Showing 15001 words to 18000 words out of 174924 words
taho da shi akan mafarkinta mai muni ne
Afeefah ta gama cinye kayan cikin zainabu ashe da gaske ne! Duk irin taimakon da
malamin
nan ya so bata ya gaza haka likitoci suna gani ta ce ga garin ku..."
Hamdiyya ta chafe cikin kuka
"in ba aikin maita ba menene wannan? an riga an cinye mata kurwa, sai da na fa
ɗ
a wlh sai da
na gargadi Aunty akan mayyar yarinyar nan.."
Gayya
r mutane bayan waenda hamdiyyar ta zo da su suka sake cigaba da taruwa suna
hayaniya akan tabbas ita ce mayyar ai dama daga Dutsen-wai ma gudu wa ta yi saboda
yunkurin kashe ta da Ƴan uwan wadda ta kashe last suke kawai a kasheta.
Ƙ
afafunta sai suka g
aza
ɗ
aukarta, ta zube yaraf a ƙasa, hawayen da suke zuba tuntuni sai suka
ƙ
afe kamar rijiyar da aka yi wa yaso. Zuciyarta na raya mata cewa da gaske ita
ɗ
in annoba ce,
da gaske ita
ɗ
in mayya ce.
Tana ji jama'a na maimaita lafiya ƙalau ta kwanta ciwon ci
ki ya turniƙe ta cikin dare daga isa
asibitin su sai mutuwa. Hujjar da suka kafa kenan suna ƙara tunzura shi wasu na ta fa
ɗ
an
abubuwan da ita karan kanta da ake yi wa ƙagen bata san yaushe aka yi ba, ina ma da bata
biyo Aunty zee ba? Ina ma da bata zo b
a! Ina ma da bata biyo ta ba!
Da gudu ta miƙe tana komawa cikin
ɗ
aki gunjin wahalallen kukan da ta fashe da shi ha
ɗ
e da
ƙ
ara na bala'i na cika ilahirin gidan ba wai don gudun rayuwarta da mijin antinta ke ta iƙirarin ita
ma sai an kasheta ta bi matarsa
ba sai don rungumar mutuwar a karan kanta, tana so a yau ta
kawo karshen komai tana so tayi mai gaba
ɗ
aya da rayuwarta wai haihuwa da hanji... bayi ta
shige kai tsaye babu wani tunani ko shawara ta zaro piya-piya da su ke ajiyewa saboda sauro
ta bu
ɗ
e tar
e da kafa bakinta a kai tana kuka me tsanani da dugunzuma zuciya, ƙwatt! ƙwatt!!
ƙ
watt!!! haka maƙogoronta ke ba da sauti a sadda ta ke ha
ɗ
iyewa tana jin ta yi sallama da
rayuwa kaman yadda mamanta, babanta, kakar ta, innarta da ma Aunty zee suka yi.
Lallai an yi mata mummunan zato da ba za ta ta
ɓ
a wankuwa ba a duniya, ta gaza! Ta kasa
rayuwa kaman kowa, a yanzu wa zai dauke ta kuma? Wa zai yarda wani nasa ya aure ta ko ya
ra
ɓ
e ta? Mutuwa ita ce abu mafi sauƙi a gare ta kaman yadda ta yankewa kanta.
Kururuwa da take ji a nesa bai sa ta sauƙe kwalbar fiya-fiyan ba sai da ta ji an yi wani irin wurgi
da kwalbar ya tafi ƙasa yana tarwatsewa kwatankwacin yadda rayuwarta ta tarwatse. Dishi
Dishi take gani jiri ya di
ɓ
eta sai taji an tare ta sun tafi a tar
e suuuuu ƙasa.
