Showing 138001 words to 141000 words out of 188614 words

Chapter 47 - FURAR DANƘO COMPLETE

wani ya zauna zin

ɗ

en yara marasa ji, idan yaga yaro yayi ba daidaiba zai hukuntashi batare da sanin iyayensa ba koya tsawatar masa ko ya masa nasiha. Amma a wannan ƙarnin sai dai mu koma gefe muna dariya ko yin ALLAH

wadarai akan abinda munada damar gyarawa ko ambaton shiriyar ALLAH wa wannan yaron kuma tai tasiri garesa. Wani kuma zakaga a gefe sana'arsa itace saida kayan laifi ko wani mummunan abu dake

ɓ

ata tarbiyyar yara, shiyyasa sai UBANGIJI ya dawo da mummunan ai

kinsa wa zuri'ar tasa danta zame masa izina idan zai gane. Abinda kayi na yarda da auren yarinyar nan da ƙudurta gyara mata rayuwa batare da ƙyamata ba da ace haka muka dageyi a cikin al'ummar mu da an samu sauƙin yawaitar lalacewar yaranmu matuƙa. Domin d

uk wanda ya taimaki wani domin tsamosa daga wata halakar rayuwar duniya data lahira, shima UBANGIJI zai tsamesa da ga wasu masifu ya kuma tsame zuri'arsa ta inda bai zato ko tsammani ba. ALLAH yay maka albarka, ya ƙara mana yawaitar irinku acikin al'ummar

mu. Dan irin wa

ɗ

an nan yaran jawosu a jiki da haƙuri da yanayinsu ya dace muyi mu kuma maida hankali wajen fuskantar minene matsalolinsu. Kaifa abinda kake kallo ba dalili ba, wani a wajensa gagarumin dalilaine da zai iya tarwatsa masa rayuwa. In sha ALLAH

U zakai nasara, wataran ba al'umma ba kai kanka sai kayi alfahari da jihadin da kayi da kuma kasancewarta iyalinka. Abu na farko da zakayi shine janta a jiki, karka ƙyamaci halin da take ciki, ka fuskanceta da ƙyau wajen gano minene ainahin abinda ya jefa

rayuwarta a wannan yanayin dan na tabbata tanada ƙyawawan halaye itama da fuskantar ta ne zai bayyanar da su, sannan ka dage da addu'a, yin sadaka da ƙyautata mata, ka fuskanci abinda tafi so ka dinga jan ra'ayinta ga shi. Sai kuma ka

ɗ

an dinga yin zafi ka

ɗ

an a wasu al'amuran dan irinsu zaka samesu da taurin zuciya da ƙin gane al'amura da wuri, dole idan ka hura wataran sai ka tauna, dan sai ka

ɗ

auki matsayin miji ne wataran, wataran uba, wataran yaya, wataran abokin, wataran ƙani, wataran ma

ɗ

a, haka zaka

dinga canja mata kamar hawainiya dan yanda mata kance maza kamar yarane yanda ka renesu haka suke kasancewa, itama mace kamar gold ce, idan ka iya zama da ita ta yanda kaso kake sarrafata da adon da kake buƙata a idon duk wanda zai kalleta. Na ƙarshe shine

haƙuri, dole sai kayi matuƙar haƙuri da zama mai juriya, dan wani lokacin zakaga kana tufkane kamar tana warwarewa, kada ka damu sai a hankali

ɗ

abi'ar zata barta dan ta riga ta shigeta sosai ta yanda wannan abunne kawai ke sakata farin ciki da ƙarfafa ta

saboda shi take kallo a matsayin dai-dai tunda a haka ta tashi taga kanta. Dolene kasa ido sosai a dukkan motsinta, ma'ana ka zama mai ankarewa akan ƙawayenta da abokan hu

