Showing 135001 words to 138000 words out of 188614 words
da Mawaddat, dan ba wai tsantsar soyayyar bace ba kawai. Abu na biyu tausayin rasa mahaifiyarta tana la
ɓ
u
ɓ
uwa ma ya taka rawar gani a kansa. Kin san mu maza munada wani abu akan ƴaƴan mu musamman idan ya kasance mahai
fiyar yaro bama tare da su, sai mu dinga jin wadda ke riƙe da su zata cuta musu ne kawai. Shiyyasa zakiga maza da yawa suna samun sa
ɓ
ani da matansu akan ƴaƴan da uwarsu ta fita a gida, kota rasu ta bari.”
“To haka
ɗ
inne kuma. Amma inaga ya kamata
ace munsan abinda yake
ɓ
oye manan ko hakan zaisa mu fahimcesa”.
“Karki damu zamu sani, lokacin mu sani
ɗ
inne dama baiyi ba, ina kan bincike yanzu haka ma”.
“To Alhamdullah ALLAH yasa muji alkairi.”
Da Amin ya amsa mata, da ga haka suka c
igaba da tattauna al'amarin Daddy
ɗ
in har zuwa wani lokaci kafin tai musu sallama ta koma gida. Ta samu Daddy na ramuwar barci da ya gagara yi daren jiya, bata tashesa ba har sai da ya tashi da kansa sannan ta labarta masa abinda ya sakasa nutsuwa kamar ya
nda suka tsara da Uncle Yousuf. Murmushi yay da fa
ɗ
in, “Ashe yaron nan nada hankali har haka”.
Dariya Mommy tayi kawai batace komai ba. Shima sai bai sake bi takanta ba ya tashi ya shige bayi fuskarsa ƙawace da murmushi...
__________
★
Gab da Azhar Smart ya tashi a barcin da yay, yaji da
ɗ
in yin barcin kuwa sosai, dan haka ya watsa ruwa da
ɗ
aura alwala yasa jallabiya ya fice massalaci batare daya nema Lulu ba. Sai da aka idar da salla ya dawo gidan sannan ya nufi
ɗ
akinta. Baccinta t
ake hankali kwance, beauty face
ɗ
inta ta sake yin wani fayau kasancewar babu
ɗ
igon kwalliya, hatta lips
ɗ
in ma yanzu babu ko lipgloss
ɗ
in a jikinsa. Samun kasan yay da tsira mata idanun nasa na tsawon mintuna, tabbas ita
ɗ
in ƙyaƙyƙyawace, sannan tana cikin
jerin mata masu tsananin kula da jikinsu ta hanyar gyarashi kwaf-kwaf a kowane motsi. Ga izza da gayu da duk wani cikakken namiji bai isa mata kallo
ɗ
aya ya
ɗ
auke kansa ba, “Sai dai akwai kau
ɗ
i da masifa kuma ba” ya fa
ɗ
a a fili yana
ɗ
an ta
ɓ
e baki da ƙaras
awa gaban gadon ya tadata. Idanunta ta bu
ɗ
e a hankali ta saukesu kansa. Yanda ya
ɗ
an ranƙwafo kanta ya sata zabura, dan yanayin ya mata kamar wani abu da ya shu
ɗ
e a baya. Tashi yay shima tsaye da kyau yana girgiza kansa. Fuska ba wasa ya ce, “Tashi kiyi sa
llah”.
Harararsa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda yanda yay masifar kafeta da idanunsan nan da bata ƙaunar ya zuba mata su, dan duk wani ƙarfin gwiwar ta sai ya sare taji komai ya kufce mata. Dama fitsari take ji dan haka ta sauka a ga
don tana wani yamutse fuska ta nufi bathroom
ɗ
in. Sai da ya bata
ɗ
an lokaci sannan yabi bayanta, anyi sa'a kuwa zata fara alwala.
“To alwalan ma a gabanka zanyi?”.
