Showing 186001 words to 188614 words out of 188614 words
ajiyar zuciya. Jikinsa ya tsaftace. Koda ya fito maimakon kwanciya sallaya ya shi
mfi
ɗ
a ya fiskanci alƙibla domin miƙa godiyarsa ga UBANGIJIN talikai mai rahama mai jin ƙai. Sai gabannin asuba da ya fuskanci ruwan daya saka mata na biyu da Aunty Khadijah ta bari ya ƙare ya je ya cire shi ma. Zama yay kawai ya saka hannunta cikin nasa ya
zuba mata ido, yanda take barcin da sauke numfashi a hankali lokaci zuwa lokaci takan saki ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa yake nazarta a kanta. Tun daga randa ya fara ganinta a airport da yaje
ɗ
akkota har zuwa masifar da ya dinga ci a wajenta, aurensu da
zaman sati uku da kwanaki hu
ɗ
u yau cikon na biyar. Ya bata sunan HAWAINIYA da kan canja akowane lokaci da kuma kowane irin yanayi. Kai tsaye baka yanke mata hukunci akan kanta dan sanin ainahinta sai ALLAH. Wato duk bawan da kake kallo yana rayuwa akan kus
kure ashe kai tsaye yanke masa hukunci da abinda idonka ya gani a kansa tamkar son zuciya ne. Duk wanda zai baka amsa a kanta zai ce maka she is bad girl ne kai tsaye, domin da wannan siffofin take bayyana kanta wa duniya. Dalilin shine haka aka raineta, h
aka ta tashi, da hakan kawai tai imani a matsayin gaskiya. “Lokaci yayi da zan san wacece ke Mawaddat? Wace irin turnuƙun ƙura kika tsallake a baya data gina miki rayuwa kamar haka? Wanene yaso lalata miki rayuwa? Miyasa mahaifinki ya nuna miki soyayya amm
a ya gagara tsayawa akan tarbiyyarki? Miyasa ahalinki sukai sakacin fuskantar rayuwarki na cikin wani ƙulli tun
a ga
ɓ
ar da ya dace ace sun fuskanta
ɗ
in? Ina son sanin wa
ɗ
an nan amsoshin da ga bakinki MATATA. na miki alƙawarin sake gina nagartacciyar rayuwa
r da zata fahimtar da ke tsakanin fari da baƙi koda sun gauraye a mazubi
ɗ
aya da izinin ALLAH. In sha ALLAHU zan share miki dukkanin hawayenki na zuci dana bayyane da tafukan hannayena na maye gurbinsu da tarin farin ciki Mawaddatan'warahmah”. Motsawar da
tai ya bama hannunsu damar sake matsewa cikin na juna tamkar mai jaddada masa ta amshi dukkan kalamansa itama. Hakan ya sakashi lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya...........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MAN
TUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Ban
k
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafarta
ma iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
8
️
⃣
9
️
⃣
.......A
ɓ
angaren Alh. Sulaiman Garko yana barin wajen Dada Alh Baita ya kira a waya. Wanda
ya shaida masa yana gida yau kam bai fita ko'ina ba. Ya tabbatar masa yana buƙatar ganinsu su dukansu a daren nan dan magana ce mai muhimmanci da shi. Babu musu Alh. Baita ya amsa masa tare da bashi address
ɗ
in inda zasu ha
ɗ
u. Sannan yay kiran su Hon. Nak
owa suma. Cikin abinda baifi awa
ɗ
aya ba suka ha
ɗ
u a gidan hutawar Hon. Misau dake anguwar Farawa. Tsaf ya zayyane musu komai da suka tattauna da Dada, su kansu sun girgiza da jin wannan ƙulli. Hon. Nakowa ya ce, “Wato su wa
ɗ
an nan na kula makirci a cikin
jininsu yake. Yanzu shima shegen Yousuf
ɗ
in nan ashe tsagerane a haka kamar na ALLAH yana wani sim-sim da kai. To anya kuwa Isma'il bai sanar masa sirrin dake a tsakaninmu ba kuwa?”.