***
A kafa su ke takawa sanye cikin uniform kasancewar assignment da aka ba su a
cikin Anchau sun gama shi kuma a lokacin ne suke shirin barin garin zuwa cikin
Kaduna, Zaratan matasa ne biyu sanye da khakin Sojoji daga yanayin tafiya
da
tsarin zubin halittarsu zai tabbatar maka da waennan
ɗ
in ko a cikin Sojoji zaƙaƙuran
ne, da wani irin ginshira suke tafiyan kowannensu na da kalar nashi kyaun, haiba da
tarin kwarjini abin da ya bambamta uniform
ɗ
in nasu abu
ɗ
aya ne, shi wadda ya fi
cin maganin fuskan nan tamau daga damtsen hannunshi akwai wani farin bandage
da aka zagaye ƙarshen uniform
ɗ
in dashi a jiki akwai zanen plus
➕
Da jan tawada
wadda zai tabbatar maka da wannan
ɗ
in Medical soldier ne.
"Ko wanchan taron na me?"
Na gefe
n da bai kai haske da wani irin ƙasaitar wanchan
ɗ
in ba ya fa
ɗ
a cikin natsuwa.
A sace ya
ɗ
an kalli wurin ya watsar kaman ba zai yi magana ba cikin halinshi na i don't care ya
furta
"How would I know Saleem after all tare mu ke da kai?"
Wadda aka ƙira d
a Saleem ya sake kallon taron a lokacin da suka tunkaro su sossai
"Ko ma menene Rayyan ba na tunanin lafiya..."
Ko ya tanka sai ma kanshi da ya mayar ƙasa yana ci gaba da takunshi cikin ƙasaita da isa
kaman yadda yake a halittarsa.
Ihu da ƙarar da ya
ratsa kunnuwansu ha
ɗ
e da furta kalaman
"sai mun kasheta yau za mu ga karshen maita"
Da jama'ar wurin suke ta furta wa wasu ma
ɗ
auke da makamai ya sa Saleem taka birki yana
riƙo hannun Rayyan da yayi kaman bai ji ba.
"Guy akwai matsala, we cannot neg
let our duty ba za mu ga ana shirin
ɓ
arna mu kama hanya
mu wuce ba"
Ko ya tanka sai birkitattun idanunsa da ya kai wurin yana nazarin situation
ɗ
in fuskar nan babu
walwala ko na miskala zarratin.
Bai yi magana ba har Saleem ya isa ga mutanen, yana tsay
e daga gefe da farko jama'ar sun so
yin gardama amma jin ya kira akan a turo squad kuma ya zaro bindiga ya sa aka fara watsewa
uncle da hamdiyya dai sai kuka da Allah ya isa suke yi, a mayar da maganan da ake ne ya ji
abin da ke faruwa.
"Wait here!"
Ya fa
ɗ
awa Saleem kan ya haye katangar gidan da ba shi da wani tsawo chan chan, bai bu
ɗ
e
kofan ba sai yayi cikin gidan yana dube dube, motsi da Sheshekar da ya ji ne ya saka shi kai
kyawawan idanunshi wurin sai suka sauƙa kan kwalbar fiya-fiya a take w
arin ya shige cikin
hancin shi da wani kalar hanzari ya fusgo madarar ruwa da ya gani nan cikin
ɗ
akin Auntyn
kasancewar ta mai jego ya fasa guda biyu ya isa gabanta ya sanya hannu yayi wani irin wurgi
da kwalbar ya ha
ɗ
e da gini ya tarwatse...
Sulalew
a take ƙoƙarin yi a lokacin da ya
ɗ
ago madarar yana shirin bata, bashi da za
ɓ
in da ya
wuce ya sanya hannunshi
ɗ
aya ya tareta suka kai ƙasa ita tana ƙoƙarin sumewa shi kuwa ya
sauƙa a kan gwiwowinshi, kanta ya
ɗ
ago da take ta kokawar numfashi ya kafa mada
rar tare da
matse hancinta sai da ta kwankwadi mai yawan gaske kan ta sake yunkurowa tayi gaba wani
kalar amai na kwace mata, tana gamawa ya sake dura mata
ɗ
ayar ta sake kwarara wani aman
ko idanunta bata iya bu
ɗ
ewa alamu sun nuna ta jima da ficewa hayy
acinta haka ya sanya
hannu ya
ɗ
auko ta zuwa waje, Fitowar shi da isowar motar Sojoji lokaci guda sai ciki aka sanya
ta ya shiga tare da barin Saleem wurin suka fice a guje kaman yadda suka saba.