ɗɗ

arta danka janyeta daga irinta a cikinsu. Sannan fa saika shirya kawo mata wani abu

mai ƙyau da idan kana yaƙin rabata da wancan ya zam kana cusa mata wannan, kasan kuskuren da mutanenmu keyi shine, kaita yaƙin cirema mutum halayen gur

ɓ

atattu amma baka bashi madadin abinda zai maye gurbinsa da shi ba, tayaya kake tunanin bazai koma ruwa

ba. Sai kuma fahimtar da ita addininta, shine babban abinda zai iya tankwara maka ita cikin sauƙi ma fiye da komai. ALLAH yay riƙo da hannayenka kai da ire-iren ka game da irin wannan sadaukarwar. ALLAH ya sakakanka muku da sakamakon alkairi ku da zuri'ark

u a duniya da lahira da duk ma wanda zai iya koda tausasa harshene akan kuskuren wani.”

        “Amin malam nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara tsahon rai mai albarka. In sha ALLAH zanyi aiki da shawarar ka dan naji da

ɗ

insu na kuma sake samun ha

sken da nake buƙata.”

       Murmushi malam ya sake yi yana tattaro littatafai daga cikin tarin wanda ke a

ɗ

akin nasa. Sai da ya kammala ya juyi ga Smart. “Ga wa

ɗ

an nan kaje da su ka fara koyar da ita, ina dai fatan kanada karatu mai zurfi game da addinin

ka?”.

           “Alhmdllh akwai gwargwadon iko, a yanzu haka ma kuma ban daina nan ilimi ba ina zuwa islamiyya Sheikh Aliyu Abdur-ra'uff Maina (MUTUM DA DUNIYARSA) kafin abubuwa su ta

ɓ

ar

ɓ

are ne na dakata gaskiya, amma in sha ALLAH ina kan shirye-shiryen

komawa na cigaba”.

      “Masha ALLAH kayi ƙyan kai kuwa, Ai Sheikh Aliyu Maina mutumin kirki kuma aminina ne sosai, kaga idan kunyi nisa ka fahimci ta fara tankwaruwa zaka iya sakata Islamiyyar da matansa ke jagoranta suma Malam Jiddah da Malam Maimunatu

”.

          “In sha ALLAHU zanyi hakan malam”.

     Sun

ɗ

an ƙara tattaunawa sannan Smart yay masa sallama ya fito saboda su Ahmad dake jiransa. Ya samu sunata hirarsu da

ɗ

aliban malam, amma duk da haka saida ya basu haƙuri sannan suka wuce yana jin zuci

yarsa sakayau ba kamar daren jiya zuwa safiyar yau da yake cikin damuwa ba akan lamarin Lulu. Sai kusan shida suka iso Shara

ɗ

a, Smart ya fita ya bu

ɗ

e musu gate suka shiga har ciki. Suna sauke kayanta da suka taho da shi ya zare jikinsa ya shiga ciki dan fa

ra duba yanayin shigarta kafin su Ahmad

ɗ

in su shiga........





     

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR

‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at

👇

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan

👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan

👇

0

9033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*

🥰

Zafafa

🫶

🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

😭🙏

_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠

📲

 

🫗



𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍



𝘿𝘼𝙉𝙆

'

𝙊

.....!!

🫗

          

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏



𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍

𝒍



𝒄𝒆

🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓

6





7





.......Da sallama ya shiga falon, tana kwance a 3sitter idanunta a lumshe tamkar mai barci, sanye take da doguwar riga mara nauyi milk color data bi jikinta ta fidda ainahin surarta, sai dai bawai ta matseta bane

ba, kanta babu

ɗ

an kwali sai gashin data

ɗ

aure a tsakkiya. Bu

ɗ

e ƙofar da jin shiru kuma ya sata jiyowa tana bu

ɗ

e luluu idanunta a kansa. Numfashi ya sauke a hankali da

ɗ

an janye idanunsa batare da yace mata komai ba ya wuce ta, itama baki ta ta

ɓ

e tare da m

aida idanunta ta lumshe. Minti kamar biyu sai gashi ya dawo riƙe da Hijjab a hannu, cikin motsa lips

ɗ

insa ka

ɗ

an kamar bayaso ya furta, “Ina tare da su Ahmad tashi kisa hijjab”.

