Showing 162001 words to 165000 words out of 188614 words
da ba'a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo
ɗ
aya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart
ɗ
in suka
shigo da tace yaje ita zata je
ɗ
akin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko'ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai
ɗ
akin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta b
ata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji da
ɗ
i tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya ha
ɗ
a Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyew
a. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji da
ɗ
in wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep
ɗ
in
ɗ
an anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda m
a zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep
ɗ
in suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa,
inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi ci
kin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke
ɗ
akin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa
da magana ko tsokana ne yake
ɗ
an murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada
a Napep muke fa, babu da
ɗ
i mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.
A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jika
r Garko family a garin nan da hawa Napep...”
Yanda Dadan ke maganar a zafafe da
ɗ
aga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin
ɓ
ata fuska amma ta dakatar da ita........
✍
️
_LABARAI
MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu
600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR C
HOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
7
️
⃣
8
️
⃣
.......Itama dakatar da itan abinda ta
i niyyar sake fa
ɗ
an da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai
ɓ
ace. “Wai miye haka kuma ban son ƙaranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”
Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka
iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama'ar
ɗ
akin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman ta
ɓ
e baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna
ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin da
ɗ
in jiki Baba ya balbale Dada da fa
ɗ
a, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki.....
Lulu tata satar kallon Smart da
tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya bu
ɗ
e musu suka shiga, gaba
ɗ
aya kayan na'a hannunsa har handbag
ɗ
inta ma. Har
ɗ
aki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya ba
rta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji da
ɗ
in abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataj
e sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata
ɗ
ayan nan bazata so a wulaƙantashi ba dan itama dai da taje gidansu ba'a wulaƙantatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.
Shima a can wanka
n ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya za
ɓ
i shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai ta
ɓ
a wulaƙantata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa'i da wutri yayi sannan ya fi
to. Shayi ya ha
ɗ
a a kofi biyu ya nufi
ɗ
akin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta ƙurama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke
ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana ha
ɗ
iyar busashen yawun daya tokare maƙoshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo ƴar saman rigar data ajiye gefe ta
ɗ
ora
akan wadda ke jikinta dan ƙarama ce ma da ka
ɗ
an ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miƙa mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciy
a da fa
ɗ
in, “Thanks.” kansa kawai ya
ɗ
an jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da fa
ɗ
in, “Kayi haƙuri da abinda Dada tayi, ni ban fa
ɗ
a mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da fa
ɗ
a ne sosai”.
Murmushi yay a karo na f
arko, sai kuma ya
ɗ
an kafeta da idanunsa da suka canja launi ka
ɗ
an. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi fa
ɗ
a kenan?“. Hararsa tayi da
ɗ
an murgu
ɗ
a baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban
ɗ
auki abinda tai
ɗ
in komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya
ɗ
an tattara mata game da case
ɗ
in yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smar
t tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiƙe. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai
ɗ
in ba ta
ɗ
ago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido
ɗ
aya. Sai ya samu kansa da sakin murmu
shi yana mai lumshe idanunsa.
Komawa tai ta zauna da fa
ɗ
in, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da
ɗ
akko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu dai
daiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma ƙasan maƙoshi, tare da fa
ɗ
a mata dokokinsa akan yanda yake buƙatar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har ƙasa ya sata dubansa
cikin tura baki ta ce.
“Hijjab har ƙasa? Ni ce zan saka hijjab har ƙasa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure ba
ne balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a ƙarƙashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunt
a juna. Ni harka ma
ɓ
atamin rai na”.
Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tash
i tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buƙatar abinda zai
ɓ
ata mata farin cikin data samu yau a wajen ƴan uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana fa
ɗ
in (akwai ƙura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitan
e da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai....
WASHE GARI ta tashi da
ɗ
okin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case
ɗ
in nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban ƙamshi take zubawa dan
ta baza turaren nata. Tana ƙoƙarin
ɗ
aura igiyar takalmanta ya shigo
ɗ
akin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har ƙasa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin ƙofar ya jingina tare da har
ɗ
e hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu kawai. Ƙ
in
ɗ
agowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta
ɗ
ago
ɗ
in ma kallo
ɗ
aya tai masa ta
ɗ
auke kanta tana miƙewa. Da ga sama har ƙasa ya sake ƙare mata kallo. Yayinda ita kuma ta ƙarasa tattare kayanta ta nufo ƙofar kanta tsaye. Kallonsa t
ai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.