“Haka ya kamata, ya kuma dace, dan hakki ne a kaina sanin ibadarki da komai
naki a yanzun”.
“Kai a wa?”.
“Mijinki”.
“Kana son shigarmin rayuwa da yawa”.
“A ciki nake tsunduma ma ai”
“Mafarki kenan”.
“Ni da ke duk a ciki muke, mai rabo a cikinmu sai ya fara farkawa ya fuskanci reality. Yi alwala l
okaci na tafiya”.
“Al....”
Sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda tuno abinda ya faru
ɗ
azu a
ɗ
akinsa saboda fa
ɗ
ar sunan nasa. Sai kawai ta
ɓ
ige da maka masa harara cikin ƙunƙuni ta furta “Zan koya maka hankali sannu-sannu”.
Duk da yaji bai
tanka ba, dan ya gaji da magana haka nan. Itama sai tai ƙwafa ta juya ta fara alwala. Shi dai yana kallonta harta kammala zata miƙe ya ce, “Dakata. Mawaddat ba haka ake alwala ba sam. Akwai kura-kurai matuƙa a cikin wadda kikayi. Dan haka ina son ki bani h
ankalinki nan duk abinda nayi kiyi, yanda ake alwala shine. Da farko yin niyya a zuci sannan ki ce Bismillahi, sannan ki wanke tafukanki na dama da na hagu kowanne sau uku. Sannan ki
ɗ
ebo ruwa ki kurkure bakinki ki zubar da ruwan sau uku. Sannan ki
ɗ
ebo ru
wa ki shaka a hanci ki fatar shi ma sau uku. Sannan ki
ɗ
ebo ruwa ki wanke fuskarka gaba
ɗ
ayanta sau uku, ki lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinki har izuwa karkashin ha
ɓ
arki, wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a fa
ɗ
i kuma tun da
ga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu. Sannan ki wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima sau uku. Sannan ki
ɗ
ebo ruwa ki yi shafar kai wato a tafin hannu ki shafo tun daga farkon goshi har ki kai ƙeya sannan ki sake
dawowa farkon goshi. Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu. Sannan ki wanke ƙafafu na dama da na hagu tun daga tafin ƙafa har izuwa gwiwar ƙafa. Ina fatan kin fahimta, amma zan fara sai kiyi duk yanda zanyi”.
Batace komai ba, sannan bat
a nuna zata ƙiyi ba. Dan ita dai tun maganarsa ta
ɗ
azun akan mahaifiyar ta ya matuƙar sanyaya mata jiki, tsaf ta dingayin yanda yake yi har suka kammala, har cikin ransa yaji da
ɗ
in rashin gardamarta a wannan ga
ɓ
ar. Dan haka ya
ɗ
ora da fa
ɗ
in, “Akwai addu'a
bayan kammala al'wala. Zan koya miki ita bata da wahala bata kuma da tsaho, sai dai ba yanzu ba sai na kammala shirina akan hakan. Muje kiyi sallarki”.
