Showing 1 words to 3000 words out of 174924 words

Chapter 1 - Haihuwa-Da-Hanji-Complete

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

FATIMA MUHAMMAD GURIN

*GUREENJOH*

*FREE BOOK*

*TSOKACI*

Wannan littafi nawa mai suna HAIHUWA DA HANJI ban san ta ya zan fasalta muku ba amma

tabbas yayi matuƙar shan bambam da sauran littatafai na don lab

ari ne na wata baiwar Allah da

ya faru a gaske, kashi saba'in cikin

ɗ

ari duk ya faru sai ka

ɗ

an da za mu ƙara ta yadda zai

ƙ

ayatar ya kuma isar da saƙon da muke buƙata ba tare da tangar

ɗ

a ba. I promise it's going to

be a hit kar ku ga don free ne yana da

ga cikin labaran da na jima ban rubuta irin shi ba don

haka ku shirya shan karatu domin duk wacce bata karanta ba an barta a baya.

*GARGAƊI*

haƙƙin mallakar HAIHUWA DA HANJI na Fatima Muhammad Gurin ne ban amince ba ban

lamunci a sauya min labari ko

ta wani

ɓ

angare ba ko a yi amfani da shi ba tare da sani na ba.

*SADAUKARWA*

Na sadaukar da littafin HAIHUWA DA HANJI ga

ɗ

aukacin makaranta littatafai na.

*001*

Wani irin ruwa ake tsulawa kaman da bakin ƙwarya, kusan duka bil'adama suna kwance lu

b

cikin tattausan katifa lullu

ɓ

e da bargo suna bacci kaman yadda dare ya zama mahutar bawa

amma ita tana duƙe a kitchen

ɗ

in dake tsiyaya saboda rashin kyaun kwanon da aka lullu

ɓ

e kai

da shi.

Wuta ne take hurawa Dukda bayanta dake ta jiƙewa har hakwaran

ta suna ha

ɗ

e wa saboda

sanyin dake shigarta hakan bai sa ta damu ba sai ma ƙara mayar da hankali da ta yi ga

haurawar da bata sarara ba sai da ta ga wutar ta kama yadda ya kamata, babbar tukunya ce da

za'a iya na

ɗ

e ta a sanyata ciki kuma tsaf ya

ɗ

auketa

saboda rashin ƙiba da kumarinta ta shiga

kokawar janyowa da ƙyar ta

ɗ

ora bisa murhun kan ta nufi wani bokiti ta fara aikin

ɗ

ibo ruwa a

kimtace tana zubawa sai da ta tabbatar yayi yadda ta saba kan ta rufe ta fito, kifi

ɗ

anye da suke

sanyawa cikin ƙanƙa

ra a wani babbar kula ta juye ta shiga wankewa don an riga an yi mata

yanka tun jiya da Magrib a bakin kasuwan, sai da ta wanke tsaf ta

ɗ

auko wani tukunyar ta zuba

su sai a lokacin aka soma kiraye-kirayen sallah daga chan nesa.

Na yi mamakin yadda

ko tsoro babu a fuskarta haka take ayyukan nan cikin ruwa a take ta

sake ha

ɗ

a wani murhun ta

ɗ

ora dahuwar miyan kifin nan, sai da ta tabbatar komai ya mata

yadda take so kan ta shiga tattaro kwanukan gidan don ta san in ta bari ma gari ya yi haske ta

sh

iga uku, wanke wanke take sauri-sauri yayinda ruwan da ya koma zuba chab chab ya cigaba

da jiƙata, har ta gama jikinta babu inda ba ya kakkarwa sauri sauri ta wanke shinkafa ta zuba

cikin tukunyar farko kan ta yi alwala har kuma lokacin babu mahaluƙin

da ya leƙo a gidan Dukda

kuwa wasu masallatan ma har sun idar da sallah.

