Showing 69001 words to 72000 words out of 186858 words

Chapter 24 - TAKUN SAKA COMPLETE

10 Sep 2026

20

tamaji abinda yace ba tace, “Babu damuwa muje”.

Kasancewar mai napep da alama kwararren matuki ne ya dinga bin Abba abaya ta yanda bazai iya fahimta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso wata anguwa mai ƙarancin hayaniyar mutane. Da alama

sabuwar anguwa ce, dan ga uncompleted buildings nan bar-katai. Sai dai kasancewar inda Abba ya faka motar a farko-fatkon anguwar ne sai ya zama wajen yayi

ɗ

an rukunin gidajen da aka kammala. Tun a titin ta sauka. Ta dubi mai napep

ɗ

in cikin raba hankalinta

biyu. “Dan ALLAH ka jirani nan bazan jimaba zan fito. na maka alƙawarin ko nawa ka bukata zan baka”.

Cikin farin ciki da tunanin yayi babban kamu yace, “Babu damuwa hajjaju a fito lafiya”.

Gaba Hibba tai batare data amsashi ba. Ta bi ta bayan

gidan inda take addu'a da fatan samun koda karamar hanya ce da zata shiga gidan. Dan Abba na shigewa aka rufe gate

ɗ

in. Sam babu wani hanya data samu, dan haka tai azamar sake dawowa ta gaban gidan zuciyarta na ayyana mata wata dabara. Gate

ɗ

in ta ƙwanƙwa

sa ka

ɗ

an tana waige-waigen bayanta da addu'ar dacewa. Batare da zaton anjita ba taji an bu

ɗ

e gate

ɗ

in. Tai saurin kallon wajen tana jan numfashi. “Barka da rana”. Ta fa

ɗ

a cikin matukar kashe murya.

Kallon sama da ƙasa mai gadin yay mata, kafin yace

wani abu tai azamar fa

ɗ

in, “Ni baƙuwar Alhaji ce”.

Maigadi yay

ɗ

an shiru alamar tunani. kafin yace, “Amma hajjaju idan Alhaji zaiyi baƙuwa yakan sanar min, yanzu ko bai fa

ɗ

a ba ya shige duk da naga kamar cikin sauri yake”.

Cikin ƙara ƙasa

da murya Hibba tace, “Ka bama kanka amsa kenan, saurin nasane yasa bai fa

ɗ

a maka ba inaga. Amma bara na kira maka shi zai fi.....”

Da sauri maigadi yace, “A'a hajiya bama sai anyi haka ba. Nasan inba da sanin Alhaji ba babu wani mahaluki kam da za

izo nan. Bismillah”.

Ya kai karshen maganar yana matsawa ya bata hanya. Wani shegen ajiyar zuciya Hibba taja tana ƙoƙarin ha

ɗ

iye busashen yawun da ya daskare mata a baki tana ƙoƙarin shigewa.

“A fito lafiya hajjajuuu”.

Maigadin ya fa

ɗ

a cike d

a shaƙiyanci.

★★★★

A

ɓ

angaren su Yaya Muhammad kam sun cigaba da hotonsu da tunanin Hibbah nacan na waya da Shuraim ne. Sunyi hotuna sosai da jama'ar da ke a sashen na Ummi kafin su fito domin tafiya massallaci karsu rasa salla. Kusan tar

e suka fito da gayyar su Kawu Hannafi da ƙannen Momy da yayunta.

