Showing 51001 words to 54000 words out of 174924 words
ma yanzu
haka yana kwance Hajiyar na a hasale, 'yan matan kuma sai kuka Toh
ita ma Afeefar da ta fito
a chan ta tsuguna ta ci kukanta isashe kan ta tashi ta tafi"
Sossai damuwa ya nuna a fuskanshi, idan tunanin shi ya bashi daidai Saleem ya fa
ɗ
awa
Afeefah yana sonta mamanshi ta ji shine suka kore ta, godiya yayiwa su Mudi ya
juya ya nufi
gida, kila ta koma kauyensu yana ji a ranshi da sauƙi ma tunda har ta fa
ɗ
a mishi sunan kauyen
kan su rabu da bai san inda zai sa kanshi ba, dole ya je ya neme ta.
Gida ya dawo Umma na ganinshi tace
"Ah Sulaiman ina asibitin? Me ya faru n
a ga kaman kana cikin damuwa?"
"Umma su saleem sun kori Afeefah a gidansu, mamanshi ta kore ta ta koma kauyensu dole
gobe in nemi leave in je in sameta ban san ya take ba kuma wayanta baya shiga"
"Wacece haka?"
Suka ji Muryar Abba!
Umma ce ta mish
i bayani yana murmushi yace
"Toh ai Alhamdulillah! Dama da niyyar aura maka mata na dawo a yau na gama maka uzuri
goben da su Yaya Zubairu za ku tafi a yi maka tambaya gaba
ɗ
aya tunda Allah ya sa ka samu
wacce kake so kuma mahaifiyarka ta gamsu da tarbiy
ar ta"
Murmushi ya saki yana jin sanyi a ranshi Dukda ta wani
ɓ
angaren yana tunanin kar Afeefah taji
ba daa
ɗ
i tunda bata sani ba kuma ba wai soyayyarsu yayi zurfi bane ita ke ture shi yana sa kai
amma dai ya ji daa
ɗ
i don da farin ciki ya koma asibitin
da bai yi niyyan zuwan ba ya tafi saboda
ya samu leave a gobe
ɗ
in don su tafi Dutsen-wai.
A waya Abba ya sanarwa yayyenshi biyu akan za'a je wa Sulaiman tambayar Na gani ina so a
kauyen Dutsen-wai, basu wani damu ba don duk su burin su ba su hada zur
i'a da masu ku
ɗ
i ba
sai su hada da gidan mutunci gidan tarbiya da sanin ya kamata shi ne abin da suke dubawa.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Gobe in muna raye sai dare za ku ji ni da yardar Allah*
*020*
Harara ya sakar mata da sauri ta mayar da idanun ta rufe ruff tsaki ya ja a fili, ya fara ƙoƙarin
neman vain
ɗ
inta... 'Asshh' ta fa
ɗ
a a hankali ji
n ya soka allurar sai ta fara kokarin janye hannun.
"Kina janye hannun nan sai na wanka miki mari akwai wanda yace ki yi ta tuna samarin ki kina
kuka har ciwo ya kama ki?"
Tsit tayi bata kuma motsan ba, kila Rayyan shine ajalinta wa ya sani don tund
a ya daka mata
tsawar nan ko numfashi mai kyau ba ta iya ja har ya gama
ɗ
aura mata drip
ɗ
in, bata ji fitan shi
ba ita kam tun tana pretending har baccin gaske ya
ɗ
auke ta a haka, don dama jiya ba baccin ta
samu ba na kirki gashi yau ta yini a kan hanya
tana galantoyi.
