Showing 84001 words to 87000 words out of 174924 words
ji daa
ɗ
i ba sam da hakan ta kasance.
Bai gama shan mamaki ba sai da ya kalli tarin dangin Mammi, iyalai da jiko
kin uncle
ɗ
inta
motoci kusan nawa har da abokanan arziki don a matsayin auren jikan Uncle
ɗ
in za'a yi, kan su
tafi Mammi ta roƙi uncle Musa akan duk runtsi a dawo da sadakin Afeefah wanda Saraki zai
bayar in ya so ko wani abu ne a bashi daban amma sadak
i na Afeefah ne.
Mutanen Dutsen-wai suna zaune kawai suka fara ganin lafiyayyu kuma tsararrun motoci suna
shigowa one after the other, babban masallacin garin da bashi da wani girma sai haraba suka yi
wa tsinke tuni dama Uncle Mansur ya aiko da masu c
anopies an kafa dayawa a harabar don
masallacin ba zai
ɗ
auki mutanen ba, an shimfida carpets-carpets anan suka yi masauki, Kawu
an nemo na ƙasan akwati don maƙon shi ma bai barshi yayi sabon
ɗ
inki cikin dubu hamsin din
chan ba bai tashi jin kunya ba sai
da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa
mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na maƙale saman katangu ana kallon ikon
Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo...
Fara haramar
ɗ
aurin a
ure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman
"Nawa ake bayarwa?"
Sulaiman ya
ɗ
an juya hannu alamar mene kenan?
"Sadakin?"
"Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ƙarancin sadaki yana
dubu
ɗ
ari da tamanin da uku ne"
A l
okacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir
ɗ
in dubu-dubu guda
biyar ya miƙawa Uncle Sanusi aka miƙawa liman an
ɗ
aura auren Afeefah Kamal da Rayyan
Moh'd Khamis akan sadaki naira Dubu
ɗ
ari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin y
anayi ne yake
ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da
dabino da sweets.
Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin
da yake ji baya misaltuwa mishi, kaw
u sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan
zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a
fina-finan ma wannan ko ya aka yi ku
ɗ
inshi daban ne, limami ne yake rike da ku
ɗ
in sadakin
kawu yaje ya
fara kokarin kar
ɓ
a sai uncle Musa yayi interrupting
ɗ
insu
"Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?"
Limamin ya gya
ɗ
a kai
"Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata"
Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya kar
ɓ
i kudin gaba
ɗ
a
ya wani irin kullutun bakin ciki ne
ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda
haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception 'yan kauyen sun ga abinci da kaji iya
gani, yana ta mamakin ya aka yi Mam
mi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk
kauyen babu gidan da ba'a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi.
Karfe goma sha
ɗ
aya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo
shi
"Malam Labaran
na ga kana kokarin shiga mota?"
"Eh wai dama in je ne in kalli inda 'yar tawa za ta zauna"
"Ah ai ba'a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu
ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin sal
ama"
Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta
dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun ha
ɗ
a ta da ƙaddarar ta
rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma
sun shaida a yanzu ta
shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da
hantar kura.
Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi zaƙin baki har motocin suka watse
illa Sulaiman da Rayyan wanda yake ji
ngine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana
mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha'awar kallon kawun baya yi don ko da kawun
ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya ha
ɗ
e fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin
kwarjini dol
e kawun ya kyale shi.
Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne
ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka
ɗ
aura mata aure
kwatankwacin na Afeefah, sadakinta ka
ɗ
ai yayi sadakin mata
ashirin a kauyen kaf... Inna Larai
na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen
bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin
ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan ka
wun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa
wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja
baja.
Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi.
Ko da suka iso Kaduna
shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa
Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye
karamin parlorn Mammi ya leƙa sai ya ga wata cousin
ɗ
inta tace mishi
"Tana sashen ka Rayyan"
Bai am
sa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi
sara mishi yake.
A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka
cikin leshi blue doguwar riga ta
ɗ
ora gyalen da ya shiga da leshi
n a kanta da aka yi wa dauri
mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka
kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta
tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye su
ka shiga zubo mata
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan
rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da
ɗ
ana a rana mafi muhimmanci
cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiy
a Allah ka sanya musu tausayi, jin kai,
bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sauƙe duk wani hakki nashi na aure...
Rayyan..."
Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu'o'in nata har a cikin
zuciyarshi ya sa han
nu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta
kira Abeeha
"Ku zo da ita"
Daga haka ta kashe.
A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai
suke yin kyau don shine yake ba ta kul
awa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share
mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana
ɗ
aukar su, suka kalli cameran suka
murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin
murmushin Mammi yayi yawa ya s
a ya kai idanunshi inda take kallo.
Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ƙaya, tayi masifar kyau cikin wani
exlusive luxery lace da aka yi wa
ɗ
inki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da
fuskarta makeup da aka m
ata ya matuƙar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne
bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah.
Mammi ta miƙe ta tarbota
"Masha Allah, Tabarakallah
ɗ
iyata you made a beautiful bride"
Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idan
un har suka zo suka zauna Mammi tana
tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya
ɗ
an tsayar
akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun
shi ta kamo na Afeefah ta ha
ɗ
e a tare
suka
ɗ
ago sai zuruf idanunsu suka fa
ɗ
a cikin na juna,
idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar
nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta duƙar da kanta daidai Mammi ta
ɗ
ora nata hannun
a kan nasu
camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga
ɗ
aukar hotuna.
Ko da za'a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta
miƙe ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma
ɗ
in amma har lokacin da space tsakanin
shi d
a Afeefah mai hoton ya kalleta yace
"Amarya ki
ɗ
an matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi"
Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi
presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana
so ya tashi don ya gaji hakan
ya sa ya
ɗ
an matsa ka
ɗ
an Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta ha
ɗ
e sai suka
kalli juna don duk sadda jikinsu ya ha
ɗ
u su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani
ma'ana na daban nan aka shiga daukar hotuna.
Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last
Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi.
Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na ta
ɓ
a bayan nata babu zato ta ji
hannunayenshi duk biyu ya zagaye
cikinta, a
ɗ
an razane ta
ɗ
ora nata biyu a kan nashi
"Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??"
Da
ɗ
an fa
ɗ
a yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin
yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin
su ma suka fice.
An yi yini an ci an sha an yi hidima har la'asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan
walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi ka
ɗ
ai ya bayyana tsadar
shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima
aka ci aka sha kan mutane suka fara
watsewa don bayan isha aunties
ɗ
in su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi
bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai ta
ɓ
a tafiya ya kyaleta a gidan ba,
kuma parts dake gidan kenan don
a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi
part
ɗ
in da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi.
Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah
tayi sall
ah aka shirya ta again cikin atampha aka
ɗ
ora mata lafaya aka miƙa ta wurin Mammi,
sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta
yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, t
a rungumeta
ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka
mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya
ɗ
aya jal da
ɗ
an ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai
take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee
na nan ta ga wai Afeefah ce a
ɗ
akin miji? A haka aka kaita
ɗ
akinta da Adu'a a Bakinta.
Mammi waya ta
ɗ
aga ta kira shi, ba'a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash
har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi ya
wa ya saukar mishi da
ciwon kai sossai.
"RAYYAN...."
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FRE
E BOOK*
*33*
"Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ƙannenka,
na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba za
ɓ
i shi kuma
ya za
ɓ
a maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwa
rka, idan har ka ci amanar ta ko ka
ha'inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta
domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda
Allah, idan ka so ta ka so
ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar
ɗ
a kunya. Ka
zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a
gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami"
A hankali ya
ɗ
an
ɗ
ora kanshi a
gefen kafa
ɗ
arta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sauƙa Mata,
hannunta ya kama
"Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce"
Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai
a yanzu haka wanda
bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a
haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba.
"Ka tashi ka sha magani Saraki"
Ta fa
ɗ
a, da kyar ya bu
ɗ
e lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya miƙe za
une, karbar pills
ɗ
in yayi ya sha wanda ta ha
ɗ
a da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin,
Miƙewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace
"Sai da safe"
"Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da Am
in kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba
da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi haƙuri ta kara juriya kafin ta samu
yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta
ɗ
an
saki kan ta
sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi baƙi kam duk babu kowa.
Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi
ɗ
auke da sallamar da iya shi ka
ɗ
ai
ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujer
a ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai
rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da
ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana
ɗ
ora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da
zai iya da kuka zai yi da
ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa
yayi ƙasa kan carpet ya
ɗ
ora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan
yanayi sai da ya
ɗ
an samu relief ya miƙe ya nufi
ɗ
akinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora
uku
kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi
yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci
ɗ
aya yana dan buga glass
ɗ
in wurin wankan da
hannunshi.
Sai da yaji zai iya fa
ɗ
uwa idan bai bar wurin ba ya fito
ɗ
a
ure da towel ya hau gadon ya kwanta
ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi
baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo.
Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya taf
i ta miƙe tana kallon
ɗ
akin
har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga
buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so
a lokacin da ya so, a hankali take bin
ɗ
akin
da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali
gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi
da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar
ba ita dake fa
ma da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma
Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da
ubangijinta.
A haka ta shiga bayin shima ta ƙare mishi kallo komai na 'yan gayu,
bata yi wanka ba don sai
da tayi wanka