Showing 66001 words to 69000 words out of 174924 words

Chapter 23 - Haihuwa-Da-Hanji-Complete

tayi maganan.

*****

Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da

gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sauƙo ta

ɗ

an kalleta tace

"Sannu Mommy"

Bata jira ta

amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na aiki, ta ce

"Talatuwa me kike dafawa?"

"Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu"

"Toh bari ki

ɗ

ora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin

ɗ

akina ba zan tarbesu da tuwo

ba"

"Amm

a S..."

"Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical 'yar aiki? Toh wallahi ki

kiyaye ni"

Sadiqa da ke shigowa ne tace

"Haaa me ke faruwa da ihu haka?"

Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa

"Amma ba ki

da hankali yanzu su Gajen ne baƙi da har za'a dafa musu kaza da wani fried Rice?

Dama shi suka saba ci a gida?"

Sabreena ta riƙe baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta

fice.

Mommy na nan zaune tana tunanin wanna

n lamarin da bata gane kanshi ba bare ƙasan shi ta

ga wucewarta kamar iska, ba'a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko

mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka....





🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku lalla

ɓ

a wannan kaina ciwo wallahi kaman zai fa

ɗ

i*

*26*

Ihu take yi sossai na neman

agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman

an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ƙasan ranshi, Mommy da ta shigo

da gudu ne ta riƙe belt

ɗ

in a tsorace take cewa

"SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa

fa kake yi wa wannan duka kaman

wanda ya kama

ɓ

arawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?"

"Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi ka

ɗ

an na mata ko kallon banza ta sake yiwa

Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ƙasa ƙasa da ita, mara

sa kunyar yara kawai..."

Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi

zaune.

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?"

Sadiqa da baƙin ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba

laifi ta

bugu ta ce

"Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan

dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba'a je ko

ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida b

a, ni zai daka? Akan Sabreena da

take ƙanwar ƙanwar bayana?"

Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce

komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa

da k

uka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan

ɗ

an ta? Ko ci

kanku bata ce ba.

Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna

suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yak

e faruwa ita bata gane

komai ba, Sabrina ta sauƙo tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta

ɗ

ora

mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba.

"Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?"

Mommyn ta fa

ɗ

a cikin m

amakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin?

"Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama

wani iri ga fa

ɗ

a da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai

yanzu?"

Samha ce me magana

n zuciyarta har lokacin yana bugawa

"Nima na kasa ganewa Samha kaina ya kulle tamau, kwakwalwana ba ya tunani daidai... Amma

bari iyayen nata su zo mu ji me kenan?"

A parlorn suka cigaba da zama chan kuwa sai ga Gaje da Yaya sun shigo, yanayin shigar

tasu

ma ba yadda suka saba zuwa ba a ra

ɓ

e a ra

ɓ

e a baya suna tsoro kar su yi ma mommyn ba

daidai ba, kai tsaye suka zauna cikin kujerun parlorn yaya yana cewa

"Hajiya Hussaina ashe ana nan, barka da gida"

"Sannunku da zuwa"

Ta fa

ɗ

a tana ta kallonsu

kaman sabbin halitta yadda suka shige cikin kujera duk ba haka suke

yi a baya ba, bata gama mamaki ba sai da Sabreena ta zo da gudu ta rungume Gaje tana musu

oyoyo

"Masha Allah, Amarya kin sha kyau da kamshi"

"kai Gaje, Baba sannu da zuwa"

Ta fa

ɗ

a t

ana daga jikin Gaje dake ta riritata.

"Barka dai 'yar arziki irin albarka, ya sabon wuri? Babu takura ko?"

"Ah baba wa ya isa ya takura ni ni da gidan mijina"

Suka yi dariya.

"Yana zuwa ya gaishe ku, sa kaya yake yi"

"Ah ba komai ai muna nan"

Mom

my tana zaune tayi tsamo tsamo kaman ruwa ya daki babban zakara har Saleem ya sauko

ya zo ya tsuguna suka gaisa da su Gaje sai albarka suke sa mishi kan ya miƙe ya kalli

Sabreena yace

"Na fita"

Da sauri ta miƙe ta bishi muryarta na fita a lokacin da

take cewa ka zo min da... Sai dai bata

ƙ

arasa da karfi ba, bayan ya fita ta dawo ta saka su Gaje gaba banza suka yi da su Mommy

kaman Allah bai halicce su a wurin ba, wasu irin hawaye ne ke zubowa Sameera tana ambaton

sunan Allah kan ta tashi ta shige

ɗ

aki tana fashewa da kuka.

