Showing 117001 words to 120000 words out of 174924 words
kowani zamantakewa da tsaro, babu ƙabila ko yare, babu
namiji ko mace, babu babb
a bare yaro haka ta shigo cikin wannan Daula ta Fulani ta kutsa kai
har cikin masarautar saboda an wayi gari da tashin hankalin garkuwa da Ƴa
ɗ
aya tilo da
Laami
ɗ
o Muhammadu Modibbo ya mallaka a wannan duniyar.
Wannan matsala ta saka Laami
ɗ
o girgiza ha
r ta kai yana tuna wani al'amari da ya faru a chan
baya da ya haddasa ciwon da yake fama da shi a tsaitsaye shekara da shekaru tashi,
kasancewar shi nagartaccen sarki, Laami
ɗ
o Mutum ne wanda ya gina al'umma mai gwa
ɓ
i,
mutum ne da kowa ke rububin ganinsh
i don agajinshi, Mutum ne da kowa ke son ha
ɗ
a alaƙa
dashi don Arzikinsa. Kyawawan halayensa ya sa ya zamana kowa ya shiga jimami a tare dashi
hakan kuma ya ba da gudummawar Gomnati na tura manyan ƙwararrarun sojoji don aiki akan
wannan lamari.
Ko da
Shigowarsu cikin masarautar a Motocinsu saboda an fara isar da su fada ne domin su
huta su kuma fara bincike daga tushe, Rayyan ne ya zama na ƙarshe wanda ya bu
ɗ
e murfin
motar sanye yake da full khaki na sojoji fuskar nan kaman ko yaushe a matuƙar ha
ɗ
e D
ukda ma
idanunshi masu
ɗ
aukar hankali da kuma karan hancinshi ne ya bayyana kasancewar akwai
facemask maƙale a fuskar tashi, yana ajiye ƙafa kan da
ɓ
en ƙasan masarautar Wani irin guguwa
mai ƙarfin gaske da ƙura ya fara tashi a take wani kalar sautin kuka
marar daa
ɗ
in ji ya kara
ɗ
e
kunnuwan ahalin masarautar har ya kai ga gigita su.
"BOƊEJO!"
Kusan shine sunan da bayi, dogarai da kuyangi ke ta ambata a ru
ɗ
e, BOƊEJO wata macijiyace
na gado wacce take da shekaru sama da
ɗ
ari tana kuma rayuwa a cikin w
annan masarauta
kaman laƙani ce na wannan masarauta kuma BOƊJO bata kuka babu dalili ta kan yi sau
ɗ
aya
idan yayi tsanani sau biyu a kowani bayan lokaci mai tsawo. Kasancewarta Jajazir a jiki da
idanu masu firgici da banda sarki ko magajin sarki babu ma
i iya arba da ita ya wanye lafiya ya
sa aka saka mata suna BOƊEJO dake nufin kalar JA.
Wasu da ba ma su ta
ɓ
a jin irin wannan kukan mai firgici da tayar da hankali ha
ɗ
e da ƙura mai
tsananin duhu ba duk sun ru
ɗ
e, a take manyan fada suka ba da umurni mai
girma na rufe
kowacce kofofin masarautar kar kowa ya fita akwai matsala, abin mamaki BOƊEJO na yin shiru
sansanin bai kai ga watsewa ba wani irin ki
ɗ
an Serewo (Algaita), Tambin (Ganguna) Da Hoddu
(kalangu da sarewa) masu mafisar ƙarfi da daa
ɗ
i suka shi
ga tashi cike da sautin da idan ka ji ka
san wannan ba dai mutum ke yi da baki ba, sojojin duk da yau ne karon su na farko a irin
wannan yanayin sun yi tunanin ma sumame ne ko wani abu don kukan BOƊEJO babu
biladaman da ba zai ka
ɗ
awa ƴar hanji ba.
Sh
i kam baya ya koma ya jingina da motar tare da lumshe ido kunnuwanshi na jiye mishi irin
rububin da ake da umurnin da sarkin gida ke bayarwa na a binciko duk wani baƙo da ya shigo
masarautar a yau ana son ganinshi a fa
ɗ
a matukar namiji ne da gaggawa umur
nin Laami
ɗ
o ne,
a take fadar ta zama babu shiga babu fita.