Sashenshi kawai ya miƙa daga nan don ya matuƙar gajiya hutu kawai yake buƙata, wanka yayi
ya fito da alwala ya zo ya shirya cikin wani morrocon jallabiya baƙi sidik mai sheki wanda ya fito
da ainihin kyaunshi fatarshi ya haska jallabiy
ar, masallaci kawai ya wuce bai dawo cikin gidan
ba sai da yayi isha, time ya kalla ya
ɗ
auke ido ya nufi cikin main parlorn kai tsaye
ɗ
akin da take
ya wuce, ta miƙe zaune bayanta jingine da jikin gadon kafafunta na cikin bargo, idanunta sun
kara girma s
un dan sauya saboda kukan da ta yini yi ga kuma bacci da tayi tayi, hulan kanta ya
zame sosai ya bayyana rabin gashinta mai sulbi, tunani take ya zata yi in ruwan ya ƙare sai taji
an yi knocking seconds uku zuwa hu
ɗ
u ya turo kofan ya sanyo kai da sallama
wadda iya shi
ka
ɗ
ai ya san yayi kayanshi.
Kanta tayi saurin mayarwa kasa Alamu sun nuna bashi da niyyar magana don har ya zo ya cire
ruwan da ya ƙare ya bare wani allura ya fasa yayi mata a canular bai ce takk ba itama bata ce
ba, kamshinshi duk ya
cika
ɗ
akin har ya gama ya juya zai fita ta furta
"Na gode"
Bai ce komai ba ya fice daga
ɗ
akin, kai tsaye wurin Mammi yayi, tana daga parlor a zaune cikin
kujera abinci ne a gabanta wanda ta gama ci yanzu cikin kula sossai da cimar tata
ɗ
in don
prof
essional cooker ya samo mata wacce take kulawa da zallar abincinta kuma take da karatu
na musamman akan cimar da ake ba wa masu ciwon ƙoda da kan tafi da diabetes, ba'a so ta ci
late kuma da ta gama ta sha magani tana so ya
ɗ
an saketa sai taje ta duba Af
eefah.
Bai yi magana ba kawai ya zo ya zauna gefenta, ta kalleshi tayi murmushi
"Gajiya ne a jikinka sossai Saraki, ka ci abinci sai ka je ka huta"
Kai ya gya
ɗ
a kawai don bashi da niyyar magana, da intercom tayi amfani ta kira su a kitchen a
kan a ka
wo abincin Saraki, simple abinci ne marar nauyi yake ci da dare suka kawo suka jere a
gabanshi, har lokacin yana kishindige kusa da ita idanunshi a lumshe.
"Tashi ka ci kar yayi sanyi babana ko in baka?"
Ya bu
ɗ
e ido a hankali ya
ɗ
an yi murmushi ka
ɗ
an
sai wani sirrin kyaunshi ya bayyana Dukda
murmushin bai jima ba sai dai tabbas duk wanda yayi wa irin murmushin zai jima bai manta ba.
Itama murmushi tayi don ita kam akwai fara'a masha Allah, abincin ya
ɗ
an ci ka
ɗ
an ya kalleta
jin tana cewa
"Ina zuw
a zan duba Afeefah"
Da Kai ya amsa ta fice, ta samu Afeefar ta idar da sallolinta tana kokarin cin abincin da aka
shigo mata dashi Abeeha na zaune cikin kujera daya daga cikin hu
ɗ
u dake gefen
ɗ
akin tana
danna waya ganin Mammi ya sa ta taso
"Afeefah
ɗ
iyata ya jikin?"
Murmushi ta saki a kunyace tace
"Alhamdulillah da sauƙi sossai Aunty na gode"
"Bana son sake ji kin ce Auntyn nan baki ji Abin da su Saraki ke fa
ɗ
a bane?"
Murmushi tayi.
"Abeeha ki kula da ita har tayi bacci zan je Saraki na jirana in
na sha sauran magungunan kuma
kin san bana iya ta
ɓ
uka komai sai da safenku"
"Toh Mammi sai da safe Allah ya kara sauƙi"
"Allah ya baki lafiya sai da safe Mammi"
Afeefah ta fa
ɗ
a ta amsa da murmushi kan ta fice.
"Na ga dai baki da niyyar sa abincin
nan bari na zuba miki"
Abeeha ta fa
ɗ
a tana zuba mata Afeefar ke cewa yayi amma sai da taji ya mata a ranta kan ta
bari kuma tace sai Afeefar ta cinye, sossai moment
ɗ
inta a gidan na yan awannin nan yayi mata
daa
ɗ
i in ka cire arangamarsu da Rayyan amm
a Mammi da Abeeha mutanen kirki ne da suka yi
ƙ
arancin samu a wannan zamani.