Akurkin

ɗ

akin da shi ne nata a gidan ta duƙa ta shige ta cire kayan jikinta bakkon kayanta ta

janyo da kyar ta zaƙulo wata kodaddiyar doguwar riga ta saka ta janyo hijabinta ta

ɗ

ora tare da

tada sallah, ga mamakina tsaf ta gabatar da Sallar ta yadda addini ya tanadar, bata jima tana

azkar ba ta fito don gudun magana amma bata tsira ba domin a kitchen

ɗ

in ta tarar da Inna larai

da sauri ta duƙa ƙasa

"Ina kwana inna?"

Kallo

nta tayi ta ta

ɓ

e baki ta bu

ɗ

e tukwanen ganin miyan ya yi ta juyo gareta

"Uban me kika shiga

ɗ

aki kike yi har miyan nan ya nuna saura ƙonewa baki shirya kwashewa

ba? Asara kike son ja min ko?"

"A'a inna sallah ne na je na yi"

Tsaki ta ja tare da nun

a mata kular da suke kwashe miyan tallar, ta je da sauri ta

ɗ

auko inna

larai ta kwashe tsaf kan ta

ɗ

aura dumamen gidan a murhun, ita kuma ta wuce ta

ɗ

auko kular

kwashe shinkafa ta taho ta janyo ledar sugar ta bu

ɗ

e a cikin kular kan ta shiga kwashewa turi

rin

na Dakar ta yana ƙonata yadda ta saba har ta gama duk sanyin da ake ta jiƙe jagwaf da gumi,

kwanukan tallarta ta cigaba da ha

ɗ

awa a wani bokitin fenti har ta gama filate na roba da ruwa

da gutsuren dollof da take wanke plates idan ta sayar aka ci ak

a dawo mata dashi.

"Je ki bugawa su Iro su zo su

ɗ

aura miki a baro su kai miki yanzun nan"

Da to ta amsa cikin sanyinta ta nufi

ɗ

akin na yaran mazan ta shiga bugawa, sai da ta kwashe

sama da mintuna ashirin tana bugu da ƙiran suna kan wasu matsakaitan

samari biyu suka fito

ɗ

ayan ya sa hannu ya hanka

ɗ

eta sai da ta fa

ɗ

i ƙasa.

"Don uban ki bamu hana ki wannan bugun bala'in ba? Shegiya kullum ba ki da aiki sai na

uzzurawa mutane ko wani farar safiya..."

"Ɗahiru ƙaniyar ka...! Kun wuce kun zo kun fitar

min da abinci ko sai kun janyo min asara?"

Babu ruwanta da sun yi sallah ko ba su yi ba damuwarta kawai su kai mata kayan sana'ar ta.

A hankali ta miƙe tsaye tana ka

ɓ

e jikinta dama ta sani ba dai a yi musu fa

ɗ

a a kan an ci

zarafinta ko an zalunce ta b

a, kowa a gidan na ganinta tamkar juji da in sun kwaso sharar su

babu inda suke zubawa sai bisa kanta.

Sumsum haka ta taho suka kama suka

ɗ

ora suna ta mitar da kullum safiya sai sun yi haka har

suka fice, tana shirin fita daga gidan kenan Inna larai t

a kwala ƙiran sunanta.

"Afifah Ke!"

Waigowa tayi da sauri kuma cikin sanyinta

"Saura in ga ba daidai ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daa

ɗ

i kuma kika sake kika ci kai ko lasa

kika yi Allah ya isa ban yafe ba ki je ki dawo ga dumamenki nan zan ajiy

e miki"

Girgiza kai tayi fuskanta

ɗ

auke da murmushi mai nauyi da ciwo ta amsa da

"Toh"

Kan ta fice daga gidan.

A inda ta saba zama gefen rumfar masu tura finafinai nan ta zauna bayan sun sauƙe mata suka

bu

ɗ

e suka cika fillet biyu idanunta cike da

hawaye tace

"Iro wallahi in..."

"Na uwarki ne ko na ta mu uwar? Ina ruwanki? Kuma wallahi ki sake ki fa

ɗ

a mata ki ga yadda

zamu yi da ke Annoba kawai"

Da ƙarfi ta runtse ido sunan ba wai sabo bane a gareta sai dai a duk sadda aka ƙira ta da hakan

ta

kan ji zafi da ciwon fiye da

ɗ

an

ɗ

anon ma

ɗ

aci a kan harshenta.

