Showing 123001 words to 126000 words out of 188614 words
ɓ
ata rai. Duk da yanda tai
ɗ
in sai bai damu ba ya kai zaune a bakin gadon sai dai nesa da ita ka
ɗ
an, koba komai yau ai ita
baƙuwarsa ce, ada bai kulata ba ma balle yanzun. Hannunsa ya kai saman goshinta, da zafi sosai alamar zazza
ɓ
i yau ma.
“Yau ma zazza
ɓ
in ne?”.
Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta
ɗ
aga masa kai kawai. Iska ya
ɗ
an furzar a hankali. Sai kuma ya ce,
“Tashi to kici wani abu sai kisha magani”.
Kalamar magani da ya ambata yasa kanta kawo wuta, cikin gamsuwa da dabarar data zo mata ta tashi zaune da ƙyar tana ƙara cin serious, sai da ta zauna sosai bayanta jingine da gadon sannan ta
ɗ
an kallesa ta
kauda idonta, ganin hankalinsa nakan wayarsa yasa taji ƴar nutsuwa dan bata ƙaunar kallo. Cikin ƙara dai-daita plan
ɗ
inta murya a karye ta ce, “Nifa paracitemol bayamin maganin zazza
ɓ
i”.
Ɗan
ɗ
agowa yay ya kalleta, sai kuma ya sake maida idon nasa
kan wayar yana fa
ɗ
in, “Sai wanne?”. Handbag
ɗ
inta da ke bedside drawer ta
ɗ
auka ta zaro wata takarda a bayan zip
ɗ
in ta miƙa masa. “Wannan shi nake sha in dai ina irin wannan zazza
ɓ
in, in ba haka ba bana warkewa da wuri”. Harga ALLAH bai kawo komai a ransa
ba tunda shi ba likita bane, dan haka ya amsa takardar, ganin rubutun Doctor ya sashi sake yarda. Sai kuma ya
ɗ
an kalli agogo, takwas da kusan rabi dare baiyi ba. Idanunsa ya maida kanta, ta janye nata da ke kallonsa a sace cike da basarwa. “Ya kamata kic
i wani abu to kafin na dawo ko?”. A
ɗ
an yatsine ta ce, “Karka damu har ka dawo.”
“Okay”.
Ya amsa mata yana miƙewa. Wani irin da
ɗ
ine ya ratsa Lulu kamar ta fasa ihu dan farin ciki. Wai yayama akai wannan dabarar baizo mata ba tuni take a wannan
bala'in. Zamewa tai ta kwanta tana murmushin da kakan da
ɗ
e baka gani ba akan fuskarta dan sai ta gadama take yi.
Napep ya samu ta kaisa har ƙofar pharmacy
ɗ
in data kwatanta masa ana iya samun maganin, koda ya basu takardar yaron saida ya kalle
sa, amma sai baice komai ba ya dai wuce wajen
ɗ
akko masa maganin. Koda ya dawo da maganin ya fa
ɗ
a masa ku
ɗ
in ya cire daga aljihu ya bashi. Napep ya sake samu ta maidashi gida. Yanzu kam sai da ya rufe ko'ina da
ɗ
aukar abubuwan da Ahmad ya siya musu sannan
ya nufi
ɗ
akin. Inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ta koma ta kwanta. Duk da taji sallamarsa bata motsa ba har sai da ya kai hannu ya yaye bargon data rufa har kanta. Jikinta har tsuma yake lokacin da ya fiddo maganin da ga leda mai tambarin pharma
cy
ɗ
in, amma sai tai ƙoƙarin kannewa.
“Yanzu mi zaki ci?”.
Ya fa
ɗ
a yana
ɗ
agowa ya kalleta. “Ni bana jin yunwa, naci abu tare da Mamy”. Ta bashi amsa idonta akan ledar nan dai. Bai san wa take cema Mamy
ɗ
in ba, sai dai yanda tai maganar cikin
serious ya sashi gamsuwa, sai kawai ya cire maganin biyu ya miƙa mata tare da goran ruwa. Bata musa ba ta amsa tasha. Sannu ya sake mata da tattare sauran maganin ya ajiye a bedside drawer da ruwan. Zamewa tai ta sake kwanciya da fa
ɗ
in, “Sai da safe”.