Mammi na komawa ta samu ya gama,
ɗ
aki ta shige ta fara shirin kwanciya cike da dauriya take
komai fuskarta dai baya nuna wa amma ita ta san me take ji, sai da ya bata mintuna
n da yake
da tabbacin ta gama yayi knocking ya shiga
ɗ
akin tana zaune bakin gado sanye da doguwar
rigan bacci har ƙasa mai kauri, frigde yaje ya
ɗ
auko mata ruwa tulin magungunanta da suke
cikin wani basket guda mai kyau ya
ɗ
auko ya za
ɓ
i na daren ya bare
ya sanya mata a tafin
hannunta, babu musu ta sha yadda ya buƙata kan ta kwanta, ya ja mata bargo ya zauna daga
gefenta tare da riƙe hannunta
ɗ
aya.
Adu'a yayi ta mata tun tana kallonshi tana danne hawayen da suke ta yunkurin zubo mata har
tayi bacci,
idanunshi da suka rine ya
ɗ
an rintse yana jin azaban da zuciyarshi ke yi, da yana da
yadda zai yi ya mayar da ciwon Mammi jikinshi da bata shekara takwas tana fama da kidney
failure ba, da ku
ɗ
i za su yi mishi maganin ciwon Mammi da ko zai yi yawo tsirar
a sai ya samar
mata lafiya, sai dai yana roƙon Allah a koyaushe yadda aka bata wa'adin watanni uku za ta
mutu amma yanzu shekara har bakwai da abin ya san ba yin su bane ba kuma dabararsu bace
Allah ne mai yadda ya so, sai dai a tsananin tsorace yake ha
kan ya sa sadaqa da duk adu'ar
shi yake kan Mamminshi itama saboda rage mishi damuwa take danne wani abin.
Sai da ya tabbatar komai intact kan ya fice daga
ɗ
akin yayi Sashenshi, Saleem ya ƙira da har
lokacin yana asibiti yana samun kulawa
"Har yanz
u babu labarin Afeefah ko Rayyan?"
Ajiyar zuciya Rayyan ya sauƙe
"Na ce ka daina
ɗ
aga hankalinka za mu same ta, ina kan bincike dai in har tana cikin Kaduna
ba zata
ɓ
ace ba just focus on your health"
Kai saleem ya gya
ɗ
a sai yake ganin kaman Rayyan
bai yi niyya bane, da yayi niyya ba zai kai
zuwa lokacin bai same ta ba, damuwarshi ya zata kwana? A ina zata kwana? Me ta ci? Duk ya
kasa kwantar da hankalinshi a gefe ga damuwar rashin ganin mommy Dukda ta mishi abin da
ya zama gyambo a zuciyarshi sai
dai uwa ce babu yadda ya iya kuma yana ƙaunarta bata da
mahadi a wannan duniya.
A
ɗ
an sanyaye yayi sallama da Rayyan, Rayyan ya bi wayan da kallo baya jin zai gaya mishi
inda Afeefah take saboda yana son Saleem
ɗ
in ya manta da ita once and for all ya
nzu in ya san
tana nan zai cigaba da sa hope a kan samunta alhali mahaifiyarshi bata
ɗ
aura wannan damara
ba na mallaka wa yaron nata cikar burin shi hakan ya sa ya
ɓ
oye mishi wanzuwar Afeefar a
gidansu.
Su Samha ko da suka zo sun ƙaraci zamansu ko ci
kanku bai ce musu ba sun gaishe shi ma
bai amsa ba, wani irin zafin su yake ji a lokaci
ɗ
aya yana mamaki bai ta
ɓ
a sanin inhumanity
ɗ
insu ya kai haka ba, suka gaji suka tafi.