"Mai shinkafa sa min na

ɗ

ari uku..!"

Ha

ɗ

iye abin da ya taso mata tayi ta kar

ɓ

i kudin ta saka a Jakan ƙugunta kan ta fara zuba

shinkafar kaman ko yaushe fuskanta babu

ɗ

igon fara'a ko sassau

ci ba kuma don komai ta

ɗ

auki

wannan mataki ba sai don kare mutuncinta.

Hakan da take ya sa maza dayawa masu kawowa 'yan mata yan tallah wargi basa samun dama

kowa ya santa duk tsiyarka tana da kwarjinin da in ta tsume hakan babu mai iya kawo mata

warg

i... Saboda tsafta da kuma natsuwarta yasa dayawa suke tururuwa wurin sayan abincinta.

Ita

ɗ

in annoba ce kaman yadda wasu ke ƙiran ta dayawa sun santa a Mayya! Dukda ita bata

ta

ɓ

a sanin menene maitar ba amma ta wurin kasuwanci su kan saya abin hannunta d

on ko

babu komai akwai zaƙin hannu muddin ita tayi girki.

Kan ka ce awa biyu duk ta sayar da abincin tas ta janyo baro ta

ɗ

ora kulolin a kai tana jin jiri na

fusgarta saboda rabon ta da abinci tun jiya da rana gashi yanzu ana neman goma da rabi, haka

t

a turo wheelbarrown ta nufi gida...

Razana tayi ta daka tsalle tayi baya sun saba yi mata hakan sai dai ta kasa sabo ita

"Ina kudina?"

Inna larai ta miƙa mata hannu a zauren wanda ko kanta bata gama sanyo wa ba, Jakan ta

sunce ta miƙa mata a wurin ta

zazzage ta kirga ta ga riba yadda suka saba samu ta sa

ɓ

i

kayanta ba sannu bare na gode tayi cikin gida abin ta, Afifah ta bita da kallo har ta

ɓ

ace kan ta

turo baron zuwa cikin gida ko sauƙe kwanonin bata yi ba ta nufi bakin kitchen inda inna larai

ɗ

in

ke zaune ta duƙa

"Abincina fa inna?"

"Laaaa kin ga mun manta da ke wallahi ina fa ta zuci zucin ajiye miki"

Runtse ido tayi da ƙarfi tana danne hawayen dake taso mata idan da sabo ya ci a ce ta saba,

kusan koyaushe za su yi rabon abincinsu muddin ba

ta gidan to za'a ce mata an manta da ita

ne, wani lokacin ma sai an sauƙe sai a aiketa kan taje ta dawo an rabar kuma a hana ta,

hanjinta har mur

ɗ

ewa suke saboda yunwa amma ya zata yi?

Miƙewa tayi ta nufi hanyar akurkinta inna Asabe ta kwala mata ƙira

daga cikin

ɗ

akin ta

"Ina za ki da baki kar

ɓ

i ku

ɗ

in nawa aikar ba?"

Bata ce komai ba ta tsaya daga kanta leda da ke kunshe da ku

ɗ

i ta jefa mata a fuska

"rashin kunya za ki min ki tsaya min kerere bisa kai? Kin

ɗ

auka kin wuce ko sai na tsinka miki

mar

i?"

