Showing 90001 words to 93000 words out of 186858 words
zai mana aikin”.
“Ni duk ban musa maka kun raini master da wani blaa blaa
ɗ
in zancenka ba. Yanzu so nake ka kirasa ka bigi cikinsa ko zamu san inda su Asiya
suke. Sannan duk yanda za'ai inason ka samamin ma'aikacin banki da zaimin aikin sirri ku
ɗ
a
ɗ
en dake a accaunt
ɗ
in Aliyu su dawo accaunt
ɗ
ina baki
ɗ
aya, ka kuma saka shi Master
ɗ
in nemo mana lauyan Aliyu duk inda yake”.
“Maganar kiran Master ba damu
wa bane, hakama zancen canja ku
ɗ
i zuwa accaunt
ɗ
inka koshi zai iya mana wannan aikin. Matsalar
ɗ
aya ce ka yarda Master bazai zama shashasha akan mace ba. Macen ma ƙaramar yarinya kamar
ɗ
iyar
ɗ
an uwanka”.
“To naji na yarda kirashi”. Abba ya fa
ɗ
a
badan ya yarda
ɗ
in ba har cikin rai. Dan yanaji a jikinsa Hibbah tayi shu'umcin na mata akan Master. Sai dai shi A.G tsananin yardar da ya bama Master
ɗ
inne yasa bai fahimtaba.
“Kiran Master bazai yuwuba a yanzu. Amma zan tura masa saƙo da kansa z
ai biyo lokacin da yaga ya dace”.
“To ashe kuwa yau a gidanka zan kwana”. Abba ya fa
ɗ
a kansa tsaye.
“Gidana kuma?”.
“Ƙwarai kuwa. Dan babu inda zanje saina tattauna da Master.
“Humm Alhaji Halilu kai fa sam baka da haƙuri. Maganar zama
anan bazai yuwuba. Kaje zan sameka gidan hutawarka. Kokuma mu ha
ɗ
u wajen su Alhaji Alu”.
“Kawai jeka shirya ina jiranka mu tafi tare”.
Ɗan tsaki A.G yaja dan Abbah ya takura masa. sai dai babu yanda ya iya dole yace ya jirasan to.
★★★★★
A
ɓ
angaren Hibbah kam Shawarar data yankema zuciyarta ne ya sata sauka a gadon ta nufi toilet. Fuskarta ta wanko ta fito.
ɗ
aukar tray
ɗ
in kwanikan da tai breakfast tai ta fita da addu'ar ALLAH yasa yabar gidan. Babu inda
ta sani amma tsabar ƙarfin hali yasata yarda zata gane. Taji matuƙar da
ɗ
in ganin baya falon, ta
ɗ
an tsaya yima falon saman kallon tsaf. Sosai tsarinsa ya mata ƙyau. Ga wani ƙamshi mai da
ɗ
i da sanya
zuciya nutsuwa na tashi duk da mayataccen ƙamshin turarensa
na neman dannewa. Tunaninta ya bata baza'a samu kitchen anan ba, dan haka ta nufi downstairs
ɗ
in kai tsaye.
Tunda ta fara tako staps
ɗ
in su Adam dake zaune a dining suna breakfast suka
ɗ
ago kusan a tare. Hibbah da ke sakkowa tayi
ɗ
an turus ganin
matasan samari kusan bakwai. (Su kuma wa
ɗ
an nan fa?) tai tambayar a zuciyarta. Kai tsaye zuciyarta ta sake ayyana mata (Kin manta minene aikin mai gidan, ba dole kiga maza ba tare da shi). Tsaki taja a ƙasan maƙoshi tana
ɓ
ata fuska. Akan la
ɓɓ
anta tace, “As
ararru”. Tana cigaba da sakkowa.
Suko su Habib tuni sun maida kawunansu ƙasa tun kallo guda da sukai mata. Tana sakkowa step
ɗ
in ƙarshe suka ha
ɗ
a baki wajen fa
ɗ
in, “Barka da safiya aunty”.
“Aunty?!” ta fa
ɗ
a tana kallonsu cikin ware idanu.
Sai kuma ta turo baki, “Kujimin mutane dan ALLAH. Rusa-rusa daku zaku wani kirani aunty wannan ai zagi ne”.
“Tofa ga mai gayya mai aiki, Kunga wata zuƙeƙiyar halitta.
Cewar Salis a hankali.
Zungurinsa Zaidu yayi cikin magana ƙasa-ƙasa yace,
“Karkai maganar banza matar babban yaya ce, akwai tazarar taku”.
“A gafarceni wlhy su
ɓ
utar baki ce”.
