Showing 129001 words to 132000 words out of 186858 words

Chapter 44 - TAKUN SAKA COMPLETE

10 Sep 2026

12

washewa yana nufar hanyar bedroom

ɗ

insa cikin

ɗ

unbin farin ciki. Sai kuma ya dawo da baya

domin

ɗ

aukar babbar wayarsa da nufin turama Master ku

ɗ

in tukuyci kafin yaji farashin sauran na aiki. Dan ya saka a ransa ko nawane Master ya nema sai ya bashi harma da ƙari. Yana ƙoƙarin ma Master transfer

ɗ

in dubu

ɗ

ari biyar na tukuyci wasu sabbin alerts

ɗ

in suka fara rige-rigen shigowa. A zatonsa wasu ku

ɗ

inne suka shigo dan haka ya bu

ɗ

e da zumu

ɗ

i.

“Wayyyyiiiihuuuuuu!!!!! Ni Halilu na mutu!”.

Ya fa

ɗ

a a matsanancin firgici har sai da su hajiya mama suka toshe kunnuwa suna miƙewa tsaye a matuƙar

firgice ganin Abba ya yanke jiki ya fa

ɗ

i a wajen wayoyin duk sunyi gefe.

★★★★★

Abinda ke a kunnensa ya danna lokacin da yake shiga motar da sukazo yabar wajen, dan tuni su Zaidu sun ware. “Habib ka

ɗ

auki yarinyarnan yanzun nan kubar gidan n

an, ka tabbatar kafin ku wuce ka kashe wayar hannunta ka cire sim card

ɗ

in ciki kayi flushing

ɗ

insa. Ga su Zaidu nan isowa. Kubi ta cikin store

ɗ

in kitchen akwai hanyar da zata fiddaku ta wancan layin.”

Sosai hankalin Habib ya tashi, dan yanzun nan d

ama ya kama Hibbah da waya. Yana tsaka da tambayarta ne kiran master ya shigo masa. Wayar ya fusge daga hanunta a fusace ya takata bayan ya fashe. murfin ya

ɓ

alle da kyar,

ɗ

an pin

ɗ

in dake jikin blackboard

ɗ

in inda computers

ɗ

in suke ya

ɗ

auka ya cire sim c

ard

ɗ

in ya karya. Yay azamar danna wani abu a jikin teble

ɗ

in yay ƙasa.

Baki Hibbah ta ta

ɓ

e dan a ganinta kafin ya gama duk wannan abun da master yace ta tabbatar ƴan sanda sunzo. Ranta fes yau ALLAH yayi dubun masu aikata sa

ɓ

on ALLAH ya cika.



Dawowar Habib yayi dai-dai da shigowar su Salis kusan a tare. Gaba

ɗ

aya firgice suke. Jakunkunansu suka shiga

ɗ

akin da suke kwana suka tattaro. Habib ya fisgi hanun Hibbah da duk abinda suke tana tsayene kamar dogariya tana kallonsu. Sai faman ta

ɓ

e baki

take irin ko'a jikinta

ɗ

in nan. Hannun ta fige tana ture Habib, a dai-dai na Master ya shigo falon shima.

“Ku tafii!!!”.

Ya fa

ɗ

a da ƙarfi jin jiniyar ƴan sanda na gabato anguwar. Yay maganar yana nuna musu hanyar kitchen, kallo

ɗ

aya zakai masa kai

kanka ka firgita dan gaba

ɗ

aya ya riki

ɗ

e tamkar wani bajimin zaki. Kobi takan Hibbah da tsawarsa ta firgita baibi ba. Ya nufi

ɗ

akin da suka kwana cikin zafin nama. Mintun uku tsakani ya dawo falon, wanda yay dai-dai da ƙarasowar ƴan sandan ƙofar gidan. Ga

kuma Hibbah data nufi hanyar waje da gudu. Baya ya take mata shima. Sabon tashin hankalin daya yunƙuro masa ne yasashi fisgo Hibbah cikin zafin nama ya yarfa mata wani shegen mari mai azabar zafi da saida jinta da ganinta suka gushe na wucin gadi. Ya kama

kunnenta ya mur

ɗ

e da shegen karfi yana magana cikin matuƙar hasala da hargowar da bata ta

ɓ

a gani tare da shi ba. “Stupid girl!!, idan ni baki kasheni ba, ke da hannunki da wannan shegen taurin kan naki zaki kashe ahalinki”. Wani irin rawa jikinta ya fara

hawaye na mata ambaliya akan fuska. Ya turata ta zube ƙasa dan ji yake kamar yay mata bugun mutuwa kozai huce daga abinda yakeji a halin yanzun. Sake miƙewa tai da gudu, Fitowarsu compound

ɗ

in gidan yayi dai-dai da shigowar ƴan sandan cikin gidan.