Komai batace masa ba yanzu ma tai wucewarta ta fita shi kuma yabi bayanta yana jin wani kaso na
takaicin abinda ya faru daren jiya akan sayen magani na raguwar masa a zuciya. “Yanzu bamu da isashen lokacin da zan miki filla-filla akan yanda ake salla, amma zan nuna miki ka
ɗ
an a ciki kafin mu fara karatu na musamman akanta.” bai damu data amsa ba ya
shiga nuna mata da fa
ɗ
a mata abinda zata iya fahimtarsa a yanzun, nan ma dai batace komai
ɗ
in ba har ya kammala ya bata izinin kabbara sallarta. Da ga haka ya samu waje ya zauna yana kallonta har ta idar. Ya dubeta zaiyi magana game da addu'a ganin har ta
miƙe da ga sallamewa kira ya shigo wayarsa. Ahmad ne, dan haka ya
ɗ
aga yana kaiwa kunne. Shaƙiyanci sosai Ahmad ke masa da ga can, har sai da ya sashi furta, “Ɗan sa ido ina ruwanka to. Kai ni karma kazo min gida ka tsaya nan nazo na sameka mu tafi”. Ƙaram
ar dariyar da ta saka Lulu kallonsa yayi ka
ɗ
an saboda jin abinda Ahmad ya fa
ɗ
a da ga can. Sai kuma shima Smart
ɗ
in da ya miƙe zai fice taji yana furta, “Irinku ne masu takurama sabbin aure da zarya har sai an cinye kayan gara da k....” daga haka ya fice ba
ta ƙarasa ji ba. Baki ta ta
ɓ
e ka
ɗ
an da ajiye sallayar tana sauke ajiyar zuciya da bata san dalili ba, da ga haka ta ajiye batunsa tai zaman dirshen a kan gado ranta fal tunanin cases
ɗ
in dake gabanta. Dole ne ma gobe idan ALLAH ya kaimu ta fita office, kwa
na kusan tara yau fashin yayi yawa ai haba. Bata sake jin motsin Smart ba har sai da Mubarak ya kawo abincin rana. Lokacinne ya shigo
ɗ
akin cikin shirinsa da alama fita zaiyi dan yaci wani faran shadda ƙal harda hula baƙa, ƙamshi yake mai sanyi ya fito a a
ngonsa dai kai tsaye. Da ga bakin ƙofa ya dakata yana fa
ɗ
in, “Ga lunch can an kawo ni zan fita su Ahmad na jirana”.
Baki ta ta
ɓ
e kawai batare da tace komai ba. Shima sai bai sake cewa koman ba ya juya yay ficewarsa dan ya fahimci ƴan izza da masi
far ne yanzu a kanta. Shi kuma bashi da wani isashen lokacin biye mata a yanzun..........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan kati
n waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
6
️
⃣
6
️
⃣
........Ya samu su Ahmad na jiransa a ƙofar gida shi da wani cousin brother
ɗ
insa babban fan
ɗ
in Smart akan ball, da yake kusan sa'ansu ne shima sai suke zumunci sosai duk da s
hi Smart
ɗ
in yana jajja baya kamar yanda halayyarsa take na rashin sakewa da mutane. Ko Faisal yayi fushi sai kuma ya dawo dan matuƙa Smart ke burgesa a filin ƙwallo, damma ƙaddara ta hana komai gudu ai da yasan yanzu Smart na cikin manyan ƴan ƙwallo da Ni
geria ke alfahari da su. Sun gaisa tare da zolayarsa irin na abokai musamman ma Ahmad da ya tasashi gaba sosai kafin su wuce Smart na roƙama Ahmad shiriya. Gidan Daddy suka fara zuwa. Inda suka sami tarba ta musamman da ga Mommy da su twins da basu koma ba
. Bayan sun gaisa da Mommy sukai godiya tai musu iso falon Daddy da ya riga yasan da zuwansu. Ya
ɗ
an sake musu fuska harda jansu da hira duk da sunata faman sinne kai musamman ma Smart. Dan koda aka kawo musu abin sha da ruwa da kayan motsa baki Faisal da
Ahmad ne kawai suka sha ruwa. Shiko babu abinda ya ta
ɓ
a. Wasa-wasa sun share kusan awa
ɗ
aya da rabi kafin su baro gidan da wasu kayayyakin Lulu da Mommy ta saka Mubeen kai musu akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kimu za'a kai mata sauran kayan. Da ga nan gid
an Uncle Yousuf suka nufa. Anan
ɗ
in ma dai tarba suka samu ta girmamawa ga Aunty Saliha. Uncle Yousuf kuwa babu ruwansa zama yay cikinsu tamkar aboki tunda su duka ukun babu baƙonsa, gara garama Smart
ɗ
in, amma su Ahmad ai tun suna dajinen majina ya sansu.