“Abinda nai tunani kenan yasa ni nemanku da gaggawa. Dan in har
zai iya irin wannan ƙulle-ƙullen kamar haka dan kada yarinyar nan ta auri
ɗ
aya daga cikin kai da Tajuddeen to inaji a raina wannan taƙamar da hura hanci da Isma'il keyi nada alaƙa da ya sanarma yaron nan komai kuwa. Dan haka nake ganin plan B dole ne mu ca
nja labarin da ga Isma'il zuwa Yousuf, hakan zai bamu damar jifan tsuntsu
ɗ
aya da dutse biyu, sannan zamufi gigita rayuwar Isma'il
ɗ
in da haukatashi”.
“Su kuma yarinyar da yaron fa?”.
Cewar Hon. Nakowa cikin zumu
ɗ
i. Duk da Alh. Sulaiman ya f
ahimci inda ya dosa, amma sai bai nuna masa a fuska ba, sai ma murmushi da ya saki kai tsaye ya ce, “Wannan aikin Dada zata ƙarasa mana shi. Bayan ta
ɗ
auke ta daga wajensa sai muje plan c akansu ita da yaron, dan dama akwai tawa da shi a ƙasa”.
Nan ma
sun gamsu matuƙa. Daga haka suka cigaba d tattauna abinda ya shafesu, musamman game da sabuwar alaƙar da suke shirin sake ƙullawa akan business. Har gabannin asubahi sannan suka watse.....
__________
★
Yanda Smart yaga rana haka yaga wannan
dare ko sau
ɗ
aya bai rintsa ba har akai kiran sallar asubahi. Da kyar ya iya dauriyar fita massalaci. Ana idar da salla ya dawo gidan. Inda Lulu take ya sake komawa. Har lokacin tana a yanda ya barta bata farka ba. Yana tsaka da tunanin tadata ko ya barta
har sai ta tashi da kanta kira ya shigo masa a waya. Yayi mamakin ganin Coach, amma sai ya
ɗ
aga. Jin muryar aunty Khadijah sa
ɓ
anin wanda yay tunani ya sashi sauke ajiyar zuciya tare da gaisheta cikin girmamawa.
Tambayar data jeho masa akan Lulu y
a sashi kallonta, sai da ya
ɗ
an furzar da iska sannan ya bata amsa da “Har yanzu bata farka ba dai”.
“Alhamdullah to karka tada ita, inasha ALLAH ina nan zuwa yanzu nan. Dan a yanayin da take a ciki bamu da tabbacin bazata sake tashi a firgicen ba. Ha
kanne kuma ba'aso da ga gareta”.
Ya gamsu, dan haka yayma Aunty Khadijah godiya ya na yanke wayar. Kwanciya ya
ɗ
anyi a kan sofar
ɗ
akin ya fa
ɗ
a duniyar tunani, hakan ya Bama barci damar dinga figarsa ka
ɗ
an-ka
ɗ
an. Tsakanin wayarsa da aunty Khadi
jah baifi mintuna arba'in ba sai gata tazo. Sosai yaji da
ɗ
i da ƙara jin kimar wa
ɗ
an nan bayin ALLAH. Bayan sun ƙara gaisawa ya fita ya basu waje. Cikin hikima ta tada Lulu wadda ta farka a firgicen kamar yanda Aunty Khadijah tai hasashe, sai dai Alhmdllh c
ikin ƙwarewar aiki ta nutsar da ita, tare da taimaka mata zuwa bathroom ta sake ha
ɗ
a mata ruwa mai
ɗ
umi. Shawarar sake gasa jikinta ta bata ta fito. Lulu da komai ke dawo mata dalla-dalla batai musu ba ta shiga ruwan zafin, sai da taji ya ratsata tako ina
ta sake samun nutsuwa sannan ta tsaftace kanta ta hanyar wankan tsarki da shi da kansa ya koyar da ita a cikin karatunsu duk da dai dama tanayi makamancinsa bayan period, amma ko randa ya koya matan yasha harara dan yay mata bayani dalla-dalla ne. Ji take
jikinta ya mata nauyi sosai, ga tauna da ƙasusuwata keyi. Bata son tuna abinda ya faru saboda ƙunar da zuciyarta ke mata. Da taimakon aunty Khadijah tai salla, bayan ta idar ta jima zaune shiru tana nazarin tushen faruwar komai na daren jiyan. Kamar wadda
aka tsikara ta miƙe da sauri dan ta manta yanayin nata. Komawa tai da sauri ta zauna tana dafe kanta ta cije lips. Ƙaramar ƙarar da tai ya saka hankalin aunty Khadijah dawowa kanta. Ta nufota da sauri tana fa
ɗ
in,
“Mawaddat yi a hankali banda gara
je kinji”. Bata iya cema aunty Khadijah komai ba sai hawayen da suka silalo mata masu zafi. Cikin muryarta da ke a disashe har yanzu ta ce, “Aunty dan ALLAH ina son ki kaini gida”.