Murmushi ya
ɗ
an saki ƙasa-ƙasa. Dan ya fahimci korarsa akeyi. Baice mata komai ba ya tattare sauran ledojin ya fice yana rage mata hasken
ɗ
akin. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, sai kuma ta miƙe zumbur da raka bayansa da harara ta dannama ƙofar key sann
an ta dawo. Cikin rawar jiki ta fisgi ledar nan ta zazzage kusan ƙwayoyin maganin biyar a tafin hanunta ta afa a baki batare da ruwa ba. Sai da ta ha
ɗ
iye sannan ta
ɗ
auka ruwan ta kora ka
ɗ
an. Wani irin farin ciki take ji na samun kayan nan cikin sauƙi, sai
kawai ta fa
ɗ
a saman gadon cike da jisha
ɗ
i tai juyi ta sake juyawa........
✍
️
_(ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Wlhy irin masu
ɗ
abi'ar nan tausayi suke ban. Dan rayuwar kawai suke batare da sun san ina ta dosa ba, idan sukai nisa sai an dage k
afin su bari, ku ga dai, kwana biyu batasha ba amma ta koma kamar mara lafiya. Iyaye dan ALLAH mu ƙara dagewa wa ƴaƴanmu, mu bar aibata ƴaƴan wasu idan muka gamsu a irin wannan halin. ALLAH ka shiryar damu
😭🙏
)._
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN T
AUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay a
t
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
6
️
⃣
0
️
⃣
........Koda Smart ya kai kayan nan kitchen ya adana wanda za
i iya lalacewa a fridge sai ya nufi
ɗ
ayan
ɗ
akin kasancewar duk yasan sirrikansu, hasalima key
ɗ
in
ɗ
akin na hannunsa dan a rufe yake tun da aka gama shirya masa kaya aunty Saliha ta damƙa masa ko ƴan ganin gidan amarya babu wanda ya leƙa cikinsa. Shima nan
ɗ
in kayane lafiyayyu aka shirya, dan shine ma matsayin master bedroom. Ɗakin yayi ƙyau sosai, komai ya zauna a inda ya dace. Duk da gajiyar da yake ji bai kwanta ba sai ya zare rigarsa da ga shi sai dogon wandon da singlet ya nufi bathroom. Bai jima ba ya
fito da alamar alwala yayi, lafiyayyen carpet
ɗ
in gaban gadon
ɗ
akin ya hau dan yin salla. Sallar isha'i yay da shafa'i da wutri. Bayan ya idar yay zaman yin addu'a mai tsayi kafin ya miƙe. Har ya zauna a bakin gadon sai kuma ya miƙe, zuciyarsa ke ayyana ma
sa ya kamata ya binciketa ko tayi sallar isha'i, ya kuma duba ko zazza
ɓ
in ya sauka. Sai dai me, yana ta
ɓ
a ƙofar ya jita a kulle. Shiru yay yana kallon hannunsa da ke saman handle
ɗ
in, sai kuma ya
ɗ
age kafa
ɗ
unsa alamar ko oho ya juya
ɗ
akin da ya fito yay kw
anciyarsa dan barci yake ji matuƙa. Dan shi a tunaninsa ko Lulun tayi hakanne dan kar ya nema wani abu a gareta.....
_WASHE GARI_ koda ya tashi sallar asuba sai da ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ganin zai makara saboda ya tashi shima a ƙurarren lokaci y
a sashi ƙyaleta ya wuce. Ana idar da sallar ya dawo gidan,
ɗ
akin nata dai ya sake nufa ya ƙara knocking. Lulu da ke kwance a ƙasa ta bu
ɗ
e idanunta da sukai matuƙar nauyi da ƙyar ta iya miƙewa cikin takaicin damunta da ake tun
ɗ
azun ta nufi ƙofar ta bu
ɗ
e, d
an ta manta ma a ina take, dai da ta
ɗ
an jingina da ƙofar na wani ƴan sakanni sannan ta mur
ɗ
a key
ɗ
in ta bu
ɗ
e ka
ɗ
an. Da farko bai niyyar shigowa ba, dan haka yace da ita, “Kin tashi kinyi salla ne?”.
“Zanyi”.