Samha dai da mommy sun kasa magana, suna kallo har ta musu iso dining suka ci suka yi nak

suka dawo parlorn, mommy ta kasa shiru tace

"Yaya...!"

Kallonta yayi

"Menene yake faruwa ne? Na rasa gane kan Sabrina tunda aka yi

auren nan,

ɗ

azu fa har sa wa

tayi Salim ya daki sadiqa abin da ba halinshi ba, ba haka na saka shi ya aureta su zauna ba ba

zan zuba idanu mu cigaba da tafiya a haka ba, Salim ko kallon mutunci ya daina min daga

aure? Me hakan ke nufi?"

"Hajiya Hussa

ina ke fa kike

ɗ

aukar abu da zafi, yaro yayi sabon aure ai ba za'a saka musu ido

ba, tarbiya daidai gwargwado mun ba Sabrina kuma idan Sadiqa tana mata gani gani da a

matsayin ta na yayarta yanzu yayansu take aure ya kamata su san maganan da za su dinga

fa

ɗ

a mata ina ga hakan sai a zauna lafiya"

Mommy ta saki baki da hanci tana kallonsu. Sabrina tayi murmushi tace

"Abin da mommy ta kasa ganewa kenan, mu ajiye batun nan ku tashi mu je ku kalli sashena"

Basu bi ta kan 'mommy ba suka bi bayan Sabrina,

numfashi ne taji bata iya ja da kyau Samha

ta riƙe hannunta

"Mommy...! Mommyyyy!!"

Hankali tashe take kiranta kiran ya fito da Sadiqa da Sameera ruwa suka dauka suna shafa

mata a fuska har ta Fara sauƙe numfashi da ƙarfi, me su Yaya suka yiwa yaronta

? Sai yanzu

tunanin za su iya cutar mata dashi ya zo mata innalillahi kawai take ta maimaitawa a tsananin

tsorace.

Su kam suna hawa Sabrina tace

"kun yi min komai iyayena, ba ni da abinda zan saka muku kun ba ni wannan daula da dukiyar

sai yadda n

aga dama zan juya shi, a yanzu ma ina ragarwa uwar ne saboda wani dalili nawa

amma itama nan kusa za ta gane ta

ɗ

auki goruba ne ta damkawa kuturuwa don kwace saleem

a hannuna sai mutuwa"

Dariya suka sheke dashi Gaje tace

"Ke gidan nan fa duk na mijin

ki ne kina da ikon yin yadda kike so, sai na ga kaman wannan

sashe yayi muku kadan kenan ku suka ra

ɓ

a ba ku kuka ra

ɓ

a su ba"

Hakane kuma gaskiya Gaje, kai Sabrina ta gya

ɗ

a

"Zan san abin da zan yi akai, amma ko za ku dawo nan

ɗ

in ne?"

"Ta ya kenan 'y

ar albarka?"

Baba ya fa

ɗ

a, ta saki murmushi

"Kar ku damu na san yadda zan yi saleem yayi musu korar kare a gidan nan"

Hira suka cigaba da yi wane sa'anninta ba iyayenta ba duk wani tuggu sun ha

ɗ

a shi a ƙarshe

baban ke cewa

"Ai duk yadda za mu yi mu ya

gi rabon mu kan a je lahira za mu yi, ko a gaban Allah laifin mu

kadan ne ita ta ga dama ta bamu hanya zuwa cikin gidanta shekara nawa ina fa

ɗ

i tashi akan ya

kula ki sai da na hakura na cire rai kwatsam ta dawo da zancen ashe muna da rabon dangwalar

arz

iki mu ma, bari mu je mu fara tattare"

Sallama suka mata suka bar gidan ransu kal...

****

"Saleem..."

Ya kira sunan yana zama gangar shi, bu

ɗ

e rinannun idanunshi yayi ya zuba su kan Rayyan

ɗ

in

ba tare da ya ce komai ba, duk wannan

ɗ

in ba halin S

aleem bane na Rayyan ne hakan ya sa

Rayyan

ɗ

in ya

ɗ

an damu.

Yana zaune kawai ya ga Shigowar saleem

ɗ

in office

ɗ

in kuma bai ce mishi komai ba bayan

sallama ya samu wuri ya kishingida.

