Showing 21001 words to 24000 words out of 186858 words
bada awanni goma domin binciko wanda ya haresu, hibbah dai kuma itace ta kai harin da babu niyyar dalilin da su suke kallo.
To yaya zata kasance kenan tsakanin Muhibbat Aliyu Hamza da Jami'an ƴan sanda da Master kenan?
🤔
. TAKUN SAAƘA wasa farin girki
👎🏻
_*
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI
SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI
NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEW
A DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull
_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABD
ULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*
INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*
🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR
🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
*_Typing
📲
_*
*_
Zafafa biyar na ku
ɗ
i ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna ha
ɗ
aki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika sa
ɓ
a mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
_________________________
*_MG's SKIN
CARE_*
*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*
💃🏻
*_To maza kuzo ga mg's skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*
*_mg's skincare na
da black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar
💯
_*
💃🏻💃🏻
*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne
a gareku
💃🏻
_*
*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi
💃🏻
_*
*_Then akwai bridal kit shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za'a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*
_Duk zaku tabbatar da hakanne
ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari
💃🏻😍
🥰
_.
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Location:kaduna buh we deliver Nationwide
Delivery is not free
buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift
_*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_
_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_
_*Kindly chat with us via 08062991549.*_
____________________
*_Chapter Nine_*
.............Tunda jami'an suka dawo da labarin rashin nasara zukatan manyansu yay matuƙar ƙunci. Awanni ƙalilan suka rage musu da ga umarnin gidan g
wamnati. Cikarsu babu Master a hannunsu kuwa yana nufin sun gaza a idanun al'ummar jiharsu da ƙasa baki
ɗ
aya. Hakama ga gwamna da muƙarrabansa.
A gefe ga gidajen jaridu da duk wata kafar ya
ɗ
a labarai sun baza kunnuwa da idanun domin ganin yanda aw
anni ashirin da hu
ɗ
u zasu cika tare da wannan
ɓ
arawo a hannunsu ko sa
ɓ
anin hakan.
Wa
ɗ
an nan tunane-tunanen nasu yasa su shirya zaman meeting na gaggawa.
Dukkan wani babba mai alhakin fa
ɗ
a aji ya hallara a
ɗ
akin da meeting
ɗ
in zai guda
na. Sai wanda ya jagoranci jami'an da suka dawo yanzun nan da shirin kamo Master da yaransa..
Kowa ka kalla a
ɗ
akin meeting
ɗ
in kasan yaci ya ƙoshi, dan babu wasu kamannin wahala tare da su. Da'ace ƙasace mai ƙyaƙyƙyawan tsari sun cancanci yin ri
taya duk su koma gefe a kawo matasa masu jini a jika da basirarsu ke aiki da kaifin ƙwaƙwalwa a zuba a madadinsu. Su kuma su zama dattijai masu bada shawara wa ƙasa ta bayan fage matsayinsu na iyayen ƙasa. Sai dai sam a wannan ƙasar tamu ba haka bane ba. A
nyi sakacin barin matasan da ke da basirar zuwa da salonsu na ƙuruciya wajen kawoma ƙasa cigaba zama ƴan ta'adda, dukkan tarin basirarnan tasu da ƙuruciya ta koma aiki ne ƙarƙashin aikata laifuka. Iyayenmu da gwagwarmayar rayuwa da raunin shekaru sukaima y
awa sun zama sune masu riƙe da madafun iko wajen zartarwa da hukuntarwa. A duk lokacin da ƙasa tai sakacin rashin amfani da basirar matasa da ƙuruciyarsu wajen aikata alkairi, to lallai shai
ɗ
anu zasuyi amfani da basira da ƙuruciyar wa
ɗ
anan matasan wajen ka
fa tantin ta'addancin da zai ruguza ƙasa.
A ƙasarmu ta gado iyayenmu sune ƴan siyasarmu, sune masu riƙe da madafun iko na mulkin gargajiya da na siyasa, sune riƙe da hukumomin ladabtar da masu laifi, sune riƙe da manyan ku
ɗ
a
ɗ
e na kasuwanci, sune riƙ
e da makarantun da ake bamu ilimi, sune.. Sune... Sune komai.