****
Washegari
Da misalin karfe bakwai na safe Sulaiman ya fito shirye
cikin manyan kaya, sallama yayi wa
umma tana ta adu'ar dacewa Baba Jummai ma Adu'a tayi ta mishi har ya fice. Gidan Yaya
Zubairu ya fara zuwa ya
ɗ
auke shi kan ya wuce gidan babban Yayansu Abban Yaya Ummaru,
dattijai ne masu mutunci da kamala kuma duk s
una da dukiyar su daidai gwargwadon.
Anan suka kama hanyar kauyen su Afeefah yana ta Adu'a da Fatan ya same ta chan Dukda bai
yi ma tunanin rashin samunta ba don ina zata koma in ba gida ba? Tafiyan awanni kadan ya
kawo su kauyen yana jin hirarsu Yaya
Zubairu da suke zaune a baya, sai da suka
ɗ
an shiga
cikin garin kan ya
ɗ
an tsaya jikin wani shago matasa ne zaune su wurin hu
ɗ
u ya sauƙe glass
"Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka"
"Barka dai Alhaji"
"Don Allah tambaya nake yi"
"To Allah ya
sa mun sani"
"Gidan su Afeefah kamal"
Tsittt suka
ɗ
an yi wannan ya kalli wanchan wanchan ya kalli wanchan..
"Kai ko me zaka yi gidan su Mayyar yarinyar nan? Ai Annoba za ka ce sai mun fi gane ta"
"Annoba"
Ya maimaita sunan, abin da ta fa
ɗ
a mis
hi kenan me yasa ake ce mata annoba? Dan kallon su
Yaya Zubairu yayi duk fuskar su ya
ɗ
an nuna mamaki.
"Gidansu nake nema"
Ya fa
ɗ
a ba tare da ya ji daa
ɗ
in furucin su a kanta ba.
"Ka ga kara gaba sai ka tambaya a chan, ba mu san ko laifi ta muku ba
kun zo yi wa kawunta
tijara abu ya shafe mu lalala bamu shirya rigimar Labaran ba"
Babu wanda ya tanka a cikinsu har ya ja motan suka yi gaba, wasu yara 'yan daidai ya samu ya
kira su su biyu
"Gidan su Afeefah kamal nake nema"
Ɗ
ayan ya
ɗ
an kalli
ɗ
ayan
"Mayyar nan fa suke nema ta gidan su Auwalu"
Ɗ
ayan ya zaro ido
"Wacce ta cinye Amadun gidan malam yahaya ta gudu duniya?"
"Eh ita ce..."
Sai
ɗ
ayan ya gya
ɗ
a kai ya juya ga Sulaiman da kanshi ya sake mugun
ɗ
aurewa.
"Idan kayi gaba ka
ɗ
auki Lay
in hagu gida na biyu in baka gane ba ka ce gidan su Annoba kake
nema ajalin duk wanda ya ra
ɓ
eki"
Suna kai nan suka gudu.
"Sulaimanu a wani irin gida ka nemo aure? Wace irin yarinya ce wannan bata da shaida mai
kyau?"
Shiru yayi shima amsar yake nema
don kwata kwata ya kasa fahimtar komai.
Gaba yayi don clearing doubt ya sake tambayar wata mata a yanzu annobar shima ya fa
ɗ
a
yana runtse ido aiko ta nuna mishi, Da gaske ne ko wasa? Ya kasa ba kanshi amsa, kaman
mafarki yake kaman kuma duniyar hallu
scination ya shiga don abin ya fi yanayi da almara,
wacece Afeefah?
Tarin mutane da suka gani kofar gidan kawu ne ya
ɗ
an basu mamaki, bayan yayi parking suka
fito su uku suka tsaya suna kallon abin mamaki, dambe ake ci da Kawu da inna larai har kofar
gida duk ana tsatsaye ana kallonsu don su in suna yi ba'a raba su in ma ka shiga karshe kai za
ka ji kunya, kuma ba karamin dukan ta yake ba, Bakinta ya ƙi shiru duk yaransu na zagaye
suna kwasar kallo.
"Wani irin tsantsar jahilci ne wannan? Sulaiman
a nan gidan ka
ɗ
auko aure? Anya da
hankalinka?"