Wambai ne ya tuna da su don kusan aikin wambai kenan karbar baƙi da kulawa da al'amuran
masarauta da sauri ya taho wurin shugabar tafiyar wanda General ne kuma abokin aiki ne ga
Rayyan ba wai
shugabanshi ba, hannu ya bashi suka gaisa yana bashi hakurin abin da ya faru
da yadda aka manta dasu, General
ɗ
in yace
"Ranka shi dade ai mu ba ƙaramin tsorata muka yi ba da wannan al'amari mun zaci sumame ne
ake shirin kawowa hanyar sanarwar taku ke
nan!"
Wambai na murmushi mai nauyi da ma'ana mai tarin yawa yace
"Wannan kuka da kuka ji na macijiyar gadon wannan masarauta ce ta kan yi kukan nan a duk
ranar da aka haifi Ciroma wato magajin sarki, haka ma wannan ki
ɗ
an kalangun kayan kida ne
da suk
e zaune sama da shekara da shekaru da kansu suke buga kansu a duk ranar da aka
haifi ciroman wannan masarauta."
Yana musu iso suka fara takawa zuwa ciki tunda ƙurar ya lafa sossai General
ɗ
in yace
"Toh Masha Allah, an samu ƙaruwa kenan?"
"Ko kuma nes
an da muka jima cikin tsumayi ta matso kusa ba, bismillah ku zauna za'a kawo
muku ruwa"
Zama suka yi bai ba General din damar sake magana ba ya fice.
Laami
ɗ
o dake tsaye har yanzu tun fara kukan BOƊEJO ne jiri ya kwashe shi ya tafi zai fa
ɗ
i a
sadda Sa
rkin ƙofa ya zo ya tabbatar da ba baƙin da suka shigo masarautar a wannan lokacin
Galadima yayi saurin tare shi.
"Allah rene (Allah ya baka kariya) bi a hankali, Sannu!"
"Galadima ka fa ji kukan BOƊEJO ka ji kalangu taya za su yi motsi a banza tsawo
n shekaru
talatin da
ɗ
aya kenan basu yi kuka ba, dole ku je ku nema min Ciroma wlh shi ne!"
Dukda a hankali yake maganan kusan kowa a fadan na ji don sun yi tsittt ne, sun san ba lafiya
ya cika ba a kwanakin sannan rabon da yayi dogon magana haka tun da
aka sanar da shi
ɓ
atan
Gimbiya Aissatou(Aisha, na yi pronouncing yadda Fulani suke pronouncing ne).
Turaki ne da aikinshi ya zama ba sarki shawara yace
"Allah sene (Allah ya yalwataka da farin ciki) ko za'a bincika cikin baƙin sojoji da suka taho
wa
nnan ƙasa tamu? Don da alama baƙin cikinmu ne ke gab da yayewa."
Tsam ya miƙe a take dogaran da suke tsaye gefen hagu da damanshi suka fara jefa kirarin
"Gyaaaaraaa kintsi da kyau..! Taka lafiya mai talakawa"
"wambai kaini wurinsu"
"Allah ya baka y
awan rai ba za'a yi ƙir...!"
Hannu kawai ya
ɗ
aga mishi, a take manyan fada da duk suke tsaye suka rufa musu baya don
tuni wambai ya shiga gaba.
Yalwataccen parlor ne mai cike da kayan alatu na sarautar zamani, an cika gabansu da tarin
kayan itacuwa d
a ma ababen alfarma har da su
ɓ
iradam
ɗ
anyen tatsa, sun yi nisa da ci amma
shi kam yana zaune ne kawai idanunshi zube a wuri guda, fuskarnan tayi ja idan ka zuba mishi
idanu za ka fahimci baya cikin natsuwarshi don karfin hali ne ya ajiye shi wurin.
"
Gyaaara kintsi da kyau..!"