Babu wata hanya ko ƙofa da suka barma matasan wajen nuna bajintarsu da ƙwazon da ALLAH ya haliccesu da shi. Kallonmu suke masu yawan wauta, masu shashanci, masu ƙuruciya, masu rashin kun
ya da rashin ganin girman na gaba da su. Masu... Masu... Ta ko ina. Amfaninmu kawai mu cigaba da zama a ƙasa har sai lokacinmu yayi. To yaushene lokacin namu zaiyi? Shin sai muma mun kai irin shekarunsu mu danne na ƙasa da mu kenan?. indai har a haka za'a
cigaba da tafiya lallai da alamar ƙasar tamu bazata ta
ɓ
a zama mai sauyawa ba ko samun ci gaba. Domin anyi sakacin ajiye lokaci an
ɗ
auki rauni.
Shi kuma lokaci a duk sanda aka gaza amfani da shi ta hanyar da ya dace wucewa yakeyi yabar mai shi da cizo
n yatsa da dana sani. A lokacin kuma daka buƙaci gyarawa sai ya kufce maka dan kayi sakaci wajen sarrafashi a sanda ya dace. To ya kamata manyan ƙasarmu su fahimci MATASANMU sune LOKACINMU. Cigaba da sakacin ƙinyin amfani da baiwarsu akan lokaci na nufin b
aragurbi amsarsu su su amfana da wannan damar wajen
maidasu masu ruguza ƙasar da ku kuke ganin kunata ginawa. Sanda zakuyi ƙoƙarin son tarosu kuma sunyi nisan da bazasuji kiranku ba sam.
Bawai munason fiddo da gazawarku bane ma duniya ko goyon bayan l
aifukan matasa. Muna buƙatar ku duba ku kuma fahimci sai da matasa ƙasa ke iya samun ci gaba. Basu dama kuma shike nufin daƙile dama a hannun masu
ɗ
orasu bisa bigiren ta'addanci. Kun cancanci kuma muyi alfahari da ku, dan kun bamu gudunmawa ta musamman bay
an kasancewarku iyaye a garemu.
Bayan ƙarin bayani da suka samu a bakin jami'in da suka fita bibiyar Master zukatansu sun ƙara
ɗ
aci. Ɗakin yayi shiru kowa na nazari da tunani a cikin zuciyarsa. Ɗaya da ga cikinsu da zuciyarsa ke raya masa wani
abu ya nema izinin yin magana.
“Bismillah, an baka dama. Ya kamata kowa ya fa
ɗ
i abinda ke bakinsa ko hakan zai bamu wani haske da ga kullewar da kawunanmu sukayi.” Ogan nasu ya fa
ɗ
a cike da taraddadi.
Kansa ya jinjina da fa
ɗ
in, “Thank
s you sir. Dama wani tunanine yakemin yawo a zuciya game da ita wannan yarinyar datai mana aikin. Shin baƙwa tunanin shine ya tsara duk hakan kasancewarsa shu'umin mutum kuwa?. Al'amarin da matuƙar mamaki ta yanda ta bibiyesa cikin sauƙi. Idan har dama ba
shirinsa bane ta yaya akai ta jefa masa abunda ta samu damar bibiyarsa?”.
Da sauri wanda ke a kusa da shi ya ashe da fa
ɗ
in, “Ashe bani ka
ɗ
ai nake wannan tunanin ba. Tabbas da alamar akwai lauje cikin na
ɗ
i game da wannan al'amarin. Nasan za'a iya sa
mun mai ƙwazo da kaifin basirarta, amma yanda al'amarin ya faru da ƙanƙantar shekarunta sai nake ganin kawai shiri ne na musamman akai. Dan bana hangen tana da wani ƙyaƙyƙyawan tunanin da har zuciyarta zata bata damar aikata hakan. Banda shirme da shiririt
a mi yaran yanzun suka iya? musamman ma ita da ta kasance MACE”. Ya ƙare maganar cikin jin zafi sosai.
