Showing 66001 words to 69000 words out of 186858 words
masu ƙyau kala biyu. Na Ummi da nata.
Tana tsaka da ƙo
ɗ
a ƙyawun kayan Yaya Muhammad ya shigo. Ummi ce kawai ta samu damar masa sannu, Hibbah kam sam hankalinta baya wajensa. Sai
da ya kai zaune yake fa
ɗ
in, “Ummi lafiya kuwa? Miya faru da Isma'il?”.
“Wlhy ban saniba Muhammad, nima man mamakin yanayin nasa ne ya sani zaman jugum nan.” (gaba daya ta kwashe yanda sukai ta bashi labari).
“Tofa, anya kuwa Ummi Isma'il
ba son Hibbah yake ba?”
Da sauri Hibbah ta juyo ta kalli Yayan nata. “Yaya so kuma? Ni?”
“Tabbas auta. Dama zuciyata ta jima tana rayamin Isma'il dan ke yake tare da mu. Dan take-takensa gaba
ɗ
aya sun nuna akwai soyayyarki a zuciyarsa. Shiyya
sa naso ace yana nan maganar nan ta taso na aurenkin nan. Koba komai ni hankalina ma zaifi kwanciya da Isma'il
ɗ
in fiye da shi Shuraim
ɗ
in nan. Duk da shima dai babu wani aibu tare da shi dan yau
ɗ
in nanma sai da na sake samun bayanan binciken da na saka a
kaimin a kansa bayan wa
ɗ
an can na baya”.
Nannauyan numfashi Ummi taja, gaba
ɗ
aya zuciyarta ta dagule. Dan harga ALLAH tana jin son Isma'il matsayin siriki a gareta. Sai dai kuma ƙaddara ta rigada ta riga fata. Dan babu ta yadda za'a gyara abinda tun
farko aka
ɓ
ata. Shima harda laifinsa da bai fito ya nuna ba, a yanzu kuma basu da hurumin rusa maganar Shuraim inba so suke su kasance ƙananun mutane ba kuma.
Ita dai Hibbah ko a jikinta. Tama cigaba da harkar gabanta ne dan kallon yaya take masa ha
r cikin zuciya.
★★★
Kwanaki uku Isma'il bai sake dawowa gidanba. Hakan duk sai yabi ya dami Ummi harta
ɗ
auka waya ta kirasa akan tana son ganinsa. Baiko musa ba sai gashi yazo da hantsi. Lokacin su Hibbah duk sun fice sai ita ka
ɗ
ai.
Ummi tanada dabaru sosai na iya sarrafa mutum bisa ƙyaƙyƙyawar hanya. Shiyyasa ta tarbiyanci ƴaƴanta da tarbiya mai ƙyau da ke bama kowa mamaki da yaba ƙoƙarin ta. Duk da Isma'il yazo mata ransa a cinkushe cikin hikima da dabarun da ALLAH ya bata ta bi d
a shi da nasiha. Cikin ƙankanin lokaci sai gashi yayi laushi, ya kuma gane cewar laifinsa ne da yabar zancem a ransa bai furtaba.
“Ummi nagode matuƙa da gaske. Kiyi haƙuri ban tashi da uwa ba shiyyasa abubuwa da yawa bana ganesu kai tsaye sai sun ƙu
re min. Idan kuma ba'an fahimtar dani bane haka zanta kallonsu a yanda na
ɗ
auka. Bazan boye miki ba ina matuƙar jin da
ɗ
in kasancewa da ke. Kuma ina miki kallo ne irin na uwa wlhy. Shiyyasa kikaga ko yaushe ina nane da ke. ALLAH ya sanya albarka a auren Hib
bah na haƙura. Amma tabbas ina sonta da ƙaunarta. Wasu kuma nagartattun halayenki ne da nata suka jani ga hakan abinda ban ta
ɓ
a tsintar kaina a ciki ba. Amma dan ALLAH koda wataran inaso ki cigaba da tuna hakan. Kuma kamar yanda kika fahimtar dani wanann b
azai zama ƙarshen zumincinmu ba. Zan cigaba da kasancewa da ku a koda yaushe tamkar da. Zanje na nema yan uwana su Yaya Muhammad mu cigaba da hidimar biki”.
“Alhmdllh naji da
ɗ
in hakan Isma'il, ALLAH yay maka albarka. Kaima ALLAH ya baka wadda tafi
Tanee
ɗ
in”.