“Ku bu

ɗ

e musu wuta gaba daya!!!”.

A.G ya fa

ɗ

a da ƙarfi.

A razane wani a ciki ya bashi amsa da cewar, “Oga yarinyarfa data bamu information akai gata tare da shi”.

“Har ita ku ha

ɗ

a”.

A.G ya fa

ɗ

a cikin karaji. Ba ƙaramin firgita Hi

bbah tayi ba. Ta waiga ta dubi Master take biyota ta kalli ƴan sandan da suka saita bindugu akansu da alamun cika umarnin ogansu zasuyi ta rumtse idanu da ƙarfi wasu zafafan hawayen nadama da dana sani na sakko mata. Ita data bada bayani akansa amma jami'i

n tsaron daya kamata ya bata kariya wajen kubutar da itane ke cewa a harbeta baida matsala. Wace irin ƙasa muke da ita kenan? Ahaka akeson wanda yaga mai laifi ya tona masa asiri.......

Master da gaba

ɗ

aya kamaninsa sun canja duk da bindugun da

aka saitasu da shi ya nufota a guje da alamar son kubutar da ita saboda harsasai guda uku da jami'an suka harbo gaba

ɗ

aya kanta sukayi gadan-gadan, sai

ɗ

aya ne ya nufosa shiko ya saka bullet proof jacket a jikinsa, yasan duk tsiya harbin bazai samu makasr

sa ba sai dai idan kwanansa ne ya ƙare yau. Yana gab da isowa gareta bullet

ɗ

in ya shiga cikin kafarsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana kaiwa duƙe, hanunsa

ɗ

aya na zaro karamar bindigar jikinsa shima ya fara maida murtani. Wani irin zabura Hibbah tai babu shiri

ta nufosa, hakan ya bata damar gocema bullets

ɗ

in da suka nufo kanta har guda biyu

ɗ

aya ya sake samun master a hannu.

Hankalinta ya ƙara matuƙar tashi ganin shi ƙoƙarinsa ya bata kariya, yayinda wa

ɗ

anda ya kamata su bata kariyar su son kasheta suk

eyi. Sam rikicewa ya hanats gane fuskar dattijo A.G. Shiko Master ya gansa ne duk da yana ƙoƙarin

ɓ

oye fuskarsa garesa. Duk da tasan ya mata nauyi haka ta miƙa hannu ta kamo nasa tana kuka. Ha

ɗ

in kai ya bata ya miƙe shima da ƙyar cikin dakiya da dauriyarsa

duk da tuni jini ya

ɓ

alle masa ta ƙafa da hannu. Kasancewar suna gab da ƙofar falon suka sami nasarar afkawa ciki, Master ya danna security jin A.G ya bama yaransa damar bin bayansu duk da dama ba daina harbin sukaiba ALLAH dai ne ya bama su Master kariya

bayan biyun da suka sameshi wasu basu sake ta

ɓ

asu ba. Jakkarsa daya yasar a falon ya

ɗ

auka, da sauri Hibbah ta amsa ta goya a bayanta. Ya fisgi hannunta cikin bama kansa ƙwarin gwiwa suka afka cikin kitchen

ɗ

in suma. Sai dai su a tsakiyar kicin

ɗ

in ya tsa

ya ya haye saman table

ɗ

in wajen duk da jini dake kwaranya masa. Hannu ya miƙa ta tsakkiyar p.o.p

ɗ

in kicin

ɗ

in ya burma sai ga ƙofa. Ya

ɗ

an daka tsalle ya fisgo wani zare mai kama da tsani. Hannu ya miƙa mata ta

ɗ

ora nata sai faman wai-waige take jin ƴan

sandan nata ƙoƙarin bu

ɗ

e kofar falon. Ta tabbatar suka shigo kuwa sun gama yawone. Cak ya

ɗ

agota duk da tanada nauyi.

Da taimakonsa ta fara hawan zaren tsanin harta shige. Kafin shima ya fara hawa. Yana gab da shigewa suka sami nasarrar

ɓ

alla ƙofa

r falon. Cikin sa'a ya ida shigewa da jan tsanin ya maido ƙofar ya rufo. Karan farko a tarihin rayuwa Hibbah a cikin zinc bisa gangancin da taso tafkama rayuwarsu. Wani ƙaton bututu kamar na ruwa suka samu cikin zinc

ɗ

in, Master da ya fara

ɗ

an galabaita sa

boda jinin dake fita a jikinsa dama ba isashen lafiyane da shi ba ya nuna mata cikin bututun da bata fitila ƴar karama mai shegen haske.