        Idanunta ta bu

ɗ

e fuskarta a tsuke matuƙa da damuwar ka

ɗ

aicin da take

ciki ita ka

ɗ

ai a gida ba waya ba wani abin

ɗ

ebe kewa dan ba'a ha

ɗ

a musu ba, kamar zata

ɗ

auke kai sai kuma ta sake yamutse fuska cikin izzar nan tata ta furta, “Dan kawai kana tare da wasu sai na kama saka hijjab. Wai mi kake nufi da ni ne? Ko dan kaga na s

aka a waccan ranar kake tunanin cigaba da jin kanka sama can”.

         “Mawaddat Umarni ne tashi ki saka hijjab ko nayi abinda bazai mana da

ɗ

i ba mu duka”. Ya fa

ɗ

a shima cikin deep voice

ɗ

insa da dakewa yana tsatstsareta da idanun da take kira na macizai

babu alamar wasa tattare da shi. Kanta ta

ɗ

auke gefe a gatsine ta ce, “To yi

ɗ

in mana”.

  “Okay haka kikafi buƙata?”. Ya fa

ɗ

a shima a dakensa yana ƙoƙarin kai hannu kanta. Tashi tai zaune tana watsa masa harara, dan babu abinda yazo a zuciyarta sai abind

a ya faru tsakaninsu

ɗ

azun, ita kuma abinda bazata iya

ɗ

aukaba kenan ta

ɓ

a mata jiki balle har yay tunanin sake maimaita abinda yay matan.

        “Au ashe tsiwar taki iya baki ne? Da ki ƙi tashi

ɗ

in mana kiga yanda zan tabbatar miki kan nawa a saman yake

.” ya ƙarasa maganar yana jefa mata hijjab

ɗ

in a jikinta ya juya ya fice. Wani irin kallon takaici ya riƙe maka maƙoshin nan ta bisa da shi, a zuciyarta tana ayyana (Mi wannan mutumin ke nufi da ni ne wai shin? Ƙoƙarin takani ko mi? Yimin gadara da nuna za

fin kai ko mi? Humm aiko gidan ya tarar in dai nice, zan bashi mamaki a gidan nan mu zuba) ta yunƙura da nufin barin falon batare da saka hijjab

ɗ

in ba. Sai dai tana miƙewar su Ahmad nayin sallama, ƙofar ta zubama ido kawai tama rasa miya kamata tayi har S

mart ya shigo a farko, ja yay ya tsaya murmushin fuskarsa na

ɓ

acewa

ɓ

at, sai kuma ya rumtse ido da masifar ƙarfi zuciyarsa na dokawa da sauri-sauri, dan da gaske fa yanada kishi mai zafi, bai fahimci hakan ba kuwa sai a yanzu

ɗ

in nan dan idanunsa har ji ya

ke suna masa wani yaji-yaji. Koda ya bu

ɗ

esu a kanta ita kanta sai da taji razani ya shigeta, dan cikin ƙanƙanin lokaci sun yi wani irin ka

ɗ

awa da canja launi, baice komai ba ya tako inda taken tsaye ya duƙa ya

ɗ

auka hijjab

ɗ

in ya warware ya saka mata. Su d

ai su Ahmad da sun riga da sun shigo basarwa sukayi, sai kuma ita Lulu a wautarta ganin ran Smart ya

ɓ

aci sai tai niyyar sake ƙular da shi. Sai da ta saci kallonsa ta gefen ido sannan ta juya gasu Ahmad tana sakin wani sassanyan murmushi da fa