Baba Saude da ke zaune da ga can falo tana murmushi ta ce, “Kinga manta da wa
ɗ
an nan shaƙiyyan
ɗ
iyata. Keda baki da lafiya ai da baki fitoba
kinma barsu zanzo na
ɗ
auka.
Sai da Hibbah ta
ɗ
an harari su Musbahu da murgu
ɗ
a baki duk da bawai jin mi suke fa
ɗ
a tayi ba sannan ta maida dubanta ga baba Saude tana sakin murmushi. “A'a babu komai mama. Ai naji sauƙi Alhmdllhi. Inane kitchen
ɗ
in?”
Cikin jin da
ɗ
in wayewar kan yarinyar da ko alamar baƙunta babu tattare da ita ta nuna mata hanyar kitchen. Kan Hibbah tsaye ta nufi kitchen
ɗ
in kuwa. Komai ƙal fes tamkar ba girki aka kammala a cikinsa ba. Ganin hakan yasa Hibbah ajiye kwanikan a wa
jen wanke-wanke ta fara yunƙurin wankewa.
Motsin wanke-wanken natane ya saka Baba Saude shigowa. “Ya ALLAHU ƴar nan inake ina wanke-wanke kina fama da kanki. Ki barsa su Habibu zasuzo su wanke idan sun gama shiritar cin abin nasu”.
(Uhm ai
da yake ƴan daudu ne) Hibbah ta ayyana a ranta. A fili kuma sai tai
ɗ
an murmushi. Karki damu mama zan wanke kawai. Ina maza ina wanke-wanke banda dai gidan naku a haguggunce yake”.
Baba saude da ba fahimtar ina Hibban ta dosa tai ba tai ƴar dariya
da fa
ɗ
in, “Ta
ɓ
. Ai indai wa
ɗ
an canne komai yi suke har girki. Babana ya musu horon tarbiya mai ƙyau ai. Sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi”.
Ɗan kallonta Hibbah tayi danjin abinda ta fa
ɗ
a. Sai kuma ta saki guntun murmushi. “Mama iyayensu dai, s
hi da ya samesu da ga sama ai ba'ace tarbiyyarsa ba”.
“To ƴar nan ai shine iyayen nasu. Dan dukansu da kike gani nan shi yay wahala da su tun daga gidan marayu, yawancinsu ma tun suna jarirai. Tarbiyarsa ce, horansa ne. Shine uwa a garesu shine kum
a uba. Shine dangi. Ai samun mutum irin babana a wannan zamanin abune mai matuƙar wahalar gaske. ALLAH dai ya saka masa da alkairi ya cigaba da dafama rayuwarsa.”
Karon farko da Hibbah tai sagade tana kallon Mama Sauden. Dan ba karamin dukan zuciy
arta zancen yayi ba. Sai kuma tunawa da fasikancin da su Abba ke aikatawa da shi da tai yasata juyawa tana ta
ɓ
e baki. A ranta
tace (dan ya taimakesu shine kuma ya ajiyesu yana
ɓ
ata musu rayuwa kenan. ALLAH ya saka musu).
Baba Saude da bata fahimci
abinda Hibbah tai ba ta cigaba da bata labarin ƙoƙarin Master da jarumtarsa akan su Khalid na tsayama rayuwarsu har suka sami ingantaccen karatu a fanin islama da boko. Hibbah dai gya
ɗ
a kai kawai take, dan zancen wani na shiga wani na fitane kawai. Ita du
k wannan tarin alkairin nasa bawai gani take ba sam. Tsiyar da suke aikatawa da su Abba ta goge mata duk wannan farin nasa baƙi ya maye gurbinsa.
Sai dai cikin son bugar cikin Baba Sauden sai catai “Uhm lallai yaci sunan nasa Muhammad Shuraim”.
Baba Saude tai ƴar dariya da fa
ɗ
in, “Wai ƴar nan kinko iya fa
ɗ
ar sunan. Ni wlhy wahala yake min sunan nan nasa na larabawa. Shiyyasa nafi ganema kiransa da baba na saboda asalin sunan sa”.
Gaban Hibbah ne ya fa
ɗ
i. Kenan sunansa ne Muhammad Sh
uraim
ɗ
in? Da sauri ta juyo tana duban baba Saude. “Oh mama bayan Muhammad Shuraim
ɗ
in yana da wani sunan yanka ashe?”.
Baki Baba Saude ta bu
ɗ
e zata bama Hibbah amsa Habib ya shigo kitchen
ɗ
in wuff tamkar an jehoshi. Waya ya mikama Baba Sauden. “B
aba Master na magana”.
Cike da farin ciki Baba Saude ta amsa wayar takai kunnenta da fa
ɗ
in, “Alo babana”.