Cikin tsari gayyar motocin

ɗ

aurin aure suka bar anguwar batare da kowa ya farga babu Abba a tafiyar ba. Yayinda aka bar mata na cigaba da himar abinci da shagali a cikin gida. Sun i

sa massallacin juma'a gab da

za'a fara khu

ɗ

uba. Kamar yanda aka tanadar musu gaba saboda za'a

ɗ

aura aure duk aka basu hanya suka shige. Sai da suka nutsu waje guda Sheikh Aliy ya fara gabatar da khu

ɗ

uba mai ta

ɓ

a zuciya akan kashe-kashen dake faruwa a ƙasar

nan na zalunci. Tare da jan hankalin hukuma da gwamnati akan sake jajircewa. Hakama jama'ar gari ba zama zasuyi kallon gwamnati da hukumaba suma. Dolene a miƙe da addu'a kuma kowa ya zama jami'in sirri akan abinda bai gamsu da shi ba. Sosai khu

ɗ

uba tai ta

siri a zukatan bayin ALLAH. Da ga haka aka fara gabatar da sallar Juma'a.

Kasancewar mutane sun san da

ɗ

aure-

ɗ

auren aure bayan idar da salla babu wanda yay yunƙurin tafiya. Sai lokacin su kawu Bello suka fahimci babu Abba tare da su. Nan fa aka shi

ga tambayar juna, sai dai kowa yana cewa bai gansa ba maybe bai ƙaraso ba..

Miƙewa ƙanin Momy yay ya fita a taron da zummar neman wayar Abba suji ko ina ya tsaya.....

★★★★★

Addu'a Hibbah ke karantowa tana ƙara kutsa kanta cikin g

idan da batasan kansa ba. Sai da ta ga ta bacema idon maigadin sanann ta

ɗ

an dakata ta sauke numfashi. Haggu da damanta ta kalla ko zataga ƙofar shiga. Cikin sa'a idonta ya hango mata window. Da sauri ta nufi windown tana addu'ar ya kasance inda zata iya h

ango su Abba.

A rufe windown take, dan haka tai gaba cikin takaici da fatan samun mafita a gaba. Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke saboda cin karo da ƙofar kitchen irin ta bayan nan. Ta kama handle

ɗ

in ta mur

ɗ

a a hankali cikin sa'a ta bu

ɗ

e. Wani

irin da

ɗ

i ne ya baibayeta kamar ta tashi sama. kitchen ne babba, komai na amfani akwai, da alama ma ana amfanin da shi, dan yanzu hakama ga alamun anyi girki a ciki. Gaba tai zuwa ga ainahin ƙofar kitchen

ɗ

in ta cikin falo, tai saurin maida kanta baya sabo

da ganin Abba zaune tare da wani mutum a dining

ɗ

in abinci jere tamkar masu shirya fati.

“Ina fatan kukun nan taka ta fita ko?”.

Mutum da ke tare da Abban ya fa

ɗ

a. Ƴar dariya Abba yayi, cikin salon narke murya tamkar wanda ke gaban mace yace,

“Karka damu nace taje waje ta zauna. Bakuma zata shigo ba sai na bata umarni kaima ka sani”.

“Hakane baƙon ya fa

ɗ

a yana sumbatar hannun Abban”.

Wani irin mugun fa

ɗ

uwa gaban Hibbah yay. Tai saurin kauda abinda zuciyarta ke bijiro mata ta sake m

aida hankali akansu.

“A.G kasan a ƙage nake da son jin abinda ke bakinka, duk da kuwa kwana biyu ina tare da kewar harka saboda jiyya data cikuykuye rayuwata. Amma soon zan dawo, fatana a

ɗ

aura auren nan yau cikamakin bukatuna su sake shiga tafin h

annuna sannan na dawo. Kaima kasan banida wani buri da ya wuce dukiyar ƴaƴan Aliyu cigaba da kasancewa a hannuna. Hakan kuma naga bazata ta

ɓ

a tabbata ba har sai na aura musu ƴaƴana, sannan na bisu

ɗ

aya bayan

ɗ

aya na halaka su. Dan duk wadda ta fara samun c

iki a cikin ƴaƴana to mijinta ne zai fara baƙuntar lahira. Ko ƴaƴan nawa da mahaifiyata basu san da shirin nan nawa ba. Sai na gama da su kaf sannan na

ɗ

inke bakin zaren *_TAKUN SAAƘA_* ta da Asiya. Wadda ubanta ne ya fara sarƙata akan mugun bugun da yay m

ini tun tana ƴar shekara goma sha

ɗ

aya kacal a duniya.”