Anan ma sun jima dan har sai da aka kira sallar la'asar sannan suka fito tare da Uncle Yousuf
ɗ
in zuwa massalaci. Bayan sun dawo basu shiga ciki ba sai mota tunda dama sunyi sallama da Aunty Saliha. Anan ma dai an bada wasu kayan Lulu da wayoyinta da lapt
op da Uncle Yousuf ya amshe. Bayan sun baro nan Smart yace ma Ahmad yana son zaije yaga Malam tunda zuwa gidan Baba da sukai niyya ya rushe sakamakon sanar dasu Baba yayi tafiya Legos da Uncle Yousuf yayi. Ahmad yace babu damuwa. Sun nufi Yakasai wajen Mal
am Nasirudden. Sunyi sa'ar samunsa kuwa a gida bai fita ba. Bayan sun gaisa Ahmad ya janyo Faisal cikin dabara suka fito suka bar Smart tare da malam
ɗ
in.
Malam Nasirudden da ya fahimci akwai magana ya dubi Smart cikin murmushi da kulawa ya ce,
“Idon Aliyu ango ne haka a waje, kai da ya kamata ace kana can gida sai bayan wata
ɗ
aya ka fito”.
Murmushi mai bayyana hakwara Smart ya saki a karo na farko, cikin sinne kai ya ce, “ALLAH ya gafarta malam idan hakan ta kasance ai kwa zaneni matsayi
nku na iyaye”. Dariya shima malam yayi da fa
ɗ
in, “Ina ai idan hakan ta faru mun san lafiya ce ta
ɓ
oye ka ai Malam Aliyu. Ya amarya da gajiyar biki?”.
“Alhamdullah Malam”.
“To Masha ALLAH, ince dai ba jikin bane ba ko?”.
“A'a malam jik
i kam Alhmdllh, dan duk yau banji ciwon kan nan ba. Wani abu ne mai muhimmanci ya kawo ni dan ina buƙatar ƙarin haske da shawara”.
“To Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya mai albarka. Ina saurarenka mike tafe da kai?”.
Zama Smart ya gyara yana sauke a
jiyar zuciya da furzar da iskar bakinsa. “Malam akan ita matar tawa ne nake neman shawara. Kasan yanda al'amuran rayuwar nan suke tafiya a wannan lokaci musamman tarbiyya da ke neman zama wani babban ginshiƙi mai wahalar aiwatarwa ga iyaye ko riƙewa ga mu
ƴ
aƴan, wasu zakaga iyayen nata iya bakin ƙoƙarinsu amma sai su fuskanci jarabawa a cikin ƴaƴan wasu su fan
ɗ
are, ko kaga tun fil'azal iyayen ne ma basu bi hanyoyin isar da tarbiyyar yanda ya kamata ba saboda soyayyar yaran. Wannan matsalar tana matuƙar tasi
ri akan addini da wasu
ɗ
abi'un da takai a yanzu hatta
ɗ
iyanmu mata na shaye-shayen abubuwan mayen nan a cikin gidajen iyayensu ko a gidan aure. Wasu sanadin abokai, wasu samari, wasu kuwa wani daliline kan jasu zuwa hakan. Karna jaka da nisa, ita matar taw
a ta tsinta kanta a irin wannan halinne, sannan ba shaye-shaye ne kawai matsalar ba, hatta a
ɓ
angaren ibada tana da matuƙar raunin da zan iya cemaka komai ma bata sani ba, saboda koda tasan wani to babban dalilai ya shafesu da
ɓ
oye abinda ta sani
ɗ
in. Kain
a gaba
ɗ
aya a cikinkushe yake yinin yau ka bani shawara dan ALLAH, dan ko mahaifana bana son su fuskanci wannan matsalar game da ita balle sauran ahalina saboda bana son mutuncinta ya samu rauni ko yaya a zukatansu”.