Kawu Zubairu yayi maganan kaman ya rusa kuka.
Kawu Ummaru ne ya je ya janye kawu Labaran daga riƙon da yayiwa larai ya ce
"Haba malam baka san wannan abin da kake yin ya sa
ɓ
a shari'a ba? Musulmi ne fa
kai sannan
mutum ba dabba ba wannan ai
ɗ
abi'ar dabbobi ne, ba matarka bace ta sunna?"
"Kyale shi ai ni wandon roba nake daidai da kugun kowa, wlh ba zan yi wahala in nemi kudina
Labaran ya dinga bin dare yana sace min ba shi ba ciyar da mu yayi ba kum
a muyi wahala mu
samu ya zama
ɓ
era, Toh ni ba Asabe bace da ka gama kassarata ta koma cima zaune babu
abin da take ba, kuma wallahi sai ka biyani kudina"
"Ni kike cewa
ɓ
arawo? Yau sai na ci ubanki Larai sai na zubar da hakwaran rashin da'ar nan
Malam
Sallau shi zai raba mu"
Babanta yake nufi, ganin za su cigaba da rigimar su kawu Ummaru ya ja shi gefe.
"Ashe baka san Annabi yayi mana hani da dukan matan mu ba? Yanzu kai ba abin kunya bane
yaranka gode-gode suna tsaye suna kallon ku ba? Dambe har
kan layi? Subhallah"
Kwarjini mutumin ya mishi da sai ya yanko mishi magana amma sai ya Buge da cewa
"Waye kai? Me kake so? In baka da abin fa
ɗ
a zan kama gabana don ina da abin yi"
Girgiza kai Kawu Zubairu yake Sulaiman kam ya mayar da kanshi kasa y
ana jin yadda
zuciyarshi ke cigaba da tsitstsinkewa don tabbas da matukar wuya Su kawu su bari su yi
surkuntaka da mutum irin kawu, yanzu wannan baban Afeefah ne? Innalillahi wainna ilaihi rajiun
ya maimaita ya kai sau biyar.
"Sunana Umaru Malami zuw
an namu ya shafi 'yar wurin ka Afeefah"
Zaro ido kawu yayi
"Ba dai a yawon tamba
ɗ
arta ba ne ta kashe muku wani kuka zo nemanta? Ni fa na jima da
yanke alaqa da yarinyar chan ba zai yiwu a dinga zuwa ana
ɗ
aga min hankali akan kashe-
kashe da take ba"
"kashe-kashe?"
Kawu Zubairu ya maimaita
"Wai baku sani ba? Ai rikakkiyar Mayya ce da ta addabi al'ummar garin nan a ƙarshe korinta
muka yi ta shiga duniya"
Jiri ne ya kwashi Sulaiman yayi baya baya ya dafa mota, zuciyarshi na harbawa da karfin gaske
tuni idanunshi suka sauya, kwalwarshi ya nemi tsayawa da aiki amma sai ya tuna farkon abin
da ya kawo Afeefah asibitin su ta sha poison ne don ta kashe kanta! Afeefah tana da tarin
damuwa da yake haddasawa jininta sauƙa sossai zuciyarta kuma na ta koka
rin samun matsala,
me kenan? Menene ke kunshe a rayuwarta haka? Duk ya rikice amsa yake buƙata sai dai ba
daga bakin wannan kaskantaccen mutumin da ya kira kanshi kawunta ba.
"Toh mun gode ko, sai anjima"
Juyawa kawu yayi ya kada rigar shi yayi gaba.
"Sulaiman wannan ƙasƙanci har ina? Yanzu inda ka zabi neman aure kenan? Toh ba'a zuriyar
Malami ba"
Kawu Zubairu ya fa
ɗ
a yana bude mota ya shiga, kawu Ummaru ma ya shiga Sulaiman da kyar
yayi composing kanshi ya zagaya ya shiga ya tada motar a hanka
li yace
"Don Allah ku yi haƙuri kawu ku yi min uzuri, wallahi Afeefah ba haka take ba ita nake so ba
kawu..."
"Sulaiman ko Afeefah ta