ɗ

in, “Sannunk

u da zuwa, ni ai da har zan fara fushi”. Ahmad bai kawo komai a ransa ba tunda dama sun san juna da jimawa sai dai bawani mu'amala ke tsakaninsu ba mai ƙarfi dan Lulu fa ita da maza zira'i maitan ne. Shima murmushi yayi yana kaiwa zaune da fa

ɗ

in, “Yauwa am

arya. Ya kuke ya gajiyar biki? Duk da dai naga angon naki shi tun

ɗ

azun”. Sai da ta sake satar kallon Smart ta ga yanda yay kicin-kicin da fuska ya kuma ƙi zama sai ta sake sakin murmushin da bama Ahmad amsa da “Gajiya kam tabi jiki, kuma ya taku gajiyar?

Ya su Uncle Hameed”.

        “Alhmdllh, Yaya kuma shima lafiya ƙalau yake”.

      Kanta kawai ta jinjina, ta juya ga Faisal shima ta gaishesa sannan ta nufi kitchen tana dariya a ƙasan ranta. Ruwa da lemo ta

ɗ

ibo da kayan cin-cin, babu jimawa sai gata ta

dawo ta ajiye gabansu. Yanzu kam Smart ya zauna, sai dai kansa a duƙe yana latsa waya. Komawa tai ta zauna itama tana

ɗ

an murmushin santin da su Ahmad keyi na dubulan. Shi dai gogan kamar ruwa ya cinyesa a falon. Sai da ƙyar yay controlling kansa kodan Fa

isal dan ta Ahmad mai sauƙi ne zai iya fahimtarsa. Sai dai murmushin Lulu sukar masa zuciya yake kishi na sake riƙe masa maƙoshi.  Haka dai ya danne har suka miƙe, kayayyakinta suka shigo mata da su sannan sukai mata sallama ita kuma ta basu kayan garar da

ta juye musu a leda kowa da nasa ta ƙaro ma sannan ta zuba wanda za'a kaima Aunty Khadijah matar Abdull-Hameed (Coach) dan suna

ɗ

asawa sosai itama kasancewar akwai ƙawance mai ƙarfi tsakaninta da Aunty Saliha. Suna fita ta koma ta zauna tana dariyar jin da

ɗ

in ƙular da Smart da tayi. Jinta take rai fess ita kam. A haka ya dawo ya sameta. Zama kawai yay baice mata komai ba dan a yanzu idan har yay magana

ɓ

acin ransa ne zai bayyana a fili, dan haka yafi za

ɓ

ar zama shiru har zuciyarsa ta

ɗ

an sassauta masa sanna

n ya tura mata ledar da wayoyinta ke ciki ya miƙe yabar wajen. Nanma da kallo ta bisa cikin ta

ɓ

e baki kafin taja ledar ta bu

ɗ

e. Sosai taji farin cikin ganin wayoyinta da laptop, cike da jin da

ɗ

i ta

ɗ

auka tai bedroom domin saka caji dan duk sun mutu ba caji

. Ga cajojin duk suna hanunta.....

   

       Kiran sallar magrib ya fiddosa a

ɗ

akinsa, ya

ɗ

an zubama kayan da su Ahmad suka shigo da shi ido dan suna nan a inda suka ajiye, iska ya furzar batare da yace komai ba ya kwashe su ya fara shiga da su bedroom



ɗ

in nata. Zaune take da laptop data jona a caji gabanta, tun

ɗ

agowar farko da tai suka ha

ɗ

a ido ta maida bata sake

ɗ

agowa ba har ya kammala shigowa da kayan. Babu alamar wasa tattare da shi ya ce, “Bakiji an kira salla bane?”.