Wanda ya gana da Hibbah dake ta faman buga pen a kan la
ɓɓ
ansa yana kallonsu da nazarin maganganunsu yay murmushi. “Wannan tunanin namu na gani
n yaranmu bazasu iya komai ba wajen taka rawar gani ke maida ƙasarmu da mu baya a koda yaushe. Da hakan kuma suke samun damar yin amfani da basirar tasu a gur
ɓ
atacciyar hanya. Tabbas ita
ɗ
in MACE ce kuma ƙaramar yarinya, amma kallonta da rauni na *
ɗ
iya mac
e* shine babban kuskuren mu. Banace inada tabbacin bata da alaƙa da shi ba, dan shi shu'umin mutum ne hatsabibi da zai iya aikata duk ma abinda bamuyi tunaninsa ba ko munyi. Sai dai banason mu kasa fahimtar cewar itama duk da kasancewar tata MACE zata iya
taka wata rawar gani a harkar tsaro da duk wani sha'ani na rayuwa duk da raunin da ALLAH yay mata. Shawarata anan itace mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse
ɗ
aya”.
Sake maida hankalinsu sukai garesa domin sonjin ƙarshen zancen.
Ya gyara
abin maganar gabansa yana binsu da kallo
ɗ
aya bayan
ɗ
aya. “Ma'anar mu jefa tsuntsu biyu da dutse
ɗ
aya shine muyi amfani da wannan yarinyar ta hanyar riƙeta a jikinmu ta zame mana ma'aikaciyar sirri. Ta wannan hanyar zamu amfanu da alkairinta da kaifin bas
irarta. Mu kuma saka mata ido wajen gano shin akwai alaƙar da zuciyarmu take zargin tsakaninta da shi ko babu?”.
“Yes! Wannan shawarar taka tayi matuƙa *A.G*”. Ogansu ya fa
ɗ
a yana tafa masa. Hakanne yasa suma sauran tafa masa duk da wasunsu bata
i musu ba sam. Dansu babu abinda zukatansu ke ayyana musu sai ganin babu abinda Hibbah zata iya matsayinta na
ɗ
iya MACE mai kuma ƙarancin shekaru.
Sun cigaba da tattaunawa har zuwa wani lokaci, kafin ogan nasu ya bada damar shigo da Hibbah.
Hibbah da damuwar ahalinta kecin ranta ta shigo fuskarta a cinkushe babu ko
ɗ
igon walwala. Babu abinda zuciyarta tafi bukata a yanzu kamar tozali da Ummi da yayunta dan tabbatar da babu abinda ya faru da su. Zama tai a kujerar da aka nuna mata
bayan ta gaishesu ranta fal jin haushinsu, musamman mutumin
ɗ
azun da tun shigowarta da shi ta fara ha
ɗ
a ido yana mata murmushi.
Bayan sun gama nazartarta da ƙare mata kallo ogan nasu yay gyaran muryar da ta saka Hibbah
ɗ
ago manyan idanun ta kall
esa. Ganin yanda ya kafeta da nasane ya sata sake maida kanta ta duƙar tana wasa da yatsun hannunta.
“Muhibbat Aliyu Hamza!”.
Ya kirayi sunanta murya babu alamar wasa. Hakanne ya saka gabanta fa
ɗ
uwa, ta sake
ɗ
agowa tana amsa masa da rawar murya. “
Na'am yalla
ɓ
ai”.
“Miye alaƙarki da Master!?”.
“Master kuma yalla
ɓ
ai? Ni ban sanshi ba”.
“Kin tabbatar?”.
Kanta ta jinjina masa.
“Taya za'ai mu yarda baki da alaƙa da shi?. Bayan tsahon shekaru biyu kenan kowace hukuma ta jami'an
tsaro farautarsa suke, amma sun gaza koda ganin farcen yatsansa. Sai gashi ke a cikin kwana
ɗ
aya rak kin haresa akan dai-dai?”.
“Ni wlhy yalla
ɓ
ai bansanshi ba, bakuma ni da wata alaƙa da shi ko sanin wanene shi. Na aikata duk abinda kukaga nayi ne
saboda wasa da rayukan mutane da sukeyi ta hanyar power rider amma badan wani dalili ba”.
“Okay, mu
ɗ
auka hakanne kamar yanda kika fa
ɗ
a
ɗ
in. Yanzu wane tunani kikeyi game da makomar ahalinki?”.
Saurin
ɗ
agowa tai tana kallonsa idanunta cik
e da ƙwalla. Muryarta na rawa tace, “Amma yalla
ɓ
ai naga na muku aikin da kuka buƙata dan na tabbata kun kamasa. Kuma kun tabbatar min hakan shine fansar ahalina ai”.