Dariya A.G yayi da fa

ɗ

in, “Baka da dama Gwarzo. Wato kai sam baka manta bashin gaba.”

“Har abada kuwa A.G. Naso fanshewa akan budurcinta hakan ya gagara, abin takaici da baƙin ciki ta s

ake hawa kaina, aka aurama Yayana uwa

ɗ

aya uba

ɗ

aya shi ya mora bayan na ƙwallafa rai. Tazo ta katantane komai, duk hanyar dana

ɓ

ullo akan wasoson dukiyarsa sai tabi ta toshe ta hanyar fargar da shi. Shiyyasa yanzu daya mutu bayan ya tara musu na shirya ha

wa kan dukiyar, sai dai nafison nacita a ga

ɓ

ar da Asiya zatafi jin ciwo da ra

ɗ

a

ɗ

i, kamar yanda na

ɗ

auki tsahon shekaru ina jin ciwo da ra

ɗ

a

ɗ

in abubuwa masu yawa a kanta. Wannan dalilin ya sani yin dakon shekaru goma sha tara ina haƙurin cigaba da juyata ta

na ha

ɓ

aka har zuwa yanzu da wasan zai fara. Sai na

ɗ

an-

ɗ

ana-ma Asiya azabar ciwon mutuwar ƴaƴanta

ɗ

aya bayan

ɗ

aya a tafin hannunta”.

“Anya kuwa hakan ta kasance Gwarzo? Dan wannan ƙaramar ƴar tata ta fi sauran yaran tsaurin ido da rashin tsoro. Shi

yyasa nake ganin wautarka na canja

ɗ

anka da zai aureta zuwa wani daban, duk da nasan wanda ka canja

ɗ

in yafi

ɗ

anka kwaƙwalwa da wayo da hatsabibanci. Kagafa shekararta sha takwas kacal amma take da dabarar ƙulla agreement da ƴan sanda akan a ƙwamusheka ran

ar aurensu domin yayunta su ku

ɓ

uta daga auren ƴaƴan naka. Ina jimaka tsoron wannan yarinyar fiye da kowa cikin ƴaƴan matarka. Koda yake nasan Master bazai ta

ɓ

a yarda da mace ba”

“Humm kai kasan tun randa ka bani labarin nan da mamakin yarinyar nan

nake kwana nake tashi a raina. Yanzu haka fa tana can tana jiran ku tattareni kenan fa?. Batasan kai

ɗ

in mutumina bane.”

Atare suka kwashe da dariya. Yayinda Hibbah dake makale tana saurarensu ta daskare a tsaye, dan zuwa yanzu ta gama fahimtar datt

ijon jami'in nan ne dai A.G da ya sakata bibiyar Master.......

Maganar Abba ta katse tunaninta.

“Karka damu ita na gama da lamarinta kaima ka sani. Shi wanann yaron dana kawo ya canji Junaidu dan ya aureta kamar yanda ka fa

ɗ

a yafi Junaid hatsabiba

nci kaima ka sani, sannan a tafin hannunmu yake a kuma ga

ɓ

ar da muke more ƙuruciyarsa. Ana gama

ɗ

aura auren zanbi shawararka na biya mata ku

ɗ

in karatun tafiya China kamar yanda take buri, da wanann damar zanyi amfani na

ɓ

adda rayuwarta. Dan rashin nata ne

zai fara karya rayuwarsu saboda tsananin son da suke mata matsiyatan sai kace ƴar gwal. Ku kuma da ya

ɓ

addata zaku amfani da wannan damar ne ku fito ku nunama duniya shi wannan Master

ɗ

in da kuke nema ruwa a jallone ya sace ta. Kaga shikenan babu mai zargi

n Halilu Hamza gwarzo kenan ko”.