Da gudu Uncle da hamdiyya suka shiga suka
ɗ
auko yaran da
ke ta kuka suna rurrungumesu a
lokaci
ɗ
aya suna ta tsinewa Afeefah, Saleem dake tsaye ya iso gangar uncle
ɗ
in
"A komai ya kamata ku dinga adalci da tunani, ƙage ko sharri ba abu bane mai kyau shin kun
ta
ɓ
a jin maita ko a addini? Ko kun ta
ɓ
a ganinta ta
yi maitar?"
"Wallahi billahi na rantse da Allah idona idon Afeefah sai na sa an kasheta gwara ku gaya mata
tun daga inda ta tafi ta san inda dare ya mata, sam Shigowar ta rayuwarmu bai mana rana ba"
Hamdiyya ta kar
ɓ
i zancen
"ba kai ka
ɗ
ai ba ai gwara ma
ta mutuwar ta da dawowa unguwar nan tsinanniya"
Juyawa kawai Saleem yayi ya bar gidan suna ta zaginta da kwashe mata albarka wasu mata na
shigowa ana ta kokarin mayar da magana ai dama an gargadesu.
BAYAN WASU AWANNI
A hankali ta shiga ƙoƙarin bu
ɗ
e
idanunta da suka matuƙar yi mata nauyi tana jin yadda kanta
yake wani sarawa, a tunanin ta za ta tsinci kanta cikin ƙabari ne kaman yadda ta jima da
sallamar da rayuwarta wa mutuwa sai kuma ta ga akasin hakan. Idan ma tunanin ta ya bata
daidai kaman na
n
ɗ
in
ɗ
akin asibiti ne take ciki duba da yanayin tsarin
ɗ
akin da kuma ƙarin
ruwan da ke shiga jikinta ta canular dake
ɗ
aure a hannunta. Tunanin dalilin mutuwar tata ne ya
bijiro mata kaman ana haska mata majigin rayuwarta...
"Aunty zee ta rasu" Daram!
Haka zuciyarta ya buga zuruf ta miƙe zaune kaman ba jiri ne ke
walagigi da rayuwarta ba, hannayenta ta sa duk biyu ta toshe dukka kunnuwanta don ji take
kaman ana maimaita mata kalaman na rasuwar Aunty zee da speakern da ya fi komai ƙara a
duniya. Tamk
ar zautacciya haka ta saki wani irin ƙara da ya shigo da nurses har uku
ɗ
akin da
gudu da ma an ba su aikin kula da ita kar ta farka ta sake yunkurin cutar da rayuwarta.
Shigowar su da fara fusge-fusgenta kusan lokaci guda rirriƙeta suke kokarin yi amma k
aman
mai tashin aljannu sai wani irin ihu take mai tafe da gunjin kuka mai ta
ɓ
a zuciyar mai saurare
don kowa ya ji kukan ya san ba na wasa bane
"Ku barni na mutu! Don Allah ku bar ni na mutu ba zan iya rayuwa ba! Ku sakeni....! Ku sake ni
na ce!"
Du
k ta haukace kuma yawan su bai sa sun iya natsar da ita ba..
"Will you shut up and stay still?? Giyar wake kika sha ne?? Hauka kike yi ne??"
Kalaman suka fito cikin wani irin amo da ya amsa duka
ɗ
akin...
🖤
Gureenjoh
🖤
HAIHUWA D
A HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*008*
"Karen hauka ne ya cije ki? Ko stupid lunatic brain naki hauka yake karanto miki?? Are you
stupid?? Ki kashe kan na
ki oya take this..."
Muryarshi mai cike da fushi ha
ɗ
e da zafi ya cigaba da sauƙa wane aradu bisa kan su ba ita
ka
ɗ
ai ba hatta nurses da suka san shi sai da suka sha jinin jikinsu a take, wani irin shiru ne ya
ratsa
ɗ
akin kan takun sawayenshi suka amsa
ya isa ganganta riƙe da scapel (aska irin ta
likitoci) ya damƙa mata a hannu ya fusgo
ɗ
ayan da karfi har canular
ɗ
inta na fita daidai jijiyar
Wrist
ɗ
inta ya sa yatsarshi babba.