Murmushi ya saki mai sanyi la
ɓɓ
ansa na
ɗ
an motsawa alamar amsawa. da ga haka ya saki jiki da Ummi suka cigaba da tattaunawa akan hidimar bikin. Bata
ɓ
oye masa zancen barinsu gidan ba da planning
ɗ
insu akan rusa auren ƴaƴan Abba da yarant
a. Shima kansa yaji da
ɗ
in haka. Ya kuma tabbatar mata zai bada muhimmiyar gudun mawa. Da ga haka yay mata sallama ya tafi.
*___________________________*
Alhamdulillahi, akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, shirin biki kam da gaske
ya
ɗ
au harama. Dan kuwa baƙi harsun fara sauka a gidan musamman na
ɓ
angaren momy matar Abba. Hakama dangin hajiya mama sun fara sauka. A
ɓ
angaren Ummi ne dai babu ko kare da yazo har yanzu. Ko'a jikinta dan dama batasa rai ba. Mutanen arziƙi ma da zata tar
a anan a cewarta sun wadaceta.
A
ɓ
angaren amaren su Yaya Umar na
ɓ
oye har sun jajje sunyi jere a sabon gidansu. yayinda suma anan su hajiya mama suna shirin zuwa suyi nasu jeren na ƴaƴansu a gidajen Hayar da Abban ya kama.
Itama dai
Hibbah kayan nata jeren har sun isa gidanta. Dan kuwa yayunta sun ha
ɗ
a ƙarfi da ƙarfe da taimakon Isma'il sun mata kaya ƴan gaske na ƴar gata. Dan data ga kayan sai kawai ta fashe da kuka dan da
ɗ
i. Ita kanta Ummi da ta gani sai da ta koka a
ɓ
oye. Musamman
da ƴan jere suka dawo cike da farin cikin tarbar da suka samu da kuma ƙyawun gidan na Hibbah.
Hibbah Amarya kuwa da su Zahidah amaren su Yaya Usman Ummi da Mama Jiddah ce ke gyaresu da ingantattun magungunan sanyi harda amaryar Yaya Umar. Sai ingant
accen tsumi da duk ta sami iliminsu da ga Sheikh Aliyn ta (karku manta masanin sirrin magunguna ne
😹
). Dan hatta maganin sanyin ma shine ya ha
ɗ
ama su Hibbah da kansa. Sai Ha
ɗ
a
ɗɗ
un kayan gyaran fata na
dilka da ƙamshi da Mama Maimoon uwargidan malam ke gyar
esu da su itama. Ta ko ina Ummi dai ta zama ƴar kallo.
Gaba
ɗ
aya Hibbah ta tattara batun wasu ƴan sanda da wani master can
😏
ta watsar, dan kasancewar su waje guda da su Hafsat ya mantar da ita komai. Iyakarsu susha shaftarsu, kowa idan nata an
gon ya kirata ta koma gefe tasha soyayya. To ita Hibbah ma bazatace soyayyar take sha ba, dan sam Shuraim bai cika damuwa da kiranta a waya ba. Yafi tura mata text massege na sonjin lafiyarta kai tsaye. Ita kuma jan aji yasa itama bata kiran nasa balle nun
a damuwarta da hakan garesa. ko sau
ɗ
aya ma bata ta
ɓ
a ƙorafi ba.
★★★
A yau laraba aka saka dukkan amaren a lalle. Dan kamar yanda aka saka su Ameerah da Hibbah anan gidansu, haka aka saka su Zahidah a nasu gidajen batare da duk wanda k
e zagaye da su yasan su waye angunan ba. An dai san ana biki, hatta da Momy da Hajiya mama sunsani tunda anguwa
ɗ
aya ne layi
ɗ
aya. Sai dai basusan anguna ba basu kuma damu da sani ba tunda ba wani mu'amula mai karfi ce a tsakaninsu ba. Hasalima sun tsanesu
saboda suna hu
ɗɗ
a da Ummi. Ko gidan sukazo aka gamu da ƙyar suke amsa gaisuwarsu.
Yau akai kamu da ya kayatar matuƙa anan harabar gidan. Dan ƙarya sosai momy ta nuna ma ƙawayenta data tara cike da gida da danginta. Sai dai kuma koda anguna sukazo
fili bisa gayyatar da akai musu sai suka ƙare da bama autarsu kulawa ta musamman. Dan har liƙeta sukai da ku
ɗ
a
ɗ
e sanda masu ki
ɗ
an ƙwarya ke bugawa. Nanfa ƙananun magana suka fara tashi, zukatan su Ameerah fal baƙin ciki da takaici. ji suke wata muguwar ts
anar Hibbah na sake shigarsu matuƙa, amma dai duk sun danne a zukata bisa hu
ɗ
ubar iyayensu akan shirinsu.