Ya kare maganar da shaƙiyancin da ya sakasu sake kecewa da dariya. Jikin Hibbah ne ya kama rawa. Tai saurin kai hannu ta toshe bakinta jin kuka zai kufce mata. Dai dai nan A.G ke fa

ɗ

in, “Gaskiya mun iya maida mutane wa

waye. Kowa ya saki baki kullum muna aikin tukuru na son kamo Master, basu san shi kansa Master

ɗ

in mune muka ƙirƙiresa ba. Yana gama tattare mana ku

ɗ

a

ɗ

en shima zamu

ɓ

addashi a doron ƙasar baki

ɗ

aya, mu kuma cigaba da amfani da rigar jami'an tsaro wajen tsu

la tsiyarmu. Yayinda duk wanda ya fito da niyyar aikin gaskiya mu

ɓ

adda banza, dan mu ba gyaran kasarne gabanmu ba. Wanda suke gaba damu kuma mu cigaba da kwantar musu kai muna nuna mun fisu san ƙasar da cigabanta, da tabbatar musu aiki muke tuƙuru. Kaga m

un toshe ko ina kenan”.

Dariya suka kuma kwashewa da shi, har sai da kira ya shigo wayar Abba sanann suka tsagaita. Ya miƙe yana fa

ɗ

in, “Alhaji Alu ne ke kira, ina kyautata zaton suna wajen

ɗ

aurin aure tashi muje dan nasan ana gab da

ɗ

aurawa kar ayi

babu mu.”

Da sauri A.G ya riƙo hannun Abba cikin marairaicewa yake fa

ɗ

in, “Gaskiya ina da bukata, shine ma dalilin da yasa na kiraka nan. Ka barsu kawai su

ɗ

aura tunda ko baka akwai masu amsa da bayarwa, ni kuma ka

ragemin zafi anan. Dan kwana biyun

nan matasan ma da muke

ɗ

an samu mu taushe wa'azin malaman nan ya fara tasiri a ransu gudunmu sukeyi shegun.” Abba ya bu

ɗ

e baki zaiyi magana A.G ya sake marairaice masa da rungumosa jikinsa cike da salon shai

ɗ

anci da bushewar zuciya irin ta masu fasadi da

rashin tsoron ALLAH a ban ƙasa

😭

. (Wa'iyazubillah. ALLAH mun tuba ka yafemu

🙏🏻😭😭

).

(Ya ALLAH ka gafarta mana badan halinmu ba, ka kare mana zuri'armu da mazanmu da ƴan uwanmu da matasan al'ummar musulmi baki

ɗ

aya

😭🙏🏻

. Abba

ɗ

an homo, A.G

ɗ

an homo

, da ire-irensu abokan ƙazantarsu da yawa dake lullube da rigunan mutunci suna cin dunduniyar al'umma da addini. Kuga dai A.G, ya shige cikin jami'an tsaronmu jajirtattu yana tsula tsiyarsa ta hanyar ruguza shirye-shiryensu batare da sun sani ba. Shin kama

r yanda ya fa

ɗ

a Master yaronsa ne? Su Master kema aiki?. Mu cigaba da kasancewa a cin TAKUN SAAƘA domin jin yaya take ne?)



Gaba

ɗ

aya jikin Hibbah rawa yake yi, ta shiga tafiya da baya-baya zuciyarta na tsitstsinkewa tamkar zata fa

ɗ

o waje.

Wani irin duhu-duhu idanunta suka farayi, abinda takeji a labari shine yau a zahirin rayuwa take gani ga ƙanin mahaifinta da idan aka tsaga jininsa za'a ga nata a ciki. Innalillahi wa inna-ilaihirraji'u. (Dole ne kafin a daura auren nan tayi wani abu) wan

nan tunanin ya sakata zabura ta fito a guje. Kotakan maigadi dake zaune yana sauraren redio bataiba ta bu

ɗ

e gate ta fice. Saurin miƙewa yay yana tambayarta lafiya?. Ina batama san yanai ba. Yay saurin bin bayanta wajen, sai dai kafinma ya leƙo ta kusa kaiw

a titi inda take tsammanin mai napep

ɗ

in nan na jiranta.