Ta amsa masa cikin yanayin mu
ryar maye da tura ƙofar zata rufe dan abun bai gama sakinta ba. Da sauri ya riƙe ƙofar gabansa na fa
ɗ
uwa, bata da wani isashen ƙarfin dan haka ya samu nasarar shigowa. Yanda ya kafeta da idanunsa da suka ka
ɗ
a sukai ja a ƙanƙanin lokaci ya sata zabga masa h
arara itama da nata dake a juye ta bar masa wajen cikin
ɗ
an tanga
ɗ
i na rashin ƙarfi ta je ta fa
ɗ
a saman gadon a rufda ciki gashinta dake a hargitse ya lullu
ɓ
e fuskar tata gaba
ɗ
aya. (Ina ta samu abinda tasha?) Zuciyar sa keta kaikawo wajen son hasasowa amm
a iya hasashen ya auna a
ɗ
an tsukun lokacin baro gidansu zuwa nan hakan bamai yiwuwa bane, sai dai idan dama tana tare da abunta. Inda take ya ƙarasa ya
ɗ
auki handbag
ɗ
in ta gaba
ɗ
ayanta ya zazzage a saman gadon. Babu komai a ciki daya danganci ƙwaya, jakk
ar ya ajiye cikin furzar da iska sai idanunsa suka sauka kan ledar maganin jiya daya sayo mata, jawo ledar yay ya fiddo maganin, an ƙara
ɗ
iba kusan shida a ciki, ya tsirama maganin ido kallon da yaron pharmacy
ɗ
in ya dinga masa lokacin da ya bashi takardar
na dawo masa a rai da zuciya. Tabbas wannan maganin tasha. Kallonsa ya maida gareta ya zuba mata idanu kawai maƙogwaronsa na kai kawo a cikin wuyarsa da
ɗ
an sauri-sauri. Da ga ƙarshe ma sai ya tashi ya fice da ga
ɗ
akin kawai.....
_________________
___
★
Cikin
ɓ
acin rai yake dubansa ganin yanda yake neman haukata kansa. Gaba
ɗ
aya kwanakin nan baida wani aiki sai shaye-shaye tunda ya baro Kano. Ƴar ƙaramar robar giya da ke a hannunsa ya fisge cikin masifa. “Wai mi kake son maida kanka ne
kai kuwa MM? Akan mace! Ka zauna ka susuta rayuwarka. Tunda ka dawo da ga kano an kasa gane kanka, ka bar zuwa aiki ka barma fita a gidan nan gaba
ɗ
aya sai shaye-shaye, kana ganin hakan da kake shine zai baka damar samunta? Yarinya sai kace wata autar mata
ko hurul-ayni Mtsowww!!!”.
Murmushin takaici MM Atik ya saki sai kuma ga hawaye sharrrr. Ya miƙa hannu zai amshi ƴar robar giyarsa da abokin nasa ya kar
ɓ
e amma sai ya hanashi. Lips
ɗ
in sa ya ciza da ƙarfi da fa
ɗ
in, “Bazaka gane ba Asim, duk yanda
zan fa
ɗ
a maka bazaka gane ba. Aure fa sukai mata, aure da wani bani ba. Idan ban mallaketa ba zan iya rasa raina, ina matuƙar sonta da buƙatarta Asim, wlhy da gaske nake ina sonta da gaba
ɗ
aya zuciyata..”
“A haba gyara dai zancenka my man, kana d
ai sha'awarta. Kai har kasan wata soyayya ne. Ni yanzu Indai dan batun yarinyar nan ne ka nutsu dan ALLAH ka dawo hayyacinka. Ba igiyar aure ba ko
ɗ
aurin kabari sukai mata namaka alƙawarin sai ta dawo taka...”
Wani irin zuba masa ido MM Atik yayi, sai
kuma yay murmushi da lumshe idanunsa ya bu
ɗ
e a lokaci guda, “Asim karka yaudari kanka nima ka yaudarani. Kasan minene aure a ƙasar hausa kuwa?....”
“Mtsoww kafin wannan zamanin yake wani abu a ƙasar hausar, amma a yanzu bana jin wasu matan na tuna
matsayin auren, dan ajiyesa suke su shigo barikin ko ƴammatan basu kaisu iskanci ba. Balle ma ita munada hanyoyi kala-kala na kamata a tafin hannunmu. Ko an fa
ɗ
a maka wani son auren take, to nayi bincike mai zurfi na gane komai har ma yanda aka ƙulla auran
. Kai dai kawai ka dawo a hayyacinka kasha labari”. Ya ƙare maganar yana tattare sauran kwalaben giya da su cigarette da shisha da MM Atik
ɗ
in ya baza, sannan ya zo ya kamashi ya kai toilet yasa a ƙarƙashin shower ya sakar masa ruwa. “Malam yi wanka ka cir
e wannan dattin sai warin hayaƙi kakeyi”. Daga haka ya fice ya barsa.
_____________
★
Da mamaki Ammah ke kallon Umma da ke faman murmushi riƙe da basket irin na saƙar kaba
ɗ
in nan mai ƙyau shaƙe da kulolin kayan abinci wai karin kumallo
ta shirya za'a kai gidan Smart. Umma data fahimci Ammah zata iya bata matsalafa sai ta sake fa
ɗ
a
ɗ
a fara'arta da katse mata tunani da fa
ɗ
in, “To kodai banyi dai-dai bane Hafsatu? Dama dai ganin haka akeyi a gidan washe garin da yaro ya tare da matarsa shiyy
asa, kuma kinga dai ai ba'a barki da ha
ɗ
a abinci ba duk gamu cike da gida ko, sai dai kuma naga kamar hakan bai miki ba”.