Numfashi mai nauyi Malam ya sa
uke yana mai jinjina kansa. “Tabbas kai
ɗ
an halak ne Aliyu, sannan ka matuƙar birgeni na kuma sake ganin kimarka a cikin idanuna. Domin ba kowa ALLAH ke azurtawa da irin zuciyarka ba a wannan ƙarnin. A koda yaushe, a ko wane irin kuskure mutanenmu sukan du
bi mai wannan akin abin ƙyama, abin hantara, abin gudu, abin zin
ɗ
e, abin shune, a tunaninsu suma wayonsu ne ya hanesu da aikatawar ko ya hani nasu zuri'ar. Muna mantawa itafa rayuwar tamu gaba
ɗ
ayanta ma jarabawace, ba kuma lallai ne abinda ya kasance jara
bawar waninka kai ya kasance taka ba. A duk sanda kaga gazawa ga wanin ka ba dandalin gulmarsa ya dace ka bu
ɗ
e ba, da zun
ɗ
ensa ko shunensa ya dace kayi ba idan zai gifta, ba ƙyamatarsa ya dace kayi ba ko hantara. Nema masa shiriyar UBANGIJI ya cancanta da
tausasa masa a duk lokacin da rayuwarsa ta ra
ɓ
i taka ko wani dalili. Wlhy Aliyu mutane da yawa sukan kasa gane cewar bakunansu ko ayyukansu ke jefa musu ƴaƴa cikin wata musifar. Zakaga kana iya bakin ƙoƙarin ka akan tarbiyyar yaranka, ALLAH kuma ya baka su
nutsatstsu da ilimi yanda ya kamata, amma dare
ɗ
aya yaro ya canja alƙiblarsa ka rasa daga ina matsalar take. Matsalar tana a tare da kai, bakinka shine matsalarka, ayyukanka sune matsalarka. Ɗan wancan dake fam
ɗ
are ya gitta ka zun
ɗ
eshi da bama abokan zama
nka labarin ai wancan yaron da kuke gani gagararrene, watsatstsene fan
ɗ
ararre, baida aiki sai shaye-shaye, baida aiki sai bin
ɗ
iyan mutane, baida aiki sai
ɗ
auke-
ɗ
auke. Ciki ta zubar babu adadi bar ganinta a cikin hijjab
ɗ
in can karuwar gida ce, jibi yariny
ar can babu abinda ta iya sai shigar banza, ta kwaile fata da bilicin ƴar isaka tafi ƙarfin iyayenta. Laifin uwarne ko ubanne basu bashi ko bata tarbiyya ba..... Waya gaya maka tsaiwarka akan tarbiyyar yaro ce kawai ke tsare maka shi
ɗ
an uwana ko ƴar uwata
? Muna mantawa akwai jarabawa, muna mantawa akwai ƙaddara, muna mantawa ƙyaƙyƙyawan furucinmu ga
ɗ
iyan wasu kanyi tasiri ga namu
ɗ
iyan, mummuna kanyi tasiri ga namu
ɗ
iyan suma. A duk fa lokacin da ka ambaci ALLAH yayima wane albarka, ya shiryar da shi, sai
kaima mala'iku suce Amin tare da kai da zuri'arka baki
ɗ
aya. Idan kace ALLAH ya wadaran wane fan
ɗ
ararre taƙadari
ɗ
an iska, sai mala'iku su amsa da Amin tare da kai da zuri'arka baki
ɗ
aya. To ashema yima wani ƙyaƙyƙyawar addu'a ko furuci tamkar kanka kayim
awa kenan ko, shiyyasa nace maka harsunanmu sune manyan linzaman da suka zame mana masifu a wannan zamanin bakwai tarbiyyar bace kawai ta su
ɓ
uce mana. Da an ta
ɓ
amu muce zamani, babu babban zamani sama da harsunanmu. Iyayenmu na baya da wahala kaga majalisa
r aibanta
ɗ
iyan mutane, da wahala kaga