Oho su Yaya Abubakar ma basusan sunai ba. Su dai kawai burinsu autarsu tayi farin ciki, tafi kuma kowa. Burin nasu kuwa ya cika. Dan ta haska ha
skawa mai tsayawa a rai duk da ango baizo ba danginsa sunzo ansha shagali da su.
Washe gari kuma alhamis akai walima da hajiya mama ta
ɗ
auki nauyi
😝
. Aka gayyato matan Sheikh Aliy sukai wa'azi, yayinda aka ci aka sha kowa yay
ɗ
iff. Gab da magrib
aka tashi. Su Ameerah kuma suka dasa nasu fatin su da kawayenau maza da mata a hotel. Babu ango ko
ɗ
aya a wajen, dan su su Yaya Muhammad ma zuwa lokacin suna manne da Umminsu dake ta musu nasiha suna sharar hawaye tamkar ba gida
ɗ
aya zasu cigaba da kasance
wa ba. Hibbah kuwa kuka take iya iyawarta harda amai. Da ga ƙarshe kuma sai zazza
ɓ
i ma ya rufe ta. Har sai da Isma'il da yazo kawo drinks da za'ai amfani da shi na
ɗ
aurin aure ya kira family doctor
ɗ
insu yazo ya dubata. Ana mata allura yay tafiyarsa shi da
doctor
ɗ
in.
*_RANA BATA ƘARYA........_*
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😂
.
*LALLAI YAU AKE TAKUN SAƘAA
😖🐒
*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI....
.._*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFA
N ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN
CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA
ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*
🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR
🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
*_Typing
📲
_*
*_Chapter Nineteen_*
...........Kamar
yanda suka saka
ɗ
aurin aure bayan sakkowa sallar juma'a su Ummi basu canja ba. Gida ya gama cika da dangin Momy da na Hajiya mama anata hidimar girki. Sai wasu tsiraru da ga abokan arziƙin Ummi na nan anguwa dana nesa.
Anguna kam suna can a gidan
da suka samu aro anan anguwar da abokansu. Sai dai tunda safe sun shigo sun gaida Umminsu. Tare da sake lallashin ƴar ƙanwarsu Hibbah da duk tabi ta takura kanta. Zazza
ɓ
in nata yama sauka tunda safe amma duk ta zama wata kalar tausayi. Magana ka
ɗ
an sai ta
kama hawaye. Ga ƙawayenta na secondary cike da
ɗ
aki amma duk ta ƙi sakewa. Sai faman shaƙiyanci suke mata ta kasa maida murtani dan bakin ya mutu murus.
Kusan sha
ɗ
aya wata ƙawar Ummi ta shigo ta sata tashi dole tai wanka. Mai kwalliya ta shigo
tai mata dai-dai misali dan da farko ma catai bataso sai da Ummi tai magana. Itama taci gayunta
ɗ
as tamkar wata ƴar talatin. Dan sam Ummi bata da ƙiba, ALLAH yayi mata jiki mai ƙyau, shiyyasa da yawan mutane idan akace itace ta haifa su Yaya Muhammad suka
n musa, inba ka nutsu wajen kallon fuskarta ba sai ka
ɗ
auka yayarsu ce kawai.
Amarya Hibbah ta fito ras abinta, tamkar ka saceta ka gudu. Ƙawayenta nata tsokanarta akan gaskiya ya kamata a
ɗ
auka hoto a turama ango. Banza tai musu dan ita sai ma yanz
u ta tuna da wani ango. Tun jiya
damuwarta kawai rabuwa da ahalinta batashi take ba. Ga shi tanajin kewar su Zahidah da babu dama suzo nan suma suna gidajen iyayensu.
A
ɓ
angaren amare su Ameera ma kowacce ta
ɗ
au kwalliya ta gani kasheni, da ka g
ansu kaga amare kam dan anata zuba iyayi da gwalli. Su barin gidan ma ko'a jikinsu suke jinsa. Ga ƙawayensu sun zagayesu sai ta
ɓ
ara da zancen banza suke zubawa suna sheƙa dariya.
Ƙarfe sha biyu da kusan kwata anguna suka shigo gidan cikin kwa
lliyar fararen shaddoji tas iri
ɗ
aya. Hatta da Ammar irin kayan ya saka shima. Idan ba'a fa
ɗ
a ba sai ka
ɗ
auka shima angon ne. Gu
ɗ
a mata da ke kai kawon girki a tsakar gida suka shiga musu. Kowa na yaba ƙyawun nasu da yima mahaifinsu addu'a da babu rabon ya
ga wannan rana.