Duƙawa tayi ta

ɗ

auka ta fice daga gidan ko

ɗ

akin bata shiga ba ta riga ta san me zata sayo, ko

kan ta dawo har inna Asabe ta gama tuka tuwon tallar tata na dare, ita ta zauna ta malmala

tana jin kanta na sarawa ayyukan sun fi karfin shekarunta amm

a ya zata yi? Mutum

ɗ

aya take

da shi a duniya Aunty zee ita ma kauyen gaba da su take kuma ta kan kwana biyu bata leƙo

mata ba bare ma hakkin riƙe ta na ga dangin mahaifinta ne ita kuma ga abinda Allah ya bata,

sai dai ta tashi tayi sallah har ta gama m

almalar tuwon na dubu goma sha biyu kaman yadda

suka saba ta

ɗ

ora miyan ta kala biyu da Alaiyahu da kubewa, bayan ta gama ne inna Asabe ta

tarfa mata sauran ƙasan tukunyar tukun a cikin tukunyar miyan Alaiyahun da ta gama

kwashewa ganin sai kashe jiki t

ake saboda yunwa bata son abinda ya samu kayan tallatarta

sam.

Sai da tayi wanke wanke tas har da kwanukan safe na tallar inna Larai kan ta shirya ana kiran

Magrib tayi sallah ta fice bakin kasuwa, yanzu ma bata kula kowa abincin kawai take sayarwa

h

ar wuraren takwas ya ƙare ta tattaro ta dawo gida dama tun shidda ta sayi kifin miyan safe ta

ba almajiri ya kaiwa inna Larai za ta saka cikin ƙanƙara ji take kasusuwanta kaman ana sarawa,

ku

ɗ

in kawai ta ba inna Asabe ta wuce

ɗ

aki ta kwanta idanunta na k

allon sama, shikenan ita

kuma a haka rayuwarta zai cigaba da tafiya? Shikenan ita kuma haka za ta ƙare? Don dai ta

san kap kauyen dutsen-wai babu namijin da zai tare ta da sunan soyayya babu kuma gidan da

za su amshe ta yadda ake ganinta annoba kuma duk

gidan da ta shiga sai ta wargaza kuma sai

an yi mutuwa kan ta fita tayi zurfi cikin tunanin ta kawai taji ana dukan kyauren palangen dake

kare kofar akurkin da

ɗ

an banzan ƙarfi sai da ta razana ta miƙe tsaye ba tare da ta sani ba.





🖤

Gureenjoh

🖤

HAIHUWA DA HANJI

(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin

(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763

Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*002*

Nannauyar numfashi ta sauƙe sai kuma ta fita daga tsoro ta shiga fargaba, kawu ne! Me ta

yi?

Jikinta a sanyaye ta miƙe tsaye ta turo kofan ta fito.

"Iskancin naki ya kai ina ƙiranki kina ji na ki yi min banza ko? Ko har kin tafi meeting naku na cin

ɗ

anyen naman mutane ne?"

Girgiza kai ta yi tana wasa da yatsun ta murya na

ɗ

an rawa ta fu

rta

"Ka yi haƙuri kawu bacci na fara ne"

Tsaki ya ja yana jefanta da mugun kallo, babu yadda ya iya ne kawai yarinyar ke zaune gidan

shi in ba haka ba babu abinda zai sa ya ajiye makashiyar mamarshi da 'yan uwanshi har ya ke

bata abinci tabbas da ana

kashe mutum a sha a banza da tuni ya yanke wuyanta ya jefar da

gawar daji tsuntsaye sun cinye, duniya in akwai wacce ya tsani ko inuwarta ya gani ya biyo

bayanta.

"Ba dai a mawankin chan za ki bar mana kwanuka su kwana ba kan safe duk shedan ya bi ya

fitsare mana kwanuka? Oh ko so kike duk ki kashe mu ne ki huta?"

Lip

ɗ

inta na ƙasa ta

ɗ

an datse a hankali kan ta saki ta furta

"Kayi hakuri zan yi"

Ya ja tsaki kan ya juya ya wuce

ɗ

akin inna Asabe.

Mawankin dai ta wuce akwai

ɗ

an guntun omo haka ta

fara wanke wanken idanunta kaman za

su cire saboda ra

ɗ

a

ɗ

in bacci har kifewa take yi bisa kwanukan tana tashi sai da kusan duk

kowa yayi bacci a gidan kan ta gama kifewa ta wuce nata akurkin sanyi kaman zai kasheta ta

shige cikin zaninta bayan ta sauya h

ijabi zuwa busasshe dukunkune haka tayi baccin. Kaman

jiya yau ma dai kowani

ɗ

an adam na kwance yana bacci haka ta fita tsakar gidan ta shiga aikin

abincin tallar inna larai.