"Nan! Nan kawai za ki katse ki mutu idan sha'awar wutan Jahannama ne yake
ɗ
ibarki, ba
mutuwa kike ƙaunar yi kafura ki tabbata cikin azabar Allah ba? Oya yanke mana!!!"
A zaune take amma sai da tayi wani tsallen tsoro saboda tsawar da ya daka mata sai da ya
ka
ɗ
a 'yar hanjin ta.
"Haba Rayyan, yarinya ce don Allah ka bita a
hankali mana ka ga yadda duk ka firgitata?"
A zafafe yace
"Za ta ci kashi ne salim? Muddin ba za ta ci kashi ba to tabbas babu zancen yaranta a lamarin
ta sai tsagwaron iskanci da ƙarancin ilimin addini... Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci
m
afi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye
ne?"
Ita dai bata san a wace duniyar take ba don tsabar yadda take ka
ɗ
uwa bata sani ba a farke take
ko a sume ya juyo da figitattun idanunsa da basu yi mata kala
da na mutane ba ya zura mata
"To bari ki ji, idan ma ba ki sani ba ki sani idan ma kin sani danne sanin kika yi to gidahumar
kwakwalwarki ta tuna kuma ta yi hadda wutar Allah ya fi gaban wasa, kar ki zaci wannan wuta
da kuke girki da shi duk zafi da ra
ɗ
a
ɗ
in na wannan duniyar, duk irin hatsarinshi da in ya
ɗ
an
ta
ɓ
a ki za ki ihu sai da aka wanke shi sau dubu saba'in kan aka jefo mana"
Kanshi ya dafa yana wani jan tsaki mai tsawo saboda rabon da yayi magana haka ya manta,
amma dole ya ƙarasa don zuciya
rshi a tunzure take ji yake kaman ya faffalla mata maruka wa
ta fi shiga cikin damuwa da zata kashe kanta?
"Tabbas duk wanda yana musulmi ya kashe kanshi da gangan ya fita daga musulunci kuma zai
mutu ya kuma tashi ranar gobe a kafiri... Ƙarbar kaddara
mai kyau ko marar kyau na
ɗ
aya daga
biyar
ɗ
in cikacikan musulunci. Ki yi gaggawar tuba domin a yanzu haka kin nunawa ubangiji ba
ki da cikakkiyar imani ki kuma gode Allah we were there on time Nonsense…!
Wani irin rawa da jikinta yake ya sa tuni askar
ya zame ya fa
ɗ
i ƙasa yana ba da sautin
kwankwataraaaan, yadda kalamanshi suke fita a hautsine cike da zafi da
ɗ
aci mai tarin zallar
gaskiya haka su ke hautsina mata 'yar hanji suna ka
ɗ
a hantarta kuma suna shiganta ba da
wasa ba.
Tun da idanunta suka
sauƙa cikin nashi a karon farko ta yi saurin sadda nata ƙasa don ba za ta
iya ko da gangancin jurar ganin cikinsu ba, ganin tana shirin zubewa a sume ya sa salim damke
hannun Rayyan da har kaman zai rufeta da duka at any moment ya ce
"Calm down please
dude"
Ya maimaita kusan sau uku don ya san hayaƙin kan rayyan ba kowa ne ke iyawa dashi ba,
hatta shi karan kanshi wani lokacin shakkar shi yake saboda wani irin kwarjini da Allah ya zuba
masa na ban mamaki, bare wannan yarinya da rubdugun rayuwa yayi m
ata ƙatutu.
"Sister ku taimaka mata ko da allurar bacci ne samu ta huta ta kuma samu natsuwa please"
Salim
ɗ
in yayi directing kalaman to nurses
ɗ
in, da sauri suka shiga ƙoƙarin aiwatarwa don babu
wadda bai san Zafin kan Surgeon General Ryan Moh'd Kham
is ba, a lokacin da suka roƙi ta
kwanta ko uhmm bata yi ba ta miƙe flat zuciyarta har a lokacin tana jin shi a tsaye kyamm
tsabar tsoro.
