Showing 96001 words to 99000 words out of 186858 words
kwanaki ƴar yayansa ce. To da
mukai bincike ta office akan yarinyar ne na fahimci haka. Shine na nemesa danjin wani abu akanta. Daga nanne ya roƙeni muyi masa wani aiki akan yayun yarinyar da uwarta shima zai taimakemu ta yanda zamu amfani da basirar yarinyar. Shine fa na saka Master a
kan aikin dan nasan zai iya, gashi kuma yarinyar dama ta shiga gonarsa. Hakan yasa muka yanke shawarar ya aureta...........”
“Aure fa kace?”.
Dr Sufi ya fa
ɗ
a da mamaki.
“Eh Doctor, dan aurenne kawai zai iya bashi damar
ɗ
aukar yarinyar ci
kin sauƙi saboda ƙanwar shegen jami'in nanne Abubakar Aliyu Hamza Gwarzo. Kasan kuma shima hatsabibin kansa ne mai fa
ɗ
a aji wajen I.G”.
Lokaci
ɗ
aya ru
ɗ
ani ya bayyana a kan fuskarsu. Engineer Zailani yay saurin tare numfashin A.G da fa
ɗ
in, “To yanzu
dai yaya akai?”.
Carab Abba ya kar
ɓ
e zancen. “Ya auri shegiyar yarinyar, sai dai ni ya wargazamin nawa aikin na hana yayun yarinyar auren nawa ƴaƴan. Yanzu hakama ya
ɓ
oyesu inda ban sani ba”.
“Alhaji Halilu kabi a hankali, na tabbata mast
er bazai aikata hakanba sai da manufa”. A.G ya fa
ɗ
a cikin jin haushi. Kafin Abbah ya ce wani Abu Alhajin Mande ya karbe da fa
ɗ
in, “Master kam banajin zai
ɓ
ata lokacinsa akan wanann shiriritar, amma ku jira na san yana gab da zuwa nan”.
Cike da zal
ama Abbah yace, “Yauwa Alhmdllhi. Gara yazo naji yaya aka fa
ɗ
i a ragaya ranka ya da
ɗ
e”.
Komai babu wanda ya sake ce masa. Dan ama kusan dai-dai rufe bakinsa maigadi ya shigo yana sanar dasu isowar Master
ɗ
in.
Da hanzari R.D ya bada damar shi
go da shi, dan sun rasa miyasa baya yarda ya shigo musu kai tsaye a duk sanda suka buƙaci ganinsa. Koda waya ya gama da su sai ya nema iso yake shigowa.
Cikin izzarsa da ƙasaita ya shigo falon da sallama ciki-ciki. A kusan tare suka amsa suna zuba
masa ido tamkar tsoffin mayu. Yana matuƙar birgesu da tafiya da imaninsu. Sai dai sam sun kasa samun kansa domin biyan bukatar zukatansu. Ya dai amince yay musu sauran ayyuka, hatta kisan kai idan sukace sunaso ayima wani yakan amshi aikin, amma sanin yay
a yake aikin har yanzu basu da tabbas. Kuma bai basu wata ƙofar masa tambaya ba, dan duk da karancin shekarunsa a cikinsu baya
ɗ
aukar raini koda na kallon bamza ne.
Zaune ya kai bisa kujera yana mai
ɗ
ora ƙafa
ɗ
aya kan
ɗ
aya cike da ƙasaita. Kafin
ya kai hannu bisa glass
ɗ
in fuskarsa ya gyara masa zama da ƙyau yana kare musu kallo ta ciki. “Barkan ku”.
Ya fada a taƙaice yana zuƙar iska da fesarwa. Sosai sukejin takaici na salon iskancinsa da izza. Sai dai basu da damar tankawa dan duk sun kas
ance a tafin hannunsa, saboda sirrikansu da yawan gaske ya gama sani.
Bakuna suka shiga washewa. Kowanne na ƙoƙarin tambayarsa yaya yake. Nanma a takaice ya amsa musu da cewar,
“Normal”.
Ya tsuke bakinsa.
A.G ya nuna masa Ab
ba. “Ina fatan ka gane wannan ko Master?”.
Cikin
ɗ
an yamuste fuskar boginsa ya ce, “Kamar..”
Haushi ya kama Abba. Ya zuba masa harara da fa
ɗ
in, “Kai saurayi miye kuma Kamar? Ni nasan ka ganeni kodan maƙudan ku
ɗ
a
ɗ
en dana sauke maka kafin kar
ɓ
a
r aiki na”.
Mai makon ya amsa Abbah sai ya duba A.G da fa
ɗ
in, “Wanann shine dalilin kiran?”.
