ƙi hutawa da saƙe saƙe a haka ya fito daga
ɗ
akin sai ya tsaya chak yana kallon Ammi da take kallonshi itama a zaune.
Jikinshi ya bi da kallo yana tuna jinin
ɗ
an shi ne nan
ko
ɗ
iyar shi, wani irin zafi da bai san ya zai
fasalta ba na taso mishi a cikin zuciya bai san ya nufi Ammin ba ya samu wuri a gefenta dab ya
zauna bai ce komai ba kanshi a ƙasa, dukkansu sun yi mamaki har ita kanta amma ta danne
tace
"Sameer ya jikin
Afeefahn?"
Ya yi shiru na seconds yana hadiye wani irin miyau ya ce
"Da sauƙi tana bacci"
Wannan ne karo na farko da maganan da ba gaisuwa ba ya shiga tsakaninsu hakan ya faranta
mata kwarai amma damuwar halin da Afeefah take ciki bai barta ta nuna ba.
"Me ya sameta haka?"
"Ammi Afeefah ta ci wani abu a sashenku da safe?"
Abeeha da har hawaye tayi ta zubarwa tace
"A'a Yaya ko ruwa bata sha ba tace ta ci abinci kenan ta fito"
"Me ya faru da ita haka?"
Ameer da Ammi suka tambaya a tare, haƙorinshi y
a sa ya datse lip dinshi na ƙasa kan ya saki
zuciyarshi na tafarfasa yace
"Ɓari tayi... Zubar da shi aka yi! ta yi misscarrage ba tare da duk mun san akwai ma
ɗ
an ba.."
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Abinda duk suka fa
ɗ
a a tare kenan, Ammi t
a sanya hannunta ta kama nashi sai ya kalleta
"Ammie
ɓ
ari biyar kika yi?"
Ta gya
ɗ
a kai bata ce komai ba
"Duk wannan azabar da Afeefah ta sha haka kika sha?"
Ta sauke numfashi tace
"Na sha wanda ya fi shi ma Sameer, shi ina mai tabbatar maka azabarshi
zai iya
ɗ
ara na
haihuwa. Ka je ka sauya kayan nan haka kar ƙarnin jinin ya zauna maka a jiki"
Idanunshi ya
ɗ
aga sama yana mayar da emotions dake taso mishi ya kalli jinin
"Ɗanki
ɗ
an watanni biyar ma kin rasa shi ko Ammi?"
Nan ma ta gya
ɗ
a mishi kai.
"Haka zafin yake?"
Bata danne ba tayi murmushi mai ciwo tace
"Duk wanda za ka ji daban yake da na uwa Sameer, uwa ce ka
ɗ
ai za ta iya fasalta wannan
zafin... Idan har ka ji zafin fitan
ɗ
an da baka ma san da zamanshi ba ka fasalta da Aliyu da na
rasa sai
da na raini cikinshi na watanni tara na haife shi na shayar dashi na ga haƙorinshi na
farko, na ga murmushinshi na farko na ga zamanshi kan Allah ya kar
ɓ
i abin shi..."
Hawaye ne ya zuba mata a lokaci
ɗ
aya da Ryan, shi likita ne amma bai ta
ɓ
a kula da abi
nda ya
shafi ciki ko haihuwa ba don duk abu da mata a baya ba kaunarshi yake ba, cikin jannah da
Abeeha duk ba zai ce ga yadda Mammi tayi ba, idan wannan bari ya saka shi jin irin wannan
zafin ya Ammi ta ji?
Bayan duk wahalar kuma aka yi ta yunkurin
kashe shi mahaifinshi bai
ɗ
auki kwakwaran mataki
da zai sa hankalin uwar tashi kwanciya ba, motsin da suka ji yasa duk suka
ɗ
ago sai ya ga mai
martaba ne da dogarai biyu don ya kasa zama dole ya biyo bayansu. Shima kuma a yanzu ya
fahimce shi dole ba za
i so rabuwa da
ɗ
an shi guda da Allah ya bashi bayan tsawon shekarun
da ya
ɗ
auka babu haihuwa ba.
Dukkansu basu da laifi, uwar da ta zama distressed ta ha
ɗ
a baƙin ciki, damuwa da wahala duk
lokaci guda zai ga laifinta ko uban da baya so ya ga yayi nisa
da gudan jinin da yake mararin
samu? A yanzu ya fahimci damuwar Ammi ta sanadiyar Afeefah ya ji a ranshi zai mata uzuri ya
ji a ranshi kaman Allah ya riga da ya rubuta ne Mammi ce zai yi rayuwa da ita har mutuwar ta
ba Ammi ba, kaman yana ji a ranshi c
ewa Adu'ar Ammi ce Allah ya kar
ɓ
a ya tura mishi Mammi.
Ta wani
ɓ
angaren he's grateful na barin shi masarautar don da bai bari ba da bai san Mammi
ba idan kuma bai santa ba da bai samu Afeefah ba the 2 most important persons da Allah ya
bashi su as his g
reatest gift.
Ƙ
asa ya kai ya riƙe hannun Ammi ya
ɗ
ora fuskarshi a kai ya ce a hankali
"Ammie ki yafe min, ki yi haƙuri na tuba!"
Ɗ
umin hawayenshi suna sauka ne da nata, kuka take sossai na farin ciki Allah ya amshi adu'ar
ta, Allah ya karkato mata da
hankalinshi cikin sauƙi. Ɗago shi tayi ta miƙe tsaye kawai ta
rungumeshi Dukda tsawon da ya fita, duƙawa yayi suka rungume juna yana jin dumin
mahaifiyar tashi na ƙara karya zuciyarshi, da kyar ya danne kukan da ke taso mishi.
Mai martaba ya dafa s
hi yana dan buga kafa
ɗ
ar shi zuciyarshi fari tas na ganin abinda ya jima
yana fata shima, komai ya wuce don Ammie
ɗ
ago shi tayi ta ce
"Sameer na yafe maka duniya da lahira baka yi min komai ba, ni ya kamata ma in nemi
yafiyarka da wahalan da na saka ka.
.. Haƙiƙa na yi kuskure mai girma wanda Allah ne ya dube
ni ya raya min kai kan tafarki amma da ban san da wani ido zan isa ga mahallici na ba da
rayuwarka ya salwanta. Ka yi haƙuri"
Kai ya gya
ɗ
a.
Mai martaba ya ce
"Ya mai jikin yanzu?"
Cike da gir
mamawa Ammie tace
"Alhamdulillah Taƙawa tana bacci ne sai dai mun rasa
ɗ
an cikin"
"
ɓ
ari tayi? How?"
Juyawa Ryan yayi ya fita Ameer ya bishi, Ammi ce ta mishi bayanin suma basu sani ba amma
da yake asibitin ku
ɗ
i ne kuma kwararrun likitoci ne suka duba t
a a bincikensu sun tabbatar da
abu ta sha yayi sanadiyar zuban cikin.
"Tirƙashi! Kar fa tarihi ya maimaita kanshi!"
Shiru Ammi tayi ba zata so wa Afeefah wannan wahalar ba, Amma Allah ubangiji ya sa lokacin
tonon asirinsu ne yayi haƙiƙa adu'ar da tak
e ta tabbatar ba zai fa
ɗ
i ba Allah sai ya bi mata
hakkin cutar da ita da aka yi.
Suna nan zaune sai ga Ameer da Ryan sun dawo ya sauya kaya zuwa riga da wando english
wears hannunsu rike da ledoji manya da alama ba gida ya je