“Eh tabbas haka muka fa
ɗ
a, sai dai kuma ba'a samu nasara ba kamar yanda mukai tun
anin za'a samu. Rashin samun nasarar kuma na nufin shigar ahalinki a ha
ɗ
ari ta fuska biyu. Na farko mu jami'an tsaro ba zamu barsu ba har sai wancan hatsabibin yazo hannunmu. Hakan shine zai wankeki a garemu mu tabbatar baki da alaƙa da shi, ahalinki kuma
su ku
ɓ
uta. Na biyu dole ne mu baki kariya yanzun dan tabbas zaki zama abin farautarsa kema dan bazai barki ba tunda kin karya masa tarihi. Dolene kowane motsinki dana ahalinki su kasance a tare damu. Idan kin amince ki cike wannan. Kokuma kiyi tafiyarki am
ma babu ruwanmu da abinda zai samu ahalinki. Zakuma mu fitar da bayanan sune ke aikata laifukan da muka nuna miki
ɗ
azun da mabanbanta fuskoki. Kinga za'a kamasu a kaisu kotu, da ga ƙarshe a yanke musu hukuncin kisa bayan duniya ta sansu matsayin ƴan ta'add
a”
Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibbah. Idanunta suka ciko da hawaye ta shiga girgiza musu kai la
ɓɓ
anta na rawa. “Dan ALLAH yalla
ɓ
ai karkuyimin haka. Wlhy bani da alaƙa da mutumin nan sam, iya gaskiyata na sanar muku.”
“
Ta hanyar shigowa kiyi aikin sirri da mu ne kawai zai tabbatar mana da hakan, ahalinki kuma su ku
ɓ
uta da ga garesa da mu kammu. Gashi ki cike wa
ɗ
an nan takardun idan har kin amince”.
Da ƙarfi Hibbah ta rumtse idanunta. Wani irin zafi da
ɗ
aci na s
auka mata cikin zuciya. Karan farko na rayuwarta da taji tsiwa batai mata rana ba. Tanajin tsana mai yawan gaske akan mutumin da batasan wanene shi ba. Yayinda gefe na zuciyar tata ke jin haushin wa
ɗ
an nan jami'ai da ke son yin amfani da damar da ALLAH ya
basu ta hanyar amfani da ita. Wani gefen kuma na haske mata ahalinta cikin bala'i mai muni da idan har ta zama sanadin shigarsu cikinsa har gaban abada bazata ta
ɓ
a yafema kanta ba. A take wani irin kangarewa da bushewar zuciya suka saukar mata. Batare da y
in wani dogon nazari ba wautar ƙuruciya ta fisgeta da zuciya wajen
ɗ
aukar pen ta hau cike takardun da
ɓ
arin jiki, batare data duba mi suka ƙunsa ba..
Fusatar tata ta basu matuƙar mamaki da al'ajabi. Sai dai zukatansu na ayyana musu tanayin komai ne
domin ahalinta. Dan fahimtar sune rauninta ya sakasu yin amfani da su wajen tursasata. Aiko sunci nasara, dan ta cike takardun kamar yanda suka buƙata. Ta kuma saka hannu bisa takardar contract
ɗ
in zatai musu aikin sirri har sai sun kama Master. Su kuma b
azasu saki wancan bayanan ƙaryar da suka shirya ba domin mata
ɗ
aurin talala saboda ƙarancin shekarunta.
Sun mata bayanai sosai da zata iya fahimta. Tare da bata date
ɗ
in da zata fara amsar horo na musamman a
ɓ
oye. Da ga ƙarshe sukai mata dogon ga
rga
ɗ
i akan riƙe dukkan abinda suka tattauna matsayin sirri. Dan inhar ta fitar tamkar ta bayyana ƴan uwanta ma duniya ne matsayin ƴan ta'adda. Daga haka suka sallameta.
Fitowar Hibbah da aka ha
ɗ
a da jami'ai biyu zasu mata rakkiya zuwa gida yay
i dai-dai da isowar Yaya Abubakar da Yaya Muhammad station
ɗ
in. Tana ƙyalla ido a kansu ta kwasa da gudu garesu. Jikin Yaya Abubakar dake gaba ta fa
ɗ
a tare da fashewa da kuka.
Shima rungumeta yay yana mai rintse idanunsa da suka ka
ɗ
a sukai jajur.
Yaya Muhammad ya ƙaraso garesu da sassarfa