Ba don ba'a sabo da wuya ba zata iya cewa wahala ya riga ya zama jininta, ba

ta san yadda

zata fassara rayuwa ba sai dai ta san ƙaddararta mai matuƙar zafi ne da ta kan rasa sanyi ko

sama ko ƙasa a duk sadda ta rura wutar ta.

Bata da farin ciki ko

ɗ

aya bata da mai tambayar damuwarta ko ciwonta har ma da bukatuwarta

waenda suk

e tare da ita amfana da ita ka

ɗ

ai suka iya amma ita bayan mafaka da kwanon abinci

sau

ɗ

aya a wulakance bata anfanuwa da su ko ta wani

ɓ

angare, manyan su zaga, matasan su

daka su kuma hantara yaran su wulakantata bata da bakin magana saboda ita

ɗ

in ta rig

a ta

zama annoba...

Eh annoba zata ƙira kanta kaman yadda kowa ke kiranta an haife ta da rashin sa'a tunda tana

ciki watanninta basu wuci biyar ba Allah ya kar

ɓ

i mahaifinta, a wurin haihuwar ta Allah ya kar

ɓ

i

mahaifiyarta ta zama cikakkiyar marainiya

daga ranar da ta fa

ɗ

o duniya, kakarta ta wurin uba ita

ce ta raine ta kan madara ta bata tarbiya ilimin addini da boko har ta shekara takwas ita ta sani

a matsayin uwa kuma uba, ta samu gata na iya tsawon lokacin da tayi da kakarta har

makarantar gom

nati na boko ta sanya ta kan kwatsam mutuwa ta yanke wannan ƙauna tun

daga sannan aka fara jita-jitar ita

ɗ

in Mayya ce! Kuma duk wanda ta ra

ɓ

a zai mutu.

Tsangwama ya fara yi mata yawa a hannun ƙanwar babanta da ta koma Inna Amina ta sha

baƙar wahala k

asancewar inna Aminar ma cikin gidan yawa take, mijinta kuma ba wai ya kar

ɓ

e

ta bane zaman dole take mishi a gida hatta abincin gidan bai amince a saka mata ba duk

abinda aka sanyawa inna Aminar suke ta

ɓ

awa a tare, ta samu innar tata da ciki a lokacin

k

awunta ya ƙi yarda ya ƙarbe ta tunda su uku kawai kakarta ta haifa.

Kawu ne babba sai babanta tukuna innar dole dai wurinta take lalla

ɓ

a wa rayuwarta.

Wata rana inna Amina ta tashi da nakuda babu wani cima mai kyau, babu cikakken kulawa da

ya kamata m

ace mai ciki ta samu, bata ta

ɓ

a zuwa awo ba ana rayuwa ne cikin wahala haka ta

tashi nakudar a gida aka kira unguwarzoma ta ci azaba ko da ta haihu babu rai ita ma bata jima

ba jini ya balle mata ko kan a ce an yi wani yunkurin Allah ya kar

ɓ

i abin shi, k

o gawar inna da

jaririyarta ba'a binne ba aka sanya Afeefah gaba da zagi, cin mutunci, baƙaƙen maganganu

babu irin wanda ba'a jefeta ba a lokacin da take jin tashin hankali da damuwar rashin innarta

Aminan.

Ta ga mutuwar kaka amma bai ka

ɗ

ata kamar na

inna Amina ba saboda yadda ta mutun a

wulakance cikin sakacin miji da kishiyoyi ta yi kuka kaman babu gobe, har jifan ta da dutse ake

yi in ta fita a haka kawu ya dawo da ita gidan shi tana da shekaru 10.

Matanshi basu kar

ɓ

eta ba, babu wacce take yar

da har yanzu ta shigar mata

ɗ

aki ko na yaransu

dole aka buga mata keji don ba shi da maraba da keji aka sanya buhu aka bata taburma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login