Ɗan kwalin kanta ta cire tana kuka ta yagashi biyu, ƙafarsa ta

ɗ

aure masa dai-dai wajen da bullet

ɗ

in ya shiga.

Sauran rabin ta

ɗ

aure masa hannunsa. Cikin taune lips ya turata cikin bututun shima yabi bayanta dan yasan jinin da yake zubarwane zai nunama su A.G inda sukabi.

Da rarrafe suka dinga kutsa kai cikin bututun batare da Hibbah tasan ƙarshemsa ba, balle

inda suka dosa. Sunyi tafiyar da har sai da ta fara galabaita saboda ƙura sannan ta fara hango haske alamar karshensa kenan. Koda suka fito batasan inane nan

ɗ

in ba. Amma dai gidane a wajen shima mai kyawun gaske. Ya fisgi hannunta ya danna cikin motar da

ke fake a wajen bayan ya yaye tanfol

ɗ

in da aka rufeta da shi. Shima shiga yay yana jan numfashi da ƙyar dan idanunsa sun fara ganin jigari-jigari. A mamakinta sai gani tai ya danna wani abu gate

ɗ

in ya bu

ɗ

e kansa. Ya fita da motar da gudu daga gidan. Har

daga nan tana iya jiyo jiniyar motocin yan sanda da karar harbe-harbe alamar gidan da suka baro kusa yake da wannan. Gudu yake tsulawa na fitar hankali wanda dole motoci da napep ke basa hanya. Masu zagi nayi masu kiransa

ɗ

an giya nayi. Baimasan sunai ba.

Dan bai tsaya ba sai a wata anguwa. Motar taga ya faka a wani dan lungu ya fita. Batare da yayi magana ba itama ya zagayo ya fisgota. Key wani mai shushaina dake a lungun zaune shi ka

ɗ

ai yana gugar takalma ya jeho masa. Ya cafe dajan hannunta suka sake shi

ga wata motar, yayinda tunkan su fice a lungun ta hango mai shushaina

ɗ

in nan na rufe waccan motar da tamfol.

Wani irin tsoransa ne ya tsargama Hibbah. Ta kafesa da ido cike da alamar tambayoyi sai dai babu damar yinsu. Yanzu kam ta cikin anguwan

ni ya dinga bi da su har suka sake zuwa wani layi sukai canjin mota, anan ko motar kawai suka samu sai mai tallan rake a gefe can shi ka

ɗ

ai. Sai da ya shiga motar ne ya yafito mai tallan raken yana cizar le

ɓ

e. da gudu mai rake ya turo Wheelbarrow

ɗ

insa zuw

a inda suke. “Rake na

ɗ

ari uku”.

Master ya fa

ɗ

a da ƙyar yana lumshe ido.

Raken mai rake ya

ɗ

ebo ya zuba a leda. Ya turo kansa ta Window

ɗ

in motar yana ajiye keys a cinyar master. “Gida mai lamba takwas, anguwar bauranya”.

Komai masbaiceb

a yaja motar suka bar wajen. Gaba

ɗ

aya hibbah ta mutu a zaune a karo na biyu, kallonsa kawai take kamar gunkiya har suka iso anguwar da mai raken taji ya fa

ɗ

a. horn yayi maigadi yay saurin wangale masa gate ya danna hancin motar. Gaba

ɗ

aya su Salis dake ts

aye sunata faman kaikawo a compound gidan mai sashe biyu sukayo inda yay fakin. Hakama baba saude dake can zaune goye da Sharifat ta mike da sauri duk da batasan ainahin abinda ke faruwa ba. Kawai dai su Habib sunje sun taho da itane acan L.E street batare

da sun mata bayanin komai ba.

Kusan gaba dayansu suka rufu akansa. Yayinda wasu a cikinsu harsun fara kuka ganin yanda ya samu harbi. Ga jikinsa harya fara saki saboda jinin da ya zubar. Da taimakonsu suka nufi sashen da ke a hannun dama suna sharta

r hawaye. Yayinda Hibbah wani irin nadama ke sake shiga bargonta, dan itama kukan da taga su Habib nayine ya sake tayar mata da hankali.

Kanta baba saude tayo ta kamata itama tana tambayarta miya faru? Jikin baba saude ta fa

ɗ

a tana girgiza kanta haw

aye na kwarara mata. Sai kuma tai saurin barin jikin baba sauden tabi bayan su Adam. Itama Baba sauden bayansu tabi jikinta sai rawa yake ganin jikin Master duk jini.

A falon suka zaunar da shi bisa wata kujera mara tudu mai laushin tsiya. Cik

in sauri Musbahu ya dakko First aid box

ɗ

in daya hango can gefe. Cikin sauri Khalid ya kai tsugunne ya fara warware dan kwalin hibbah data daura masa. Yayinda Idris ke kwance na hannun shi kuma. Cikin rumtse ido Khalid ya zuba masa ruwan magani akan wajen.

Wata wahalalliyar ƙara Master ya saki yana sake damƙe hannun Zaidu dake gefensa. Khalid na kuka yasa wani ƙarfe cikin ramin ya fisgo bullet

ɗ

in. Baki kawai Master ya datse da azabar ƙarfi. Tashi Khalid yay ya koma wajen hanun, yayinda Habib ya duka gaban

kafar ya cigaba da treating

ɗ

inta. Acan ma Khalid ya cire bullet

ɗ

in hannun, ganin Habib bai gama treating ƙafar ba sai shi ya cigaba dana hannun.

Tunda aka cire bullets

ɗ

in wani irin zufa ke ketoma Master akowacce hudar gashinsa. Yayinda yaketa

faman sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da suka kammala tsaf suka goge jinin da duk ya bata ko'ina sannan ya bu

ɗ

e idanunsa da sauri saboda abinda yazo masa a rai yanzun nan.

“Ya ALLAH! Akwai matsala, akwai matsala!!”.

Ya shiga fa

ɗ

a yana j

ujjuya kansa. Hankali tashe su Salis ke tambayarsa wace irin matsala kuma?.

Bai iya basu amsa ba, sai wayar da ke a jikinsa ya laluba da sauri yana duban su Adam. Cikin wani yare da ko Baba saude bata ta

ɓ

a ji Mastern yayi ba yayma su Adam maga

na. Cikin sauri suka nufi hanyar fita a falon suna amsa masa da girmamawa. Su biyar suka fice aka bar Idris da Khalid kawai.

Da ido yayma Idris maganar da su ka

ɗ

ai suke fahimtar yarensa ta hakan. Idris ya jinjina masa kai da duban baba Saude da h

ar yanzu take sharar hawaye.

“Baba muje na kaiki ki huta ko? Karki damu komai yayi dai-dai insha ALLAHU ”.

Badan baba Saude taso ba tabisa

ɗ

auke da Sharifat dake barci a bayanta. Dan tunda ta fasa kuka sanda su Habib ke shiga gida suna ce

mata tafito saita lalla

ɓ

ata tai barci lokacin da suka shigo mota, koda suka iso gidan kuma saita goyata da gyalenta.

Kuka sosai Hibbah keyi wanda ke sake hasala zuciyar Master. Sai dai da yake yanzu hankalinsa nakan wani abu daban yasa ya shareta.

Sai da yaji ta cigaba da cika masa kunne ne ya daka matsawar da ba ita kadai ba hatta da Khalid sai da ya zabura.

Idan baki bar min wannan garshekan kukan ba saina daddage kanki da bullets a gidan nan!!. Kuma ki tashi min anan kafin na hambaraki a

ƙ

asa kanki ya bugi tiles

ɗ

in nan!!”.

Da gudu ta miƙe tabi bayan su baba saude. Dan yanzu kam ta tabbatar ada ba Master ta sani ba yanzu ne taga ainahin Master ganin idonta ba labari ba. Gaba

ɗ

aya idanunsa sun koma na ainahin tsohon bahagon zaki da

babu abinda ya sani sai farauta. Idanunsa kai kace aman wuta zasuyi saboda tsabar jan da suka koma.

Kansa ya dafe da fa

ɗ

in, “Ina ji kamar na kashe yarinyar nan a yau na manta da shafin rayuwarta a tarihina.”

Sosai tausayinsa ya sake



ɗ

arsuwa a zuciyar Khalid. Ya tabbatar yau Hibbah ta ballo ruwa na gaske wanda batasan harda aikin taimakon ahalinta suka fita ba. Mastern su baya kuka sai domin tausayin al'umma. duk ha

ɗ

arin da zakaga ya jefa kansa a cikin domin taimakon wanine. Kullum wa

hala yake da mutane batare da sun san manufarsa ba. Kowa kallon

ɗ

an ta'adda takadari yake masa. Hatsabibi shu'umi

ɓ

arawo. Amma hakan bayasa ya sare daga aikinsa duk da wa

ɗ

anda yake dan su

ɗ

in ko 1% basu fahimcesa ba.............



*_Asirin da xoxo

taimin yau ya warware

🙄😏🚶🏻😖

_*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUK

A ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YA

R UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login