“Gida kuma Mawaddat?”.
“Eh aunty, dan na tsani gidan nan da komai
na cikinsa. Wlhy idan na cigaba da zama komai zai iya faruwa”.
“Ki kwantar da hankalinki Mawaddat. A cikin wannan halin da kike ai wannan gidanne yafi cancanta da ki zauna fiye da ko ina. Karki ru
ɗ
ar da kanki, domin yau
ɗ
inki tanada banbanci da jiyan
ki. Aliyu mijinki ne, abinda ya faru tsakaninku kuma yanada banbanci da wanda zuciyarki ke kallo a baya. Bawan ALLAHn nan tun jiya hankalinsa a tashe yake da ganin halin da kika shiga, bana jin ko rintsawa yayi a daren jiya, dan ALLAH ki sakama ranki haƙur
i ku fuskanci juna wataran zakiyi alfahari da hakan”.
Kuka Lulu ta sake fashewa da shi tana mai girgiza kanta, “Aunty dan baki san miya faru bane....”
“Ba sai na sani ba Mawaddat, ki adana wannan sirrinkine. Ni dai fatana ki kwantar da hank
alinki ki saurari mijinki. Aliyu mutumin kirkine fiye da yanda kike zato ko tsammani. Ke da kanki zaki bama wani labarin hakan wata rana...”
“Aunty shi azzalumi ne, macuci ba mutumin kirki ba. Kuma wlhy saina
ɗ
an
ɗ
ana masa fiye da abinda ya
ɗ
a
n
ɗ
ana min, ni zai yaudara ya sakama disere tablet acikin abu na sha ya min fya
ɗ
e. Natsanesa aunty, bana son sake ganin fuskarsa a rayuwata. Kuma wlhy sai na shayar da shi mamaki, dama sai da Dada ta fa
ɗ
amin amma na kasa fahimtarta. Yayi hakane saboda yasan
gobe zamu rabu. Bazan yafe masa ba, kuma a yau
ɗ
in nan komai ma ya ƙare, ya kuma saurari abinda zai biyo baya”.
A bazata suka tsinkayi deep voice
ɗ
insa cikin kunnuwansu dan basu san da shigowarsa
ɗ
akin ba. “Ni ban saka miki komai kisha domin samun
biyan buƙatata ba. Sannan aure nayi kamar kowane aure mai daraja da fatan mutuwa ta raba. Amma kiyi haƙuri ki bani dama na miki bayani maybe ki fahimceni kuma ki yarda” ya ƙare maganar yana ajiye tray
ɗ
in hannunsa mai
ɗ
auke da kofin shayi da plate da aka
saka soyayyan ƙwai.
A zafafe Lulu dake masa wani irin kallo na tsantsar tsana tace, “Har abada babu yarda a tsakaninmu. Baka da abinda zaka fahimtar da ni Munafuki, azzalumi, maƙaryaci, mayaudar...”
“Mawaddat!!”.
Aunty Khadijah ta ki
ra sunanta cikin daka tsawa. Yayinda Smart ya lumshe idanunsa har cikin rai kalmomin guda hu
ɗ
u da suka fito da ga bakinta na ratsa shi. Ƙoƙarin matsawa yay gaban gadon da kofin shayi a hannunsa yayinda aunty Khadijah ke cigaba da mata fa
ɗ
a. Bai gama tabbat
ar da takai maƙurar tsorata da shi ba sai da yay ƙoƙarin riƙota tai wata irin zabura, sai dai azaba da rashin isashen ƙarfi ya sata kasa yin kowane irin yunƙuri face sake fashewa da kuka ta furta, “NA TSANEKA ALIYU!!”.