“A'a ina” R.D yay azamar fa
ɗ
a saboda sanin wulaƙancin Mastern. Ka
ɗ
an da ga aikinsa ya karta musu rashin m ya tashi yay tafiyarsa.
Abba da
ya fahimci gadara bazatai ba sai ya kwantar da murya. “Kai ko saurayi dan ALLAH ka saurareni. Wlhy ina cikin matsala fiye da zatonka. Kuma ba kowa bane ya sani wabilahillazi sai kai. Miyasa munyi maganar ka auri yarinya kawai sai ka wargaza auren nawa ƴaƴa
n kuma? Bayan kuma duk na sanar maka ƙudirina akansu”.
Nan ma banza yay masa bai tanka ba, sai ma agogon hanunsa da ya kalla. Da sauri A.G da ya fahimci ma'anar kallon agogon ya ce, “Ayi haƙuri a sauraresa Master. Rashin tabbatar wannan aikin zai iya
saka masa ciwon zuciya wlhy. Nasanka kuma baka karya alƙawari, ga shi bamu san dalilinka na hana auren yaran nasa ba”.
Kamar bazai tanka ba kuma sai ya dubi Abban. “Mi kake buƙata yanzun?”.
Baki Abba ya washe yana gyara zama. “Yauwa
ɗ
an alb
arka. Su yaran da ka wargaza auren yaran nawa da su nakeson sanin inda suke su da uwarsu. Idan da hali kuma a karminsu
ɗ
aya bayan
ɗ
aya dan ALLAH kamar yanda mukai da kai a farko, ni yanzu ma basai sun auri yaran nawa su wani sami ciki ba. Sanann akwai duki
yarsu da ke a hannuna da kaddarori duk sunayensu ubansu ya saka matsayin masu gadarsa, dole sai sun saka hannu su da lauyan baban koda zan iya amfana da su. To shi kuma lauyan ya
ɓ
ata
ɓ
at tsahon shekaru shegen shine nakeson a kwashe ku
ɗ
a
ɗ
en a maidosu accau
nt
ɗ
ina. Takardun kaddarorin kuma a maida sunana. Amma inason a fara kashemin ita yarinyar da aka
ɗ
aura aurenku da itan sannan, dan wlhy da baka
ɗ
auketa ba a jiya ni da kaina da zan kasheta”.
“Zamu sake sabon ciniki. Dan baka sanarmin gaskiya ba a
wancan aikin shiyyasa na wargaza auren ƴaƴanka. Ni idan za'a bani aiki bana son ƙarya bana son munafinci. Yanzu ma idan ka ƙara zakaga ba dai-dai ba. Ka tattara dukan bayanai da accaunt no. Ɗin da ku
ɗ
in suke da takardun kaddarorin ka bama A.G tare da ku
ɗ
i
n aikina”.
Yawu Abba ya ha
ɗ
iye da ƙyar, dan awancan aikin fa 5mil ya bashi. Amma dan tsabar wulaƙanci ace wai sun ciwu batare da an masa aikin ba. Shikam ya fahimci yaron nan zigidir yake son masa. To amma ai yanzu ku
ɗ
a
ɗ
ene masu nauyi zai samu. Dan
haka ya sake gyara zama. “Na yarda zan sake biya. Amma nawane to? Dan ALLAH amin ragi”.
Cike da shan ƙamshi Master ya
ɗ
an dubesa ta cikin glass
ɗ
in idonsa ya
ɗ
auke kai. “Zaka fara bada 10mil yanzun nan, bayan naga takardu da nauyin ku
ɗ
a
ɗ
en asusu
n zan fa
ɗ
i farashi”.
“Bantan uba kana nufin 10mil
ɗ
in ma ba farashi bane?”.
“Ku
ɗ
in saka data and transport ne”. Master ya fa
ɗ
a a gadarance.
Abbah zai kara magana A.G ya zunguresa. Kallonsa yay a marairaice tamkar zaiyi kuka. Amma sai ya
girgiza masa kai alamar karya sake cewa komai. Dole Abbah yay ƙasa da kansa. A zuciyarsa kuwa sai jama Master kwando-kwandon tsinuwa yakeyi.
Da ido Alhajin Mande yay ma A.G alamar ya sallami Abba. Kansa ya gya
ɗ
a yana duban Abban. “Alhaji Halilu ka
je ka tattara abinda ya ce idan na fito zan biyo ta gidanka na amsa”.
Miƙewa Abba yay yana fa
ɗ
in, “To. To bara naje
ɗ
in, amma dan ALLAH ka
ɗ
an sake nemamin ragi ku
ɗ
in yayi yawa wlhy, dan ya zabtare kaso biyu bisa ukun abinda na mallaka idan aka ha
ɗ
a
da biyan farko. Gashi nayi hidimar kamawa shegun yaran can gidajen haya babu gaira babu sabar”.