Murmushi Ammah tayi da
ɗ
an girgiza kanta. Cikin nutsuwar nan tata ta ce, “Ko
ɗ
aya ba haka bane Umman Nasiba, naga kawai an sak
aki aiki ne tunda safen nan....”
Caraf Umma ta amshe da fa
ɗ
in, “Yo minene ALLAH na tuba. Ai an riga an zama
ɗ
aya. Hydar a gidan nan kuma ai ya cancanci fiye da haka. Shi ka
ɗ
aine yaron da bai gajiyawa wajen binka har cikin
ɗ
aki ya gaisheka kullum kuma
cikin girmamawa da mutuntawa. Bari kiga Huwaila ta miƙa musu tunda tace zata gane gidan lokaci na ƙara ja”.
Murmushin ƙarfin hali kawai Ammah ta saki da fa
ɗ
in, “To ALLAH ya saka da alkairi”.
Umma ta amsa da “Amin”. tana ficewa
“Anya
wannan al'amarin Hafsatu ba akwai wata a ƙasa ba. Matar da tunda aka fara bikin nan ta kasa
ɓ
oye hassadarta ce zata girka abinci akaima Babangida kuma a barta?”. Addah Rukayya ce mai maganar cikin jimantawa. Kafin Ammah tace wani abu Gwaggo Sa'adah ta fit
o a
ɗ
aki ita da Addah Suwaiba. Har rige-rigen fa
ɗ
in, “Wannan yaudara ce akwai wata a ƙasa” suke su biyun. Adda Suwaiba ta cigaba da fa
ɗ
in, “Babu ma wani batun ai mata kawaici magana ta gaskiya fa, kawai a dakatar da su ba ga Hawwah can na musu girkin ba sh
i kuma ai yaya da shi?. Matar da bata ta
ɓ
a ƙaunarki ba tun da jajayen sawu sai yanzu ne zata ƙaunaceki Hafsatu, ai daga ji ma kasan akwai ƙulunboton data shiryama abincin. Ita idan yaran nata sunyi auren barinku take ku girka abinci ku aika musu ko sai ke,
naga Yalwati ma ta aurar da yara maza har uku a gidan nan ai batai mata hakan ba dan tasan bama yarda zatai ba sai ke sarkin kawaici”.
“Addah ni a ganina ku barta, idan ma wani sharrin take nufi ai ALLAH bazai bata nasara ba. Ballema ni sai nake
ga kawai dai tayi hakane saboda tujarar da malam yay mata jiya da dare”.
Gwaggo Sa'adah ta ce, “Humm Addah kenan. Yau ya fara mata tujara ne da har hakan zai sakata saduda. ALLAH ki yarda ke dai akwai wani abu a ƙasan kawai. Bakuma zamu gane hakan ba
sai anje ankai musu abincin sun cutu mudawo muna dana sani”.
Duk da zuciyar Ammah ta sake raunana sai bata iya sake cewa komai ba, sai ƴan uwan natane ke cigaba da tattaunawa dan na cikin
ɗ
aki ma duk sun fito. Gwaggo Sa'adah ce ta nufi kitchen in
da Hawwah ke girka karin kumalon da za'a kai gidan Smart. Cikin sa'a ta iske ta kammala tana kan zubawa ne. “Yauwa kin ha
ɗ
a ne Hauwa'u?”.
“Eh Gwaggo” cewar Hawwah. Gwaggo Sa'adah ta ce, “Yauwa to sannu, bara na turo su Asma'un suyi su tafi rana nayi
”. Da ga haka ta juya ta koma. Ƙwafa Umma dake leƙarsu ta window tayi, jitake kamar ta fito ta shaƙe wuyar Gwaggo Sa'adah. Oho dai tata ƴar aiken ai harta wuce. Kafin kuma su isa ta tabbatar Hydar da matarsa sunci nata abincin. Tai wata ƴar dariyar gatsa-t
sa tana barin window
ɗ
in har
ɗ
iyarta Ismaha na kallonta. Amma sai ta basar dan tasan wacece Ismaha da
ɗ
an banzan jan wa'azin tsiya.........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?
,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai ka
tura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧
𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
6
️
⃣
1
️
⃣
........Ƙarfe kusan tara Lulu ta tashi da ƙyar a dalilin ka
ɗ
awar alerm
ɗ
in ƙaramin agogon da ke a side drawer
ɗ
inta da ya
gallabeta tun takwas. Amma nauyin