Maimakon amsa mata sai ya
ɗ
an kauda idanun nasa a kanta ka
ɗ
an batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take bu
ƙ
ata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da
ɗ
an kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.
Cikin husky voice ya ce, “Idan baƙyason rasa shari'ar ko makarar go and change your dresses. Na fa
ɗ
a miki duk abinda
bakina ya furta shine nake buƙata kuma bana canjawa da ga ra'ayina akan duk abinda na riga na tsara.”
Cikin
ɓ
acin ran da ya fara yunƙuro mata ta ce, “Aliyu!!...”
Hannu ya
ɗ
aga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and
vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buƙata to bana buƙatar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.
Jitai jiri ma na neman kamar
ɗ
ibarta. Amma sai batace k
omai ba tai masa wani irin kallo mai ƙunshe da abubuwa masu yawa ta juya kawai ta ajiye kayan hannunta a saman gadon. Komawa tai wadrobe ta
ɗ
akko hijjab zata saka kawai, amma sai ta tsinkayi muryarsa yana fa
ɗ
in, “Kayan duk zaki canja zuwa wasu, bana son wa
nnan turaren kuma idan zaki fita, idan zaki saka a gida fine ko zakiyi wanka da shine ba babu damuwa a gareni. Sakawa a fita ne dai bana so dan haramunne ma a gareki ba fa
ɗ
a ta bace.” bata tanka masa ba, sai kayan data
ɗ
auka ta nufi toilet dan taga baida a
lamar fita, ita kuma taci alwashin bazata kulashi ba a yanzu saboda abinda ke a gabanta. Tsaf ta sake shiryawa cikin wasu kayan ta saka hijjab
ɗ
in ta fito, sai ya samu kansa da kafeta da ido. Dan tayi ƙyau matuƙa a cikin hijjab
ɗ
in fiye da waccan ranar. Sh
i da kansa ya
ɗ
ibar mata kayan yay gaba tabisa a baya tana taunar lips na danne masifar dake cimata zuciya. Baya ya ajiye mata kayan tare da miƙa mata hannu alamar ta bashi key
ɗ
in motar dake hanunta.
Rai a
ɓ
ace ta ce, “Bana buƙata”.
“Kema kin san a
ikina ne ai hakan”. Ya fa
ɗ
a babu wasa shima a tattare da shi. “Aina fa
ɗ
a maka na kore ka”.
“Ban koru ba, dan bake kika
ɗ
auke ni aiki ba ai ko”. Ya sake bata amsa a dake yana zare key
ɗ
in tare da jan hanunta ya tura ta kujerar kusa da driver ya maid
a ya rufe. Zagayawa yay shima mazaunin drivern. Koda yaje gaban gate sai da ya fita ya bu
ɗ
e sannan ya zo ya fita da motar ya sake komawa ya rufe gidan sannan. Tunda suka
ɗ
auki hanya babu wanda ya tankama wani, gara shi ma ya miƙa mata ƙaramin flaks da ya h
a
ɗ
a mata tea a ciki. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tana harararsa. Murmushi kawai yay batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga tuƙinsa. Kai tsaye office ya kaita, inda suka samu abokan aikinta suna tsaiwar jiranta duk da safiya ce sosai. Mota
r na shigowa suka shiga mata marhabun su Zainab na mata spry da ƙyalkyali mai ƙamshi da ga sh
i har ita. A take aka shiga musu murnar auren. Kamar yanda ya dake yana amsawa itama sai ta dake tana amsawa. Sunci kusan mintina goma a wajen kafin Zainab ta kwas
hi kayanta suka wuce office, shi kuma sai ya fito bayan sun
ɗ
an yi magana da security
ɗ
in nan da a yanzu suka saba sosai ya samu napep ya shiga ya koma gida.........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilk
isa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyay
enmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
7
️
⃣
9
️
⃣
.......Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da z
aman shari'ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta
ɗ
an ta
ɓ
a aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security
ɗ
in nan ya dannama Smart waya ya sanar ma
sa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep
ɗ
in. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa'id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart y
ay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da ƙyar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haƙora. Fuska ta yamutse cike da izz
arta ta ce, “Sanar mata tana da baƙuwa”. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.
Kallon gidan ta dingayi side by side tana ta
ɓ
e baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa
'id
ɗ
in ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani