Showing 39001 words to 42000 words out of 186858 words
/>
_Turaren Kaya_
_Gyaran jiki_
_Na amare_
_Da masu jego_
_Da sabulai masu gyara fata_
*_Da magungun nan mata_*
_Irin su kaza_
_Tantabara_
_Tsumi_
_Gumba_
_Zuma_
*_Duka akan farash
i mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan
👇🏼
_*
Wushishi road KADUNA
08067807620
09057713999
_________________________
*_Chapter Thirteen_*
............Gaba
ɗ
aya jin su Hibba ya
ɗ
auke
ɗ
af a cikin kunnuwansu
lokaci guda. Dukansu sun zuba masa ido tamkar wa
ɗ
anda sukai gamo da wata baƙuwar hallita. Namiji ne tsayayye da za'a iya kiransa namijin gaske a kowacce irin nahiya ko ƙabila. Sanye yake cikin shadda oxblood da ta fidda ainahin kalar fatarsa mai sheƙi. Fu
skarsa cike take da ƙasunba da wani madaidaicin gemu mai kama da na gayu irin na ustazan wanan ƙarnin (
😳
Bily
🤐
).
A kallo
ɗ
aya zaka fahimci rashin son hayaniya daga garesa. Da alama kuma ba mutum bane mai yawan sakewar fuska a mu'amula ko a yanayi
.
Ganin sun shagala wajen kalon sa ya saki wani shegen murmushi yana ƙarasa takowa gaban Hibbah gab. Haka kawai takaici ya kama Hibbah da kallo guda tai masa ta
ɗ
auke kanta tun
ɗ
azun. Cikin
ɓ
ata fuska da yatsineta ta ce, “Malam lafiya? Tun
ɗ
azun
ka ke ta binmu sai kace wani mai gadin mu”.
Murmushi ya kuma saki, jerarrun haƙoransa farare na bayyana. Ƙoƙarin saka ƙwayar idanunsa cikin nata yake, amma sai taƙi. Sai ma harara da ta sake zuba masa ta
ɗ
auke kai. A hankali taja siririn tsakin
da yasa Hafsat da Zahidah shurin ƙafarta da galla mata tagwayen mintsini.
“ALLAH ya isa”. Ta fa
ɗ
i tana hararsu bayan ta saki ƴar siririyar ƙarar data saka baƙon nasu ƙyalƙyalewa da wata dariyarsa da ke fita a nutse. Harara ta sake zuba masa zata
bar wajen yay saurin shan gabanta.
Haushi ya sake kama Hibba. A tsiwace tace, “Malam kana shigarmin hanci fa”
“Ba malam
ɗ
in bane ai. *_Muhammad Shuraim Aliyu_* ne. Idan kina son nabar shiga hancinki address da number kawai nake buƙata”.
“Baka da man kai” ta fa
ɗ
a tana ra
ɓ
awa ta gefensa ta wuce batare da ya samu koda harar ba yanzun. Badan Zahidah da Hafsat sun so ba sukace masa (bye) suna bin bayanta. Motarsa yay azamar komawa ya cigaba da binsu duk da uban sauri da Hibbah ke zabga
wa tamkar zataci da ka. Jitake a ranta da da akwai lungunan da zatabi ya kaita gidansu da shi zatabi dan taga ƙarshen naci. Sai dai kash, tun daga islamiyyar har zuwa gidansu layine
ɗ
o
ɗ
ar.
Itace ta fara shigewa gidansu, dan ata wannan hannun itac
e farko kafin su Hafsat. Dan haka mai mota Shuraim ya tsayar da su Zahidah. Dole suka tsaya dan baiyi kama da wanda za'a cigaba da yarfatawa ba.
“Kuyi haƙuri fa na takura muku, naga maha
ɗ
i nane babu damar yin sakaci. Dan ALLAH miye sunan ƙawarku
?.”
Kallon juna Hafsat da Zahidah sukayi. Roƙonsu da ya sake yi ne ya saka Hafsat cewa, “Muhibbat! Aliyu Hamza”.
“Masha ALLAH, nice name. Nan ne gidansu?”.
A taƙaice suka bashi amsa da eh. Shima sai bai sake jan zancen ba yay musu
godiya ya koma motarsa ya wuce.
“Gaskiya Hibbah ƴar yawa ce, amma fa guy
ɗ
in nan ya ha
ɗ
u ALLAH. Yaci sunansa Muhammad Shuraim”. Zahidah ta fa
ɗ
a tana lumshe ido.
Hafsat tace, “Shiyyasa ai na fa
ɗ
a masa sunanta. Waya gaya mata ana sakaci d
a irin wa
ɗ
an nan gayun a wanan ƙarnin.”
“Barta ai zamuyi maganinta. ALLAH dai yasa har a hallaya haka yake, da kuma zancen aure yazo mu raƙwashe. Dan zanso Hibbah ta auri guy
ɗ
in nan kodan ta kere sa'a a cikin shaggun su Amlah
ɗ
in gidansun can. Ma
su shegen kakkafi da son asani. Su adole suna hawa motoci. ALLAH idan suka ga guy
ɗ
in nan sai sun haukace. Sai dai kuma ya musu nisa da na Hibbarmu ne”.
“Insha ALLAH”. Cewar Hafsat tana ƙyalƙyala dariyar mugunta. dan harta hango idon ƴan gidan su H
ibbah da kullum suke mata iyayi akan su sun waye, sun girmeta. Suna hawa motocin da Abbansu ya saya musu su ƴaƴan so banda Hibbah.
★
_____________
★
____________
★
A
ɓ
angaren Master kam tunda suka koma L.E street shida yaransa sukai luf a
binsu tamkar basa ƙasar. Da wannan damar jami'an tsaro suka sami na barazanar cewar ya tsorata da harin da suka kai masa ne, ƙilama sun sami nasarar kashesa dan sun harbesa.
A lokacin da yaga wannan rahoto ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba ƙwarai d
a gaske, ya saki wani malalacin mmurmushi mai ƙunshe da ma'anoni masu yawan gaske da shi ya barma kansa saninsu. Har cikin ransa yana mamakin sai yaushe ne ƙasarmu ta gado zata canja ne? Ji dai shareriyar ƙarya da wan
ɗ
an da suke amsa sunan iyaye manyan ƙas
a suka karkace suka gilla dan kawai su burge su kuma kankaro ma kansu girma.
Yaransa kansu abin ya basu dariya. Har cikin ransu suna tausayin ranar da Master
ɗ
insu zai maida murtani ga wa
ɗ
an nan mutanen. Inhar bai kaisu kwance ba tabbas sai ya saka
su kuka da hawayensu ko su ajiye aikin koda lokacin ritaya
ɗ
insu baiyi ba.
Shi ba'a sakashi yin abu dole, dan haka baice uffanba sai ma sake lafewa da yay domin tabbatar da zancen nasu. Yayinda a gefe kuma idanunsa ƙur akan batun matar g
wamna da hukumar sa'ido akan ta'annati da kayan gwamnati take bin cika har yanzun. Jira suke suyi wani sakaci ko ka
ɗ
anne ya sake banka
ɗ
o wasu surukan nata ma duniya harma da su kansu...
____________
★
__
★
__
★
___________
“K ku
ma lafiya kika shigo kina cikama mutane baki da iska?”. Ummi ta fa
ɗ
a tana kallon Hibbah da dawowarta kenan da ga islamiyya.
“Babu komai Ummi. ALLAH yunwa nake ji ne”.
“Shi abincin da kika tafi da shi fa?”.
“Ummi naci fa. Kawai wa
ta yunwar dai nake sake ji”.
“To ALLAH ya ƙyauta, sai kije ki fara yin wanka kiyi salla sannan kizo kici”.
“Ummi dan ALLAH ki barni in fara ci ni dai”.
Komai Ummi bata sake ce mataba. Sai ma miƙewa tai ta shiga takawa a hankali do
min zuwa
ɗ
akinta tai salla. Dan har yanzu jikin nata bawai yayi ƙarfi yanda ya kamata bane. Abincin ma Yaya Usman ne ya yisa kafin su wuce tasu Islamiyyar.
Sai da Hibbah taci tai nak da abinci sannan ta shige
ɗ
akinta. Bata fito ba sai wajen 8:30 da t
ajiyo hayaniyar yayunta. Cike da
ɗ
okin dawowar tasu ta fito. sai dai ganin harda Isma'il ya sata yin turus.
Komai babu wanda ya ce mata a akan yanayin nata. Sai ma tsokanarta fa
ɗ
a da Ammar ya shigayi. Amma sai bata tayashi sunyi ba. Masifa ma taketa
faman yi a ranta na yanda yayun nata suka sakema Isma'il
ɗ
in kai kace
ɗ
an gidan ne. Shi kansa yanda yake komai kansa tsaye sai ka rantse gidansu ne.
Bata wani jimaba tai musu sai da safe ta shige, ta barsu a falon suna kallon ball suna hira da cin a
binci. Ummi ma tunda ta leƙo suka gaisa da Isma'il
ɗ
in ta koma ciki abinta. Dan haka Hibbah bata san sanda Isma'il yabar gidan ba.