Waige-waige ta shigayi dan babu mai napep babu alamarsa. Cikin hakki da rawar jiki ta ciro wayarta dake maƙale cikin zani ta hau laluben wayar Yaya Muhammad. Harta katse bai

ɗ

aga ba. Ta sake

kira nan ma bai

ɗ

aga ba. Ta maida akalar kiran nata kan Yaya Abubakar tana fassewa da kuka. Sai dai shima harta katse bai

ɗ

aga

ɗ

in ba.

“Yaya ku

ɗ

aga dan ALLAH”. Ta fa

ɗ

a a ki

ɗ

ime tana zubewa ƙasa da sakin wani kuka mai ban tausayi. Tunanin kiran A

mmar ne yazo mata a zuciya. Cikin sa'a kuwa ya

ɗ

aga a bugu biyu, sai dai batajinsa sosai sai tsananin hayaniyar ƴan

ɗ

aurin aure. Da ga can shima sai faman fa

ɗ

in, “Hello! hello! Auta bana jinki wlhy, ki yi haƙuri zan kiraki za'a fara

ɗ

aura auren ne”.



Kafin tace wani abu ya yanke wayar ƙit. Daga wayar tai zata dasa da kasa sai kuma ta fasa. Tai azamar yage niƙaf

ɗ

in fuskarta ta jefar da tunanin fara gudu tabar cikin anguwar kozata sami abun hawa. Inda rabo sai ta isa massalacin kafin a fara

ɗ

aura auren.





★★

Matashin saurayin da ke can baya ka

ɗ

an da Hibbah cikin wata farar mota ya gyara zaman abinda ke kunnensa, cike da girmamawa yace, “Boss ta fito. da alama abin hawa kuma take nema, tunda na ka

ɗ

a mai napep

ɗ

in da ya kawotan”.



Bansan amsar da aka bashi ba da ga can, ya dai gya

ɗ

a kansa cikin ƙara bama wanda yake maganar da shi girma, tamkar yana gabansa ya sake fa

ɗ

in. “Yes Master. Insha ALLAH”. Da ga haka yay ma motar key tare da

harbata kan titin ya nufi Hibbah da ke tsaka

da tattare hijjabi da alama gudun da ta yankema zuciyarta shawara take shiryamawa.

Sai dai jin tamkar tahowar mota a bayanta ya sata sauri juyowa ga titin tana ƙoƙarin yin alamar tsaidawa. Bai tsaya ba sai da ya

ɗ

an gota ta sannan ya dawo da bay

a. Yana tsayawa ko tunanin taga waye bataiba ta bu

ɗ

e murfin ta shiga baya. “Bawan ALLAH dan ALLAH babban masallacin juma'a na Sheikh Aliy Maina zaka kaini, ka taimakeni kayi sauri na roƙeka dan ALLAH.”

Jin shiru bai amsata ba bai kuma tada motar b

a ya sakata cigaba da magana cikin tsumar jiki da ƙaguwa. “Malam dan ALLAH ka taimakeni, wannan ita ka

ɗ

aice damar da nake da ita ta ƙu

ɓ

utar da ƴan uwana da ni kaina. Tana kufcewa mun fa

ɗ

a gararin rayuwa”.

Yanzun ma komai bai ceba. Sai handkerchief



ɗ

in da ke saman cinyarsa ya

ɗ

auka ya jefa mata a kan fuska. Hannu tasa ta ka

ɗ

e handkerchief

ɗ

in da fa

ɗ

in, “Malam wane irin wulaƙanci ne haka? Minene wannan ka.........”

Ta kasa ƙarasa abinda take shirin fa

ɗ

a

ɗ

in saboda duhu da ya mamaye ganinta bak

i

ɗ

aya. Tai ƙoƙarin fisgo numfashin da ke san kufce mata tana kai hannu bisa ƙofar da laluben

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login