       Tsayawa tai da ga da

nna laptop

ɗ

in sai dai bata

ɗ

ago ta kallesa ba. Amma ta tsuke fuska alamar jira take yace kule tace cass. Takowa yay gabanta a hankali ya rufe laptop

ɗ

in ya tura gefe. Dole ta

ɗ

ago yanzun kam ta dubesa da iyakar duk wani ƙarfi dan nuna masa yana shiga mata

hanci fa. Kallon tsakkiyar ido sukema juna kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, dan ta gagara fa

ɗ

ar abinda tai niyyar da farko. Ita ta fara janyewa cikin ta

ɓ

e baki. Sai kuma ta miƙe batare data tanka masa ba ta nufi toilet. Bayanta yabi dan yanzun ma

yana son tai al'ala a gabansa kamar

ɗ

azun, kasancewar shi yana da ita sai ya tsaya yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ganin tayi kamar yanda ya nuna matan

ɗ

azun, sai yaji kuma nauyin da zuciyarsa yayi ya ragu, dan har cikin ransa yaji ta burge

sa, in dai har haka take da saurin fahimta da

ɗ

aukar abu komai zai zo da sauƙi kenan, kafin dai tayin ne yake ganin zasu dinga kai ruwa rana.

       A karan farko ya ja musu jam'i yau, abi mafi sakata sake nutsuwa a wannan jam'i yanda Smart ke raira karat

un Alkur'ani a nutse da fitar sauti nagartacce. Bayan sun idar cikin fuskewa tai yunƙurin miƙewa domin bar masa wajen amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo mata hannu. Hannun ta kalla sannan ta

ɗ

ago fararen idanunta ta zuba masa. Shima

ɗ

in dai ita yake kal

lo dan haka suka zubama juna ido kowanne najin idon

ɗ

an uwansa na ratsashi har tsakkiyar ruhinsa. Da ƙyar Smart ya iya aro jarumta da ga cikin

ɗ

unbin ƙwarin gwiwar sa cikin fitar sauti ƙasa-ƙasa ya furta, “Inada kishi! Inada kishi mai zafi! Inada kishi mai

tsanani Mawaddat. Wannan gaskiya ce da nake gaya miki ita danki haddace a cikin muhimman abubuwanki ki kuma kiyaye saboda gudun randa zaki iya tabbatar da ainahina akan wannan kalmar. Komai zan iya

ɗ

auka, idan nace komai ina nufin komai amma banda kasa ri

ƙ

e kanki ko killace kanki ga wanina koda kuwa uwa

ɗ

aya uba

ɗ

aya suka haifemu da shi. Ki cigaba da sanin *_SMART_* kawai, idan kika ce *_ALIYU HYDAR_* ki ke son gani a zahirance, to fa tabbas wasan zai iya canjawa da ga duk yanda kike iya tunanin ko kwallon

sa a tsarin zuciyarki. Duk abinda kikaji nace bana so to da gaske bana sonsa, idan kuma bana son abu bana iya dogon kawaici a kansa game da

ɗ

aukar hukunci mai tsauri. Idan har kina son cigaba da gudanar da duk abinda kika fara da ga gidanku cikin salama to

ki kiyaye....”

        Rikitaccen abinda ta hango a tsakkiyar idanunsa mai kama da guguwar hayaƙin turnuƙun yaƙi ya sata kasa iya maida murtani. Ba wai ta fahimci ainahin curarrun kalamansa bane ba a yanda shi yake son ta fahimta

ɗ

in, a salon da yay maga

nar ne kawai ke son tilasta fassara mata su. Ba'a komai take garaje ba musamman maida murtani, dan haka ta shanye kamar komai bai mata zafi ba dan tana buƙatar fashin baƙi kafin ta maida raddi, dan haka kanta tsaye batare data janye idanunta da ga cikin na

sa ba duk da hakan na cutar da ita ta ce, “Ka gama?”.......





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at

👇

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan

👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan

👇

0903318

1070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*

🥰

Zafafa

🫶

🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

😭🙏

_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠

📲

 

🫗



𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍



𝘿𝘼𝙉𝙆

'

𝙊

.....!!

🫗

          

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏



𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍



𝒄𝒆

🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓

6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login