Washe gari dai an tafi islamiyya babu fushi. Sai dai kuma damuwar ƴan sandan can da ke damunta har yanzu ya sa
kata komawa wata silent kwana biyun nan. Ko magana ma bata cika sakin jiki tayi ba. Sannan har yanzu bata sake hawa computer ba. Dama wayarta tunda ta dawo take a kashe taƙi ta kunna.
Yau ma suna fara tafiya a kan hanyarsu ta zuwa islamiyya ta fahim
ci ana binsu a baya. Wani takaici ne ya turnuƙe ta dan tsaf ta gane guy
ɗ
in jiya ne da tun a ƙofar gate ta watsar da lamarinsa. Ba kuma ta sake tunawa da shi ba sai yanzu da taga motarsa. Sam Zahidah da Hafsat su basu lura da shi ba. Hakan yasa Hibbah fusk
ewa batace komai ba har suka shige cikin islamiyya.
Ƙarfe biyar suka ta shi yau ma tamkar kowane weekend. Da ga nan kuma sai wani satin. Gaba
ɗ
aya ta sake watsar da lamarin wani Shuraim. Amma a mamakinta sai gashi ta sake ganin yana biye da su
har gida. Kamar
da safe yanzu ma bai yunƙurin fitowa ba. A yanzu kam su Zahidah sun ganshi. Koda sukaima Hibbah magana sai tai musu tsaki ma.
Ƙyaleta sukai ganin shima bai fito a motar ba.
★★
Duk yanda Hibbah taso watsar da la
marin Shuraim sai hakan bai yuwu ba yau. Dan lokaci-lokaci yakan fa
ɗ
o mata a rai. Sai dai takan ja tsaki da murgu
ɗ
a baki tamkar tana a gabansa. Har takai abinda takeyi
ɗ
in ya bama Ummi haushi ta balbaleta da fa
ɗ
a har su Yaya Muhammad suka shigo.
Sun
e suka bama Ummin haƙuri da fara tambayar Hibbah cikin lallashi ko wani abu ke damunta ne?. Sam batasan wani boye-
ɓ
oye ba. Musamman ma awajen yayunta da suke da matukar shaƙuwa da juna. Kanta tsaye ta shiga basu labarin abinda takema tsakin.
“Woow
, ƴar Tanee
ɗ
in Ummi anyi saurayi Congratulations. Yau
ɗ
aya a tarihi dole na rubuta na ajiye na ha
ɗ
a da shagalin barbaje kolin fati na musamman a gidan nan nayi suriki a matsayina na yaya mai lasisin cin gadon Muhibbat Aliyu Hamza (Tanee)”. Ammar ya fa
ɗ
a y
ana tafa hannaye cike da tsokana. Filo Yaya Abubakar ya
ɗ
auka ya jefe sa da shi. Dariya gaba
ɗ
ayansu suka kwashe da shi saboda yanda Ammar ya baje a ƙasa da bata fuska alamar yaji zafi..
Hibbah kam dariya sosai take masa harda fa
ɗ
owa saman kujera.
Ta saka yatsun hannunta a kunne tana masa gwalo kamar yanda yara keyi. Filon da aka jefesa da shi ya
ɗ
auka zai jefo mata ta tashi da gudu tai hanyar
ɗ
akinta.
“Ummi kanta sai da tai dariya. Cikin dariyar ne ta ce, “ALLAH dai ya shirye ku, kai da Tan
ee
ɗ
in bansan wanda yafi wani shashanci ba. Ni tashi ka
ɗ
akkomin magunguna na a
ɗ
aki tunda ita ta gudu nasan ba sake dawowa zatai ba kuma”.
Amsawa Ammar yayi da to yana mikewa ya nufi
ɗ
akin Ummin. A dai-dai kuma wanann lokacin Abba da hajiya mama d
a wasu tsoffin maza biyu suka shigo falon da sallama.
Da ga Ummi har yaranta da mamaki suke kallonsu, musamman ma Abba da basusan ya dawo gidan ba. Tsoffin kuma Ummi ce kawai ta sansu. Da ƙyar ta iya bu
ɗ
e baki cikin ƙarfin hali ta ce, “Kawu sannunk
u da zuwa”.
Farin ne kawai yace, “Uhumm”. Ɗaya kam bai tanka ba. Sai dai bin su Yaya Muhammad da yake da kallo tamkar idanunsa zasu fa
ɗ
o ƙasa.
