Showing 15001 words to 18000 words out of 188614 words
jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa
, cikin sa'a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur'ani kiran ya shigo, cike da zumu
ɗ
i Asma'u da wayar ke'a gefenta ta ce, “Lah Yaya ne”. Kallonta Ammi da Maryam
ɗ
in duk sukayi, ita kuma ta
ɗ
aga da sallama. A hankali ya amsa
mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da fa
ɗ
in, “Zan samu ruwan zafi a wajenku?”.
“Eh Yaya”.
Ta amsa masa cike da girma
mawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, “Ya dawo ne?”. Kai ta
ɗ
aga mata da fa
ɗ
in, “Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyi”. A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke'a
tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baƙar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan ƴaƴanta idan yana fa
ɗ
a haka yanzu ma ta ha
ɗ
iye
, sai da ya gama ta bashi haƙuri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuƙar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana
ɗ
aki amma suka samu baya nan
ɗ
akin ma a bu
ɗ
e, neman number sa ta shiga yi amma sai ba'a
ɗ
aga ba, daga ƙarshe
ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma'un.
Koda Asma'u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga,
ɗ
akin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar mag
riba yay tashi a
ɗ
aki sannan
ya fice massalaci yin isha'i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk
ɗ
akunan matan gidan ya gaidasu. Da
ɗ
akin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai ya
wan fara'a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa'anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake
sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda ƙaramar tazo jikinsa tana kawo masa ƙarar
ɗ
an uwanta dake bima babbar
ɗ
akin nasu cewar ya karya mata pencil
ɗ
inta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, “Ya
yanmu ƙarya take ita ta karya abunta a makaranta suna fa
ɗ
a da Ameer. Kuka ta saka itama tana fa
ɗ
in, “Ƙaryane Yaya shine”. Hannu ya
ɗ
aga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, “Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun
ɗ
azu suke rikicin nan ni harna gaji ma da magana”.
Fa
ɗ
a yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo
ɗ
akinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa
ɗ
akin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan ƴ
aƴa a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran ƴammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a
ɗ
an fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba a
utarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miƙewa. Dakatar da shi Umman tayi da fa
ɗ
in, “Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?”.
Ɗan murmushin ƙarfin hali yay mata da fa
ɗ
in. “Ba komai Umma na fitane da safe sosai
wani uziri”.
“Uhhm to yayi”. Ta fa
ɗ
a a taƙaice.
Iska ya
ɗ
an furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa
ɗ
anta na hu
ɗ
u kawai ya
samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur
ɗ
in yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi
yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya.
“Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kanka”. Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana ƙunƙuni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da ƙarfi.
Ammah na zaune
su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa a
binci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da
ɗ
auke kai ta ce, “Lafiya ka fita tunda safe?”.
Samun kansa yay da fa
ɗ
in, “Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne”.
A han
kali ta sauke numfashi. “Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka kar
ɓ
i rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowan
e bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar
ɗ
awainiya da ku tun kuna ƙan
ana har girmanku, bai tauye kowannenku ga
ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe id
anunmu”.
Gaba
ɗ
aya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gya
ɗ
a kai da tausasa harshe ya ce, “Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu
'a”.
“Addu'a kullum cikin yimuku muke babu fashi”.
Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da
yay shafa'i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope
ɗ
in nan ya
ɗ
akko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa
ɗ
auke da rubutu mai
ɗ
an tsaho, abubuwan da aka rubuta
ɗ
in ya matuƙar bashi mamaki harma ya r
asa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya fa
ɗ
a to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Taka
rdar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci......
_______________________
★
Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa a
kan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf
ɗ
in ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za'a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kan
su. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf
ɗ
in yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya
ɗ
aga mata ya
ɗ
auke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?.
“A'a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy.....”
Bata gama ru
fe baki ba sai gashi ya fito kamar a
ɗ
an rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya bu
ɗ
e masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart
ɗ
in shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya
ɗ
akkoma
key yay masa sallama. Juyowa yay ya
ɗ
an kallesa, har ya
ɗ
auke kai sai kuma ya sake jiyowa.
“Alhamdullah” ya fa
ɗ
a yana miƙo masa key
ɗ
in batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key
ɗ
in, dannawa yay motar tai ƙara, d
an haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya bu
ɗ
e masa yaga ya bu
ɗ
e gaban motar ya shiga yana fa
ɗ
in, “Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ru
ɗ
ewa irin haka ba ƙarami bane ba”.
Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba
ɗ
aya ba.........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSA
N SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibra
him Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
VIP
🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*T
HANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenku
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
🔟
........Ko parking bai gama yi da
ƙyau ba Uncle Yousuf
ɗ
in ya fice, ba'a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito
ɗ
auke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya bu
ɗ
e masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da
ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA'S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya
fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin.