"Menene? Me yake damunka?"

"Ni ma ban sani ba Rayyan, kawai ina ji

n ƙunci ne raina babu daa

ɗ

i zuciyata na mini zafi ba na

iya bacci"

"Saleem kana karatun Alqur'ani?"

Ya girgiza kai don ya fi 2weeks rabon da yayi karatu in ba a sallah ba.

"Alqur'ani wani dafa'i ne na yaye ƙuncin zuciya saleem, idan ka ga ba zaka iya

bacci ba kayi ta

nafilfili kana karatun za ka ji sauƙi, ka fi kowa sani na har a yanzu bana bacci kaman na mutane

amma da na riƙe ibada ban zauce ba... Ka roƙi Allah ya yaye maka dukkanin damuwowinka"

Kai ya gya

ɗ

a, Rayyan bai kara cewa komai ba ya tash

i yayi playing karatu a office

ɗ

in ya je ya

ɗ

auko ruwa ya kawo mishi ya

ɗ

an sha tare da kwanciya a three seater abin mamaki tun karatun

na shigar shi har bacci mai tsananin daa

ɗ

i da natsuwa ya

ɗ

auke shi ba tare ma da ya san yayin

ba.

Saleem ya yi bac

cin Awa biyu cip kan ya farka har lokacin Rayyan na office

ɗ

in yana wani aiki a

system ganin ya farka ne ya mishi sannu, kai ya gya

ɗ

a ya miƙe ya shige toilet da ke ta tashin

kamshi wanke fuska yayi tare da alwala don ana ta kiran la'asar, bayan ya fito R

ayyan ma ya

rufe duk abin da yake yi don baya tunanin daga masallaci zai dawo office

ɗ

in ya shiga bayin

yayi alwala ya fito yana gyara hannun lafiyayyar farar shirt

ɗ

in shi da ya

ɗ

ora akan navy blue

wandon jeans, rigar suite

ɗ

in ya dauka da briefcase

ɗ

i

nshi suka fice yana kulle office

ɗ

in. Sai da

ya zube abubuwan a mota suka isa masallaci suka yi sallah.

"Za ka iya driving

ɗ

in ko in mayar da kai"

"No zan iya"

Ya fa

ɗ

a a hankali.

Da kallo ya bishi har ya shiga motar shi ya bar wurin, ƙasa natsuwa ya

yi da yanayin saleem

ɗ

in

duk sai ya tsaya mishi, da wannan 'yar damuwar ya nufi gida horn yake dannawa a kofar gidan

da gudu aka wangale mishi gate ya cusa motar ciki, idanunshi ne suka fa

ɗ

a kanta sanye take

da wani stylish crepe Adire ta ha

ɗ

a shi da ma

tching colour purple na Jersey, daga inda yake

yana hangar labbanta dake shekin man baki sossai tayi kyau amma shi ba kyaun yake gani ba.

Dr. Sulaiman dake tsaye yana mata magana ya

ɗ

an zubawa idanu kan ya ƙarasa parking

ɗ

in ya

sauƙa sai ya

ɗ

auke kai

kaman bai san akwai halittu wurin ba, tafiya yake kaman ba zai taka

ƙ

asa ba har ya

ɗ

an gota su Dr. Sulaiman ya taso

"Assalamu Alaikum warahmatullah Dr. Rayyan"

Sai da ya

ɗ

an lumshe ido ya bu

ɗ

e kan ya

ɗ

an waigo ya kalleshi ba don ya san muhimmancin

sa

llama ba babu abinda zai sa ya amsa, hannu ya miƙa mishi suka gaisa ya juya ya shige ciki

fuskar nan kaman an mishi mutuwa.

Sai da ya

ɓ

ace ta sauke numfashin da ta riƙe Dukda ko kallon inda take bai yi ba, kwarjinin shi

ya matuƙar cika ta ta tabbatar

haka Sulaiman ma don babu wanda baya shan jinin jikinshi a duk

sadda Rayyan ya matuƙar tsumewa, ita dai ta san Rayyan ba ya rasa nasaba da sarauta.

"Afeefah me kika ce?"

Dr. Sulaiman ya fa

ɗ

a

"Zan tambayi Mammi in shaa Allah in ta amince tunda gobe ha

lf day juma'a sai ka zo mu je in

na tashi school"

"Toh shikenan, ga wannan"

Ya miƙa mata leda kin kar

ɓ

a tayi sai da ta ga ranshi ya

ɓ

aci kan ta amsa don bata yadda ta iya.