Yaya Muhammad da ya lura da kallon ƙurullar da kuma yanayin da Ummi ta shiga tamkar na ru
ɗ
ani ya
saka shi fara gaishesu. Haka yasa suma sauran ƙannensa fara gaisuwar.
Amsa musu sukai suna cigaba da kallonsu. Yayinda hajiya mama keta faman ƙya
ɓ
e baki. Abba kam sai wani harare-harare yakeyi.
Ummi tai ƙasa da kai cike da ladabi ta hau g
aishesu itama. Basu wani amsa mata da ƙyau ba. Sai ma baƙin tsohon ne a kausashe ya ce, “Uh lallai Asiya an samu guri kam tabbas. Ga manyan sojoji kuma a gefe masu tare miki fa
ɗ
a. Dama irin wanan ai ake gudu akan auren masu asali irin naki. Saboda shi hali
naso yakeyi har jikokin bayan-baya. Gashi ko mun gani yau da idanun mu”.
Idanu Ummi ta lumshe a hankali kanta a ƙasa. Wasu zafafan hawaye suka silalo saman kumatunta. Sai dai cikin dabara ta kai hannu ta share dan kar ƴaƴanta su gani. Cikin dauriy
a da juriyar da kowa ya santa da shi
ta
ɗ
ago murmushi a saman fuskarta. “Kawu ina fatan kunzo lafiya?”. Ta fa
ɗ
a domin son kauda wancam zancen da ya fara.
Sai dai sam bataci nasara ba. Dan kuwa hajiya mama ce ta amshe da fa
ɗ
in, “Ni ko zan fa
ɗ
a maka h
ali naso yake Hannafi, dan kuwa gashi nan a zuri'a ta. Wlhy badan jinin
ɗ
an inna (babansu Hibbah) na yawo jikin wa
ɗ
an man yaran ba da tuni na da
ɗ
e da sallama su, babu wanda ya cuceni sai malam da ya ƙarrafa wannan auren da har na mutu bazan ta
ɓ
a daina kuka
da ALLAH wadai a kansa ba. Wai fa kuga wa
ɗ
an nan sanƙama-sanƙaman yaran ne babu mai ko neman aure. Kuma uwarsu ta zuba musu ido saboda ita
ɗ
in bata hanyar.......”
“Wa
ɗ
an nan kuma fa? Da ga ina?”. Cewar Ammar da ya fito da ga
ɗ
akin Ummi yaci karo
da abinda bai bari ba. Furucinsa kuma ne ya katse zancen da Hajiya mama ta
ɗ
akko tiryan-tiryan.
Babu wanda ya bashi amsa. Sai zuba masa ido da tsoffin sukai tare da Abba. Baki ya bu
ɗ
e zai sake magana Ummi ta girgiza masa kanta. Kansa ya
ɗ
auke kawai
tare da durƙusawa gabanta ya na ajiye
ɗ
an basket
ɗ
in da magungunan nata ke a ciki. Ɓalla mata ya shigayi yana miƙa mata tare da saka mata ruwa akan baki.
Wani uban salllami farin tsohon nan ya shiga jerawa yana tafa hannaye. “Kai mizan gani haka ni B
allo (Bello
😂
). Wannan wane irin kafurcine kuma haka Hasiya?. Wannan ƙurmisheshen gardin
ɗ
an ke baki ruwa a baki kuma?. A to lallai zancen Hannafi gaskiya ne. Da alama ma ke kinfi uwar taki iya shege”.
A fusace Yaya Umar ya miƙe zai bar falon. Abba
ya katsesa a gadarance da fa
ɗ
in, “To mara mutunci da baiyi gadon arziki ba sai ka tsaya dan zuwan nakune ai”.
Ido Yaya Umar ya rimtse da ƙarfi yana dunƙule hannunsa.
“Kai fitsararre, idan shi ka rainashi ai mu ka
ɗ
aga mana ƙafa kodan rashin
saninmu da kai ko.”
Ƙafa Yaya Umar ya
ɗ
aga zai cigaba da tafiya wasu hawaye masu zafin gaske na gangaroma kumatunsa.
“Dawo ka zauna”. Umarni da ga Ummi ya hanashi ajiye kafar da ya
ɗ
aga
ɗ
in.
“Iyeee! A lallai Haƙilu kuna ganin jalalar
rayuwa. Wato itace kawai mai sawa da hanawa akan ƴaƴan, bayan wahalar da kaci na kula da su tsahon shekaru. Tabbas Hasiya kinyi asara kekam.
Da sauri Ammar ya
ɗ
ago ya kallesa. Ya miƙe tare da nuna Kawu Bello da
ɗ
an yatsa cikin kaushi da
ɗ
aci yace
, “Kai