Da ke ta ƙarato su ne yasa suka fahimci kaman mai martaban ne da karan kanshi ya taho
hakan ya sa duk suka miƙe tsaye, General
ɗ
in ne ya ta
ɓ
a Rayyan hakan ya sa shima ya miƙe
ya mayar da kanshi ƙasa yana jin yadda zuciyarshi k
e tseren gudu, Laami
ɗ
o ya shigo parlorn
tuni kwarjini da girman matsayinshi ya saka su sake natsuwa, tsabar yadda yake jin a lokacin
zai iya mutuwa idan bai yi ido hu
ɗ
u da cikar Muradin shi ba binsu ya fara yi
ɗ
aya bayan
ɗ
aya
yana kallon fuskokin su, ji
kinshi har rawa yake idanunshi sun cika tafff da kwallar marari da
bege.
A lokacin da ya iso kan Rayyan ya tsaya kawai yana kallon irin tsawon Fulani da yake dashi,
bambancin ya gina jikinshi hakan ya
ɗ
an rage mishi tsawon ka
ɗ
an amma Dukda haka ya ma
kere Lamidon da ka
ɗ
an.
"Babana!"
Laami
ɗ
o Ya fa
ɗ
a cikin wani karyayyen murya yana kai hannunshi ya dafa kafa
ɗ
ar Rayyan da ya
saka shi dolen
ɗ
ago idanunshi da suka cika da kwallah masu zafi suka ha
ɗ
a idanu.
Jiri ne ya kwashi Laami
ɗ
o ya tafi kaman za
i fa
ɗ
i tsabar wani abu da ya dake shi sai Rayyan yayi
saurin sa hannu ya tare shi yana
ɗ
aga idanunshi sama don hana hawayen shi zuba amma
inaaa sun riga sun taho, Laami
ɗ
o ya fusge facemask din dake fuskarshi cikin harshen fulatanci
yake cewa
"Baban
a kaine? Da gaske kai ne a gabana? Sameeer..."
Za ka iya fahimtar ru
ɗ
u, farin ciki da tarin damuwa duka a cikin Muryar tashi.
A hankali Rayyan ya ce
"Abeey!"
Sai Laami
ɗ
on ya rungumeshi shi kuwa ya
ɗ
ora kanshi a kan kafa
ɗ
ar shi yana barin hawayen
shi z
uba cikin wani irin yanayi marar fasaltuwa, tuni jama'ar parlorn suka fara fita sai da aka
watse tas aka bar su su biyu kachal rungume da juna, kan kace kobo kunnuwan masarauta sun
fara aiki inda sashe sashe, bayi bayi, kuyangi kuyangi ake ta zancen dawo
war Ciroma Sameer
Muhammad Modibbo cikin masarautar bayan shekaru ashirin da shidda da
ɓ
acewar shi.
Babbar macece mai cike da wani irin izza da ƙasaita da kana kallonta sai gabanka ya fa
ɗ
i, bata
da fara'a ko na miskala zarratin haka komanta tana yi ne
cikin isa da wani irin mulki da ta saba
shimfi
ɗ
awa cikin masarautar shekaru da dama, Fulani Adama kenan uwargida ga Laami
ɗ
o
kuma uwar
ɗ
akin duk wata mace da zata shigo gidan ko a mata ko a kwarkwara tana da irin
izza da har kan ba mutane tsoro, ga kafa
ffen zuciya da salo salo wurin shimfida mulkin son rai
da samun duniya a tafin hannu.
Jeka-ka-dawo take a tsararren falon nata, sanye cikin shigan alfarma da kamshi na musamman
tun kukan BOƊEJO na farko taji kaman an tsire mata zuciya ne hakan yasa ta
kasa zaune ta
kasa tsaye, duk wani abinda zai hana Fulani Adama natsuwa ba ƙarami bane, Shigowar
Amintacciyarta da gudu yasa tayi hanzarin Juyowa tana zuba mata firgitattun idanunta masu
ka
ɗ
a 'yar hanji.
"Allah ya ja kwanan Fulanin Laami
ɗ
o, farin ci
ki masarauta, Uwargida kuma hasken zuciyar
Laami
ɗ
o uwar yarima da yardar..."
"Bana son
ɓ
ata lokaci Menene ya faru? An yi baƙi ne? Me ke shirin faruwa ne Balki?"
"Gobara daga kogi ranki shi dade..."
Baya baya tayi ta kai zaune cikin tsadaddun kujerunt
a hannayenta duk biyu dafe da Goshi.
A chan wani tsararren sashe cikin wasu kujerun alfarma Fulani Fa
ɗ
imatu ce zaune fuskarta
Jajazir idanunta har sun jirkice Dukda tsaf take cikin shiga ta alfarma da ƙawa kallo
ɗ
aya za ka
yi mata ka san cewa ba ta ci
kin natsuwar ta kukan BOƊEJO kaman ƙara mata damuwa cikin
damuwarta yayi don ta gigice ta kasa zaune ta kasa tsaye a sadda Kuyangarta ta shigo ta zube
ƙ
asa
"Allah ya kara miki lafiya da yawan rai, Allah ya kare gabanki da bayanki"
"Menene kande? Me k
e faruwa?"
"GIZO BA YA HANA RUWA GUDU...! Zakarar da Allah ya nufa da chara..."
Dafe zuciyarta tayi tana fashewa da rikitaccen kuka mai tsuma rai.
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(
Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*45*
"Babana...Sameer ka gane ni?"
Laami
ɗ
o ya fa
ɗ
a har lokacin gani yake kaman mafarkin da ya saba ne yana motsawa zai iya
ganin Rayyan ya
ɓ
ace, ra
uninshi ne ke sake bayyana a gaban dattijon wanda dama tun yaranta
shi ne mutum
ɗ
aya jal dake ganin hawayen shi sai Baba Maudo wanda ke matsayin Galadima
kuma
ɗ
an uwa na jini ga mahaifiyarshi.
Hannun Abeey ya riƙe ya zaunar da shi tare da yunkurawa ya
kai ƙasa kan gwiwowinshi
gabanshi kanshi a ƙasa a hankali ya furta
"A gafarceni taƙawa"
Riƙo hannunshi Abeey yayi ya
ɗ
ago shi ya zaunar dashi gefenshi yana jefar da duk wani
formalities na sarki don a yanzu uba yake.
"Da gaske ne kenan..! Kai ne da
gaske nake gani Sameer? Ina ka shiga ka manta da asali? Me
ya fitar da kai daga cikinmu ya nesanta ka? Wani irin rayuwa kayi a wani wurin da babu mu har
zuwa wannan lokaci Sameer? Na yi nema! Na yi nema har yau ban fidda ran ganinka ba ashe
da rabon sa
ke ganinka kafin in bar duniya!"
Yana maganan yana ta duba jikinshi ko zai ga wani alamun wahalar rayuwa amma ya ganshi
fes kuma fresh don ko daga tafin hannunshi da ya riƙe ya fahimci yana cikin hutu da jin daa
ɗ
i
Dukda haka sai da ya tambaya zamanshi U
ba mai cike da yunwar ganin
ɗ
an shi namiji
ɗ
aya tilo
da ya mallaka a duniya.
"Abeey ka kwantar da hankalinka don Allah, ni ne! Sameer ne a idanunka ba zan jefar da sunan
da ka yi min yanka ba sai dai Rayyan ne a idanun duniya wanda shi ne sunan da has
ken
rayuwata kuma wacce ba ni da kamarta a wannan duniya ta bani... Abeey Aisha tana chan
hannun azzalumai shine abin da ya kawo mu duk wannan za mu yi daga baya na tabbatar
Abokan aikina suna chan suna jira na"
Kallonshi kawai Abeey ke yi yadda ya
ke jera maganan da rashin cikakken fara'a mai tsanani da
ya kamata ya gani a fuskarshi.
"Aisha na da muhimmanci kwarai kasancewarta mace cikin miyagu amma kai ma kana da
muhimmanci Ciroma... Mahaifiyark.."
Da sauri ya katse shi
"Abeey...!"
Sai yayi s
hiru don bai saba katse maganan mai martaba ba, duk jimawanshi wani wurin an haife
shi ne cikin masarautar kuma ya tashi da horo mai tsanani da kuma jarumta na asalin 'ya'yan
sarki waenda ake musu mafarkin sarauta a gaba don haka yana sane da komai bai m
anta ba.