Duk wani kai kawo da ake a kanta shi dai nashi ido ne. Yayinda acan ƙasan zuciyarsa yaketa tufƙa da warwara akan abubuwa da dama. Musamman akan a
binda ya dawo da shi aiki cikin wannan family
ɗ
in a karo na biyu. Tabbas ya amshi aiki, sai dai kuma bada manufar wanda ya bashi aikin ba. Dan ko ka
ɗ
an baiji wani kurari daga garga
ɗ
insa sun tsoratashi ba. Hasalima shi wanda ya bashi aikin da yasan shi
ɗ
in
wanene maybe dabai bashi
ɗ
in ba. Amma zaiyi, dan in bai amsa ba zai bama wani da zai iya masa yanda yake so... Ringing
ɗ
in wayarsa ne ya katse masa tunani, ya ciro wayar daga aljihu yana miƙewa ya fito. Sallama yay bayan yakai wayar kunnensa, daga haka bai
sake magana ba sai saurare. Bayan ya katse kiran ya cire wayar a kunnensa yana furzar da iska ka
ɗ
an. Cike da iya nazari yake bin farfajiyar asibitin da kallo a kaikaice, can idonsa ya sauka akan abinda yake nema. Basarwa yay ya share na wasu mintuna, kafi
n ya nufi fita gate
ɗ
in a nutse. Dai-dai inda almajirai ke zaman bara ya dakata, naira
ɗ
ari biyu dake aljihunsa ya ciro ya saka a kwanon barar wani gurgun almajiri dake kan katako mai tayu, almajirin ya shiga jera masa addu'a. Yana ƙoƙarin juyawa matashin
saurayin dake gefensa ka
ɗ
an yazo ta gefensa suka bangaji juna, kallon juna sukai kamar cikin jin haushi. Sai dai shi saurayin yay saurin fa
ɗ
in, “Yi haƙuri abokina ban lura bane ba”. Kai kawai ya ka
ɗ
a masa yabar wajen batare daya tanka ba.
Maimakon k
omawa cikin asibitin sai ya samu waje a harabar ya zauna abinsa, can kusan mintuna uku yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu sai yaji takardar da saurayin nan ya saƙala masa a aljihu sanda sukai karo batare da ya lura ba. Zarota yay ya warware cike da mamaki,
sai kuma ya shiga
ɗ
an waige-waige amma babu alamar saurayin ko wani da zai ce hankalinsa a kansa yake.
_“Ni kamar iska nake, a duk lokacin data ka
ɗ
a sai anji sautinta a dukkan ƙofofin gashi na jiki. Idan kuma nai shirin zuwa waje matsayin guguwa
tarwatsa komai da kowa na gari nake hatta ruwan kogi baya tsira da ga mamayata. Ka kula, in ba hakaba ni na ƙulleka a cikin ƙullina Aliyu Hydar Mawashi”_.
Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi na
ɓ
acin rai. A take zuciyarsa ta fara kaikawo da saur
i-sauri cikin ƙirjinsa. Takardar ya ninke ya maida aljihu, yana batun tashi waya ta sake yin ringing a jikinsa. Wayar dai da Alhaji nan ne ya bashi jiya, yana kuma ƙyautata zaton takardar nan ma da ga garesa take duk da ya kirashi ne
ɗ
azun a wayarsa. Shi s
am yama manta da wayar. Cirota yayi daga aljihun, kamar bazai
ɗ
aga ba sai kuma miya tuna ya
ɗ
aga tana gab da tsinkewa ya kai kunne. Baiyi magana ba daga can ma akai shiru, ganin ana neman shafe minti guda ya katse shirun da fa
ɗ
in, “Inada abinyi fa Malam”.
Ƙaramar dariya akai daga can tare da fa
ɗ
in, “Wannan girman kan naka da gizago kesani ƙara jin ka dace da buƙatar aikina Smart Mawashi. Mutanena sun sanar min ka koma aiki, weldone daka kasance mai biyayya irin haka da saurin gane abu....”
“Na koma ne badan kurarinka ko farfagandarka ba! Ko a tunaninka sakawa ana bibiyata da kawomin wasu banzayen saƙwanni a takarda ko kiran wayata zaisa nayi abinda kake so?”.
Ya fa
ɗ
a cikin katseshi murya a dake. Dariya akayi da ga can, Alhaji ya ce, “M
u
ɗ
auka haka
ɗ
inne to. Sai dai ka sani ni samaniya ne mai rufe rufin kowanne gida da daji. Abinda kaga ya faru har ya kawoku asibiti yau ka
ɗ
auka shine signing na contract
ɗ
inmu da kai. Ya rage naka ka fara aiwatar da ayyukanka yanda ya dace ko kai kuskuren
nunamin zafin kai na cigaba da nuna maka sauran kalolina. Dan a duk inda Jiƙamshi family suke ni nan da kake ji da gani zagaye nake da su har a cikin
ɗ
akin kwanansu, har ma da kai kanka a yanzu....”
Baki ya bu
ɗ
e zai yi magana ƙittt aka yanke wayar,
da sauri ya cirota daga kunnensa, ƙoƙarin kiran layin ya shigayi sai dai yaƙi shiga, ya koma wajen massage danya tura sai ya gama babu app na massage a wayar kwata-kwata. Cikin tsarguwa ya
ɗ
an fara dube-dube, sai dai babu alamar wani da hankalinsa ke a kan
sa a eriya
ɗ
in wajen gaba
ɗ
aya. Wayarsa ya ciro ya kwashe number da zummar yin kira sai dai kuma taƙi shiga, wadda aka kirashi a farko ya gwada kira itama taƙi shiga. Yay
ɗ
an shiru ransa a dagule, tunanin kiran wani abokinsa yay da zummar masa tracing layu
kan sai kuma ya fasa saboda tuna maganar mutumin. (A duk inda kake idanuna a kanka suke koda a cikin
ɗ
akin barcinka ne). Fasawa yay ya maida wayar aljihu yana jin zuciyarsa ta masa nauyi da tunani kala daban-daban.
Gaba
ɗ
aya wannan yinin haka
ahalin Jiƙamshi gaba
ɗ
aya suka yisa a asibitin tare da shi. Bai yi yinƙurin komai akan son sanin abinda ke damunta ba. Yana dai biye da motsin kowa har zuwa azhar da Uncle Yousuf ya buƙaci ya kaishi gida zai
ɗ
an