Ummi da ƙawayenta na zaune a falo suka shigo. Tai sagade tana kallonsu idanunta na cika da ƙwalla. Tanaji a ranta inama ace Aliyu na raye wannan rana...... Durƙusawar da sukazo gabanta sukai duka ne ya katse tunaninta. Tasa hannu
ta share ƙwallar da suka taru mata a ido tare da kai hannu ta dafa kan Yaya Usman da ke kusa da ita. Sai kawai ta fashe da kuka. Har rige-rigen matsawa suke gabanta kowa ya riƙe hannunta idanunsu na cikowa da ƙwallan suma.
Sosai abin ya birge mu
tane ya kuma basu tausayi. Ummi ta shiga kwarara musu addu'oi da sanya albarka ana amsawa da amin. Kafin a kira Hibbah itama mai hoto yay musu. Itama kanta sai da tai hawayen jin da
ɗ
in ganin ƴan uwanta kamar ka sacesu ka gudu dan ƙyawun da sukayi. Sai dai
tanajin
ɗ
acin kasancewar su Amlah matsayin matansu bayan su Zahidah.
Suna tsaka da hotunan kira ya shigo wayar Hibba. Tayi ƙoƙarin sharewa aka sake kira. Yaya Muhammad dake kusa da ita ya
ɗ
auka wayar ya duba. Ganin Shuraim ke kiran nata ne ya sashi
hararta yana miƙa mata. “Auta bana son rashin ji fa. Maza kije da ga waje sai ki
ɗ
aga”.
Kanta kawai ta
ɗ
aga masa. Tare da tashi tabi ta kitchen
ɗ
insu ta zagaya baya domin kiran Shuraim
ɗ
in......
“Yauwa A.G zamu iya magana yanzu na fito”.
Muryar Abba ta saka Hibbah saurin dakatawa a ƴar barandar kitchen
ɗ
in nasu. Abu biyu ne yaja hankalinta ga Abban. Na farko yanda yake tsaye a la
ɓ
e wajen tamkar wani tsohon munafuki, na biyu sunan A.G da taji ya ambata. Wanda inhar hasashenta yayi dai-dai
sunan dattijon jami'in nan haka yake shima A.G. Maganar Abba ta sake katse tunaninta.
“A.G nawa, kasan mutunuyar taka tana nan tana jira kazo ka saceni ni da duk masu hannu a
ɗ
aurama yayunta aure da ƴaƴana.”
Batajin mi ake fa
ɗ
a da ga c
an, sai dai yanda Abba ya tuntsure da dariya ne ya saka zuciyarta tsargawa duk da batasan wane A.G
ɗ
in ba. Abba ya ciga da fa
ɗ
in, “Inaga zan fito yanzun nan kuwa insha ALLAH, dama munyi shirin wucewa wajen
ɗ
aurin auren ne. To amma su zan barsu su wuce kai
kuma mu ha
ɗ
u a gidan hutuna muyi magana”.
Gaba
ɗ
aya jikin Hibbah rawa yake, tai saurin leka bayanta. Ganin hankalin yayunta da su Ummi duk yana kan yin hoton ya sata saurin jan ƙofar kitchen
ɗ
in tayo waje. Bayan Abba da ya bar wajen tabi da sauri.
Kasancewar da sanda yake tafiya saboda kafarsa da bata gama warkewa ba yasa Hibbah cin masa, sai dai a sace take binsa yanda bazai gane ba. Suna gab da fita ta
ɓ
arauniyar ƙofar da ke bayan
ɗ
akunan su Abba taci karo da hijjab
ɗ
in wata mata dake alwala a fan
fo. Dauka tai ta saka, tai saurin bin ta gate ta fice batare da an ganeta ba dan harda nikaf. Cikin sa'a ta
cimma Abbah ta baya saboda harda gudu ta ha
ɗ
a duk da tarin mutane dake shirin tafiya
ɗ
aurin aure a ƙofar gidan nasu. Ganin Abban ya shiga wata baƙar
mota dake fake a barauniyar ƙofar tasu itama tai azamar tare mai napep.
“Malam dan ALLAH motar can nakeso kabi, amma banason ya fahimci shi
ɗ
in muke bi Please”.
“Babu damuwa hajiya, amma kenan ku
ɗ
inki zasu kasance masu nauyi fa?”.
Batare da