"Abeeyy ka yi haƙuri ka gafarceni ka bar maganarta for a while ina cikin farin cikin ganinka cikin
koshin lafiya, adu'ar da nake ta yi kenan duk ranar da zan riskeka in riskeka cikin lafiya da
kuzari in ga wannan farin cikin dake shimfide bis
a kamilallayar fuskarka, ka haske ni da
annurinka, ka cika ni da kwarjininka ka min hirar tarihin Fulani masarautunsu da ma
al'adunsu..."
Muryarshi ne ke rawa ya mayar da kanshi ƙasa yana datse harshe don kuka ne ke zuwa mishi
mai ciwo, shi ka
ɗ
ai ya sa
n irin ra
ɗ
a
ɗ
in kewar mahaifinshi da yayi a wannan duniyar, shi kadai
ya san irin halin da ya shiga na rashin shi kusa dashi ba tare da ya bari damuwar shi ya fita fili
ba don ya san shi aka fi cuta, an cutar mishi da mahaifi ainun da baya tunanin zai iya
yafe wa.
Mai martaba ma hawaye yake zubarwa, amma fahimtar wani abu da yayi ya sa bai iya sake
magana ba suka yi shiru. Chan da
ɗ
an jimawa ya ce
"Aisha! Ta ya ta
ɓ
ace Abeey?"
"Makaranta suka tafi da 'yar uwarta Zara'u akan suna da jarabawa dake ƙara
towa za su kai
yammaci Dukda sun san ban yardar musu kaiwa dare a waje ba Fulani Adama ce ta ba su go
ahead a kan za su dawo ba tare da na sani ba hakan ya sa suka yi dare har wannan al'amari ya
faru anan yankin makarantar tasu dayake daga su sai Driver
shima a raunane yake yana asibiti
kwance"
"In shaa Allahu za mu tabbatar babu abinda ya same ta, lafiya za ta fito."
"Ku tabbatar da hakan Ciroma. Allah ya taimaka amma za ka dawo ko?"
Ya kalli Abeey.
"Zan dawo ko don saboda kai Abeey..."
Kallonsh
i kawai Mai martaba yake yi yana ayyana abubuwa masu dumbin yawa a ranshi. Ya
girgiza kai
"Ba saboda ni ba dole ka dawo Sameer saboda al'ummarka da suke jiranka dole ka dawo
saboda ba zan iya cigaba da nesanta da kai ba tunda Alhamdulillah kana raye cik
in koshin
lafiya."
Ba tare da ya
ɗ
aga kai ba ya ce a hankali
"Wannan magana ce mai tsawo ranka ya dade ya kuma ba ka yawan rai, ina da family ina da
kanne da suka dogara da ni sannan ina da Mata duk basu san wanene ni ba..."
Murmushi mai ciwo mai
martaba ke yi duk Sameer ya taka waennan matsayi har ya kai ga
Auren wata a waje ba Zara'u da aka bashi tun daga ranar da aka haife ta ba, yana da wasu
zuri'ar da suka zama priority a gareshi da har bai iya
ɓ
oye wa ba hakan ya sosa mishi rai ainun
haƙiƙ
a ba zai bar duk abin da ya nesanta shi da Sameer ya sha a banza ba, Sameer dake da
sunan babanshi amma yake ture sunan yake makala Rayyan bayan ga asalinshi, da kyar ya
hadiye wani abu mai
ɗ
aci
"Ina jiranka Ciroma, zan jira har ka dawo da ƙanwar ka c
ikin gidan nan daga nan za mu
ɗ
ora"
Kai Rayyan ya gya
ɗ
a suka sake yin shiru na tsawon lokaci kan mai martaba ya miƙe tsaye
Rayyan ma ya miƙe kanshi ƙasa ya furta
"Allah ya baka yawan rai ya ƙara maka lafiya da imani!"
Kai kawai mai martaba ya gya
ɗ
a bai
ce komai ba ya fice dogarai dake bakin kofa suka fara
zabga kirari har ya wuce.
Rayyan ya
ɗ
auki facemask
ɗ
in shi ya mayar, ya zare bakin shade dake gefen aljihunshi ya saka
ya gyara hulanshi ya fito daga parlorn, yana bayyana a waje hadimai da dogara
i suka shiga
zubewa.
"Allah hokke jam (May Allah give you peace) Ciroma Sameer
ɗ
an Laami