“Babu damuwa kaje. Zamuyi magana da shi”. A.G ya fa
ɗ
a cikin ƙosawa.
Sai da sukaji fitar motar Abba a gidan suka maida hankalins
u ga Master da ya lafe cikin kujera idanunsa da ke cikin glass a lumshe. Dr Sufi ya fara magana yana
ɓ
alle murfin robar ruwa. “Master taruwarmu anan tana da nasaba da wani babban aiki da ya sake taso mana. Amma kafin mukai maganarsa nakega ya kamata ace ku
ɗ
a
ɗ
en hannunka daketa taruwa kusan shekara biyu mizai hana a
ɗ
an raba wasu a ciki kar asusun ya cika da yawa har wani yay mana ƙafar angulu. Kaga tunda aka fara aikin nan biyanka kawai muke ku
ɗ
in aiki amma ku
ɗ
a
ɗ
en ko nera bata shiga aljihun
ɗ
aya da ga ciki
nmu ba, sabanin da da kayi aikin kake bamu abunmu”.
Miƙewa yay zaune sosai tare da zare glass
ɗ
in idonsa. Ya zubamasa razanannun idanunsa masu kama dana Zaki. “Likita kasan bana magana biyu, shiyyasa tun farko na sanar muku sai na kammala muku wan
nan aiki zan baku sakamako. Ko kana tunanin da ku
ɗ
a
ɗ
en nan nake harkar rayuwata ne?”.
Da sauri Alhajin Mande ya ce, “Haba karma ka kawo hakan a ranka Master. Mu da kake gani anan mun matuƙar yarda da kai shiyyasa muke iya fasa maka sirrin cikinmu,
karka manta tun kana ƙaramin
ɗ
an jagaliya kake tare damu. Sam ba haka Dr Sufi ke nufi ba. Amma nima sai nake ganin ko kaso
ɗ
aya bisa uku ne na ku
ɗ
in a
ɗ
an raba mu farfa
ɗ
o koda bayan ka gama wannan aikinne na yanzu da zamuyi magana. Dan shima asusun manyan
gwasake ne”
Komawa yay jikin kujerar ya kwanta yana maida glasess
ɗ
insa cike da salonsa na izza. “Zaku bani accaunt numbers naku na sirri. Bayan aikin nan ya kammala zakuji billions
ɗ
ari-
ɗ
ari”.
Wani irin kallon zazzaro idanun mamakin jin nauy
i ku
ɗ
a
ɗ
en da kawai tsakurowa zaiyi ga abinda ya tara musu sukai. Atake bakunansu duk suka washe. Alhaji Sallau yace, “Kace abin na gaske ne Master mu ƙara ƙaimi”.
Wani
ɗ
an salo kawai yay masa da yatsunsa
🤙🏻
ba tare da ya bashi amsa ba.
Wan
i irin shegen da
ɗ
i ya baibayesu. R.D ya jawo takardun gefensa yana fa
ɗ
in, “Wa
ɗ
an nan sune jadawalin sunayen wa
ɗ
anda za'a wawashe ma asusu. Uku da ga ciki munason a fallasasu wa duniya bisa handamar da suka shuka akan ku
ɗ
a
ɗ
e. Na farko I.G na ƴan sanda. Sai
ministern man fetur. Da shegen can Barau na ALLAH shaharren
ɗ
an kasuwa a zahiri a ba
ɗ
ini kuwa ku
ɗ
in kwangilar gwamnati ne yake handama da ga aminansa da suka
ɗ
aure masa ƙugu a gwamnatin. Sai gwamnan jihar gabas damu.”
Wani shegen murmushi Master
ya saki yana miƙewa. ga accaunt no
ɗ
ina nan naji alert. Da ga safiyar jibi idan ALLAH ya kaimu zakuji sakamakon aiki.”
Dariya suka shiga ƙyalƙyalewa da shi suna tafawa. R.D ya miƙa masa takardun sunayen duk wa
ɗ
anda suka lissafo da bayanai akansu yana
fa
ɗ
in, “Master muna son rayuwar shegen I.G
ɗ
in can ta salwanta fiye data kowa. Kaima dai kasan yanda yake tsaye kullum akan son damƙoka da gurfanar da kai harma da alwashin da yake
ɗ
auka na tabbatar da hakan. Ko nera kartai saura a asusunsa. Akwai bayanai
shiryayyu akansa da fitarsu sai ta saka zuciyarsa bugawa kafin ma hukumar daƙile ta'annati da kayan gwamnati ta fara bincike a kansa. Kaga sai muga da wane taurin kan nasa zai cigaba da bibiyarka balle ya gano sunanmu da ke manne da naka a ba
ɗ
ini”.