Batare da Hibbah tasan mi ake fa
ɗ
a da ga can ba taga Baba Saude na gya
ɗ
a kai da fa
ɗ
in, “To to babu matsala babana sai a dafa maka. ALL
AH ya dawo dakai lafiya”. Da ga haka ta mikama Habib wayar. A dai-dai nan kuma su Salis suka shigo
ɗ
auke da kwanikan da sukaci abinci.
Ganin Hibbah ke wanke-wanke suka zaro idanu waje. “Aunty da kanki? Rufa asirinmu kar boss yay mana walmakalufatu”.
Cikin bata fuskar haushi biyu Hibbah ta juyo tana dubansu. “Malami kubar wani kirana da Aunty niba auntynku bace.”
Dariya kawai sukayi batare da sunce mata komai ba. Sai ma Habib da ya sake fa
ɗ
in, “Aunty kibar wanke-wanken zamuyi Please”.
Harara ta dallara masa. Yay saurin
ɗ
ora hanunsa saman baki yana fa
ɗ
in, “Na tuba”.
Dauke kanta tai batare data tanka ba. Idris ya matsa tacan gefe yana tattare hanun rigarsa. Bara to na miki
ɗ
auraya kawai. Banza tai masa ta cigaba da wanke kwanik
an a cikin kumfar data ƙara ganin sun ƙaro kwanikan. Wannan taruwar tasu a kitchen
ɗ
in ya hanata jin
ɗ
ayan sunan na Master. Hakan kuma ba karamin takaici ya sakata ba shiyyasa ta ha
ɗ
e fuska har suka kammala wanke-wanken bata sake kulasu ba. Sai sauraren hi
rarsu da Baba Saude da takeyi. A ranta kuwa sai gulmarsu take wai sun cika surutu.
Suna kammala wanke-wanken Baba Saude tace taje ta huta zata
ɗ
aura girkin rana. Cike da jin da
ɗ
in hakan Hibbah tace zata tayata. Duk yanda Baba Saude ta lalla
ɓ
ata a
kan tabari sai ta ƙara jin sauƙi ta dage zatayi. Fahimtar yarinyar babu ruwanta akwai sauƙin kai yasa baba Saude barinta sukai girkin tare. Kusanma Hibbahr ce tayi komai ka
ɗ
an baba sauden ta tayata.
Har sukai girkin suka ƙare tas Habib na nane dasu
a kitchen
ɗ
in yaƙi fita. Hakan ya ƙarama Hibbah takaici matuƙa dan bata samu yanda take so ba.
Sai dai cikin sa'a Baba Sauden ta fita jera abinci dining dai-dai Habib
ɗ
in yana fita a kitchen
ɗ
in saboda lokacin salla yayi zasuje massallaci.
Harara ta raka bayansa da shi tana sauke numfashi, dan duk surutunta da rawar kai ta kula wa
ɗ
an nan samarin sun damata sun shanye. Sauran kayan da suka rage ta
ɗ
akko ta fito zuwa dining
ɗ
in itama. Tana tsaka da taya baba Saude shirya kwanikan taji ƙar
ar waya nokia. Da sauri baba Saude ta nufi falon tana fa
ɗ
in, “Tofa wake kirana ni Saudatu?”.
Wani
ɗ
an tsalle Hibbah tayi dadi kamar zai karta. Sai kuma tai saurin kama kanta ganin baba saudan ta dawo dining
ɗ
in tana fa
ɗ
in, “To nidai Bara'u banajin
ka sam. Nasan dai so kake kayi magana da Zaituna gashi kuma bana gida ina wajen aiki. Ka kira wayar Habu mai shago sai ya bata dan nasan yanzu ta dawo gida”. Da ga haka ta cire wayar a kunnenta tana mita.
“Kai samarin zamani dai babu kunya. Kigafa
wanann ja'irin
ɗ
an makwafcinane. Akwai ƴar maƙwaftanmu da yake so bata da waya kullum sai ya kira a wayata sunyi wayar dare. Yau kuma bansan wace fitina tasashi kira da ranar ALLAH ba”.
Hibbah da ke cikin jin da
ɗ
i tai ƴar dariya kawai.
Bab
a sauden ma sai bata sake cewa komai ba ta ajiye wayar a dining
ɗ
in ta cigaba da aikinta. Aiko wani sanyi ya sake sauka a zuciyar Hibbah. Cikin dabara da wayon da ALLAH ya bata ta shiga gyara zaman kayan dining
ɗ
in harta iso ga wayar. Cikin dabara ta
ɗ
auka
tai ƙasa da ita tasa a silent. Kafin ta faki idon Baba Saude ta tura a cikin zani.