Kai tsaye wurin Mammi tayi don ta bata ledar ba ma ta bukatar bu

ɗ

ewa kan ta ka

i mata, da

kuwa ta san abinda zata tarar da bata shiga ba fa

ɗ

a sossai Rayyan ke yi na shi baya son

tarukuce idan abinda zata yi kenan ta tattara ta bi samarin nata yaushe har ta tafasa da zata

ƙ

one? Haka ta ga Abeeha na yi? Toh shi ba irin tarbiyar da y

ake ba ƙannenshi ba kenan in

kuma tana gidan dole tayi abinda ta ga su Abeeha na yi.

Jikinta rawa ya

ɗ

auka, Mammi ta riƙo hannunshi

"Duk fa

ɗ

ar nan na Sulaiman ya zo ba tare da ka sani bane? Kayi hakuri ni ce na mata izinin fita

ba haka kawai tayi fit

an gaba gadi ba kuma ko mintuna biyar bai kai ba idan nima na yi laifi sai

in ji..."

Shiru yayi bai ce komai ba.

Tana tsaye a gefe kaman yajin kosai kafafunta kaman za su kayar da ita saboda yadda suke

rawa don mugun kallon da ya aika mata, ledan han

nunta ya kalla

"Ba kin ga kalar rainin da bana so ba Mammi? Mun ce ba mu dashi ne da zai kunso koma

menene a leda ya kawo mata? Ko ta tambayi abu ba'a yi mata ba?"

"Saraki...! Bana so! ka ga bana so don Allah, ka duba yadda ka firgita ta? In kuma hank

alina

kake so ka

ɗ

aga ka cigaba"

Da

ɗ

an fa

ɗ

a tayi maganan, haushin kanshi ya ji ina ma ruwan shi da zai damu da tarbiyar ta?

Shi ba wani tsiyar yake dubawa ba sai kar ta lalace da tara samari tun bata kai lokacin ba,

Miƙewa yayi ya nufi fita daga

ɗ

akin

ranshi a ha

ɗ

e fuskar nan murtuk, wani irin chill abu ne ke

bin jikinta na tsoro, bata san me yasa shi baya wani damuwa da damuwarta ba a ranta take jin

kaman bai yi na'am da zamanta a gidan nasu ba, ita idan ba don mammi ba wlh ko inuwa ba

zata so ha

ɗ

a

wa da shi ba bare har magana, gashi nan tana ta aikata laifin da zai ji haushinta.

Kamshinshi ne ya daketa a sadda ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba ta lumshe ido sai da ta

tabbatar ya tafi ta sauke numfashi ta isa wurin Mammi tana jin hawaye na tsin

ke mata

"Mammi ki yi haƙuri ban san ba'a haka anan ba, na fita ne ba don wani abu ba sai don Roƙon

da Dr yayi ta min a kan ko ba zan

ɗ

auke shi Masoyi ba in

ɗ

auke shi wa da zan iya neman abu a

wurinshi yayi min, ya ce min Mamanshi ta damu tana so in je

ta ganni ta ji lafiya ta don kaman

'ya itama ta

ɗ

auke ni wlh ba ni na roƙe shi ba Mammi kin ga da kyar na kar

ɓ

a har saida ranshi

ya

ɓ

aci..."

Dafa ta Mammi tayi

"Natsu Afeefah! Ki natsu kar masifar Saraki ya dame ki, haka yake wlh kin ga su jidda bas

u isa

su kula saurayi ba sai ya fara zuwa ya ganshi yayi bincike ya amince mishi kan ya zo idan yayi

bincike bai mishi ba ko wayanshi suka sake

ɗ

auka mai karbar su a gidan nan sai ya shirya, na

sani a yanzu babu zancen aure tsakanin ki da Sulaiman shiya

sa na bari kika fita, kuma ai ba'a

mayar da hannun kyauta baya... Goben ki shirya sai ku tafi da Abeeha in ta dawo school ku

gaishe da mahaifiyar tashi kinji?"

Tsoro ne ya sake rufe ta jin yana duka, itama kenan zai iya bugun ta in tayi ba daidai ba

"A'a Mammi ba sai na je ba, zan bashi uzuri..."

"Kar ki wani damu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login