Komai Master bai ce ba. Sai amsar takardun da yay ya nufi hanyar fita yana
ɗ
aga musu hannu alamar bye.
Yana gama ficewa kusan dukansu sukaja tsaki. Dr Sufi yace, “Shegen yaro mun
ɗ
orasa akan samu amma yana neman fin ƙarfin yanzu
ɗ
an banza hat
sabibin aljani”.
Cikin takaici Engineer ya kar
ɓ
e, “Nifa wlhy namafi tsanarsa sama da maƙiyan namu a yanzu. Nakanji kamar na kar shege a wuce wajen tun yanzu”.
“Kulll” Alhajin Mande ya fa
ɗ
a yana gyara zama. “Kudai mu cigaba da lalla
ɓ
ashi da
haƙuri ku
ɗ
a
ɗ
en nan da aka tara su dawo hannunmu. Cikin sauƙi zamu sakashi a tarko mu da kammu musa a kamashi, sai mun ƙasƙantar da shi a gaban duniya da kullum burin kowane jami'i ya ga gwiwarsa a ƙasa kafin mu
ɗ
urama shege allurar guba namansa ya zaganye
kowa ya huta. Dan ba karamar fitina uwar wannan ta haifama duniya ba”.
“Mu kuma ta haifa mana abinda ya amfanemu ai”. Cewar A.G.
Dariya suka sheƙe da ita baki
ɗ
aya suna tafawa.
★★★★★★
A gidan Ummi kuwa zuwa magrib duk w
asu baƙi sun kama gabansu. An kimtsama kowacce amarya sashenta an barta ta jira shigar ango. Sashen Ummi ma dai babu kowa sai ita da samarin ƴaƴanta. Suma
ɗ
in sun fita sallar isha'i basu kai da dawowa ba.
Da Ummi taji motsi sai ta kalla ƙofa da tun
anin ganin Hibbah ta shigo. Sai dai shiru kakeji. Harga ALLAH zuwa yanzun zuciyarta a matuƙar raunane take. ji take kamar numfashin Hibbah baya tare da nasu a cikin gidan. Dan babu yanda za'ai Tanee
ɗ
inta ta kwana ta yini batare data sakata a ido ba. Musam
man idan ta tuna miya faru akan aurenta.
Kai anya kuwa bata yaudarrar kanta ma. Tayama akai ta amince cewar Hibbah na tare da su Zahidah bayan abin daya faru, dan babu kuma yanda za'ai ace Hibbah bata sani ba. Zaram ta miƙe da ga zaune da take a sam
an sallaya dan idar da sallarta kenan ta isha'i.
A yanayin ki
ɗ
ima ta fito falon ƙirjinta da zuciyarta na wani tsitstsinkewa. Gaskiya haƙurinta ya ƙare da kanta zataje sashen su Zahidah ta bincika.
Yanke wannan hukuncin a rantane ya sakata
nufar ƙofar falon. A dai-dai nan suma su Yaya Muhammad suka kawo jiki zasu shigo. Baya Ummin tai tana dubansu cikin rauni.
A take suma kuma yanayin nata ya saka gabansu fa
ɗ
uwa. “Ummi lafiya? Kuwa”.
Yaya Muhammad ya fa
ɗ
a yana matsowa kusa da
ita sosai.
A raunane ta ce, “Muhammad Tanee. Dan ALLAH ku fa
ɗ
a min gaskiya ina yarinyata take ne? Zuciyata na tabbatar min kuna
ɓ
oyemin wani abu”.
Cikin son kauda mata hankali yaya Umar ya kama hannunta yana fa
ɗ
in, “Ummi zauna kiji, kwant
ar da hankalinki indai auta ce tana cikin ƙoshin lafiya.”
“Ban yarda ba Umar, dan zuciyata tana bani numfashin Tanee yana nesa da nawa”.
Cikin in ina Yaya Abubakar ya bu
ɗ
e baki zai yi magana akai knocking ƙofar.
“Tanee!”
Ummi ta
ambata da sauri tana duban ƙofar. Gaba
ɗ
ayansu suma ƙofar suka duba, sai dai sanin Hibbah bata tare da su yasa su basuyi wannan zaton ba. Mikewa Ammar da illahirin jikinsa ke tsuma yay ya nufi ƙofar. Batare da tunanin tambayar wanene ba ya bu
ɗ
e ƙofar da ja
nta baya yana kai kansa zai leƙa aka
ɗ
aura masa bindiga.
“Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”. Ya ambata yana jan jikinsa baya.
Hakkane kuma ya bama wanda ya
ɗ
aura masa bindigar akai damar sakko ƙafarsa