A dai-dai wanann lokacin Master ya turo ƙofar falon ya shigo da sallama ciki-ciki. Cike da mutuntawa a garesa baba Saude ta washe baki tana fa
ɗ
in, “Babana sannu da
dawowa”
Saurin juyowa Hibbah da sam ba jin sallamarsa tai ba tayi, idonta ya sauka akansa dai-dai yana gya
ɗ
a ma Baba Saude kansa. “Baba ya gidan?". Ya fa
ɗ
a a taƙaice yana ƙoƙarin wuce Hibbah da ya nuna tamkar ma bai ganta a falon ba.
“Gida
Alhmdllh babana. Dan yau na ƙara samun ƴar tayen hira”.
Sarai ya fahimci Hibbah take nufi, dan haka ya fara hawa steps
ɗ
in kawai batare da ya sake cewa komai ba.
Harara Hibbah ta raka bayansa da ita. Wani sashe na zuciyarta najin tsananin taka
icinsa da kallonsa mutum mai tsananin girman kai da wulaƙanci. Sai da ya
ɓ
acema ganinta ta
ɗ
auke kanta da duban Baba Saude, “Uhm Mama tunda mun gama nima bara naje nai salla”.
Juyowa baba saude da ke nufar kitchen tai ta dubeta. “Eh
ɗ
iyata kin fini
gaskiya kam. jeki kiyi nima bara na ha
ɗ
a ma Babana abinci da Habibu sun dawo sai ya kai masa saman”.
“To mama”. Hibbah ta fa
ɗ
a tana nufar upstairs. Harta hau step na biyu baba Saude ta dakatar da ita. “Kinga yi haƙuri ko zaki dawo ki tafi masa ma
da abincin ma kawai, a saman nan ake shirya masa shi. Dan tunda kikaga ya dawo to yunwa yake ji”.
Hibbah dai da yake neman hanyar ku
ɓ
uta take kafin baba Saude ta farga da rashin wayarta da sauri tace, “To baba ki bari kawai su dawo sai sukai masa kam
ar yanda kuka saba. Kar kuma kaiwar tawa yasa hakan bai masa ba”.
Gamsuwa da zancen nata da kuma sanin halinsa yasa baba Saude fa
ɗ
in, “Eh gaskiyarki kuma, dan dama inba Habibu ba babu ma mai yawan hawan saman kai tsaye sai inshi ya bukaci ganin wan
i a cikinsu. Jeki kawai”.
Hibbah da batai tsammanin samunsa zaune a falon ba tai
ɗ
an diri-diri. Ƙoƙarin ha
ɗ
iye abinda ya tsarga matan a maƙoshi tai tana
cigaba da takowa ganin baiko nuna alamar yasan da shigowarta ba, kamar barci yake m
a a hakan.
Ta
ɗ
an ta
ɓ
e baki saboda ganin wani zaman ƙasaita da yay a cikin kujera. Hanyar
ɗ
akin data tsinci kanta a ciki ta nufa zuciyarta na tsitstsinkewa saboda shegen sanyin da falon ya
ɗ
auka. Amma shi ko a jikinsa, da alama ma matsanancin da
ɗ
i ya
ke masa.
“Kin koma satan waya ne?”.
Ƙasaitacciyar muryarsa mai amo da kamewa ta daki dodon kunnenta. Cak ta tsaya da rumtse idanunta da ƙarfi, dan duk tsiwarta tana shakkar wanda baizo mata da wasa ba. Ko yau da safe takaicin tuno maganarsu
Abbah yasata iya maida masa murtani badan bata ganin girmansa a idanunta ba. Ko bai tanka maka ba kwarjininsa da kame kai yasa ma'abocin mu'amulantarsa jin shakkarsa.
Juyowa tai a hankali tana
ɓ
ata fuska ranta fal mamakinsa. Ta
ɗ
an saci kallonsa a
mma sai taga yana a yanda ta shigo ta samesa ido lumshe bai motsa ba. Duk yanda taso yin tsiwar ta gagara koda motsa la
ɓɓ
anta tsabar yanda ya cika mata idanu har bata ganin wani fili a falon, dan fuskarsa tamau take babu alamar yasan minene fara'a.
Cikin pretending da shagwa
ɓ
ar da takema su Yaya Muhammad ta ce, “Ni wlhy ba
ɓ
arauniya bace. Tunda dai ba'a ta
ɓ
a cewa na ƙwamushe ku
ɗ
a
ɗ
en bankin mutane b?”. Tai maganar da
ɗ
an murgu
ɗ
a baki duk da zuciyarta kuwa babu abinda take sai lugude.