Jan Rayyan da ke tsaye ya zubawa gini idanu yayi suka fice, ha
ɗ
ad
ɗ
en office ne mai cike da
ƙ
awa tamkar ba asibiti
ba suka shiga, fasalta kyau da tsaruwar office
ɗ
in bata lokaci ne sai wani
masifaffen ƙamshi yake fitarwa tare da sanyin Ac mai ratsa jiki. A doguwar kujera Brown mai cin
mutum uku salim ya mishi masauki, ya nufi chan dungu wurin wani tsararren frigde y
a bu
ɗ
e ya
ɗ
auko mishi ruwa masu sanyi ya taho ya miƙa mishi bayan ya
ɓ
alle murfin ba tare da yayi
magana ba ya kar
ɓ
a kaman fa
ɗ
a ya kafa kai, sai da ya shanye tasss kan yayi wurgi da goran
"I need some space Salim"
Maganan ya fito daga chan ƙasan maƙo
goronshi in ba ma salim
ɗ
in hankalinshi na kanshi ba ba
zai ta
ɓ
a cewa shine yayi maganan ba, dama kuma ya san za'a yi hakan dole ya fice ya barshi
nan yana zamewa kwance cikin kujerar Dukda tsawon shi ya zartawa kujeran nesa ba kusa ba.
Salim na fita
ɗ
akin ya koma ya janyo kujera ya zauna tare da tsura mata idanu, duk da ba zai
ƙ
ira ta kyakyawa ajin farko ba sai dai tana da nata qualities
ɗ
in na daban da ba kowa ke da shi
ba kuma da matuƙar wuya a same su wurin wata macen, baƙa ce amma baƙin mai hask
e tana
da doguwar tsiririn fuska da dogon hanci duk da idanunta ya musu kallo ne na tausayi don a
rine suke a kuma firgice zai iya ƙiransu manya kuma farare, girarta kaman ita ta zana yanayin
tsawon gashin idanunta da ma masu sheƙi irin na baƙaken Fulan
i dake kwance lublub bisa
goshinta za su tabbatar maka da cewa tana da tarin suman kai, bakinta kalar peach da ya ƙara
haskaka kalar skin
ɗ
inta ya amshi fuskartata.
Ta yi mishi yarinya kwarai da tunanin kisan kai, kuma ya tabbatar duk abin da zai saka
mutum
tunanin kashe kan shi ba ƙarami ba, ba zai ce ga iya adadin lokutan da ya
ɗ
auka yana
gwamutsa biyar da goma ba a kan matsalar yarinyar sai motsin ta ya ji, da
ɗ
an hanzari ya
mayar da hankalinshi kanta don dama tuntuni kallonshi na a gareta.
"S
annu 'yanmata kin farka?"
Tsura mishi idanu ta yi tana tariyo abin da ya faru a
ɗ
azu da sauri ta shiga dube dube tana jin
gudun zuciyarta na wani irin ƙaruwa ganin firgici a idanunta ya sa ya miƙe ya isa gangarta yana
furta
"Natsu 'yanmata dodon
ɗ
azu b
a ya nan, da ma matuƙar wuya ki sake ganinshi a gangarki."
Numfashi mai nauyi ta sauƙe duk da tarin tsoron da take ciki hakan bai hana kalamanshi na
ɗ
azu na sake bijiro mata ba, wani irin sanyin jiki da tsoron Allah na lullu
ɓ
eta a take ta fara tuba
ha
wayenta na
ɓ
allewa take furta
"Allah na tuba ya Allah! Wallahi na yi nadama Allah na san kana sane dani da kuma halin da
nake ciki ya Allah ka sassauta min, Allah ka ba ni ikon ƙarbar kaddara ta a yadda ta zo min
Allah ka yafe min..."
Sossai take kuka
har tana