“INA ƘAUNARKI MAWADDATAN'WAR
AHMAH”. ya amsa mata da tashi disashshiyar muryarsa yana tsayawa cak, kofin shayin ya ajiye a bed side drawer duk tausayinta sai ya sake mamaye masa zuciya. So yake tai haƙuri ta kwantar da hankalinta ya jera mata kalaman yabo da jinjinar ban girma, sai da
i yasan bazasuyi tasiri ba a yanzu gareta, dan haka ya tattarasu ya adana a wani killataccen sashin adana manyan sirrikansa a zuciya.
Ganin Lulu na neman sake rikice musu aunty Khadijah tace yaje falo ya jirata. Kusan mintuna biyar da fitar tas
a sai gata ta fito. Kallonsa tai cike da tausayawa. “Kayi haƙuri Aliyu ba laifinta ban itama. Wlhy gaba
ɗ
aya a ru
ɗ
e take. Dan ma a hakan fa jiya an taimaka mata da wuri shiyyasa al'amarin yazo da sauƙi. Ni yanzu ina ganin mafita
ɗ
aya ce, ka samo wadda zasu
zauna tare, sannan dole kayi haƙuri na samu ko Maman Ra'is ce (Aunty Saliha) tazo ta ƙara lallashinta. Dan yanzu ni zanje asibiti ne inada theatre. Insha ALLAH komai zai dai-daita da zarar ta daina jin ra
ɗ
a
ɗ
in a ranta. Sannan ka
ɗ
anyi nesa da itan na
ɗ
an
lokaci koda yinin yau ne haka zuwa gobe”.
“In sha ALLAHU aunty Khadijah. Nagode sosai da ƙoƙarin ki kuma”.
Sosai aunty Khadijah taji da
ɗ
in yanda ya fahimta
ɗ
in. Yayinda tausayin Lulu ke cigaba da ratsata itama harma da shi kansa Smart
ɗ
in.
Dan yarinyar tana cikin wani yanayi ne mai ban tausayi. Bayan wucewarta
ɗ
aki ya nufa ya canja kayansa, koda ya fito sai yay tunanin bari ya
ɗ
an leƙata kafin ya wuce, dan gidansu yake son zuwa ya
ɗ
akko mata Maryam ko Asma'u. Kamar zai fice sai kuma dai ya n
ufi
ɗ
akin nata, ya samu tana toilet, sai books guda buyu da ya gani a saman gadon da pen. Juyawa yay ya fita saboda so yake yaje ya dawo da sauri. Maganar aunty Khadijah na cewar zatai magana da Aunty Saliha tazo yasa shi bai rufe gidan ba, dan yasan sun f
isu kusa da nan zata iya yiwuwa ta iso kafin shi ya dawo.. Da'ace bawa yasan gaibu ko abinda zai iya faruwa a bayansa
da Smart bazai yi wannan fitar ba. Da bai bar ƙofar gidansa a bu
ɗ
e ba. Da ya bari har aunty Saliha ta iso kafin ya tafi.......
✍
️
*_Tofa
masu karatu. Mizai faru? Mike shirin faruwa? Amsoshin na a FURAR DANƘO book 2 in sha ALLAHU
👌
_*
_Kumin afuwa wannan karon rubutun duk yazo a yanayi na shiririta sai dai godiyar ALLAH. Yau da gobe kenan dan na fiku son naga na kammala gaba
ɗ
aya
😭
. Amma
in sha ALLAH muna gab da hutawa baki
ɗ
aya. Zamu koma part 2 ne dan in numbers na nisa rubutun gundurata yakeyi wlhy
🤦
. Amma insha ALLAHU zamu ƙarƙare akan lokaci._*
_Akwai ƙura fa ta gaske a book 2, dan duk wani abinda muke san sani na ƙ
unshe ne a cikinsa. Kudai kuyi addu'a ALLAH yasa mu koma pages goma goma mu kammala a kwana goma. Kun san fa ina matuƙar son goma
😂😂
._
Bilkisu Ibrahim Musa
(Bilyn Abdull ce)
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MAN
TUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Ban
k
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafarta
ma iyayenmu
😭🙏
_*